Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

I'M SORRY


I'm Sorry

I'm Saying Sorry First 
I'm Saying Sorry Last
I'm Saying Sorry For The Future 
But Mainly For The Past

I'm Sorry That I Hurt You
I'm Sorry That I Care
I'm Sorry That I Want To
No Matter What Be There.

I'm Sorry That You Hate Me
I'm Sorry That I Lied
I'm Sorry That You Now See
How Much That I Have Cried.

I'm Sorry I'm Not Good Enough, 
I'm Sorry I Let You Down, 
I'm Sorry For your Tears, 
And I'm Sorry For My Fears.

I'M Sorry For Being Hardheaded
I'm Sorry For Never Listening
I'M Sorry That I'm jealous 
I'm Trying Very Hard To Change It.

I'm Sorry That I Wasn'T There For You
And I'm Sorry For Not Listening
When You Needed It The Most
You Were Right And You Had The Right To Be Mad

I'm Sorry That You Felt The Need To Apologize
And I'm Sorry That You Were Hurt
I'm Sorry That I Can Only See The Good
And Always Try To Avoid The Bad

I'm Saying Sorry For All My Mistakes
I'm Saying Sorry For Being Blinded
Blinded By The Perfect Thought Of You And Me
When Really We Dont Have A Chance

I'm Sorry For Being Protective, 
And I'm Sorry For Being Cautious.
I'm Sorry For Forgetting Things, And Asking Stupid Questions.

I'm The Stupid One
I Let You Down And I Feel It Deep Within Me
We Both Made Some Errors 
And Said Something Wrong 
But That's How Life Is

I'm Sorry For Not Being Perfect, 
I'm Sorry That I'm a Disappointment, 
I'm Sorry I'm Not Always Honest

Nobody's Perfect 
Not Even Me And You 
So I'm Sorry For That Too
And I'm Sorry For Everything But ...

Please Forgive Me 
We Can Change Things Back To Normal
I'm Sorry If This Is Not What You Want
But Its The Only Thing I Can Think Of."

I Want To Make You Love Me
Like You Did Once Before
I Want To Make Your Heart See
What Mine Is Living For.•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------

    +23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Facebook
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹───── ─m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76• 


Share:

RANI


        RANI

Sallama a Gareku abokaina
Ina yini ya aiki da rana?
Ya iyaye, yayyi da ƙannena?
Ni dai makafci ne in kun tuna
Na iya sarrafa kalmomi da magana
Ina canja salo kamar riguna
Yau ma nishaɗi nake yi da Murna
Domin a karon farko a ruhina
Zan bayyana zancen da ke raina
A ƙarƙashin so kuma ra'ayina
Ina fatan zaku ji idan kun zauna
In yaso daga baya ma tattauna. 

Na daɗe da shiga bege tsawon ƙarni
Na zamo sahoro a cikin ƙarni
So kawai nake yi ba Damina bare rani
Gashi babu alamun nasara a gare ni
Amma hakan bai sa na yi gurnani
Ba balle ma in yi gunguni 
Farko dai muryarta ce ta jawo ni
Idanuwanta kuma suka ƙamar da ni
Murmushinta shi ne ya sumar da ni
Iya kafcenta kuma ya sace ni
Ban gajiya da kallonta tsawon yini
Idanuwana kan ƙame a kanta kamar gini.

Maganar gaskiya tana da farin jini
Ban damu ba ko da za ta ƙi ni
Ni dai kumatunta suna burge ni
Shigarta a kullum tana ɗasa ni
Na sha mafarkin gashi ta aure ni
Na yarda in aure ta ko zata dinga zane ni
Kamar yadda ta yi wa wasu a mardaani
A wasu lakuta na kan yi ta tunani
Yadda za'a yi in cire son da yayi rauni
A zuciya kuma gashi babu magani
Seriously I gotta say that I love Rani
Kuma ban damu ba ko da zata raina ni.

A sanda naji ance ta yi aure
Haka na sulale a jikin ƙyaure
Fatata tayi kaushi kamar ɓaure
Ji nake kawai tawa ta ƙare
Kamar wata kazar da aka banƙare
Na kasa yin zuciya kamar kare
Na kasa tashi ma balle in ware
Sai na koma gefe na takure
Tunanuka a ƙwaƙwalwa suka kaure
Damuwa ta sa na koma kamar zare
Idan na tuna gashin kanta kamar fure
Sai in ji na gaji da kwanan zaure

A rayuwar kafce irin ta sinima
Tun daga yara har sahun su Mama
Kogin sonta kaɗai na ƙunduma
Wuƙar sonta a zuciyata ta luma
Hakan yasa hasken idanunta nake nema
•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------

    +23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Facebook
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹───── ─m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76• 
Share:

KADDYWOOD: A POEM

KADDYWOOD

In the mist of the seductive world of cinema
Comes a sparkling light with rays of hope
A light of hope so strong that it pulled me out of my dilemma
And giveth me the vital courage that I needed in order to cope
With the ever challenging difficulties of cinema.

Today, we are Kaddywood
But tomorrow is yet to be seen
We may not be as big as Hollywood
But strong is what we have been
Do not compare us with Bollywood
Not yet, for it remain to be seen.

But let me assure you of something
We're already in comparison with Nollywood 
Do not doubt us on anything
We're beyond Kannywood
And even without doing anything
We're on our way to dethrone Lollywood 

Who knows what we will be tomorrow?
That, too, remain to be seen
And if you're a fan of Tollywood
Or even, for that matter of Mollywood
Then, get ready for Kaddywood
For we can give you joy better than Pollywood.

We've determined to make it far,
The sky is going to be the beginning
So that even from afar,
You will see our light shining
For, we can say, so far
We're actually spinning.

For God bless our hearts with courage
Our brains storms with knowledge
Our souls are filled with love
Our essence was cleansed from all hatred
And We're tied to success like magnet
And, by the will of the lord, we will be the proud of our Continent


Haiman Raees 🌹 


Share:

LUGUDEN LUGWIGWITA AGWALUMA

LUGUDEN LUGWIGWITA AGWALUMA

A kwanaki kaɗan da suka gabata ne dai masu ruwa da tsaki na wani sabon shirin Masana'antar bulbula soyayya gami da sambaɗe-Sambaɗe ta birnin in-da-yaya mai suna Talala-da-biye-biye suka saki hoton farko na wannan shi wanda yake ɗauke da hoton shahararriyar masifaffiyar jarumar nan watau Kan-gwangwani. A hoton farkon dai da aka fitar an nuno jarumar ta canja siffarta gaba ɗaya daga sanda zuwa AGWALUMA. 

Sai dai a maimakon a yaba wa jarumar a matakin farko dangane da irin wannan ƙoƙari nata, sai ga shi mutane daga ko'ina suna ta yi mata luguden laƙumar agwaluma gami da latse-latsen lemo. Babu irin tofin ala-tsinen da bata sha ba. Sai dai wani rahoto da ke yawo ya bayyana cewa mafi yawancin masu suka da caccakar yanayin da jarumar za ta fito a cikin shirin wai masoya Jarumi hantaru ne. Jummai gantali dai da Hantaru kusan shekaru uku kenan suka ɗauka suna bata kashi da cece-kuce. 

Mu dai anan sai dai mu ce Allaah shi sauƙaƙa. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

FASSARAR WAƘAR SAWARE

Fassarar Waƙar Saware

Sunan Waƙa: Saware

Sunan Shiri: Phantom

Shekarar Fita: 2015 

Sauti: Pritam

Rubutawa: Amitabh Bhattacharya

Kamfani: T-Series

Rerawa: Arijit Singh

Fassarawa: Haiman Raees 🌹 

MATASHIYA: kalmar Saware ko Saanware a haƙiƙaninta tana nuni ne zuwa ga mutum mai ɗan duhun fata. Kamar ace baƙi-baƙi kenan. Sannan ana amfani da wannan kalma wajen kiran sunan ubangiji Krishna wanda ya kasance ɗaya daga cikin ababen bautar Hindu saboda ya kasance yana da duhun fata. Amma idan ka ji marubuta Waƙa ko na rerawa ko kuma na zube sun yi amfani da kalmar, to a mafi yawancin lokutta suna magana ne akan masoyi, abin ƙauna, masoyiya, ko kuma abar ƙauna. Wannan kuma ya samo asali ne duba da irin yadda suka amintu cewa Krishna abin so ne ga kowa. 

* Pehle Kyun Na Mile Hum, Tanha Hi Kyun Jale Hum
  
Me yasa ba mu haɗu da wuri ba? Me yasa zukatanmu ke gasuwa da kaɗaici? 

* Milke Muqammal Hue Hain, Ya They Tanha Bhale Hum

Shin mun haɗu ne domin zama cikakku ko kuma dai gara mu kasance cikin kaɗaici? 

* Saware... (x3)

Ya abar ƙauna 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara ya ke Muguwar Masoyiya 

* Pal Pal Ginke Guzara Maano Karza Utaara

Na kansace mai tafiyar da lokuta na ina mai ƙirga kamar ina rage bashin da ke kaina 
  
* Tum Se Munaasib Hua Hai Phir Se Jeena Humaara

A dalilin ki, na samu dalilin yin rayuwa 

* Saware... (x3)

Ya abar ƙauna

Hmm…

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara ya ke Muguwar Masoyiya 

* Dhalti Raat Ka Ik Musaafir Subah Alvida Keh Chala

Matafiyin dare yayi bankwana da sanyin safiya 

* Jeete Jeete Raah Ho Saka Na Marke Haq Ada Kar Chala

A lokacin da yake raye, ya gaza zama hanyar da mutane za su bi, amma yayin mutuwarsa, aikin ya kammala 

O...

* Na Humaara Hua Na Tumhara Hua

Da abinda na yi fata har abinda kika yi fata babu wanda ya faru 

* Ishq Ka Yeh Sitam Na Gawaara Hua

Soyayyar mu ta gaza kaiwa zuwa ga bigirenta 

* Sun Bairiya Saware… (x2)

Ki Saurara ya ke Muguwar Masoyiya 


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 

Share:

FASSARAR WAƘAR SHIVSHANKARFASSARAR WAƘAR JAI JAI SHIVSHANKAR 

Sunan Waƙa: Jai Jai Shivshankar

Sunan Shiri: War

 Shekarar Fita: 2019

Sauti: Vishal & Shekhar

Rubutawa: Kumaar

Kamfani: YRF

Rerawa: Vishal Dadlani, Benny Dayal

Fassarawa: Haiman Raees 

Dhoom Takit Tik Takit Tik Dhin...
Dhoom Ta Ta Ta Dhin Ta Ta...

