GASKIYA DOKIN ƘARFE

    💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     DARUSSAN RAYUWA


  ࿐​ ​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION࿐​

༄༄ PWA ༄༄

 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖
                ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ     
            ɮʏ✍🏻:
👉🏻© ɧãımãŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                    Fitowa ta 05 
   
     GASKIYA DOKIN ƘARFE 

Shekaru aru-aru da suka gabata, mutanen birnin Sin suna da wata al'ada, al'adar ita ce: Kafin a naɗa yarima ya zama Sarki sai ya fara yin aure tukunna. To a irin wancan lokaci ne aka samu wani Yarima wanda yake gab da hawa karagar mulki, don haka yana buƙatar matar da zai aura. Saboda haka sai ya gayyaci dukkan 'yan matan dake birnin domin su zo ya zaɓa wacce zai aura. 

To akwai wata tsohuwar baiwa a gidan sarautar wacce take da wata 'ya kyakyawar gaske, ita kuma wannan budurwa ta daɗe tana ƙaunar wannan ɗan sarki, babu yadda ta iya ne yasa dole ta haƙura. Yayinda tsohuwa taji wannan shela da ɗan sarki yasa a yi, sai taje gida ta sanarwa da wannan 'ya tata. Ita kuwa yarinya ko da taji haka, sai tace itama zata je fada a ranar da ake son ganin sauran 'yan matan garin, wannan hukunci da ɗiyarta ta yanke yasa wannan tsohuwa ta shiga cikin matsananciyar damuwa. 

Sai ta kada baki tace da ita: "To in kin je fada me zakiyi? Kin san fa kyawawan mata 'ya'yan manya ne zasu je wannan wuri, ke to me zai kaiki? Sai yarinya ta buɗi baki tace: "Mama na san cewa ba zai zaɓe ni ba, amma wannan ita ce dama ta Ƙarshe a gareni da zan iya kasancewa tare da shi, kuma hakan zai saka ni farinciki sosai". 

Kashegari kuwa da wannan budurwa taje fada sai ta iske kyawawan 'yan mata 'ya' yan attajirai da masu mulki sun cika fadar maƙil. Kowacce daga cikin su ta saka kayan da tafi so na ƙarshen akwati, kuma taci ado na gaske. Kowa burinta yarima ya zaɓe ta. Bayan ya musu jawabin maraba, Yarima da kansa sai ya ƙalubalanci waɗannan 'yan mata da cewa: "Zan baiwa kowaccen ku irin fure taje ta shuka, bayan wata shida duk wacce furenta yafi na kowa kyau, to ita zan aura". Daga nan sai ya gabatar musu da irin fure da yawa yace kowacce ta zaɓa wanda take so. 

Duk 'yan matan nan kowacce sai ta zaɓi iri ta wuce, ita ma 'yar tsohuwar baiwar nan sai ta zaɓa ta tafi gida. Da taje gida kuwa ta shuka wannan iri tayi ta kula da shi da zuciya ɗaya, domin tayi imani cewa in dai har son da take yiwa yarima na gaskiya ne, to wannan fure zai yi girma sosai. Bayan wata uku sai yarinya fa ta lura furenta ko tsirowa bai yi ba, daga nan sai ta dinga bibiyar manoma tana neman Shawarwari amma duk sai wannan ƙoƙari nata ya tashi a banza domin kuwa fure dai ko tsirowa bai yi ba. Yayin da darare ke wucewa, ita kuma burinta na son ganin ta auri yarima ne yake ƙara gujewa daga gareta. 

A haka dai har watanni shida suka cika cif ba tare da wannan fure ya tsiro ba. Duk da cewa ta san bata da furen da zata kaiwa yarima, amma hakan bai hana wannan yarinya ɗaukar tukunyar da ta shuka wannan iri zuwa fada ba. Yayinda ta isa fada a ranar da aka ce kowa yazo da nashi, sai ta taras da sauran nasu sun zama manyan fure masu kyau da ban sha'awa, ita kaɗai ce nata bai tsiro ba ma balle yayi girma. 

Daga nan sai yarima ya fito ya duba dukkan furen da 'yan matan suka kawo, nan take ya zaɓi na wannan yarinya 'yar gidan tsohuwa a matsayin matar da zai aura. Duk sauran 'yan matan sai suka kama ƙorafi akan cewa me yasa zai zaɓe ta alhalin nasu ya dama nata ya shanye ita kuwa nata ko tsirowa bai yi ba? Anan sai yarima ya basu haƙuri tare da cewa su saurara zai yi musu bayani. Bayan sun natsu sai yace: "Wannan yarinya da kuke gani ita kaɗai ce ta samar da furen da ya cancanta ace ta zama matar Sarkin gobe, ita ce kaɗai ta shuka furen gaskiya. Saboda dukkan irin da na baku an riga an lalata su ta yadda ba zasu taɓa iya tsirowa ba, Yayinda duk sauran suka canja nasu domin su burge ni, ita kaɗai ce ta kawo min abinda yake shi ne daidai, gaskiya da gaskiya kenan, don haka ita zan aura". Daga nan sai sauran 'yan matan suka koma gida suna masu jin haushin kawunan su. 

DARASIN LABARIN: Bai kamata mu kasance cikin jin haushi ko damuwa ba yayin da muka ga abubuwa suna tafiya ba yadda muka yi tsammani ba, mu dai mu kasance masu tsare gaskiya bakin gwargwadon mu a dukkan lamura zamu ga ci gaba. Domin Hausawa na cew GASKIYA DOKIN ƘARFE! 


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive

Recent Posts

Unordered List

  • Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit.
  • Aliquam tincidunt mauris eu risus.
  • Vestibulum auctor dapibus neque.

Sample Text

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipisicing elit, sed do eiusmod tempor incididunt ut labore et dolore magna aliqua.

Ut enim ad minim veniam, quis nostrud exercitation test link ullamco laboris nisi ut aliquip ex ea commodo consequat.

Pages

Theme Support

Need our help to upload or customize this blogger template? Contact me with details about the theme customization you need.