Skip to main content

Posts

Showing posts from December, 2019

LABARIN NAN YANA ƊAUKE DA TAUSAYI SOSAI

Wani Labari mai ban tausayi
wasu iyalaine talakawa a wani kauye cikin pakistan sunada 'Da namiji Kwaya daya rak sun bashi ilimi na addini dana zamani ya zama shahararren ENGINEER yananan sai yasami wata attjira ya aura yananan a kauyen nasu tare da iyayensa sai nan take matarsa ta matsa masa tace ta gaji da zaman kauye, sai suka tattara nasu ya nasu suka koma birni ba da jimawa ba sai yaga wani talla ana neman Engineers a JEDDAH A SAUDI ARABIA kenan yaron kuwa yana da sa'a sosai sai yasamu aikin nan take ya koma can da aiki shekaru da dama yana turowa iyayensa kudi.

Gaba gaba dai kwata-kwata ya daina turo kudi kuma duk shekarar Allah sai yayi Hajj Ana haka sai ya fara mafarki a cikin baccinsa wani bawan Allah nace masa HajjINKA BA KARBABBIYA BACE.
sai abin ya dame shi yaje ya tambayi wani Malami wanda aka yadda dashi mai fassarar mafarki malamin yace masa yaje yaga iyayensa nan take ya hau jirgi sai pakistan da isarsa yaje kauyen nasu duk abubuwa sun canja masa, ba kamar yadda ya…

TARIHIN SARKIN MOROCCO MOULAY RASHID ISMA'IL

TARIHIN SARKIN MOROCCO, MOULAY RASHID ISMA'IL.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN. 08060869978
An haifi Moulay Ismail Rashid a wajajen shekarar 1646 a birnin Fez na kasar Morocco. Ya gaji mulkin Morocco ne tun yana da shekaru 26 a duniya bayan da ɗan uwansa mai mulki ya faɗo daga kan doki ya mutu. A wancan lokacin Moulay Ismail ya samu daular Moroco rarrauna saboda yawaitar faɗace-faɗace tsakanin kabilu gami da rikicin sarauta da yayi tsamari a daular. Baya da haka ma, birnin Marrakesh yayi bore ga shugabancinsa, inda mutanen garin suka shiga biyayya ga ɗan amminsa mai suna Ahmad ibn Muhriz. Don haka da fara mulkinsa, sai ya jagoranci runduna zuwa Marrakesh dake kudancin birninsa, ya faɗawa garin da yaki har kuma yaci nasarar kwace ikonsa, amma sai shugaban boren Ahmad bn Muhriz ya tsere ba tare da an kame shi ba. Sarki Moulay Ismail na ɗaya daga cikin sarakuna masu karfin iko waɗanda duniya ba zata taɓa mancewa da sunansu ba. Da fari dai, ya ɗauke cibiyar daularsa daga birnin Fez zuwa Meknes, …

TARIHIN TSOHON GARIN GANGARA DA YADDA AKA YI GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI

TARIHIN TSOHON BIRNIN GANGARA DA YADDA GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI.
SADIQ TUKUR GWARZO
Kirarin Garin: Gangara Ta Naturɓe, idan kaji ina kwana bako ne.. Sai dai Nyalli Jam. Wannan gari tsoho ne, jimawarsa kuma har takai wasu na ganin ya girmewa tsoffin birane misalin Malumfashi, Getso, Baɗari da birnin Kano. Fulani kabilar Natirawa ne akace suka kafa garin lokaci mai tsawo daya shuɗe, sannan labari na gaskiya ya dusashe dangane da tsohon birnin, ko kuma lokacin kafuwarsa, wanda a yanzu ya zama kufai, amma dai zuwa yanzu an iya gane sashen ganuwar tsohon birnin. Haka kuma marinar garin da tsoffin kukoki nanan a inda tsohuwar rayuwar Natirawan ta auku shekaru ɗaruruwa da suka gabata. Babban limamin Garin mai suna Mallam Adamu, ya bayyana mana cewar an samo sunan garin 'Gangara' ne daga kalmar 'Gagara', ko kuma ace garin daya Gagara acishi da yaki, domin tunda wannan birni yake babu wani sarki daya taɓa cinsa da yaki. An samu cewa garin Gangara na usuli shahararre ne, …

