HAPPY BIRTHDAY SHAMHARU 01

HAPPY BIRTHDAY SHAMHARU 01

Happy Birthday....
Happy Birthday, Happy Birthday, Happy Birthday Shamharu, Happy Birthday gwanina.

Da Sunanka Rabbana Tabara
Komai zanyi da sunanka zana fara 
Gani nazo Haiman bana gadara 
Waƙar murna ayau fa zana tsara
Gun Shamharu gamji kake sha sara
Baitocin nan daga zuci zana rera
Ya rabbana ara mini hikima domin na waƙe gwanina...


Tsira da aminci kullum ka ƙara
Ga Manzonmu Rabbana ka ƙara
Da Iyalansa a ciki duk ka tara
Da Sahabbansa ba ragi na ƙwara
Munyi murna har kuka munka fara
A bikin nan ba batu na kyara
Kowa yayo bushasha yau ne birthdayn gwanina...

Shi Shamharu tuni ya zarce tsara
Sha'aninsa yake yi ba gadara
Taimakon nan yana yi don ya tara
Dama zakara dole ne yayi cara
Ita ko kaza sai dai tayi kyarkyara
Ko ka ƙi shi ka sani ka makara
Ƙaryarku magauta baku iya ganin ƙarshen gwanina...

A fagen acting shi ne gwarzo zakara
Suna nasa an riga an zizara
Lamba na yabo gashi nan duka ya tara
Da ya Faso murmushi za'a fara
In ƙarya ne ku taɓo 'yan Zamfara
Yabon gwani dole ne ayi a ƙara
Lallai Shehu ya shanye tunanin su ɓauna...

Gani dai sayayyar Shamharu ta sa na zamto Tsara
Da wasu n min kallon hakanan sai kace sun hango shara
Amma saboda soyayyar shamharu gashi ayau in kun Lura
Faffaɗar tawaga fa na ja da na wuce sai dai Ƙura
Lallai Haƙiƙa Shamharu dole ne ace maka Sha-sara
Domin kuwa ka zam zaki wake batun wasu wai kura
Allaah ka kare min Shamharu wanda shi ne Gwanina...

Shamharu SRK ka bar maƙiya da masassara
Kana cin Shinkafa su ko ka bar su da Masara
Ko ba sa so dole ne a barka ka sarara
Kai ne tilo jarumin da ya wuce fassarar masu fassara
Masoyansa da mun gansa sai mu ji kamar an zuba Ƙanƙara
A cikin zukatanmu bamu ganin masu hantara
Yau mun ce Happy Birthday Shamharu sarki gwanina... 

A dalilin SRK ga shi yau na zamo tamkar Rarara
In dai akan Shamharu ne bani ma fahimtar Harara
Da zaku gane ku maƙiya kunga ai da kun Gyara
Tun da shi dai Shamharu da Rabbana fa ya Dogara
Magana ce dai ta kuɗi wanda dai tuni ya tara
In ko yin Kafce ne wannan ko kowa ya Sara
Allaah Raini Arɗo muna bayan abban Suhana...

Masoyanka a kullum ƙaruwa suke kamar ƙaburbura
Hakan yasa maƙiyanka suke ta Hattara
Mu ko sonka ya wuce ayo kankara 
Soyayya tasa wasu ma ke kiran Barira 
Da nufin ta taho ta biyo ta gidan su Furaira
A zaton su zaka ɗauki ɗaya a cikin su ka yo Ƙwarƙwara
Sun manta cewa dai Shamharu baya layin Jimina... 

Shamharu dai shi ba ya damfara
A Rayuwarsa ba ya yin zara 
Hakane yasa ya yo zarra 
A duniya tabbas ya fa shahara
In yayi tufka ba ya warwara
Mutum dubu shi kaɗai fa suke jira
Yana da masoya a cikin karkara
Yau ga 'yan birni na bulkara
Lallai Sarki ya gagara 
Maƙiyanka ayau sun botsara 
Don na ji su jiya wai suna mura
Salon Iskanci su suka Ƙirƙira
Daga ji kasan ba Fikira 
Ƙila ma yara ne 'yan taɓara
Waɗannan da suka bauɗe fanɗara

Hey....... Gwanina 

Ku kuma dangin 'yan takura 
Ƙiyayyar taku a fili ƙarara? 
Wai giwa ta faɗi a kakara
Naji har danginku kuke kira
Duk dai wai don ayi kangara
Ku sani shi Shamharu fa ya ɗara 
Walkin Ƙarfe tuni ya ɗaura 
Ku kira shi da dogo ɗan Daura 
Masu son yaƙi sai su ɗauro ɗammara
Don naga wasu sun jawo algarara

Haaaa.... Gwanina 

Ka ga ka cika 54 a wannan shekara
Kuma wannan alami ne na gangara
Domin daga nan sai furfura
Ya kamata a kama neman gafara 
Ga ayyukan laifi ayi kaffara
Allahu Ya Sa fa mu sam tsira
Roƙona ko yaushe Allaah Ya kauda asara
Sannan yayo shingen Ƙarfe a tsakani da fatara
A kullun ya zam a ci gaba da samun nasara

# HappyBirthdaySrk
# NASRUN MINALLAAHI ƘAREEB
# SRKUNIVERSENIGERIA
# SHAHRUKHKHANFANSNIGERIA 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

MRJ INVESTMENTS

Kasancewar na taso a Karkara, nayi Matuƙar sabawa da abincinmu na gargajiya. Amma da yake a birni nake aiki, dole take sa nake Maneji da ...

Blog Archive