YARO MAI ƘARFIN IMANI

    💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     DARUSSAN RAYUWA


  ࿐​ ​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION࿐​

༄༄ PWA ༄༄

 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖
                ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ     
            ɮʏ✍🏻:
👉🏻© ɧãımãŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                    Fitowa ta 03 
   
     YARO MAI ƘARFIN IMANIShaykh Fath al-Mowsily Ya ruwaito cewa; Watarana na haɗu da wani yaro yana tafiya shi kaɗai a cikin daji. Da Alamu yana tafiya yana magana ne shi kaɗai. Sai nayi mishi Sallama shi ma kuma ya amsa min kamar yadda ya kamata. Sai na tambaye shi da cewa "Ina zaka ne haka samari?' sai ya bani amsa da Cewa; 'zan je ɗakin Allaah ne (Makkah)'. Sai na sake tambayar sa da cewa; 'To me kake faɗa ne? Sai ya ce min QUR'AN nake karantawa. Sai na ce mishi, “Ai kai yaro ne ba lallai bane akan ka sai kayi karatun QUR'AN a koda yaushe' 

Sai yace dani, “na ga mutuwa ta ɗauki mutanen da basu kai ni yawan shekaru ba, saboda haka ne nake mata tanaji domin tana iya zuwa ta ƙwanƙwasa min ƙofa a kowane lokaci'. Da Mamaki a fuskata sai na ƙara ce masa, gashi takun ka ƙarami ne kuma inda zaka yana da nisa, sai yace dani "Aikina shi ne inyi takun (tafiya) amma samun damar kaiwa inda Zani wannan hukuncin Allaah ne'. Sai na sake tambayar sa da cewa, 'To ina Kayan tafiyar ka Kuma ina Abin hawan ka?' sai ya bani amsa da cewa; 'Imani na shi ne kayan tafiya ta ƙafata ita ce abin hawa na". Sai nace mishi ina nufin gurasa ne da ruwa",

Sai ya bani amsa da tambaya yana mai cewa; “ya kai wannan shehi, shin idan mutum ya gayyace ka gidansa kana ganin ya dace ka tafi da abincin ka zuwa wannan gida? Sai na bashi amsa da a'a, sai ya ci gaba da cewa; "to nima haka, Ubangijina ya Gayyaci Bawan Sa izuwa Ɗakin Sa, ƙarancin Imani ne kawai ke sa mu ɗebi guzuri. Duk da haka kana Tunanin ubangiji na Zai barni na tagayyara ne? 

 “Har abada Ba Zai bari ba” na bashi amsa. Daga nan sai ya tafi. Watarana sai muka haɗu da shi a garin Makkah, sai ya gabato gare ni yace dani; "Ya shaikh shin har yanzu kana da raunin imani? 

Na Tsakuro wannan labari ne daga cikin Littafin Stories of the Pious Na Shaikh Ahmad Ali

Haƙiƙa wannan labari darasi ne babba amma ga masu hankali da tunani. Allaah Ya Azurta Mu da kyakkyawar fahimta Aameen. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive

Recent Posts

Unordered List

  • Lorem ipsum dolor sit amet, consectetuer adipiscing elit.
  • Aliquam tincidunt mauris eu risus.
  • Vestibulum auctor dapibus neque.

Sample Text

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipisicing elit, sed do eiusmod tempor incididunt ut labore et dolore magna aliqua.

Ut enim ad minim veniam, quis nostrud exercitation test link ullamco laboris nisi ut aliquip ex ea commodo consequat.

Pages

Theme Support

Need our help to upload or customize this blogger template? Contact me with details about the theme customization you need.