SUNAYEN ZAMANI

*SUNAYEN ZAMANI*
Gaskiya abin tir ne da ashsha dangane da yadda wasu musulmai suka kaucewa tsarin koyarwar addini, yana da matukar kyau mu dinga taka tsan-tsan wajen sanin kalar sunan da za mu raďa wa yaranmu, domin haqiqa suna yana tasiri a kan wanda aka sa ma wa, wato ya kan bi tsatsan asalin mai sunan, wannan shiyasa babu wasu sunaye da suka fi dace wa musulmi ya sa wa yaransa fiye da sunan *Annabawa* da *sahabbai,* da kuma sunayen da Annabi (SAW) ya yi mana suggesting irinsu *Abdullahi* da *Abdurrahman,* etc.  .
Amma su wasu musulmai a yau waďanda suka jahilci addini ko suka biye wa son zuciya gani suke a waďancan sunayen tsofaffi ne, _they were outdated,_ sai suka koma ga qago sunaye marasa inganci suna saka wa yaransu, wani ma sunan idan ka bi diddigin sanin ma'anarsa sai ka samu cewa suna ne na wani abin qi ko wani dabba ko dai wani abu da be dace da kimar ďan adam musulmi ba, wani sunan kuwa a fina-finai da littafai kawai ake tsakuro su sai a laftawa yaro, shiyasa sai ka ga y…

SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI?

*_SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI?_*

                       *Tambaya* Malam yaya zakkar ma'aikaci ya kamata ta zamo? Domin wasu ma'aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa zakkah to amma wasu sukanyi gini ko sayen filaye ko gonaki da kudin kafin shekara ta zagayo sun kare 

                           *Amsa* To dan'uwa, hukuncin wannan albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
staidai yana daga cikin dabarun da sharia ta haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa …

SO SANADIN RAYUWA

_*SO SANADIN RAYUWA*_ 
 _Tare dani_ _*Ibrahim so dole Sasha bhai Singh*_ 

Kashi na (( 01 ))

KASHE-KASHEN SOYAYYA.
Soyayya ta kasu izuwa gida uku kamar haka:
1 Soyayya Don Sha’awa. 2 Soyayya Don Abin Duniya. 3 Soyayya Ta Ha’ki’ka Ko Gaskiya.
1-SOYAYYA DON SHA’AWA: A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu. To irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.
2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA: Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya. Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a fara shirye-shiryen nesanta da juna.
3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA: Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da ba a gina ta a kan…

FAHIMTAR BANBANCI

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_
      _*💗KUNDIN MA'AURATA // 03💗*_ .              _*FAHIMTAR BAMBANCI*_ _Idan ya kasance ko yaushe maza ne a gaba, dole sai abin da suka ce a gida shi ne za a yi, abin da suka kawo kuma in ba a karba ba ya zama matsala, sannan mace ba ta isa ta yi aiki ba sai sun yarda, in ma suka ga dama sai ka ga sun han ta, tanan za a iya cewa sun yi kaka-gida sun qwace wa mace haqqinta, masamman in ya kasance alqalin da zai yanke hukuncin bai da basira, domin in muka koma baya za mu ga hatta wajen neman aurennan mace na jira ne sai an furta ana son ta, sannan namijin ya riqa zuwa gidanta zance ba ita ta zabo shi take zuwa zance in sun gama ta kamfato kudi ta bashi ba, hidimomin da ake yi har zuwa ranar daura aure duk ba ruwanta da su._ . _Macen duk da ta dauki nauyin wannan har zuwa daura auren, kuma ta ci gaba da daukar nauyin gidan ka je ka leqo abin dake faruwa, ka ga wanda yake da haqqin yanke hukunci a gidan, asali matsalolin da muke fama da su a yau, ba sa rasa n…

ZAGIN DA ME BADA UMARNIN SHIRIN FIM ƊIN KABIR SINGH YA KE SHA ZAI ZAMA ƘALUBALE GA DUK WANI MAI SHIRYA FIM

ZAGIN DA ME BADA UMARNIN SHIRIN FILM DIN KABIR SINGH YAKESHA ZAI ZAMA KALU BALE GA DUK WANI ME SHIRYA FILM:
By Abba India Dala.
Wannan Director Me Suna Sandeep Reddy Vanga Yayi Rubutu A Shafin sa Kan Rashin Jindadinsa Akan Wani Fyade da Akayi Har Yake Ganin Ayi Gaggawar Hukunta Wadanda Sukayi Amma Hakan yasa Yabar Baya da kura Domin Kuwa Da Yawan Mutane Suna Cewa Munafinci ne Yasa Shi Haka Dan Suna Ganin ya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Nunawa Jama'a Cewa Ba Wani Abu Bane ga Fyade Kamar Yanda Yayi A Wasu Fina-Finan sa Guda Biyu Watau ARJUN REDDY da KABIR SINGH ga Duk Wanda Ya Kalli Film Wadannan Fina-Finai da Zaka ga Cewa Ma Wasu Munanan Halin na Matasa Irinsu :- Shaye-Shaye, Rashin Ganin Girman na Gaba, Yawan Fushi da Rashin Daukar Shawara da Saurin Lalata Yara Yan Mata. Duk Wadannan ya Nuna Ba Wani Abu Bane Domin Duk ya Nuna su Acikin film dinsa Musamman na kwanan nan watau Kabir Singh Wanda Shiyasa Nima Film din bai min ba ta Fannin Labari. To Hakan ne Yasa Wannan Director yake ta Sh…

MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYA TA

*_MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN KISHIYATA?_*

                        *Tambaya:* Asslmu alaikum Mun kasance mu biyu awajen mijinmu, Sai ya kasance yar'uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar girkinta yakan shigo ya tara dani da rana ko da daddare, Tambaya anan shi ne malam shi hakan ya halasta? Kuma idan na mishi magana ya daina zuwa baya ji, ba gidan mu daya ba, Dan Allah hukuncin hakan da mafita?

                              *Amsa:* Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tun da hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a ranar kwananki da kwananta.
Saboda lokacin da Nana Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi ﷺ ya sake ta, ta dauki kwananta ta bawa Nana A'isha,kamar yadda Bukhari ya rawaito. Bayan haka Annabi ﷺ yana yin kwana dai-dai a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana mata kwana biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda ta sarayar da hakkınta.
Ya wajaba mai gida ya guji dukkan abin da zai kawo matsala da fitintinu a ts…

SHIN KANA AFUWA KUWA?

SHIN KANA AFUWA KUWA?
Mu karrama wadan da ke son mu, da daddadar kalma da kyakkyawan mu'amala, domin bamusan wanda mutuwa zata fara dauka ba a tsakaninmu.
 Saboda wallahi shaukin bayan mutuwa abu ne mai ciwo da zuciya take wahaltuwa akanshi !!!
 Inama banyi ma wane kazaba....  Inama nayi hakuri lokacin da tayi/yayi min kaza....
 Irin wannan shine galibin kalaman da zukata ke fadi yayin da rabuwa tashiga tsakaninmu da wadanda muke tare.
Rayukan mu, an halicce su domin su zauna na wani lokaci a duniya sannan su tafi.  Yi murmushi.
 Yi afwa. 
Yi sassauci, mance da laifi ko batanci da aka taba yi maka a duniya wannan mai gushewa ne.
A rayuwa za'a iya samun sabani amma matukar a hanyar Allah ake rayuwa,ya kamata ace anbar abinda ya faru ya wuce.... 
Mu sassauta lafuza yayin sabani da bacin rai muyi amfani da lafuza masu sauki.
Mu raka amsar uzuri, domin ko sautin fashewan glass yana da saurin gushewa sai dai kananun kwalaben kan jima mutum ciwo komai dadewa haka mummunar magana take zaka ji sa…

GWARZON NAMIJI 02

🌴**GWARZON=NAMIJI**🌴(02)

1=KAUNA --gwarzon namiji shine kadai ke nunawa mace kauna bawai soyayya ba don akwai gagarumin banbanci tsakanin kauna da soyayya,
Misali wanda yake kaunar ka shine kadai zai zauna dakai a kowanne yanayi kake,  shine wanda kana shiga wata matsala yana kara kaunarka, kauna itace me saka tausayi wanda duk wani yanayi da mutum ya shiga me kaunar sa bazai taba juya masa baya ba,  haka zalika shine zaiso 'yan uwar matarsa yaso 'ya'yanta, 
2 BIYAN BUKATUN MACE --wajen biyan bukatun iyalinsa kuwa baya bada uziri yakanyi duk yanda zaiyi don farin cikin iyalinsa, shine wanda baya dogaro da dukiyar matarsa, domin namiji baya zama gwarzo matukar matarsa tana daukar nauyin kanta kona yaransu komai kankanta, 

3 ME GAMSARDA MACE-- gamsar da mace lokacin saduwa yana karawa namiji kwarjini awajen mace akasin haka kuma yana kawo raini wanda wannan ba dabi'ar gwarzon namiji bane domin shi ya kanyi kokarin magance duk wata matsala da zata hanashi gamsar da iyalansa, …

GWARZON NAMIJI 01

🌴**GWARZON=NAMIJI**🌴 (01) Da sunan Allah me rahma me jinkai tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina farin cikin gabatarda wannan littafin tareda fatan zai amfanar da al’umma allah yasa albarka acikinsa
Akowanne zamani Allah yana kawo jarumai gwaraza wadanda suke sadaukar da farin cikinsu domin farin cikin iyalansu, daga cikinsu ne ake samun gwarzon namiji wanda duk yanda al'umma takai ga lalacewa tofa wadannan basa kasa a guiwa wajen nuna kyakyawar mu'amala ga iyalansu,
Akwai abu uku da gwarzon namiji yakeda wanda shine ma babba makasudin da yasa kowacce mace ke fatan samunsa, haka zalika sune abu mafi girma da mace keso wajen namiji,

_Zamu chigaba da yardar Allah..._
Rubutawa✍🏼 Tareda tsarawa= (Dr. Auwal Muhammad Azare)
Gabatarwa = (Usaini Amfanima) 
Daga *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp  Ga masu sha'awar shiga wan nan zaure sai su aiko da cikakken Suna ta WhatsApp zuwa ga lambar mu 07036073248 ta WhatsApp.

MATSALOLIN MA'AURATA DA KUMA MAGANIN SU

*_Matsalolin ma'aurata da kuma maganinsu ._* 
Tare dani _*Ibrahim so dole ...*_     
     _Kashi na 01_ 
    *Dacewa da juna ko rashin dacewa da juna.* 
Babbar matsala ta farko da ake samu a Rayuwar Aure shine idan ya kasance ka auri macen da bata dace da kai saboda daya daga cikin wadannan dalilai: 1. Macen da aka aura maka ita ba dan tana sonka ba, sai san anfi qarfinta a gidansu. 2. Macen da ka aura wacce ka tabbata dan abin duniya (kudi, suna, sarauta dss) ta aure ka. 3. Macen da kaima ba dan soyayya ka aure ta ba sai dan sha’awa, kyawunta, dangantakarta dss 4. Macen da kake tunanin ta aure ka ne kawai saboda bata da wani zabin. 5. Macen da bata gama yin hankali ba. Wadannan da ma sauran dalilai da yawa wanda sukan kawo rashin dacewa tsakanin ma’aura suna kawo babbar matsala a Rayuwar Aure, wanda yawanci sai bayan anyi auren ake gane haka, lokacin da an riga an makara da ayi wani gyara akai. Saboda haka ina kira garemu ‘Yan Mata da Samari mu daure mu yaqi zuciyoyinmu mu auri masoyan …

I've Made A Vow

I've made a vow...
I've made a vow,
to no one but you,
I pledge my love to forever be true,
I'll take care of you and treat you right,
I'll lay beside you all through the night,
I'll feed you and clothe you and keep you warm,
I'll hug you and kiss you and give shelter in the storm,
I'll help you and guide you and clear a path,
I'll protect you and shield you from an angry man's wrath,
I'll listen to your problems help you solve them too,
I'll make you a rainbow and let the sun shine through,
I'll take your side even if you're wrong,
Just to prove our love is strong,
I'll plant you flowers and make them grow,
They'll be a symbol of love that only we'll know,
I'll whisper your name when no one is near,
So low that only you can hear,
You'll feel my love even if we're apart,
You'll know that we are one in heart.
By : Vesta Sikora

LABARIN KYANWA DA ƁERA

LABARIN KYANWA DA BERA
Akwai wata itaciyar kuka a bayan wani gari. A gindin itaciyan nan akwai wani bera, a cikin kogonta kuma ashe akwai wani muzuru na kwana. Kukar kuwa cikin gonar wani mutum ta ke. Kullum dare sai muzurun ya fito ya je ya yi ta wa mutumin nan barna. Da mutumin ya ga haka, sai ya samo wata raga ya yi tarko, don ya kama kome ke shiga ke yi masa barna. Allah ko ya ba shi sa’a. Da asalatu ran nan muzurun ya ga beran, ya zabura zai kashe, zai ya fada cikin tarkon, ya yi ya yi ya fita, ya kasa. Bera kuwa da ya waiga ya ga tarko ya kame muzurun, sai ya yi rawa yana murna. Yana nan yana murna, ya duba haka cikin kara kusa da raminsa, sai ga wani maciji nan yana jira ya rabo da muzuru ya hadiye shi. Ya duba sama don ya hau, sai ya ga shirwa na kewaya, tana jira ya motsa ta fyauce shi. Bera ya tsaya, ya rasa inda za shi. Abu ya zama masa gaba siyaki baya damisa. Yana nan sai ya tuna wata dabara, ya ce, “Na san dai da maciji da shirwa ba mai iya zuwa kusa da muzuru. Yanzu ba abin…

MU LEƘA KITCHEN

LEMON DANYAR SHINKAFA DA DANKALI. Danyar shinkafa  Dankali  Dabino Madara  Sugar Citta Kaninfari  Falavor Yadda za ki haďa shi shi ne, idan kika sami Danyar shinkafa, wato ta tuwa .sai ki jika ta tare da dabinonki wanda kika rigaya kika bare, sannan daman Dankalinki ma kin rigaya kin bare shi, sannan kin yayanka yadda zai yi mi ki saukin markađe. To shi ma sai ki hada shi a cikin Danyar shinkafarki tare da dabinonki da Dankalinki, Bayan kin hada su guri guda dukkaninsu sannan kin sanya cittarki tare da Kaninfarinki, sai ki hada ki markađa.Bayan kin markađa.Bayan kin markađa kayanki, sannan sai ki tace, sannan sai ki kawo suganki ki zuba daidai yadda kike bukatarsa .sannan sai ki kawo Falavor ki zuba .Bayan kin gama hada lemonki kin ji komai ya yi miki daidai, sannan sai ki sanya shi a cikin gidan sanyi don karawa lemonki armashi ga mai🏠. 


FURA ME AYABA🍺🍺
INGREDIENTS: 1.Fura 3 idan manya ne kuma 2 2.Yoghurt 3.Peak milk 1 4.Banana 1
PROCEDURE: Ki samu fura mai kyau, ki zuba a blender, ki zuba y…