* Toh Aaj Yaar, Ghar Pe Yeh Bol Do

A yau abokai, kowa ya sanar a gidansu 

* Aayenge Der Se, Fiqre Sab Chhod Do

Cewa za ku dawo a makare kuma kada kowa ya damu 

* Aaj Haq Se, Apne Hisaab Mein

Tare da cikakken iko, a ƙashin kanku 

* Hum Jo Karne Chale, Galti Wo Jod Lo

Ku rubuta shaiɗancin da zamu aikata 

* Toh Aaj Yaar, Kuch Lamho Ke Liye

A yau abokai, na ɗan wasu lokuta 

* Bigdi Raahon Pe, Tum Pairon Ko Mod Do

Ku canja akalar ku zuwa ga sangartacciyar hanya

* Aaj Haq Se, Duniya Ko Bhool Ke

Tare da cikakken iko, ku manta da duniya 

* Jitne Hain Qaayde, Woh Saare Tod Do

Ku karya dokoki duka 

* Ho Khulle Ground Mein Aake, Ooncha Sound Baja Ke

Za mu je wani katafaren fili mu saki sauti da ƙarfi 

* Red Wala Color Laga Ke, Nachenge Hero Ban Kar

Bayan mun shafa jan kala za mu yi rawa kamar Jarumai 

* Ho Jai Jai Shiv Shankar

Jinjina ga ubangiji Shiva/Shankar!

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

* Hum Aaye Bann Than Kar

Mun fito a shirye 

* Ke Mood Hai Bhayankar

Domin muna cikin yanayi mai ban mamaki 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

* Ho Jai Jai Shiv Shankar

Jinjina ga ubangiji Shiva/Shankar!

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

Takit Tik Takit Tik Dhin...

* Dhun Ke, Geele Geele Sur Sun Ke

Yayin sauraron daddaɗan sautin 

* Baari Baari Yahaan Jam Ke

Ɗaya bayan ɗaya cikin dagewa 

* Aaja Desi Kamar Pe Thumke Uchaal De

Kawai mu girgiza kwankwasanmu 

* Ho Saare, Sharmaana Aaj Chhad Ke

Kowa da kowa, ku manta da kunyar ku 

* Zara Zara Nasha Kar Ke

Ku shaƙar da kanku ko da kaɗan ne 
 
* Jitni Bhi Hai Sharam Dil Se Nikal Dein

Kuma ku kawar da duk wani shamaki daga zukatanku 

* Apni Hi Sharton Pe Nachna

Za mu yi rawa ne bisa ƙa'idar mu 

* Aaj Rangon Se Koi Nahi Bachna

Yau dai kam babu wanda zai tsira daga kaloli 

* Subah Tak Ab Nahi Thakna Re Ho...

Babu wanda zai gaji sai gari ya waye 

* Ho Do Do Round Laga Ke, Sau Sau Pound Uda Ke

(mu) ɗan sha ko zagaye biyu ne, mu watsa kuɗaɗe sama 

* Koi Vilayati Bhaang Chadha Ke, Nachenge Hero Ban Kar

(muna) shan baƙin kayan maye, muna cashewa kamar Jarumai 

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

* Hum Aaye Bann Than Kar

Mun fito a shirye 

* Ke Mood Hai Bhayankar

Domin muna cikin yanayi mai ban mamaki 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

* Ho Jai Jai Shiv Shankar

Jinjina ga ubangiji Shiva/Shankar!

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

* Jai Jai Shiv... Jai Jai Shiv... Jai Jai Shiv...

Jinjina ga ubangiji Shiva! 

* Jai Jai Shiv Shankar

Jinjina ga ubangiji Shiva!

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau 

* Jai Jai Shiv Shankar

Jinjina ga ubangiji Shiva!

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau

* Jai Jai Shiv... Jai Jai Shiv... Jai Jai Shiv...

Jinjina ga ubangiji Shiva! 

* Jai Jai Shiv Shankar

Jinjina ga ubangiji Shiva/Shankar!

* Aaj Mood Hai Bhayankar

Ina cikin yanayi mai daɗi yau 

* Rang Udne Do, Hey! Hey! (x2)

Bari kaloli su fantsama ko'ina 

* Jai Jai Shiv... Jai Jai Shiv... Jai Jai Shiv...

Jinjina ga ubangiji Shiva!

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Share:

CINIKI DA KASUWANCI A SHARI'A 04


CINIKI DA ABINDA YAYI KAMA DA CINIKI/KASUWANCI AH SHARI'AN CE. 

      Fitowa Na (004) 

Ci Gaba Da Bayani Daga Inda Muka Tsaya: Ko Sayar da Abu akan Cewa Babu Wani Lokaci Takamaimai Na Karban Kudin, Shi Ma Bai Halatta Ba, Boye aibin abin Sayarwa bai Halatta ba, shine Yin Algushu, Wato a Hada mai Kyau da Kuma Mara Kyau Bai Halatta ba, Manzon Allah Saww, Yana Cewa Duk Mai Yin Algushu Toh Baya Cikin Mu Inji Manzon Allah, Saboda Kayan Ki Kinada Mai Kyau Da Mara Kyau Bai Halatta ki Hada Su Waje Guda Domin Ki Siyarwa Wani ba da Sunan ai Dukkan Su masu Kyau Ne, Alhalin Sai An je an Bude ah Ga illar Su, Annabi Yace Duk Mai Yin Haka Baya Cikin Mu Inji Manzon Allah, 
       (RUDI) bai Halatta a Ciniki ba, Wato a Ziga abin Sayarwa Fiye da Matsayin Sa, ke kina sai da Kaya, amma kin cika kayan da Zakin baki, duk wannan bai Halatta ba, idan ma zakiyi Zakin Baki Ki Zoga Kayan ki, to Wani ne yakamata ya Zuga miki Wannan Kayan Yabi Kayan ya Cika Shi Da Zakin Baki amma ba ke ba, ko ke zaki yi haka, amma bara kiyi shi yadda ya wuce gona da iri ba, Yaudara ba ta Halatta ba a Cikin Ciniki, 
          Haka nan 'boye aibobin Haja Duk Bai Halatta ba, Ke Kin San Da Cewa Kayan da Zaki Siyar nan akwai amma sai ki boye ma mai Siya kika Nuna ai yanada Kyau Sosai, Sanda Ya Siya ya Samu ai abin bai da kyau kin Cuce Shi, Hakan Bai Halatta ba,
       Hada mai Kyau da Kuma Mara Kyau Bai Halatta ba, Bai Halatta ba Mutum Ya Boye abinda ya san Cewa Lallai idan ya Bayyanawa mai Saye Zai Ji Ba Ya So Ko Kuma Zai Sa Ya Rage Masa Fasashi, ke Kinsan Da Cewa Wannan Zanin Naki ko Kayan Naki akwai illa, Kada Ki Bayyana illar shi mai Siya yace Fasa, ko Kuma Ya Rage Miki, Farashin Shi, Sai Kika Siyar da Shi ah haka, Duk Wannan Bai Halatta Ba, 

Wanda Ya Sayi Bawa Ya Sami Aibi a Tare Dashi, Toh Yana da Damar Ya Rike Shi a Haka, amma Babu Wani abu da Za'a Ba Shi, Ko Kuna Ya Mayarwa da Mai Shi Ya Karbi Kudin Sa, Sai Dai idan wani Aibin Daban Wanda Shi Ma bata Cinikin Ya Faru ga Bawan a Hannunsa ba, 
     To Sai Ya Karbi Gwargwadon Kudin da Aibin Farko ya Rage Daga Hannun Mai Shi, ko Kuma Ya Mayarwa da Mai Shi Ya Karbi Kudin Sa, Sannan Shi Kuma Ya Dawo da Kudin aibin da ya Faru a Hannun Sa ya Rage. Idan Mutum Ya Dawo da Bawa Bayan Ya Saya Saboda Wani aibu amma ya Riga Ya Saya Yayi Amfani da Shi, to Wannan Amfanin da Yayi da Shi Halas Ne______________

Ku Biyomu Ah Fitowa Na Gaba In Allah Yakaimu Lafiya. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Za Ki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.
Share:

CINIKI DA KASUWANCI A SHARI'A 03

CINIKI DA ABINDA YAYI KAMA DA CINIKI/KASUWANCI AH SHARI'AN CE. 
    
          Fitowa Na (003) 

Ci Gaba Bayani Daga Inda Muka Tsaya; Duk abinda Ya Haihu Daga Naman Dabbobi Masu Nau'i Guda, Kamar Kitse, toh Kamar Hukuncin Naman Sa Ne, Nonon Su Nau'i Guda Ne da Kitsen Su da kakidensu Duk Nau'i Guda ne, 
          Wanda Ya Sayi Kayan Abinci Bai Halatta Gare Shi Ya Sayar Da Shi Ba Tun Kafin Ya Gama Karbarsa Ya Shigo Hannun Sa, Wato Kamar Misali Mutum Ya Saya Wani Kayan Abinci, amma Tun Kafin ah Ba Shi Wannan Abincin da Ya Siya Har Ya sa Abincin a Kasuwa zai Siyar Da Shi, ko Kuma Ya Siyar Yana Jira ne kawai ba Shi ya kaiwa wanda ya siyarwa, Hakan Bai Halatta ba. Idan ya Saye Ne Ta Hanyar Aunawa Awo ne Nau'in ko Na Ruwa, amma Ban da (KASHI) 
          Haka Nan Hukunci duk Wani Kayan Abinci ko Kayan Miya ko Abin Sha, Sai dai Ruwa Kadai. Amma abin da Ya Shafi Kayan Magunguna ko Na Shuke-shuken da Ba'a matso mai daga cikin su ba, to Dukkanin Su, Hukuncin Haramcin Sayar da Su Kafin a Gama Karba bai Shafe Su Ba, 

Haka Nan Hukuncin Samun Fifiko a Nau'i Guda a wajen Musayar Su, Babu Laifi a Sayar da Kayan Abincin da aka Saya Bashi tun Lafin a Gama Karbar Sa, 
           Haka Nan Babu Laifi ayi Tarayya a Cikin Sa, Babu Laifi ayi Tauliya(wato a Sayar Wa da Wani Kaya Kamar Yadda aka Saye Shi) Kin Saya (3000) Babu Laifi kema ki Sayar Da shi ah Kamar Yadda kika Siyo Shi, Haka Nan Babu Laifi ayi ikala, (Wato a Canja abinda aka kulla Cinikin a Kansa, Kamar Misali Wannan Bai Yi Miki, Kuma Gashi Har Kun Gama Cinikin Sa, to Babu Laifi idan Bai Miki Ba Ki Ce ah Canja Shi Zuwa Wanda Ya Miki Sai Ku Yi Ciniki a kansa,
           Duk Wadannan Abubuwan Guda 3 da aka yi Bayani akai, Babu Laifi a Cikin Kayan Abinci aunanne da aka Saya tun Kafin a Gama Karbar Sa, duk wani Ciniki ko Kwadago ko Haya da aka kulla Shi a bisa Kasada ko Gagari Dangane da Kudin, Ko Kuma abin Sayen ko Lokacin Biyan Shi, to Duk Bai Halatta ba. 

Kulla Ciniki a Bisa Kasada Bai Halatta ba, Haka Nan Sayar da Wani Abu Wanda Ba'a San Kansa ba, shi Ma Bai Halatta ba, ko Sayar da abu a kan Cewa Babu Wani Lokaci Takamaimai na Karban Kudin Shi Ma Bai Halatta ba, Kena aka Sayar Miki da Wani Abu kuka gama Ciniki Kasuwan ku Yayi, amma ita Wanda ta Siyar Miki Da Wannan abun babu Ranan da Zata Miki Wannan Abinda kika Siya, Hakan Bai Halatta ba_____________ 


Ku Biyomu ah Fitowa Na Gaba In Allah Yakaimu, Abinda Mu kayi Kuskure Allah Ka Yafe Mana, Abinda Muka Fada Daidai Allah Ya Sa Ladan a Mizani Amiin. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Za Ki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.

Share:

CINIKI DA KASUWANCI A SHARI'A 02


CINIKI DA ABINDA YAYI KAMA DA CINIKI/KASUWANCI AH SHARI'AN CE. 

        Fitowa Na (002) 

Ci Gaba Da Bayani Ciniki Daga Inda Muka Tsaya; amma Wadanda Jininsu Ya Sassabe Daga Wadannan Kwayoyi Da 'Ya'yan itatuwa Da Kayan Abinci, To Wannan Babu Laifi a Sami Fifiko a Wajen Yin Musayar Su, Toh amma Shi ma Sai Dai ayi Hannun Kuturu da Makaho. 
              Bai Halatta a Sami Fifiko a Cikin Nau'i Guda ba, Sai dai idan Abubuwa ne koraye( Wato Wadanda ake Ci ba Sai an Dafa Ba, Kamar irin Karas misali) da Kuma Abubuwan Marmari. Da Alkama da Sha'ir da Sult Duk Ana Daukar Su a Matsayin Nau'i Daya Ne Dangane da Abin Da Yake Halatta ko Yake Haramta a cikin Su. Zabibi Gaba Dayan Su Nau'i Guda Ne, Dabino Gaba Dayan Su Nau'i Guda Ne, Masu 'bawo kowane Nau'i Guda Ne a wajen Sayarwa ko Yin Musayar Shi. 

An yi Sabani a Zancen Imam Malik Allah Yakara Yarda Gare Shi, akan Abubuwa Masu 'bawo dangane da Musaya, (Wato ko Za'a Dauke Su Kansu Ba Dangane Da Zakka Ba, Wato Cewa Gaba Dayan Su ana Daukar Su Nau'i Guda Ne. 
            Naman Dabbobin Gida da Kuma Naman (DAWA) Masu Kafa hudu (4) Duk Nau'i Guda Ne a Wajen Yin Musayar Su, Naman Tsuntsaye Shi Ma Dukkanin Su Nau'i Guda Ne a Wajen Yin Musayar Su, Naman Dabbobin Na Cikin Ruwa Shi Ma Duk Nau'i Guda Ne a Wajen Yin Musayar Su, Duk abinda Ya Haihu Daga Naman Dabbobi Masu Nau'i Guda; Kamar Kitse, toh Kamar Hakuncin Naman Sa Ne, Nonon Su Nau'i Guda Ne da Kitsen Su da Kakiden Su Duk Nau'i Guda Ne______________


Ku Biyomu Ah Fitowa Na In Allah Ya Kaimu Lafiya, Abinda Muka Kuskure Allah Yafe Mana, Abinda Muka Fada Daidai Allah Ya Sa Ladan a Mizani Amiin. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Za Ki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.
Share:

CINIKI DA KASUWANCI A SHARI'A 01

CINIKI DA ABINDA YAYI KAMA DA CINIKI/KASUWANCI AH SHARI'AN CE. 

       Fitowa Na (001)

Allah Mai Girma Da Daukaka Ya Halatta Yin Ciniki, Ko da Ga Mahaifiyar Ki Ne Ko Mahaifin Ki, Zaki Iya Ciniki Da Shi Ki Siyar Mai Da Wani Abinda Ya Gani Kuma Yake Bukatan Siye, amma Ya Haramta Kudin (RUWA). Kudin Ruwa a Zamanin Jahiliyya Ana Sa Su Ne akan Bashi, Wato ko Dai Mutum Ya Biya Bashin idan Lokacin Yayi, Tare da Kudin Ruwa da Aka sa Masa Ko kuma a kara Masa Lokaci Kuma a kara masa Wani Ruwan akan Na Farkon da Ya Karba, Ko ah Yanzu Ma Ana Yin Haka( Wannan ita ake Kira Riban Nasa'i, Wato Riba Ta Jinkirtawa). Misali Kene Kina Son a Baki Bashin Dubu Daya(1000) Sai Kika je Wajen Wata Yar Uwan Ki, Kika Ce Don Ta Taimake Ki da Bashin 1000, Sai Tace Zaki Samu, amma fah Idan Kin Tashi Biyanta Bashin Zaki Biyata 1500/1200/1100,Sannan Idan Kin Yi Jinkiri Baki Biya Ba Har Lokacin da Kukayi Ya Wuce, Nan Kuma Sai Tace Toh, Zaki Kara mata 1600/1700, akan wannan Shirin Ku Na Da Kenan, ko Kuma 1150/1250, toh Duk Wanna Riba Ne, Kuma Allah Ya Tsine ma Masu Yin Haka, Kuma Azabar Allah Ya Tabbata Gare Su Matukar Basu Tuba Sun Daina ba Har Allah Ya Dauki Rayuwar Su ah Haka, Maza Da Mata Duk Yanzu Kasuwancin Da ake Yi Kenan, toh Yar Kiyi Gaggawan Tuba Zuwa Ga Allah Kuma ki Daina Alaka a Cikin Kasuwancin ki da Riba
              Yana Daga Nau'in Riba, Wato Ruwa Ban da wadda ta gabata: Cin Riba Haramun Ne Babba, duk Mai Yin Shi Wallahi Yayi Gaggawan Tuba Zuwa Ga Allah Kuma Ya Daina Tun Yanada Sauran Numfashi, Karamin Zunubin Mai Cin Riba, Shine Kamar Misalin Namiji Ya Yi Jima'i Da Mahaifiyar Shi, Kenan Wannan Yakai Babban Laifi Mai Girma a Wajen Allah, Wajibi Ne Mata Da Maza Masu Yin Wannan abun suyi Gaggawan Tuba Zuwa Ga Allah Kuma ki Daina tun Kinada Sauran Numfashi ah Rayuwar Ki Na Duniya, 

Musayar Azurfa da Azurfa Hannu da Hannu a wajen Yin Wannan Musayar, amma wani yafi wani, Haka Nan Ma Musayar Dinare da Dinare, Musayar Dinare da Dinare ko Azurfa da Azurfa Wannan Bai Halatta Ba Sai Dai ayi Musayar Daidai da Daidai, Kuma Hannun Kuturu da Makaho a Wajen Yin Wannan Musayar( Wato Ba Tare Da Wani Jinkiri Ba ace Kibani Naki, amma Nawa kuma Sai anjima A'a Hannu da Hannu) 
            Nau'in Abinci, Na Kwayoyi, ko Masu 'bawo Da Makamantansu Na Duk Irin Abinda Za'a Iya adana Shi Da Abincin Yau da Kullum, ko Abinda Ya Shafi Dangin Kayan Miya, Toh Kowane Nau'in Guda Bai Halatta a Musanye Shi Da Irin Sa, Sai Dai ayi Daidai da Daidai ah Wajen Yin Wannan Musayar Kuma Hannun Kuturu da Makaho, Bai Halatta a Sami Wani Jinkiri a ciki ah Lokacin ba, 

Gyararren Abinci ba a Bisa Cewa Sai Zuwa Wani Lokaci Ko Da Nau'in Su Ba 'daya Ba Ne, ko Kuma Wanda Za'a ajiye ne ko Wanda ba Zai Ajiyu Ba, 
     Abubuwan Marmari da Masu Bunku a Kasa da Abin da Ba a ajiyarsa Duk Babu Laifi Ayi Musanyarsu Tare Da Fifiko, ko da Nau'in 'daya ne, amma ayi Musayar Hannun Kuturu da Makaho a Wajen Yin Wannan Musayar, amma kayan Marmari Busasshe Wanda Zai Ajiyu, da Kayan Miya da Abin Sha, Ban da Ruwa, Duk Wadannan Bai Halatta ba a Sami Fifiko a Cikin Musayar Su idan Nau'i Guda Ne________________

Ku Biyomu Ah Fitowa Na Gaba In Allah Yakaimu. 

Daga Zauren Muslim Woman Mata Zallah 
WhatsApp Group. 

MUHAMMAD TUKUR JALINGO 
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka 
08164223447. 
This Group Is Only For Woman Please.

Share:

BABA INA MAMA?


*🌹BABA INA MAMA?!🌹*

بسم الله الرحمن الرحيم.

_🌹Lokacin labari, 😊, gaskiya duk wnda be karanta ba to an bar shi a tafiyar se de ya kalle mu a can kawai ☺_

🌹Bayan ya binne matarsa a kabari, se ya dawo gida, ya sami ɗan karamin yaronsa yana kuka yana kiran mama! Mama! Yana ta zagaye yana neman mamansa a cikin gidan.

🌹Da karamin yaron ya ga babansa ya shigo yana tsaye a jikin kofa, se ya taho da gudu zuwa gurinsa yayi tsalle ya rike babansa yana tambayarsa - "Baba ina mamana?" - Sai ya kalli fuskar ɗan nasa tare da ajiye dogon numfashi yace "Tana Aljanna". Se yaron ya tambayi babansa cikin hawaye da shasshekar kuka - "Baba ina ce hanyar zuwa Aljanna?" Baba bashi da amsa, kawai se ya kalli sama cikin nutsuwa, yaro ya sake tambaya, "Baba ina ne hanyar zuwa Aljanna?" Ina so naga Mama, Ina so na ganta, ina so zan je hurin ta, ina ce hanyar Aljanna?

🌹Se baban yace - Ya kai ɗa na, hanyar zuwa Aljanna itace bin hanya madaidaiciya. Hanyar Annabawa da Manzanni, da Sahabbai da Tabi'ai. Hanyar Zuwa Aljanna shine tsayar Tawheedi, da zuwa masallaci da yin salloli biyar a rana cikin jam'i.

🌹Hanyar zuwa Aljanna shine yin Azumi, karatun AlQur'ani, aikin hajji idan ka sami iko, jihadi, da haquri da tsare mutuncin kai, da yin imani da Allah da aiyuka na kwarai. Hanyar Aljanna shine bin hanyar neman ilimi, da taimakon marayu, zama lafiya da mutane da yin biyayya ga iyaye.

🌹Se karamin yaron ya goge hawayensa, tare da murmushi a fuskarsa ya rungume babansa tare da sumbatarsa yace - Baba ina so na haɗu da mama sosai, ta tafi ta barni, nayi alkawari - zan zama mutumin kirkir, zan bi dukkan maganganunka don naje na samu mama acikin Aljanna kuma na ce mata - ɗan ta yayi kewarta sosai, ina ƙaunarki mama. Mama zata ji dadi soaai idan ta ganni a can mu rayu cikin farin ciki dani da kai da ita. 💘

🌹Ya Allah ka dora mu kan hanya madaidaiciya zuwa Aljanna madaukakiya, mu hadu da masoyan mu. Amin 💞

_*🌹Godiya ta musamman ga malamata kuma my sister حبيبتى 😘 cikin rayuwata, ina matuqar ƙaunarki sbd Allah "Muhazzabin" 💘*_

✍Rubutawa:- *Abdullah A Abdullah Abu Khadeejat (أنصار السنة)*
08/Shawwal/1440
12/06/2019.

+2348060027244

https://www.sirassalafeey.wordpress.com

*ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH* 08108685876
Share:

NASIHOHIN LOKACIN SANYI 02

NASIHOHI A LOKACIN SANYI (fitowa ta biyu)
MU KYAUTATA ALWALA A LOKACIN SANYI
Idan sanyi ya tsananta mutane da yawa sukan tauye alwalar su, saboda kyamar amfani da ruwan sanyi, sai kaga wani ya kasa wanke gabar sa dukkanta, ko ya rika barin lum’a a jikin sa.
عن أبي هريرة، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «ألا أدلكم على ما يمحو الله به الخطايا، ويرفع به الدرجات؟» قالوا بلى يا رسول الله قال: «إسباغ الوضوء على المكاره، وكثرة الخطا إلى المساجد، وانتظار الصلاة بعد الصلاة، فذلكم الرباط".
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda, lallai manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace: “ku saurara! Shin kuna so in nuna maku (ayukka) wanda Allah yake goge zunubbai saboda shi? kuma yake daukaka darajoji saboda shi? Suka ce: e ya Manzon Allah, yace: “kyautata Alwala a lokacin kyama (kamar lokacin sanyi) da yawan taku zuwa Masallaci, da jiran sallah bayan sallah, wadannan sune masu katangewa (daga sabon Allah).  
Muslim (251) ya ruwaito shi.
عن عبد الله بن عمرو، قال: رجعنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم من مكة إلى المدينة حتى إذا كنا بماء بالطريق تعجل قوم عند العصر، فتوضئوا وهم عجال فانتهينا إليهم وأعقابهم تلوح لم يمسها الماء فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «ويل للأعقاب من النار أسبغوا الوضوء".
An karbo daga Abdullahi bin Amru yace: mun dawo tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam daga Makka zuwa Madina, har muka kawo wajen wani ruwa a kan hanya, sai wasu mutane sukayi gaggawa a wajen (sallar) La’asar, sai sukayi alwala suna masu gaggawa, sai muka same su, dugadugan su suna bushe, ruwa bai shafe su ba, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace: “bone ya tabbata ga dugadugai daga wuta, ku kyauata alwala”.
Muslim ne ya ruwaito shi.

Share:

LUWAƊI A AL'UMMAR MUSULMI


*Luwadi a al’ummar musulmi.*😢😢


Luwadi a wannan zamanin ya zama kamar ruwan dare a tsakanin Matasa. Sun biye ma sha'awa irin ta shaidan wacce ta mamaye zukatansu, Sun afka cikin mafi munin Qazantar laifin da aka taba aikatawa adoron Qasa.

Ina gujewa masu irin wannan dabi’ar domin zasu fuskanci tashin hankali a duniya, a lahira kuma za’ayi musu azaba linki biyu. Yanzu har akwai wata sha’awa tsakanin namiji da namiji? Haba mutane, ina zamu tafi da wannan masifar? 

Hakika duk a cikin nau'o'in zina da danginta, Luwadi shine mafi Muni, kuma mafi Qazanta. Kamar yadda Allah yake gaya mana acikin Alqur'ani, sutaul-ankabut aya ta 27

وَلُوۡطًا اِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهٖۤ اِنَّكُمۡ لَـتَاۡتُوۡنَ الۡفَاحِشَةَ مَا سَبَـقَكُمۡ بِهَا مِنۡ اَحَدٍ مِّنَ الۡعٰلَمِيۡنَ‏

Ma’ana; “ka tuna Annabi lut (As) lokacin da yace wa mutanensa "me yasa kuke yin irin wannan alfashar? Babu wani wanda ya rigaku aikata irin wannan alfasha daga cikin talikai (HALITTU BAKI DAYA)".

Kuma acikin suratu An-naml aya ta 55, Allah yace; 

ﺍَـﺌِﻨَّﻜُﻢۡ ﻟَـﺘَﺎۡﺗُﻮۡﻥَ ﺍﻟﺮِّﺟَﺎﻝَ ﺷَﻬۡﻮَﺓً ﻣِّﻦۡ ﺩُﻭۡﻥِ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎٓﺀِ​ؕ ﺑَﻞۡ ﺍَﻧۡـﺘُﻢۡ ﻗَﻮۡﻡٌ ﺗَﺠۡﻬَﻠُﻮۡﻥَ 

Ma’ana “ku kuna zuwa ma mazaje ta fannin sha’awarku maimakon mata, bari dai ku mutane ne wadanda suka kasance jahilai".

Acikin irin wannan halin ne, Annabin Allah yayi baki a gidansa, daga nan sai mutanen nasa suka zo suna masu gaggawa, akan sai sunyi luwadi da wadannan bakin kamar yadda acikin suratu-huud aya ta 78 Allah yake cewa; 

ﻭَﺟَﺎٓﺀَﻩٗ ﻗَﻮۡﻣُﻪٗ ﻳُﻬۡﺮَﻋُﻮۡﻥَ ﺍِﻟَﻴۡﻪِ ؕ ﻭَﻣِﻦۡ ﻗَﺒۡﻞُ َﺎﻧُﻮۡﺍ ﻳَﻌۡﻤَﻠُﻮۡﻥَ ﺍﻟﺴَّﻴِّﺎٰﺕِ ؕ​ ﻗَﺎﻝَ ﻳٰﻘَﻮۡﻡِ ﻫٰٓﺆُﻟَﺎۤﺀِ ﺑَﻨٰﺘِﻰۡ ﻫُﻦَّ ﺍَﻃۡﻬَﺮُ ﻟَـﻜُﻢۡ​ ۚ ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮۡﺍ ﺍﻟﻠّٰﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺨۡﺰُﻭۡﻥِ ﻓِﻰۡ ﺿَﻴۡﻔِﻰۡ ؕ ﺍَﻟَﻴۡﺲَ ﻣِﻨۡﻜُﻢۡ ﺭَﺟُﻞٌ ﺭَّﺷِﻴۡﺪٌ .

Ma’ana; da mutanensa suka je masa suna gaggawa zuwa gare shi, kuma a gabani, sun kasancence suna aikata munanan ayyuka. Yace “ya mutane na, wadannan ‘ya’yana ne sune mafiya tsarki a gareku. Kuji tsoron Allah kar ku wulakantani a cikin baqi na. Shin babu wani namiji shiryayye daga gare ku?”.

Kunga anan har ‘ya’yansa mata yayi musu tayi, amma suka ce basu yadda ba. Kamar yadda wasu malamai sukace, ya gabatar da ‘ya’yansa mata ga wadannan mutanen domin ya fanshi bakin sa. Amma mutanen suka ki amince wa.

Acikin suratu-hijr aya ta 70 ya kara ce musu;

قَالَ هٰٓؤُلَاۤءِ بَنٰتِىۡۤ اِنۡ كُنۡـتُمۡ فٰعِلِيۡنَؕ‏

Ma’ana; “idan kun dage akan sai kunyi, toh ga ‘ya’ya na nan.

Amma duk da haka suka ki, daga karshe Allah yayi musu azabar da bai taba yiwa wata al’umma kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala'iku suka ciccibe garin zuwa sama, suka watsa narkon azaba sannan suka Kifar dasu.

Acikin Suratu Huud (as) Allah yace:

ﻓَﺠَﻌَﻠۡﻨَﺎ ﻋَﺎﻟِﻴـَﻬَﺎ ﺳَﺎﻓِﻠَﻬَﺎ ﻭَ ﺍَﻣۡﻄَﺮۡﻧَﺎ ﻋَﻠَﻴۡﻬِﻢۡ ﺣِﺠَﺎﺭَﺓً ﻣِّﻦۡ ﺳِﺠِّﻴۡ

Ma’ana "Yayin da al’amarinmu yazo, sai muka sanya saman birnin ya zama kasanta(kamar juyin waina) sannan mukayi musu ruwan duwatsun wuta na sijjeel".

Allah ya azabtar dasu abisa zunubansu, kuma duk wanda yake aikata irin wannan mummunar alfashar toh ya sani shima irin wancen hukuncin ne dashi, domin kaima an aiko maka da annabi kamar yadda aka aikowa da su ma wadancen mutanen.

LUWADI Mummunar Annoba ce wacce ta kauce wa hanyar da Allah ya halicci dukkan halittunsa akai. Don koda dabbobi ba zaka tarar suna yin irin wannan abun ba.

Allah ya tsare mana imaninmu😭😭
Abdulhadi Dankama
Share:

WATA FA'IDA

WATA FÃ'IDAH

An tambayi Al-Imãmu Ash-sha'abiy (r) wata tambaya sai yace: ban sani ba, sai akace da shi: ba kajin kunya da cewarka ban sani ba alhali kaine malamin mutanan Irãƙi? 

Sai Al-Imãmush Sha'abiy (r) yace: Amma su mala'iku ba suji kunya ba lokacin da sukace:

(-Ba mu da wani ilimi face wanda ka sanar da mu-)

‏سُئل الشعبي عن مسألة ؛ فقال: " لا أدري"
فقيل له: ألا تستحيي من قولك لا أدري ، وأنت فقيه أهل العراق ؟!
فقال رحمه الله : "لكن الملائكة لم تستحي حين قالوا: {لَا عِلْمَ لَنَا إِلَّا مَا عَلَّمْتَنَا ۖ} !".

[إعلام الموقعين (4/167-168)]


Share:

FULANI BA DAMA


Musha Dariya wani ba fulatani ne yakai saniyarsa kasuwa dan ya sayar yawuni ba'a siyaba da yadawo sai matarshi tace Ina kajene saiya gaya Mata yanda akayi saitace in sati yadawo kakoma kace tanada ciki haka kuwa akayi yana zuwa kasuwa yace tanada ciki nanda nan aka Saya akabashi kudi masu yawa dan fulani yace hakane ana nan sai akazo neman auren yarshi sai liman yace sadaki 10.000 dan fulani yace aa aramma akara saboda yarinya nan tana da ciki hhhhhhhhhhhhhhhhh hmmmm

Share:

VERSE OF THE DAY

VERSE OF THE DAY:

 THE EVIL OF GREEDY MISERLINESS SUPERSEDING GENEROSITY 

{وَلَا يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ يَبْخَلُونَ بِمَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ هُوَ خَيْرًا لَّهُم ۖ بَلْ هُوَ شَرٌّ لَّهُمْ ۖ سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُوا بِهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ وَلِلَّهِ مِيرَاثُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ} [آل عمران : 
 
"And let not those who [greedily] withhold what Allah has given them of His bounty ever think that it is better for them. Rather, it is worse for them. Their necks will be encircled by what they withheld on the Day of Resurrection. And to Allah belongs the heritage of the heavens and the earth. And Allah, with what you do, is [fully] Acquainted." Qur-an 3:180

May Allah the Almighty make it easy for us. Ameen

Share:

AERODYNAMICS

Menene Aerodynamics?
.
Aerodynamics kalmomi biyu ne, aka hada suka bada
wannan kalma. Aero yana nufin abun da yashafi iska(air)
ko kuma iskar kan ta, shi kuma Dynamics yana nufi motion
na abu da kuma forces nashi.
.
Aerodynamics a takaice yana nufin kimiyar tafiyan abu
acikin fluid. Idan akace fluid ana nufin abu kaman iska ko
ruwa. Fahimtar wannan kimiya tabada gudunmuwa wajen
tafiyar da kayan sufuri acikin iska, da cikin teku, da kuma
cikin sararin samaniya kaman jirgin sama da jirgin ruwa na
yaki.
.
A duk lokacin da abu yake tafiya acikin fluid dole ne zaka
samu yana fuskantar kalubale ko turjiya(resistance) daga
wannan fluid din. Kaman yanda nayi bayani asama idan
akace fluid ana nufin abu kaman ruwa ko kuma iska. To
lokacin da abu yake tafiya acikin fluid zaka samu yana
fuskantar kalubalen da zaisa karfin gudunsa ya ragu.
.
Misali idan kana tuka mota daga gabar kayi yamma. Sai a
lokacin kuma iskar daga yamma take tanayin gabar. Kaga
kenan wannan iskar tana kalubalantar tafiyar motarka. To
jirage ma yayin da suke tafiya acikin iska suna fuskantar
irin wannan barazana da kalubale, wanda hakan zaisa
jirgin yayi descend.
.
Descend yana nufin gudun jirgi yarage, wanda zaisa
yafado kasa. Aerodynamics ilimin kimiyane wanda gaba
daya yana bayanin tafiye tafiyen abubuwa acikin fluid.
Samun wannan ilimin yakawo cigaban sifirin sararin
samaniya da tafiyar da jiragen ruwa kaman nuclear
submarine wato jirgin ruwan yaki da mutane masu nutso a
teku wadanda ake kira divers.
.
Idan muna biye da kafafen daya labarai, wasu lokutan
zamuji an sanarda cewa tafiye tafiyen jiragen da aka tsara
an sokesu saboda matsalar yanayi. Wannan yana faruwa
ne saboda ana tunanin karfin iskan yayi yawa wanda zaisa
asamu matsala yayin da jirgi yake sama, ko kuma jirgin
yabace gaba daya daga taswiran masu kula da shi.
.
Aerodynamics bawai jirgin ruwa da jirgin samane kadai
yake magana akai ba - hatta mota da mashin da keke da
suke tafiya akan titi suma haddasu, saboda akan titin ma
akwai iska.
.
Abun dayasa nake bada misali da submarine wato jirgin
ruwa na yaki, shine shi submarine yana iya kwanaki
casa'in(90days) ko sama da haka acikin ruwa idan ya
nitse bai leko sama ba. Kuma yana iya yafiya acikin ruwan
bayan ya nutse kaman yanda kada(crocodile) take tafiya
bayan ta nitse acikin ruwa, yanda ba'a gane cewa akwai
wani abu acikin wannan ruwan.
.
Daga karshe muna barar addu'arku ga dan uwa Malan
Real Zaharaddeen M Kt akan Allah yabashi lafiya.
.
Dalibin Physics
Nura Mahdi Idris
Share:

SABODA KUƊI

SABODA KUDI!
Wata yarinya ce aka yi wa cikin shege, mahaifinta da mahaifiyarta suka kama dukanta suna cewa ta gaya musu wanda ya yi mata shi. Yarinyar ta ce wani mai kudi ne na shiyyarsu yayi mata shi. Da aka je aka kira mai kudin, aka tambaye shi, sai ya kyale su har sau uku, sannan ya ce: “Ni ne na yi mata. Idan ta haifi namiji zan ba babanta Naira miliyan 5, mahaifiyarta Naira miliyan 3, yarinyar kuma Naira miliyan 2. Idan kuma ta haifi mace, zan ba babanta Naira miliyan 3, innarta Naira miliyan 2, ita kuma yarinyar Naira miliyan 3” Ya ci gaba da cewa: “Idan kuma cikin ya zube…” Bai ida maganarsa ba sai baban yarinyar ya yi farat ya ce: “Sai ka sake yi mata wani cikin!”hhhhhh 😂🤣🤩

Share:

SHIN MUSULMI ZAI IYA YIN SALLAH A COCI?


MUSULMI ZAI IYA SALLAH A COCI ! ! *Tambaya:* Assalamu alaikum, Malam Shin ya halatta musulmai su yi sallah a coci kamar ranar juma'a ? *Amsa:* Wa alaikum assalam, da yawa daga malamai sun tafi akan haramcin hakan ko kuma karhanci saboda coci ba ta rabuwa da hotuna, kuma mala'iku ba sa shiga dakin da yake akwai hotuna ko kare a ciki, kamar yadda ya zo a Sahihil Bukhari. Ibnu Khudaamah ya rawaito halaccin sallah a coci mutukar tana da tsafta daga Umar dan Abdulaziz da Auza'i, da wasu jiga-jigan magabata, ya Kafa hujja da cewa: Annabi s.a.w. ya yi umarni da mutum ya yi sallah duk inda ta riske shi, kamar yadda ya yi bayanin hakan a Al-Mugni 1/407. Zance mafi inganci, In har akwai lalura ta rashin wurin sallah ya halatta musulmi ya yi sallah a coci kamar su rasa inda za su yi jumaa, kamar yadda Abu Musa Al-ash'ary ya yi sallah a wata Coci mai suna Nahya a Damashka, hakan ya zo a Musannaf a hadisi mai lamba ta: 4871, in babu kuma to haramun ne. Allah ne mafi sani. *Amsawa:* 16/10/2016 *DR Jamilu Zarewa*

Share:

OFFERING SALUTATIONS ON THE BELOVED PROPHET MUHAMMAD S.A.W


OFFERING SALUTATIONS [Salawaat] ON OUR BELOVED PROPHET MUHAMMAD (Sallallahu Alaihe Wasallam), IT'S MERIT and EXCELLENCE

 Bismillahir Rahmaanir Raheem.

Let's continue from the first reminder. Please request for a copy if you couldn't receive it.
Aayah 56 of Surah Ahzaab says:
“Indeed ALLAH and HIS angels send blessings on the Prophet. O you who believe, you should ask and send blessings and peace on him.”
 
Allah’s showering blessings on HIS Messenger means that HE, ALLAH is very kind to HIS Prophet. HE praises him, blesses his work, exalts his name, and showers HIS mercies on him. Blessings of the angels mean: Angels love the Prophet most dearly and pray to ALLAH to bless him with the highest ranks in Paradise, cause his religion and Shari’ah to flourish and exalt him to the laudable position. In our invocation we mean: “Yaa ALLAH (SWT), the Lord of the worlds: just as your Prophet has done us countless and endless favors, so do You also show him endless and limitless mercy; raise him to the highest ranks in this world and bless him with the greatest nearness to Yourself in the Hereafter.” please note that the Prophet doesn't need this from us as a favour but he is doing us a favour to earn the rewards of ALLAH and HIS Angels praises on him that's why it is recommended after praising ALLAH to praise the Prophet the sunnah way (Salaat Alan Nabi).
 
Abu Muhammad Ka’b bin Ujrah (RA) said that the companions submitted to the Prophet (SallallahuAlaihe Wasallam): “Yaa Rasuul ALLAH, we already knew how to greet you (i.e., saying Assalaamu Alaikum), but how should we invoke blessings upon you?”
 
In his reply The Prophet (sallallahu alaihi wasallam) asked them to recite salawaat as follows; Allah humma salli alaa muhammad wa-alaa aali muhammad kamaa sallaita alaa Ibraaheem wa alaa aali Ibraheem inna ka hameedum majeed. Allah hummabarik ala muhammad wa ala aali muhammad kamaa baarakta alaa Ibraaheem wa alaa aali Ibraheem inna ka hameedum majeed.
Meaning "O Allah, let Your Blessings come upon Muhammad and the family of Muhammad, as you have blessed Ibrahim and his family. Truly, You are Praiseworthy and Glorious. Allah, bless Muhammad and the family of Muhammad, as you have blessed Ibrahim and his family. Truly, You are Praiseworthy and Glorious"[Bukhari and Muslim]. There are other narrated forms that are all permissible in case you come across them but the above is the best to recite regularly seeking your share of blessings from ALLAH. 

*_We ask ALLAH to reward our little efforts and heal our hearts from any sorrows and grant us our wish_*. Aameen.
Share:

AKWAI MATSALA BABBA GA MA'AURATA


AKWAI MATSALA BABBA GA MA'AURATA*.

🌻Matukar MA'AURATA ba sa ganin girman iyayen junansu to akwai matsala a zamantakewar su Kam. 

🌻Ya za kayi da wadanda suka Haifa maka wacce zata iya zama sanadiyyar cikar Addinin ka, suka ki yarda su mallakawa kowa ita sai kai kadai a duk fadin duniyar nan, idan har baka girmama su ka darajasu kuma ka gode musu ba? 

🌻Ya za kiyi da wadanda suka Haifa miki Wanda zai zama Shugaba kuma abin Alfaharinki wajan nuna soyayya da kulawa gareki, sannan yazamto garkuwa ne ga mutunci da darajar ki, idan har baki girmama su ba.? 

KUJI TSARON ALLAH KU KYAUTATAWA SURUKANKU. 
Allah yakyautata.

✍🏻 Idris M Rismawy
Share:

INTERNET MARRIAGES


INTERNET MARRIAGES
.
About two or three years ago on this platform, I said 'Whoever brings her marriage to facebook, will be divorced on YouTube and will observe her Iddah period on instagram'. When we keep advising people to take their marital life off the internet, people think we are preaching an extreme version of Islam or it's because African men are not romantic. We are all aware of the ongoing saga in the last few days about the highly glorified romantic couple on earth. Many of our sisters both the married and teens alike have been following their pages, downloading their videos and pictures for years now, perhaps some women even wish their husbands were like him, perhaps many of our sisters have been crushing on him, yet the same people are now criticizing him, such is life. 
.
If you place your marriage in public, people will have an opinion in your marriage; when it falls, when it rises, when it's jolly, when it's tough, when it enjoys wealth and when it suffers poverty, because you were the one that submitted your marriage for public scrutiny in the first place, so you have to keep explaining to people, without getting paid for it. 
.
I have always expected since all this years that people who are close to them would advise them about Gheerah and secrecy, even though women in their nature loves to be displayed and celebrated, the companions were the best of generations and had the best of marriages, yet they concealed it, but Allah still made their marriages apparent to us because those were the real blessed marriages. Ateekah bint Zaid radiAllahu anhaa was an extremely beautiful female companion, when she was under Umar, he disliked her idea of going to the mosque so that she won't be seen by other men, when she was under Zubair Ibn Awwam too, he tried to discourage her, infact one night, Zubayr hid in a dark spot, when Ateekah was passing on her way to the masjid for Ishaa, Zubayr poked her at the back, out of fear, she ran back home and since then she never went to the masjid again, so one day Zubayr enquired about the reason, and she told him that 'people have become corrupt' . Zubayr smiled and said 'I was the one who touched you', but the message has been passed. This was narrated in At'tabaqat of Ibn Sa'ad. 
.
The companions were shy of people seeing their spouses but the men of today proudly show off their spouses to the world. When you play ball with her, you post it. when you eat with her, you post it. The prophet salalahu alayhi wassalam said: 
Be secretive in your affairs, for it's true that the fortunate person is always envied. (As'Saheehah)  
We know what envy means and it leads to nothing but hatred, jealousy and the evil eye against such people. You all taught that all their followers loved them, but we can all see the hate comments and mockery being bombarded at them now. Either their marriage is a scam or not, it is not for us to condemn them or conclude until they prove themselves. I hope our sisters have learnt a lot from this Shenanigan, if you bring your marriage to the net, everybody will automatically become your e-inlaw. 
.
People now post their pregnancy conception news online, I hope you will also post the miscarriage if it happens ? 
People now report their spouses in online groups that contains thousands of people, how can thousands of people advise you at the same time, which of the thousand advices will you choose?  
May Allah not put us in a situation where we will now have to prove our marriage to the world with documents before people believe or disbelieve in our marriage.
Share:

HADITH OF THE DAY

حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ سِنَانٍ، قَالَ حَدَّثَنَا فُلَيْحٌ، قَالَ حَدَّثَنَا هِلاَلُ بْنُ عَلِيٍّ، عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ، قَالَ صَلَّى لَنَا النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم ثُمَّ رَقَا الْمِنْبَرَ، فَأَشَارَ بِيَدَيْهِ قِبَلَ قِبْلَةِ الْمَسْجِدِ ثُمَّ قَالَ ‏"‏ لَقَدْ رَأَيْتُ الآنَ مُنْذُ صَلَّيْتُ لَكُمُ الصَّلاَةَ الْجَنَّةَ وَالنَّارَ مُمَثَّلَتَيْنِ فِي قِبْلَةِ هَذَا الْجِدَارِ، فَلَمْ أَرَ كَالْيَوْمِ فِي الْخَيْرِ وَالشَّرِّ ‏"‏ ثَلاَثًا‏‏


Narrated By Anas bin Malik : The Prophet led us in prayer and then went up to the pulpit and beckoned with both hands towards the Qibla of the mosque and then said, "When I started leading you in prayer, I saw the display of Paradise and Hell on the wall of the mosque (facing the Qibla). I never saw good and bad as I have seen today." He repeated the last statement thrice.


حضرت انس بن مالک رضی اللہ عنہ سے روایت ہے کہ انہوں نے کہا: نبیﷺ نے ہم کو نماز پڑھائی پھرآپﷺ منبر پر چڑھے آپﷺنے دونوں ہاتھوں سے مسجد کے قبلے کی جانب اشارہ کرکے فرمایا: میں نے ابھی ابھی جب تم کو نماز پڑھائی جنت اور دوزخ کو دیکھا ان کی تصویریں اس دیوار میں قبلے کی طرف نمودار ہوئیں تو میں نے آج کے دن کی طرح نہ بھلائی دیکھی اور نہ برائی تین بار یہ فرمایا۔
Bukhary. Hadees no 146
Kitab ul azan

Share:

FASSARAR WAƘAR JIYA REFassarar Waƙar Jiya Re

Sunan Waƙa: Jiya Re

Sunan Shiri: Jab Tak Hai Jaan

Shekarar Fita: 2012

Sauti: A. R. Rahman

Rubutawa: Gulzar

Kamfani: YRF Music

Rerawa: Neeti Mohan

Fassarawa: Haiman Raees 

* Chali Re Chali Re Junoon Ko Liye

Na fara tafiya ta cikin so da kwanciyar hankali 

* Qatra Qatra Lamhon Ko Piye

Ina mai jin daɗin rayuwa 

* Pinjre Se Udda Dil Ka Shikra

Tamkar Shaho, haka zuciya ta fice daga kejin ta 

* Khud Hi Se Maine Ishq Kiya Re

Na fara don kaina da kaina 

* Jiya Jiya Re Jiya Re, Jiya Jiya Re Jiya Re,
Jiya Jiya Re Jiya Re Jiya Oh Ho (x2) 

Ya ke zuciya, ki Rayu, ki Rayu wa Burin ki 

* Chali Re Chali Re Junoon Ko Liye

Na fara tafiya ta cikin so da kwanciyar hankali 

* Pinjre Se Udda Dil Ka Shikra

Tamkar Shaho, haka zuciya ta fice daga kejin ta 

* Khud Hi Se Maine Ishq Kiya Re

Na fara don kaina da kaina 

* Jiya Jiya Re Jiya Re, Jiya Jiya Re Jiya Re,
Jiya Jiya Re Jiya Re Jiya Oh Ho (x2) 

Ya ke zuciya, ki Rayu, ki Rayu wa Burin ki 

* Make The Way For Akira

Ku bada hanya wa Akira 

* Pop It Up Move Aside She Is Here

Ja can, matsa gefe gata nan 

* Hey Get Up Everybody Wanna Be Her

Kai miƙe kowa fa so yake ya zamo ita 

* Wanna See Her She Is Akira
(suna) Son ganin ta, ita ce Akira 

* Chotte Chotte Lamhon Ko Titli Jaise Pakdo Tho

Da ace zamu tattara ƙananun lokutta kamar malam-buɗe-littafi 

* Haathon Mein Rang Reh Jaata Hai Pankhon Se Jab Chodo Tho

Kalan zai tsaya a tare da mu ko da mun cire fuka-fukan mu 

* Waqt Chalta Hai

Lokaci Tafiya yake yi

* Waqt Ka Magar Rang Utarta Hai, Akira

Kalan lokaci disashewa yake yi Akira 

* Udte Udte Phir Ek Lamha Maine Pakad Liya Re

Amma na kama lokaci mai tashi 

* Jiya Jiya Re Jiya Re, Jiya Jiya Re Jiya Re,
Jiya Jiya Re Jiya Re Jiya Oh Ho (x2) 

Ya ke zuciya, ki Rayu, ki Rayu wa Burin ki 

* Make The Way For Akira

Ku bada hanya wa Akira 

* Halke Halke Dardon Mein Muskurana Acha Lagta Hai

A Yayin ɓacin rai ko baƙin ciki, na kan so yin murmushi 

* Roshni Jo Deta Ho Tho Dil Jalaana Acha Lagta Hai

Domin samar da haske, kunnawa zuciya wuta ma abu ne mai kyau. 

* Ek Pal Sahi, Umar Bhar Isse Saath Rakhna, Akira

Ko da na ɗan wani lokaci ne, ki riƙe shi a rayuwa Akira 

* Zindagi Se Phir Ek Vaada Maine Kar Liya Re

Na yi wa rayuwa Alƙawarin cewa... 

* Jiya Jiya Re Jiya Re, Jiya Jiya Re Jiya Re,
Jiya Jiya Re Jiya Re Jiya Oh Ho (x2) 

Ya ke zuciya, ki Rayu, ki Rayu wa Burin ki

* Chali Re Chali Re Junoon Ko Liye

Na fara tafiya ta cikin so da kwanciyar hankali 

* Pinjre Se Udda Dil Ka Shikra

Tamkar Shaho, haka zuciya ta fice daga kejin ta

* Khud Hi Se Maine Ishq Kiya Re

Na fara don kaina da kaina

* Jiya Jiya Re Jiya Re, Jiya Jiya Re Jiya Re,
Jiya Jiya Re Jiya Re Jiya Oh Ho (x3) 

Ya ke zuciya, ki Rayu, ki Rayu wa Burin ki


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring

Share:

FASSARAR WAƘAR AE ZINDAGI GALE LA GALE


FASSARAR WAƘAR AE ZINDAGI GALE LA GA LE (Take 1)

* Sunan Waƙa - Ae Zindagi Gale Laga Le (Take 1)

* Sunan Fim - Dear Zindagi

* Shekarar Fita - 2016

* Haɗa Sauti - Amit Trivedi

* Rubutawa - Gulzar da Kausar Munir

* Sunan Kamfani - Sony Music India

* Mawaƙi - Arijit Singh

* Mai Fassara - Haiman Raees 

* Ae Zindagi Gale Laga Le (x2)

Ya ke Rayuwa! Ki Rungume ni 

* Humne Bhi Tere Har Ik Gham Ko

Duk wani baƙin cikin ki nima na... 

* Gale Se Lagaya Hai, Hai Na

Rungume shi ko ba haka ba? 

* Ae Zindagi Gale Laga Le 

Ya ke Rayuwa! Ki Rungume ni

* Humne Bahaane Se…

Bada uzuri a sirrance 

* Chhup Ke Zamaane Se…

Ɓoye wa duniya baki ɗaya 

* Palkon Ke Parde Mein Ghar Bhar Liya

Nayi gidana a bayan mayafin idanuwa 

* Tera Sahara Mil Gaya Hai Zindagi

Ya ke Rayuwa! Na samu goyon bayan ki 

La La La La La…

* Tera Sahara Mil Gaya Hai Zindagi

Ya ke Rayuwa! Na samu goyon bayan ki 

* Ae Zindagi Gale Laga Le (x2)

Ya ke Rayuwa! Ki Rungume ni 

* Humne Bhi Tere Har Ik Gham Ko

Duk wani baƙin cikin ki nima na... 

* Gale Se Lagaya Hai, Hai Na

Rungume shi ko ba haka ba?

* Ae Zindagi Gale Laga Le, Ae Zindagi…

Ya ke Rayuwa! Ki Rungume ni, Ya ke Rayuwa!

* Ae Zindagi Gale Laga Le, Gale Laga Le

Ya ke Rayuwa! Ki Rungume ni, Ki Rungume ni

* Ho… Gale Laga Le

Ki Rungume ni

* Ae Zindagi Gale Laga Le, Gale Laga Le

Ya ke Rayuwa! Ki Rungume ni, Ki Rungume ni

Ho… Gale Laga Le
 
Ki Rungume ni<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 
Share:

FASSARAR WAƘAR AAYA TERE DAR PAR


Fassarar Waƙar Aaya Tere Dar Par

Sunan Waƙa: Aaya Tere Dar Par

Sunan Shiri: Veer-Zaara

Shekara: 2004

Sauti: Madan Mohan

Rubutawa: Javed Akhtar

Kamfani: Yash Raj Music

Mawaƙa: Ahmed Hussain da Mohammad Hussain

Mai Fassara: Haiman Raees 

Aa.... Aa.... Aa.... Aa.... Aa.... Aa.. Aa..

* Jo bandishein thi zamaane ki tod aaya hoon

Na yanke duk wata alaƙa ta da duniya 

* Main tere vaaste duniya ko chhod aaya hoon

Saboda ke Na bar duniya a bayana Nazo 

* Aaya tere dar par diwaana (x2)

Masoyinki yazo har bakin ƙofar ki 

* Aaya hoon aaya, aaya tera diwaana

Yazo, masoyin ki yazo 

* Aaya hoon aaya, aaya tera diwaana (x2) 

Yazo, masoyin ki yazo 

* Tera diwaana, tera diwaana, tera diwaana

Masoyin Ki, Masoyin Ki 

* Aaya hoon aaya, aaya tera diwaana (x2) 

Yazo, masoyin ki yazo

* Tera diwaana, (tera)

Masoyin Ki, Naki 

* Tera diwaana, (diwaana)

Masoyin ki, Mai haukan so 

* Tera diwaana, tera

Masoyin Ki, Naki 

* Tera diwaana

Mai haukan son ki 

* Tera diwaana, tera diwaana, tera diwaana

Masoyin Ki, Masoyin Ki

* Aaya hoon aaya, aaya tera diwaana (x2) 

Yazo, masoyin ki yazo

* Ye hai tera hi saudaayee, ye hai tera hi shahdaayee (x2)

Duk ke kika jawo, shi masoyin ki ne na gaske 

* Tere ishq mein hai isse mar jaana

A cikin soyayyar Ki Zai mutu 

* Aaya hoon aaya, aaya tera diwaana (x2) 

Yazo, masoyin ki yazo

Aa.... Aa.... Aa...

* Tera jalwa jo paaun, main har gham bhool jaaun

Idan na samu annurin ki, zan manta dukkan Damuwoyi na 

* Tera jalwa jo paaun, main har gham bhool jaaun

Idan na samu annurin ki, zan manta dukkan Damuwoyi na 

* Ye aansoo jo hai behte, bas itna hai ye kehte

Waɗannan hawayen da ke Kwaranya abinda kawai suke cewa shi ne 

* Kahaan tu aur kahaan main, paraaya hoon yahaan main

A ina kike kuma nima a ina nake? Ni baƙo ne a nan 

* Aa... Karam itna agar ho, ki mujh par ik nazar ho

Zai zamo albarka mai girma idan kika kalle ni 

* Karam itna agar ho, ki mujh par ik nazar ho

Kiyi jin ƙai ki kalle ni ko da sau ɗaya ne 

* Jaan-o-dil vaar doon main, zindagi haar doon main

Zan iya baki zuciyata, zan iya rasa rayuwata saboda ke 

* Jaise shama pe marta hai parvaana

Kamar yadda ƙwaro ke faɗawa wuta 

* Aaya hoon aaya, aaya tera diwaana (x2) 

Yazo, masoyin ki yazo

* Aaya tere dar par diwaana (x2)

Masoyinki yazo har bakin ƙofar ki 

* Diwaana tera (x5)

Masoyin Ki 

* Diwaana tera (x3)

Masoyin Ki 

* Diwaana tera (x3)

Masoyin Ki 

* Aaya tere dar par diwaana 

Masoyinki yazo har bakin ƙofar ki 

* Aaya kis mod pe afsaana (x6)

A cikin wani yanayi, labarin nan kuma ya canja salo 

Aa...... Aa...... Aa......

* Ye sitam ka rivaaj kyun hai, jaisa hai ye samaaj kyun hai

Me yasa waɗannan Al'adun Sun faye mugunta ne, me yasa wannan al'ummar take haka ne? 

* Ye jo duniya ki hai rasmein, main hoon ab inke bas mein

Wannan wasu ɗabi'un duniya ce, kuma yanzu ina ƙarƙashin ikon ta ne 

* Ye jo duniya ki hai rasmein, main hoon ab inke bas mein

Wannan wasu ɗabi'un duniya ce, kuma yanzu ina ƙarƙashin ikon ta ne 

* Na poochho kya gila hai, mujhe gham kyun mila hai

Kada ku tambaye ni dalilin wannan ƙorafin, ko kuma me yasa nake ta fama da damuwoyi 

* Tumhein main kya bataaun, mohabbat jurm hai kyun

Ta yaya zan iya faɗa miki, cewa so laifi ne? 

* Koyi rota hai kyun, aisa hota hai kyun

Me yasa wani ke kuka, me yasa hakan ya faru? 

* Kyun dil se har ek hai anjaana

Me yasa kowa baƙo ne ga zuciya? 


* Aaya kis mod pe afsaana (x6)

A cikin wani yanayi, labarin nan kuma ya canja salo 

* Ye kis maahol mein ham hain, khushi ke bhes mein gham hain

Wani irin yanayi ne kuma haka muke ciki, farinciki ya ɓoye a bayan farin ciki 

* Kisse apna kahe kisse beghaana

Wa zamu kira namu kuma wa zamu kira baƙo? 


* Aaya kis mod pe afsaana (x2)
A wani irin yanayi, wannan labarin ya canja haka? 

* Aa...... Aa...... Aaya kis mod pe mera afsaana (x2)

A wani irin yanayi, wannan labarin ya canja haka

* Afsaana mera afsaana mera (x5)

Labarina 

* Afsaana mera afsaana mera (x6)

Labarina 

* Afsaana mera (x3)

Labarina 

* Aaya kis mod pe afsaana, afsaana, afsaana

A wani irin yanayi, wannan labarin ya canja haka

* Aaya kis mod pe afsaana (x4)

A wani irin yanayi, wannan labarin ya canja haka?

# HappyBirthdaySrk
# NASRUN MINALLAAHI ƘAREEB 
<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 
Share:

DARUSSAN HINDI (20)

🇮🇳 MU KOYA YAREN HINDI 🇳🇬
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
"MUJALLAR FINA FINAN INDIYA".
Tuesday , 19h , November , 2019 .
Darasi Na Ashirin ( 20 )
Masu Gabatarwa
Ismail Abubakar Jr.
Tare Da Abokiyar Aikita Meenat Sulaiman
Kyonki - Because
Shubh Kamnayein - All The Best
Anuwadh - Translate
Yaariyan - Friendship

Sadasya - Member
Soya - Slept
Baad Mey - After
Pehle - Before

Kasam - Promise
Bagya Accha Ho - Good Luck
Aayat - Abu Mai Shigowa
Niryaat - Abu Mai Fita

Chatur - Mai Wayo
Kutil - Dolo
Gaur - Secondary
Mukhya - Primary

Uday - Rana Tsaka
Ast - Yam Maci
Puratan - Tsoho
Nutan - Sabo

Jal - Ruwa
Ihal - Kasa
Ladki - Mace
Ladka - Namiji

Prakash - Haske
Andhkaar - Duhu
Pyaar - So / Soyayya
Nafraat - Ki / Kiyayya

Pyaara - Masoyi
Haan - Eh
Samay - Lokaci
Din - Rana

Raat - Dare
Subah - Safiya
Dopaher - Rana Tsaka
Sham / Sandhya - Yamma

Aaj - Yau
Aanewala Kal - Gobe
Beeta Hua Kal - Jiya
Saptah / Hafta - Sati

Ham Yaha Mein Ruko - Zamu Tsaya Anan.

#Via
Ismail Abubakar Jr.

Share:

SHARUƊƊAN AMSAR AYYUKAN BAWA A WAJEN ALLAAH


SHARUDDAN AMSAR AIYUKAN BAWA AWAJAN ALLAH TA'ALA

Aiyukan bawa na fili da na boye basu samun karbuwa har Allah ya bashi sakamakonsu sai sun cika sharudda guda biyu-2:-

1-SHARADI NA FARKO:
"IKHLASY"
Shine tsarkake aikin zuwa ga Allah shi kadai,da kuma kyakkyawar niyya zuwa ga Allah alokacin gabatar da aikin. 

Allah yana cewa:
‏( وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ ۚ وَذَٰلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ ) البيِّنة (5) Al-Bayyina

(Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai).
 
IKHLASY:
Shine manufar bawa acikin dukkan maganganusa da aiyukansa na fili da na boye yana yinsune da neman yardar Allah shikadai. 
Allah yana fada:
( ﻭﻣﺎ ﻷﺣﺪ ﻋﻨﺪﻩ ﻣﻦ ﻧﻌﻤﺔ ﺗﺠﺰﻯ ﺇﻻ ﺍﺑﺘﻐﺎﺀ ﻭﺟﻪ ﺭﺑﻪ ﺍﻷﻋﻠﻰ ‏) ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻠﻴﻞ 19/

(Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka).

ﻭﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﺇﻧﻤﺎ ﻧﻄﻌﻤﻜﻢ ﻟﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﺮﻳﺪ ﻣﻨﻜﻢ ﺟﺰﺍﺀً ﻭﻻ ﺷﻜﻮﺭﺍً ‏) ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ 9/

(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya".

ﻭﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻳﺮﻳﺪ ﺣﺮﺙ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻧﺰﺩ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺣﺮﺛﻪ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻳﺮﻳﺪ ﺣﺮﺙ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻧﺆﺗﻪ ﻣﻨﻬﺎ ﻭﻣﺎ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻣﻦ ﻧﺼﻴﺐ ‏) ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ 20/
(Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira). 

ﻭﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﻣَﻦْ ﻛَﺎﻥَ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟْﺤَﻴَﺎﺓَ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ ﻭَﺯِﻳﻨَﺘَﻬَﺎ ﻧُﻮَﻑِّ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﺃَﻋْﻤَﺎﻟَﻬُﻢْ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻻ ﻳُﺒْﺨَﺴُﻮﻥَ ﺃُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻟَﻴْﺲَ ﻟَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻵﺧِﺮَﺓِ ﺇِﻻ ﺍﻟﻨَّﺎﺭُ ﻭَﺣَﺒِﻂَ ﻣَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻭَﺑَﺎﻃِﻞٌ ﻣَﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ ‏) ﺳﻮﺭﺓ
ﻫﻮﺩ 16-15/
(Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba. Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne).

Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai dukkan aiyukan sai da niyya suke tabbbata,kuma lallai kowane mutum Ida abinda yayi niyya,......)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ‏( ﺑﺪﺀ ﺍﻟﻮﺣﻲ 1/ ‏)

Kuma Annabi s.a.w yana cewa:
"Allah Wanda Albakarsa ta yawaita kuma shi madaukakin sarki ne yace:
(Ni Allah ni nafi wadatuwa da abinda masu shirka suke hada tarayya da ni acikin bauta,duk wanda ya aikata wani aiki,wanda ya hadani da wani acikinsa,zan bar wannan aikin da wanda yayi aiki). 
@ﻣﺴﻠﻢ 

2-SHARADI NA BIYU-2
"Aikin ya dace da abinda Allah ya shar'anta kuma yayi umarni wato, kada mutum ya baitawa allah sai abisa bin koyi da Annabi s.a.w.  

Dukkan abinda yazo daga allah da Manzonsa s.a.w da shine kadai ake bautawa Allah abisa koyi da sunnar Annabi s.a.w. Dukkan ibadar da bata cika wannan ba,bata samun karbuwa awajan Allah Ta'ala. 
Manzon Allah s.a.w yace:
 " ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﻋﻤﻼً ﻟﻴﺲ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﻓﻬﻮ ﺭﺩ " ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ

"Duk wanda ya aikata wani aiki, wanda babu umarninmu acikin wannan aikin to an mayar masa da aikinsa". 
‏( ﺍﻷﻗﻀﻴﺔ 3243/‏) ،

ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺭﺟﺐ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
Yana cewa:
"Wannan Hadisin wani tushene mafi girma daga cikin Tushen musulinci, kuma da shi ake banbance aiyukan bayi..". 

 " ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺑﺎﻟﻨﻴﺎﺕ:
Tana banbance aiyukan boye, tana tabbatar mana da dukkan aiyukan da akayi su badan Allah ba,ko badan Allah shi kadai ba,wannan aikin baya samun karbuwa da lada awajan Allah. Haka kuma dukkan aiyukan da babu koyi da Annabi s.a.w abin mayarwane baya samun karbuwa awajan Allah. 
@ﺟﺎﻣﻊ ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ ﻭﺍﻟﺤﻜﻢ ﺝ 1 ﺹ 176 .

Kuma Annabi s.a.w yayi Umarni da bin shiriyarsa da koyi da sunnarsa acikin dukkan Ibada: sai yake cewa:
" ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺑﺴﻨﺘﻲ ﻭﺳﻨﺔ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺮﺍﺷﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﻬﺪﻳﻦ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻱ ﻋﻀﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﺎﻟﻨﻮﺍﺟﺬ " ﻭﺣﺬَّﺭ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻓﻘﺎﻝ : "

Ina umarnin ku da roko da sunnata da kuma sunnar Khalifofina shiryayyu,ku rike sunnata da Hakoran gaba. 
Kuma yayi Hani da tsawatarwa akan aikata bidiya. 

Kuma ina maku gargadi akan aikata fararrun al'amura acikin Ibada,domin dukkan Bidi'a bata ce. 
ﻭﺇﻳﺎﻛﻢ ﻭﻣﺤﺪﺛﺎﺕ ﺍﻷﻣﻮﺭ ﻓﺈﻥ ﻛﻞَّ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ " ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( ﺍﻟﻌﻠﻢ 2600/‏) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﺑﺮﻗﻢ 2157

Ibn Qaiyim Allah yayi masa Rahama yana cewa:
"Allah ya sanya Ikhlasy da Koyi da Bin Annabi s.a.w sune Sharudda karbar aiyukan bayinsa,idan kuma bawa yayi wani aiki na ibada babu wadan nan sharuddan,wannan ibadar bata samun karbuwa awajan Allah". 
@ﺍﻟﺮﻭﺡ 1/135

Allah yana cewa:
 ‏
( الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )
الملك (2) Al-Mulk

Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻔُﻀَﻴْﻞ : ﺃﺣﺴﻦ ﻋﻤﻼً ،
ﺃﺧﻠﺼﻪ ﻭﺃﺻﻮﺑﻪ . 
Aiki mafi kyau shine wanda ya cika sharadi guda biyu:
1-Anyi shi dan Allah kadai da ikhlasy. 

2-Anyi shi daidai wato bisa ga koyi da sunnar Annabi s.a.w.  

Allah bamu ikon cikasa wadan nan sharuddan acikin aiyukan mu baki daya.
Share:

TARIHIN JARUMI NANDAMURI KALYAN RAM

An Haifi Jarumi Nandamuri Kalyan Ram a ) 5 ga watan July shekara ta 1978), Yaka sance Jarumin India ne Shi Sannan Kuma Mai daukar Nauyin shiri Wanda akafi Sanin Aikinsa a Masana'antar Telugu cinema .Ďane ga Jarumi Sannan kuma Dan Siyasa Nandamuri Harikrishna , Mahaifiyarsa Lakshmi. Sannan Kuma Jikane ga N. T. Rama Rao, Wanda yaksance shima Jarumi Sannan kuma kwararren dan Siyasa . Sai kuma Jarumi Jr. NTR yaka sance Kani ne ga Jarumi NKR . Sannan yanada Kamfani mallakar Kansa Wanda ya bawa Suna bayan Mutuwar Kakansa Mai Gayayi NTR , An bawa Kamfanin Suna . N.T.R. Arts. Jarumin ya kafta roles a wasu fina finai da ya zama Kwari kamar su Athanokkade, Hare Ram, Pataas, Ism da 118. Sannan kuma yanada Kamfani nasa na VFX company wanda aka bawa Suna da "Advitha Creative Studios",Kamfanin da aka samarda fina finai masu himma kamar su Legend, Nannaku Prematho da Krishnashtami.
An haifi Nandamuri Kalyan Ram a 5 July 1978 Shekarun sa 41 an haifeshi a garin Hyderabad, India a yankinTelangana, India)
Mazaunin: sa Hyderabad, Telangana, India .
Kasar sa ta haihuwa: india.
Inkiyar sa : NKR.
Inda yayi karatu :MS at Illinois Institute of Technology, Chicago, US,BE a Coimbatore .
Aikin sa : Jarumin Film , Mai daukar Nauyin Shiri.
Shekarar da ya Fara Film 1989; 2003–
Matar sa :Swati
Ya'yansa : Sourya Ram da Taraka Advitha
Mahai finsa :Baban shi Harikrishna Nandamuri
Mahaifiyar sa :Lakshmi Nandamuri.
Dan uwan sa na jini: Jr. NTR
Yayar shi : Nandamuri Suhasini.
Kakan shi: N. T. Rama Rao .
Kawun sa :Nandamuri Balakrishna .
Wani Kawunsa kuma :N. Chandrababu Naidu .
Antin shi :Daggubati Purandeswari .
Dan uwan sa :Nara Lokesh .
Dan uwan sa kuma :Nara Rohit .
Wani dan uwan nasa :Taraka Ratna .

Share:

TARIHIN BIRNIN AUYO


Tarihin Tsohon birni 'auyo'.
Daga
Gaddafi Hussain Auyo
08149217486 da
Sadiq Tukur Gwarzo.
Garin Auyo tsohon gari ne, domin kuwa tarihi ya bayyana mana cewa Auyo na ɗaya daga cikin tsoffin birane kuma mashahurai a wannan kasa waɗanda sukayi sharafi har kuma ya zamo suna cin gashin kansu tun tsawon zamani daya gabata.
Haka Kuma birnin Auyo ya jima yana ɗauke da tsarin masarauta wadda sarakuna ke tafiyarwa cikin ka'idoji gami da lura.
Dangane da daɗewar Auyo, tarihi ya bayyana mana cewa ko lokacin da fir'auna Remesis II na zamanin Annabi Musa (A.S) yayi yekuwa tare da gangami daga manyan birane yana mai neman waɗanda suka kware akan sihiri da surkulle, a wannan karawar da tarihi ya ruwaito Firaunan yayi da Annabi Musa A.S, an samu cewa tabbas akwai matune a Auyo, har kuma wasu shahararru akan sihiri daga kasar Auyo sun halarci wancan taron tare kuma da jarraba tsibbace-tsibbacen su a wurin, amma daga bisani da Annabin Allah Musa yayi galaba akan ɗaukacin Masihirtan, ance suna cikin waɗanda suka gaskata Annabi Musa (A.S) kuma sukayi masa mubayi'a.
Har ila yau, akwai zance na gaskiya mai nuna cewar lokacin da tawagar wakilai daga kasar Borno a zamanin wani Sarkinsu da ake kira 'Maidinama' suka tafi birnin Madina domin su karɓo addinin musulunci a wajen Shugaba, Manzon Allah (s.a.w) har kuma suka tarar Manzon Allah yayi wafati sai Sayyadina Abubakar R.A ne ke Halifanci, har da mutanen Auyo acikin tawagar.
A wancan lokacin ance shima Sayyidina Abubakar ɗin yana fama da yakuna, don haka yace su zauna kafin a samu natsuwa, har kuma Allah ya karɓi rayuwar sa. Amma da fara Halifancin Sayyidina Umar R.A sai ya taso da maganar, ya haɗo rundunar sahabbai da littattafai suka taho Borno..
Kasar Auyo ta kasance mai daɗaɗɗen tarihi, domin kuwa anyi imanin cewa duk wasu garuruwa da ake alakantawa da hausa bakwai ko banza bakwai, to kuwa Auyo ta girme su.. A ciki harda Daura, domin dai abisa kiyasi na bincike an gano cewa Auyo tafi shekara dubu biyar da kafuwa.
Ance wani mutum mai suna 'Auya' shine ya kafa garin na Auyo, don haka daga sunan sane aka samo kalmar 'Auyo', kuma shi ɗan kabilar 'Bagirmine' waɗanda akace tun da jimawa suna zaune a arewaccin kasar Sudan.
Kasar Auyo tana da mashahuran malamai masanan addinin musulunci. Tarihi ya bayyana mana cewa daga cikin malaman da sukayi fice a kasar kano akwai da yawansu waɗanda asalinsu Auyakawane.
Garin Auyo yana ɗaya daga cikin garuruwan da anan baya-baya aka haɗe aka samar da masarautar Hadejia. Amma wannan gari sam ba koma baya bane acikin tarihin kasar Hadejia, kasancewarsa tsohon gari wanda ya daɗe da wanzuwa zamuna masu tsawo da suka shuɗe, gashi kuma sanan-nan gari daya tattara mutane masu baiwa iri daban-daban kama daga dakaru da baraden yaki zuwa uwa uba malamai mahardata alqur'ani mai girma.
Auyo ta jima ɗauke da masana masu ilimin taurari dana bugun kasa da masu lakkuna da sauran iliman asararu na tsaron kai da tsaron kasa, haka ma suna da mutane wadanda suka shahara wajen sihiri da surkulle irin na wancan lokacin. Don haka muna iya cewa ita tunjimin gari ne wanda kome mutum yaje nema yana iya samu..
Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form