SHIN SU KENAN MATSALOLIN MU?


SHIN SOYAYYA DA ZAMANTAKEWAR AURE DA SIYASA DA KACE-NA-CE TSAKANIN MALAMAI DA DALIBAI AKAN MAS'ALOLI SHINE DAMUWAR WANNAN AL'UMMAR ???
.
A'A wadannan ba sune asalin damuwar wannan al'ummar ba, damuwar wannan al'ummar shine RASHIN TSAYUWA AKAN BAUTAR ALLAH DA GASKIYA !!!
.
Mafi yawan Malamai da daliban ilimi da marubuta addini da rayuwa sun fi karkata wajen wa'azi da kira da rubuce-rubuce akan abubuwan da suka shafi SOYAYYA DA ZAMANTAKEWAR AURE DA SIYASA DA KACE-NA-CE TSAKANIN MALAMAI DA DALIBAI AKAN MAS'ALOLI. cikin kashi 100%, 80% Na wa'azozi, Nasiha rubuce-rubucen addini da rayuwa suna ta'allaqa ne akan abunda na lissafo. 20% ne wasu daga ciki suke bada himma wajen ganin an gyara BAUTAR ALLAH (SWT)
.
A hakikannin gaskiya matukar ba a gyara BAUTAR ALLAH ba to babu wani abu da zai tafi daidai yadda ake bukata. Kullum cikin kawo salon yadda za'ayi soyayya da zamantakewar aure ake yi amma kuma kullum cikin saki mutuwar aure ake babu abunda ya chanja face ma abunda yayi gaba. Amma duk da haka an dage da wadannan bangarorin wanda kuma matukar ba a gyara tushe ba babu yadda za'ayi a samu sa'idah.
.
Ana matukar wujijjiga bautar ALLAH ana aikata shi son rai ba tare da an cika sharuda ba.
.
→ Akwai dubban mutanen da basu san tsarki da hukunce-hukuncensa ba kuma wai suna bautawa ALLAH, bayan ALLAH yace baya karban aiki sai mai tsarki.
.
→ Akwai dubban mutanen da basu iya karatun Fatiha (Ummul-kitab) kuma suna yin Sallah, bayan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya tabbatar mana da cewa babu Sallah ga wanda yayi sallah ba tare da karatun Fatiha ba.
.
→ Akwai dubban mutanen da suke yin Sallah cikin 2-3 minutes sun idar, ba wani abu suke yi ba face kawai dungurawa suna yin Sallah ne kawai don sunga mutane suna yi. Shin ina zikirorin cikin sallah ???
.
→ Akwai dubban mutanen da sun iya komai na sallah amma ba zasu yi ta akan lokaci ba, sai su hada Azahar da La'asar, Magrib da isha ba shigan lokaci.
.
→ Akwai dubban mutanen da suke cewa Sallah suna da aiki amma kuma basa iya cewa AIKI suna da Sallah !!!
.
→ Akwai dubban mutanen da Suna amsa kiran waya da zarar ankira su, amma kuma basa iya amsa kiran ALLAH a lokacin da ya kira su.
.
Shin ba a kyautata bautar ALLAH ba ta ya za'ayi sauran al'amura su tafi yadda ake so ??? A hakikannin gaskiya dole sai an jajirce an gyara matsololin game da bautawa ALLAH sannan abubuwa su ringa tafiya daidai.
.
Akwai Malamai da daliban ilimi da marubuta addini da rayuwa suna wa'azi suna nasiha suna kira suna tunatarwa suna koyarwa suna rubutawa da yadda za'ayi a Bautawa ALLAH, amma inda matsalar take ba a mai da hankali akai, hatta masu copys da Sharings din rubuce-rubuce sunfi duba ga abunda ya shafi soyayya da zamantakewar aure, Siyasa, kace-nace-nace akan mas'aloli wanda ba a tsaya aka magance tushe ba an tafi zuwa ga mas'alolin da wasu ma ba wajibi bane an bar muhimman abubuwa wanda suke wajibai ga ibadar mutum wasu ma basu karanta littafan kasa-kasa ba irinsu Akhdari, Ashmawy, Risala, Iziyyah, Qawa'idi da dai sauran littafai da dama da suke koyar da ibadah da hukunce-hukuncensa.
.
Da wannan nake kira ga Malamai da Daliban ilimi da Marubuta Addini da Rayuwa da masu copys da Sharings da a fifita bangaren IBADAH (Bautar ALLAH) sama da ko wace mas'ala ayi kokarin ganin al'ummah sun fa'idantu da yadda zasu bautawa ALLAH cikakkiyar bauta.
.
Su kuwa Al'ummah kowa yayi kokarin ganin yasan ilimin yadda zai bautawa Ubangijinsa domin bautar ALLAH ita ce farkon abunda za'a fara yiwa mutum hisabi dashi a ranar Alqiyama, sannan duk ilimin da zai koya ya biyo bayan wannan.
.
Matukar bamu gyara tsakanin mu da ALLAH ba to ba zamu taba cimma wani buri na rayuwa ba.
.
ALLAH Yasa mu dace (Ameen)

Rubutawa Faridah Bintu Salis ( bintus~sunnah)

*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura 

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*
WhatsApp

Ga masu sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsapp sai a turo da CIKAKKEN SUNA Zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsapp.
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive