UWAR GULMA

*UWARGULMA*
Wasu matan aure ne su 3 suka je rafi dibar ruwa, a hanyarsu ta
dawowa gida, sai suka shiga
hirar duniya, suna fadawa juna
matsalolinsu da laifukansu.
Ta farko ta ce:
Ni laifina shi ne, kullum idan mijina baya nan, sai na satar masa kudi,💵 idan ya dawo yana cigiya, sai na ce 'yan uwansa ne suka shiga dakin, da haka da haka duk na hada shi da 'yan uwansa👩‍👩‍👧‍👧. _Na san ko idan ya gano gaskiya an banu,😂 don Allah ku taya ni addu'a_🙏🏻.
Ta biyun ta ce:
To ai ke wannan qaramin laifi ne😳, ni 'ya'ya goma na haifa a gidan
mijina, amma duka ba nasa ba ne; duk na rariya ne (shegu ne). Na san duk ranar da ya gane hakan na shiga 9 🙀, "ni ma ku taya ni addua🙏🏻 .
Ta ukun sai hawaye suka riqa zubowa
daga idanuwanta, da kawayenta biyun suka tambayeta, me take yi wa kuka? Sai ta ce "ni laifina daya ne👆🏻... _ta ci gaba da kuka_😫, da kyar suka rarrasheta ta yi shiru, suka qara tambayarta, sai ta ce 👉🏻 *mutum 50* ke *gidan yari*🏣 a dalilina, ga shi ina bakin cikin rabuwa daku😡 don ba shakka zaku shiga sahun wadancan 50 din, don bana iya barin magana a cikina😷, yanzu hirar nan da mukai daku, har na qagara in je gari in ci gaba da yadawa mutane,😜 _"ku taya ni addu'a"_
*MENE NE MAFITA??*😳😳😳 *Mata kenan* 😜😜😜....
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive