Skip to main content

Posts

Showing posts from 2020

FASSARAR WAƘAR SOORAJ DOOBA HAIN

FASSARAR WAƘAR SOORAJ DOOBA HAIN YAARON 

Waƙa: Sooraj Dooba Hain Yaaron
Fim: Roy
Harshe: Hausa 
Shekara: 2015 
Sauti: Amaal Malik
Rubutawa: Kumaar
Kamfani: T-Series
Rerawa: Arijit Singh & Aditi Singh Sharma & Amaal Malik 
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Matlabi… Ho Ja Zara Matlabi…
Son kai... Zamo mai son kai. 
• Duniya Ki Sunta Hai Kyun…
Me ya sa za ki saurari duniya? 
• Khud Ki Bhi Sun Le Kabhi…
Wasu lokutan ki saurari kanka ki mana. 
• Matlabi… Ho Ja Zara Matlabi…
Son kai... Zamo mai son kai. 
• Duniya Ki Sunta Hai Kyun…
Me ya sa za ki saurari duniya? 
• Khud Ki Bhi Sun Le Kabhi…
Wasu lokutan ki saurari kanka ki mana. 
• Kuch Baat Galat Hi Ho Jaaye
Babu wata matsala don kin faɗi wani abu mara kyau. 
• Kuch Der Ye Dil Bhi Kho Jaaye
Bar wannan zuciyar ta ɗan ɓace na wani lokaci. 
• Befikar Dhadkanein, Iss Tarah Se Chale
Bari bugun zuciyar da bai da damuwa ya tafi a haka. 
• Shor Goonje Yahaan Se Wahaan…
Har sai an jiyo sautinsa daga waccan kusurwa zuwa wannan. 
• Sooraj Dooba Hai Yaaron
Abokai, rana fa ta…

KALAMAI MASU DAƊI GA MIJI

SIRRIN MALLAKAN MIJINKI
Kalamai Masu Dadi Ga Miji
Yakamata ace mace tasan irin kalaman da zata rika furtawa a lokacin da take magana da mai gida.
Mata da yawa awajen iya magana da miji anbarsu abaya tayanda zakaga mace kafin ta auri miji ana soyayya sosai ko waya zatayi dashi saita nutsu bazata sake tayi shirmeba amma da zaran anyi aure an dan samu watanni sai kaga yanda zatayi magana da yayanta ko kaninta haka zatayiwa miji wanda azahirin gaskiya ba haka akeba ya kamata ya zama miji zance dashi na musamman ne kalamanki su zama na daban sautinki kasa kasa babu musu dashi ballantana ki karyatashi to baki iya zanceba tayaya zai zauna yayi hira dake?
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)
Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)
 Zauren Macen Kwarai
Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.

KALAMAI MASU DAƊI GA MIJI

SIRRIN MALLAKAN MIJINKI
Kalamai Masu Dadi Ga Miji
Yakamata ace mace tasan irin kalaman da zata rika furtawa a lokacin da take magana da mai gida.
Mata da yawa awajen iya magana da miji anbarsu abaya tayanda zakaga mace kafin ta auri miji ana soyayya sosai ko waya zatayi dashi saita nutsu bazata sake tayi shirmeba amma da zaran anyi aure an dan samu watanni sai kaga yanda zatayi magana da yayanta ko kaninta haka zatayiwa miji wanda azahirin gaskiya ba haka akeba ya kamata ya zama miji zance dashi na musamman ne kalamanki su zama na daban sautinki kasa kasa babu musu dashi ballantana ki karyatashi to baki iya zanceba tayaya zai zauna yayi hira dake?
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)
Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)
 Zauren Macen Kwarai
Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.

HANYAR MALLAKE ZUCIYAR MATARKA

*SIRRIN MALAKAN MIJINKI*
*Hanyar Mallaken Zuciyar Matanka*
Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu. 
Saboda haka mazajen da suke son ganin sun mallaken zuciyar matansu ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyi kamar haka;
1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha marasa kan gado ba.
2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.
3. KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin matansa, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zasu dunga burge matanka.
4. KIRKI DA…

KUNUN ALKAMA

KUNUN ALKAMA
yin kunun alkama bashida banbanci da yanda akeyin kowanne irin kunun saidai akwai gagarumin babanci wajen ciko nonon mace domin shi wannan kunun koda mace tana shayarwa zata iya shansa saboda zai temaka mata koda ta gama shayarwa nononta bazasu kankance su zama kananaba amma ba aso mace me cikin tarinka shansa...
yanda zakiyi alkamar zaki samu ki hadata da farar shinkafar tuwo da aya danya saiki jikasu zaki iya saka gyada danya saiki kayi markadensu idan an markada saiki tace kiyi kunu dashi kamar dai yanda kika saba dama kunu ko koko zaki iya saka kayan hadi don yayi miki kamshi kuma wadansu suna zuba madara aciki lokacinda za asha adadin yawansa kuma duk yanda kikeso zakiyi...

YANDA AKE KUNUN ALBASA

ga yanda zakiyi ki samu albasa ki yankata sannan ki dafata da zallan ruwa har sai ruwan yayi baki sai ki sauke ki tace albasar ki zubar saiki xuba xuma acikin ruwan sannan ki zuba garin gero ko kamu da garin alkama sannan ki xuba madara paek ko.nono ko kuma ki saka garin madara lu…

SARKI MALHANU DA 'YAN MATA

SARKI MAHLANU DA 'YAN MATA
A wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani mutum wanda yake da 'ya'ya biyu. Dukkan su yan mata ne, kuma sun isa aure.

Rannan sai wannan mutum ya tsallaka ruwa izuwa wani gari domin ziyara. Da isar sa sai yake jin labarin sarkin Garin wanda hamshaki ne yana neman aure, kuma an gwada dukkan yan matan garin amma basuyi masa ba.

Dawowar sa gida keda wuya sai ya sanar da iyalinsa. Babbar 'yarsa wadda sunan ta Mpunzikazi, tace zata je domin auren sarki.
Mahaifinta yayi murna da haka, ya turawa yan uwa da abokansa na arziki don suzo a rakata izuwa garin ta yadda zata zamo matar sarki, amma sai mpunzikazi tace tafi son a barta taje ita kadai.
Washe gari taci kwalliya ta kama hanya, tana cikin tafiya sai ta hadu da Bera. Bera ya matso gareta yace "kina so na nuna miki hanya?''. Sai kuwa mpunzikazi tayi tsaki, tace "gafara nan, waye kai da zaka nuna min hanya?"
Daga nan bata kara bi takansa ba ta wuce.
Shikuwa sai cewa yayi "indai a haka zaki to…

KURA DA KARE

Kura da KareGata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
Akwai wani mafarauci ana ce da shi Fautaranga, sai wata rana ya je gidan namun daji (dabbobin daji) ya ce da wa za mu farauta? Sai kura ta ce ni, sai ya ce da ita “dama ke nake nema”, sai suka tafi tare da kura. Suna cikin tafiya sai kura ta ce da shi tana jin yunwa, sai ya ce da ita ta bari sai sun ƙara gaba zai bata abinci.
Suna cikin tafiya sai suka isa wani kogi, sai ya ce da ita ta sha ruwa iya shanta. Da ta sha ta ƙoshi, sai shi kuma ya kafa bakinsa ya shanye dukkan ruwan kogin. Bayan ya shanye sai suka ɗebo kifayen cikin kogin suka cinye. Suna nan har dare ya yi, saboda haka da za su kwanta barci sai Fautaranga ya ce da kura “kar ki kwanta a bayana ina tusar ƙashi” sai kura ta ce bata yarda ba sai ta kwanta. Suna kwance can cikin dare sai kura ta ji ƙashi ya zo ya cake ta ya koma, sai ta tashi ta koma gabansa ta kwanta, da ta kwanta sai da gari ya waye sai kura ta ce da shi ashe dama abin da ka faɗa gaskiya ne ba ƙarya ba?
Daga nan…

SHARHIN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

SHARHIN FIM ƊIN ROWDY RATHORE 

Rowdy Rathore fim ɗin Indiya ne da aka fitar a cikin shekara ta 2012 a cikin harshen Hindi. Fim ne na faɗa, rawa, soyayya da kuma barkwanci. Sannan wannan shirin maimaicin wani shirin harshen  Telugu ne mai suna Vikramarkudu wanda aka fitar a shekara ta 2006. Na ba wannan shiri tauraro huɗu. 
MA'AIKATAN SHIRIN 
• Bada Umurni - Prabhu Deva • Ɗaukar Nauyi - Sanjay Leela Bhansali & Ronnie Screwvala • Rubutawa - Shiraz Ahmed • Labari - K. V. Vijayendra Prasad • Asalin Labari - S. S. Rajamouli • Sautin Waƙoƙin Shirin - Sajid-Wajid • Taken Shiri - Sandeep Chowta • Horas da 'yan wasa - Santosh Thundiyil • Tacewa - Aarti Bajaj • Kamfanin da ya shirya - UTV Motion Pictures &  Bhansali Productions • Kamfanin da ya yaɗa - UTV Motion Pictures • Ranar Fita - 1 June 2012 • Tsayin shiri - mintuna 143  • Ƙasa - India • Harshe - Hindi • Kasafi - ₹45 crores • Jimillar Kuɗin da ya kawo - ₹203.39 crores
Wannan fim an ɗauki mafi yawancinsa ne a Mumbai da kuma Hampi. A lok…

KWAƊI DA SARKIN SU

KWADI DA SRKIN SUGATANAN GATANANKU Wai wasu kwadi ne suke zaune a cikin wani tafki cikin jin dadi da walwala, ba abin da suka nema suka rasa, idan sun gaji da wasansu cikin ruwa sai su tsallaka kan tudu su sha iska. Ba su damuwar kowa, kuma babu wani abu da yake damun su. Suna nan haka sai wasu daga cikinsu suka ce, ina amfanin zamanmu haka babu wani Sarki da zai rika mulkinmu, ba mu da wasu dokoki da za su tafiyar da tsarin rayuwarmu.
Allah kuwa ya amshi addu'arsu! Ana nan wata rana sai wani dan guntun reshen bishiyar da take bakin tabkin ya karye, ya fado kwatsam a gefen tabkin. Kwadi suka tsorata suka fada ruwa da gudu. Sai wasu daga cikinsu suka ce ai Sarkin da suke roko a turo musu ne Allah ya turo musu. Kwadi na cikin ruwa suna jira su ji irin dokokin da Sarki zai shata musu, suka ji shiru, su kuma suna jin tsoron su matsa kusa da shi. Ana nan dai har wani mai karfin hali daga cikinsu ya matsa kusa da reshen itacen nan da ya fado, sannu-sannu har ya kai ga taba shi, icce bai mo…

FASSARAR WAƘAR RISE OF SULTAN

Fassarar Waƙar Rise Of Sultan

Waƙa: Rise Of Sultan
Fim: Sultan
Harshe: Hausa 
Shekara: 2016
Sauti: Vishal & Shekhar
Rubutawa: Irshad Kamil
Kamfani: YRF Music
Rerawa: Shekhar Ravjiani 
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
• Khoon Mein Tere Mitti
Akwai yashi a jininka. 
• Mitti Mein Tera Khoon
Jinin da ka zubar ma na cikin yashin. 
• Khoon Mein Tere Mitti
Akwai yashi a jininka. 
• Mitti Mein Tera Khoon
Jinin da ka zubar ma na cikin yashin. 
• Upar Allah Niche Dharti
Allah na samanka, ƙasa/duniya kuma ita ce a ƙarƙashin ka. 
• Beech Mein Tera Junoon
Kuma duk abinda ya wanzu a tsakiya ba komai bane face soyayyarka. 
• Re Sultan!
Ya Sultan! 
• Khoon Mein Tere Mitti
Akwai yashi a jininka. 
• Mitti Mein Tera Khoon
Jinin da ka zubar ma na cikin yashin. 
• Khoon Mein Tere Mitti
Akwai yashi a jininka. 
• Mitti Mein Tera Khoon
Jinin da ka zubar ma na cikin yashin. 
• Upar Allah Niche Dharti
Allah na samanka, ƙasa/duniya kuma ita ce a ƙarƙashin ka. 
• Beech Mein Tera Junoon
Kuma duk abinda ya wanzu a tsakiya ba komai bane face soya…

SARMA SARMA DUDUF

Sarma Sarma Du DufGata nan ga ta nan ku...
A wani a gari da akwai wata yarinya wacce tace ita baza ta aure kowa ba sai mara taba jikin shi!!! ko wani namiji ya zo wajen ta sai tace A’a yana da tabo a jikin sa.
Haka dai ko da yaushe take yi har watarana wasu doddani su biyu suka ji labari. Sai suka je gidan tururuwa suka yi wanka suka zama samari masu kyau.
Suka kama hanya sai garin da yarinyar take. Da suka isa sai suka karasa gidan su yarinyar. Aka yi masu sallama da ita ta fito. Da ta duba na farko ashe tururuwa ta chije shi a wuya dan haka sai tace ay shi yana da tabo. Sai ta duba jikin dayan sai taga babu tabo a jikin sa ko guda daya sai ta yarda cewa zata aure shi.
Suka yi aure sai ya kai ta gidan sa wanda suke zaune tare da maman sa. Ranar farko bayan sun kwanta bacci ita da kanwarta, sai kuwa suka ji a bakin kofa ana “sarma sarma du duf” ashe uwar mujin nata ce. yarinya: wane ne nan yake mana sarma sarma du duf?
uwar miji : uwar mijin ki ce taki miki sarma sarma du duf
yarinya: me kik…

MAGUNGUNA

MAGUNGUNA

ZUBAR RUWA A GABAN MACE.  YAYA ZA A MAGANCESHI?
Zaki iya samun garin hulba da ganyen magarya ki tafasa ruwan kirinka dunduma wajen wato kina zama aciki sannan kina shafa man zaitun Insha allahu za kiga amfanin maganin
Kokuma ki samu zuma da garin tafarnuwa da garin zogale da garin habbatussauda ki cakuda ki rinka sha sau3 akowace rana shima wannan yana aiki 

Kuma zaki iya dafa ruwan gishiri kina zama aciki ko kuma kina shan hulba da ruwa duk zasu iya miki amfani


Sannan zaki iya daka tafarnuwa kina zuba garin a abinci kinaci

HASKEN MA AURATA littafin auwal azare

GIZO DA ƘOƘI DA KANTU

Gizo da Ƙoƙi da KantuGata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
Wata rana ce dai, wata rana ce dai, da Gizo da Ƙoƙi da Kantu, suka shirya suka tafi daji farauta. A kan hanyar su ta tafiya, sai suka ci karo da ruwa. Da suka shiga ruwan nan don su tsallake shi, sai Kantu ya fara marmashewa, sai Gizo ya ce da shi, kai Kantu, idan ka ci gaba da marmashewa zan cinye ka. Shi ke nan, sai Kantu ya daure, suka ci gaba da tafiya. Can sun shiga tsakiyar ruwa, sai Kantu ya sake marmashewa, sai Gizo ya juyo ya cinye shi.
Bayan Gizo da Ƙoƙi sun tsallake ruwa, sai Gizo ya ɗaura lilo a gindin wata bishiya yana ta fillawa/hillawa. Can yana cikin lilo yana jin daɗi, sai ya hango wani damo, sai ya bi shi da gudu ya kama damon nan, ya yanka, ya gasa, ya hana ƙoƙi ko hanji.
Da Gizo ya koma ya hau lilonsa yana ta hillo, can sai ya ji cikinsa ya fara ƙugi, sai ya ce da Ƙoƙi cikinsa yana ciwo. Saboda haka sai Ƙoƙi ta goya shi dan ta kai shi gurin mai magani.
Ƙoƙi tana cikin tafiya sai ta zo gindin wata babbar bishiya…

GIZO DA NOMAN GYAƊA

Gizo da Noman GyaɗaWata rana Gizo da Ƙoƙi, abin duniya ya yi musu zafi. Sai Ƙoƙi ta ce da Gizo, “Ina ga da za mu yi noma da mun samu sauƙi”. Da Gizo ya ji haka sai ya ce, “Ƙwarai hakan ya dace”. Sai Ƙoƙi ta ce, “to me ka ke ganin zamu noma? Mu shuka shinkafa ne, ko alkama, ko kuma acca?” Sai Gizo ya ce, “a’a, mu shuka gayaɗa kawai”. Sai suka yarda akan cewa za su shuka gyaɗa. Amma ashe shi Gizo yana nufin ya yiwa Ƙoƙi wayo da wannan shawara tasa.
Da aka tashi yin shuka, sai Gizo ya ce da Ƙoƙi, ai ba a shuka gyaɗa sai an soya ta. Sai Ƙoƙi ta amince ta soya gyaɗa, ta baiwa Gizo ta ce ya je ya shuka. Da Gizo ya je gona dan yin shukar gyaɗa, sai ya ɗaura lilo a jikin bishiya, ya hau lilon nan yana cin gyaɗa, yana rera waƙa kamar haka:
……………………….
Da haka-da haka, yau ya je gona, gobe ya je, har wannan gyaɗa ta ƙare, ba tare da ya shuka ba.
Da damina ta yi nisa, sai ƙoƙi ta fara tambayarsa maganar gona, shi kuwa Gizo sai ya hau bada labari yana cewa, “Ai gonar nan ta yi kyau sosai”.
Da kakar gya…

ƘARIN NI'IMA

KARIN NI IMA
wannan hadin shine ake cewa kankanr jaraba wanda suka iyata ba a kwace musu miji  kema ki koya kiga yanda zaki tara ni ima
kawai ki samu kankana (water milon) me kyau saiki fere samanta da wuka ma ana kiyi mata kofa a sama saiki samu kanum fari (Clave) ki dakashi ki zuba acikin kankanar sai kuma ki samu dabino shima ki nikashi ki zuba a cikin kankanar sai kuma Kwakwa (coconut) kwallo daya ki fasa ki zuba ruwan a cikin kankanar sannan itama kwakwar ki gurzata ta zama gari ki zuba aciki kankanar shikenan kin hada saiki ajiyeta a waje me tsafta kamar firig bayan sa o i goma sha biyar (15 hours) saiki fara sha harya kare wannan yana aiki sosai....


HASKEN MA AURATA littafin auwal azare

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE
Shekarar Fita - 2012
 1. Jisne bhi yeh socha ki main dar gaya ... woh saala arthi pe apne ghar gaya 
Wanda duk yake tunanin na tsorata ne... To wawan shi zai koma gida a akwakwu. 
Akshay Kumar

 2. Don't angry me!
Kada ka fusata ni. 
Akshay Kumar 

 3. Naam sunte hi pichwaade mein bhukamp aa gaya na?
Ashe jin sunan ba kamar jin tsawa bane a mazaunanka? 
Akshay Kumar
 4. Sau saal zinda rehne ke liye sau saal ki umar zaroori nahi ... sirf ek din mein aaisa kaam kar jao ... jisse duniya tumhe sau saal tak yaad rakhe
Domin a rayu tsawon shekaru 100 ba ka buƙatar sai ka shekara 100... Ka yi wani abu a yini ɗaya... Ta yadda duniya za ta tuna da kai har na tsawon shekaru 100. 
Yashpal Sharma
 5. Pyar karne ke liye pechaan ki nahi ... dil ki zaroorat hoti hai. 
Ba ka buƙatar sanin mutum domin ka faɗa soyayya... Zuciya ka ke buƙata. 
Akshay Kumar 
 6. Meri sirf ek hi khawaish hai ... jab maut mere samne aaye tab main darra hua na lagon ... bas mera haath meri mooch ko t…

WAƘAR KUKAN SO

WAƘAR KUKAN SO 
RUBUTAWA: Jamilu Abdurrahman 
Rerawa: Lalo 
Shekara: Mayu, 2020 
Kukan so nake yi rabuwa ta mini rauni, mai sona ta guje ni wayyo.
Soyayya kun sani ta na da daɗi,  Ɗanɗanonta kun sani yana fa da garɗi,  Yanayinta in kana ciki sam bai da misali,  Barin ace ka samu ɗiya mai kyawun hali,  Tabbas rayuwa ta yi daɗi sai dai farinciki.
Mai Sona tana da kyawun hali ba muni,  Ga kyan suffa za ta birge ka in ka ganta,  Kwalliyarta ko Indiya ai sai an tona,  Muryarta kamar ta tsuntsuwa mai waƙa,  Shekaru mun ka ɗauka muna soyayya. 
Na nemi izini kuma dama har an bani,  Daga baya aka janye damar da aka bani,  Wai karatu za ta yi shi ya sa aka hanani,  Na yi mita na yi mita amma aka share ni,  Ashe gulma ce aka shirya a gareni. 
Da ni da ita juna mun amincewa,  Hakan yasa ruɗin zuciya mu ke kaucewa,  Tafiyar mu tana nan amma sam ba riba,  Babu halin in ganta bare ma mu yi magana,  Daga ƙarshe ta bayyana mini dukkan makircin. 
Wani laifi ne da akai na kisa aka ce ni ne,  Bayan bayani ya bayyana cewa ba ni ne…

FASSARAR WAƘAR TUJHE DEKHA TO

FASSARAR WAƘAR TUJHE DEKHA TO 
Waƙa: Tujhe Dekha To
Fim: Dilwale Dulhania Le Jayenge
Harshe: Hausa 
Shekara: 1995
Sauti: Jatin Lalit
Rubutawa: Anand Bakshi
Kamfani: Saregama
Rerawa: Lata Mangeshkar, Kumar Sanu
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
• Tujhe dekha to yeh jaana sanam
Yayinda na ganki, masoyiya ta sai na koyi cewa. 
• Pyaar hota hai deewana sanam
So hauka ne masoyiya. 
• Tujhe dekha to yeh jaana sanam
Yayinda na ganki, masoyiyata sai na koyi cewa. 
• Tujhe dekha to yeh jaana Sanam x2
Yayinda na ganki, masoyiya ta sai na koyi cewa. 
• Pyaar hota hai deewana Sanam x2
So hauka ne masoyiya. 
• Ab yahan se kahan jaaye hum
Yanzu ina zan je daga nan? 
• Teri baahon mein mar jaaye hum
Zan mutu a hannyenki. 
• Tujhe dekha to yeh jaana sanam
Yayinda na ganka, masoyina sai na koyi cewa. 
• Pyaar hota hai deewana sanam
So hauka ne masoyi. 
• Ab yahan se kahan jaaye hum
Yanzu ina zan je daga nan? 
• Teri baahon mein mar jaaye hum
Zan mutu a hannyenka. 
• Tujhe dekha to yeh jaana sanam
Yayinda na ganki, masoyiyata sai na koyi…

FASSARAR WAƘAR TUMERI

FASSARAR WAƘAR TERI MERI 
Waƙa: Teri Meri
Fim: Bodyguard
Harshe: Hausa 
Shekara: 2011
Sauti: Himesh Reshammiya
Rubutawa: Neelesh Misra
Kamfani: T-Series
Rerawa: Shreya Goshal & Rahat Fateh Ali Khan
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
Aa ..
• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil
Naka da nawa, nawa da naka, labarin soyayyar mu tattaura ne. 
• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye
Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 
• Ik Ladka, Ik Ladki Ki Yeh Kahani Hai Nayi
Wannan wani sabon labari ne akan Saurayi da budurwa. 
• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye
Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 
• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil
Naki da nawa, nawa da naki, labarin soyayyar mu tattaura ne. 
• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye
Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 
• Ik Dooje Se Hue Judaa, Jab Ik Dooje Ke Liye Bane
A rabe mu ke da juna, duk kuwa da cewa an halicce mu ne domin juna. 
• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil
Naki da nawa, nawa da na…

FASSARAR WAƘAR SATAKLI

FASSARAR WAƘAR SATAKLI 

Waƙa: Satakli
Fim: Happy New Year 
Harshe: Hausa 
Shekara: 2014 
Sauti: Vishal-Shekhar
Rubutawa: Irshad Kamil
Kamfani: T-Series
Rerawa: Sukhwinder Singh
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
MATASHIYA: ubangiji Krishna da Radha masoya ne na gaske a tarihin indiyawa, kuma su na daga cikin ababen bautawa a ƙasar.
• Radhe Radhe Bolo Jai Kanhaiya Lal Ki (x4)
Jinjina ga Radha da ubangiji Krishna!
• Ek Baari Milni Thi Mili Ek Baari
Sau ɗaya dama ya kamata ace na samu, kuma na samun. 
• Zindagi Hai Jaise Koi Ladki Kanwaari
Rayuwa kamar budurwa ta ke. 
• Pati Hi Na Yaaron Badi Line Maari
Na kasa yaudararta duk kuwa da na ƙoƙarta matuƙa. 
• Ab Lag Raha Hai Ye Ladki Atakli
Ga shi yanzu da alama budurwar (rayuwar) ta maƙale. 
• Satakli Re Satakli Ho Thodi Satakli
Yanzu kam na ɗan yi hauka. 
• Badle Jo Kismet Ke Ye Taare
Kamar yadda taurarin ƙaddara su ka canja.
• Satakli Re Satakli, Sakal Akal Satakli
Yanzu kam na ɗan yi hauka, fuska ta da ƙwaƙwalwa ta sun yi hauka. 
• Waah Waah Ji, Waah Waah Ji, Waah W…

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KAL HO NA HO

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KAL HO NAA HO 
Shekarar Fita - 2003
Aaj ... aaj ek hasi aur baant lo ... aaj ek dua aur maang lo ... aaj ek ansoon aur pee lo ... aaj ek zindagi aur jee lo ... aaj ek sapna aur dekh lo ... aaj ... kya pata, kal ho naa ho. 
Yau... Ki ɗan ƙara yin murmushi ɗaya yau... Ki ƙara yin wata addu'ar yau... Ki ɗan ƙara sha yau... Ki ƙara rayuwa yau... Ki ƙara ganin wani mafarki yau... Wa ya sani, ba lallai ne gobe ta zo ba. 
Shah Rukh Khan 
2. Pyar ka pehla kadam dosti hai, aur aakhri bhi ... bus beech ke kadam reh gaye hain. 
Matakin farko na soyayya shi ne abota kuma shi ne na ƙarshe... Matakan da ke tsakani ne kawai suka rage. 
Saif Ali Khan 
3. Tumhare paas joh hai tumhare hisaab se kam hai ... lekin kisi doosre ke nazar se dekho ... toh tumhare paas bahut kuch hai.  Abin da kike da shi kaɗan ne a ganinki... Amma da zaki kalle shi a matsayin wani can daban... Kina da abubuwa da yawa. 
Shah Rukh Khan 
4. Main aankhen band karta hoon toh tumhe dekhta hoon ... aankhen kholta …

SUN YAUDARE KA...

🚫 SUN YAUDAREKA DA CEWA KAI YARO NE KARAMI.
Daga malama Aisha isah.
Ku kyaleshi yaro ne karami. Ku saukaka masa yaro ne karami. Ku rabu dashi yaro ne karami 
Yana saba umurnin 'iyayensa, ya daga musu sauti, amma mutane suce a kyaleshi yaro ne karami.‼
Yana yawo da abokan banza, yaki dawowa gida sai cikin dare, idan kuma za'a hukuntashi mutane suce matashi ne zai daina yaro ne karami.‼
Baya sallah, yana karya sannan yana daukan kayan mahaifiyarsa ba tambaya, dukda haka sai ace arabu dashi yaro ne karami.‼
Haka muka lalace da daukan kura_kuran yarammu dana abokan arzikimmu a matsayin yarinta, Kalmar yarintan kuma 'ita taci gaba da basu lasisin yin abinda suka gadama.
A fayyace yake, wannan yaudara ce babba, ya jama'a musani shifa farawar shekarun samartaka shine farkon lokacin daura nauye nauyen shari'a ga yarammu, lokacine da mala'iku suke fara rubuta abinda suke aikatawa kuma za'a musu hisabi akansu. Kenan kuwa wadannan shekaru shekaru ne na hankali da nutsuwa da sh…

LABARIN YUSUF DA BALA

Yusufu da Bala
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
Akwai wasu yara su biyu; Yusufu da Bala, wata rana ana biki a gidansu, sai aka aike su su je daji su yanko yakuwar miya. A kan hanyarsu ta tafiya sai suka ci karo da wani ƙaton zakara da ganga rataye a wuyansa. Sai zakaran ya tambaye su, “Yara-yara ina za ku je ne?”, sai suka ce da shi, “Za mu je mu yanko yakuwa ne”, sai ya ce, “Na yi muku ɗan kiɗa ku ji?”, sai suka ce, “e”, sai ya fara”.
Tamagungun-tamagungun muƙut sai ya haɗiye su.
Can a gidansu yaran kuwa, aka ga yara sun jima basu dawo ba, saboda haka sai iyayensu mata suka bisu, sai suma suka haɗu da wannan zakara. Da zakara ya gansu kawai sai ya fara waƙa:
Zakara: Ku-ku-ku ina za ku, tarmanamana Mata: Neman ‘ya’yanmu za mu tarmanamana Zakara: Su ‘ya’yan ina za su, tarmanamana Mata: Ɗiban yakuwa za su, tarmanamana Zakara: Ɗiban yakuwar mene, tarmanamana Mata: Ɗiban yakuwar taushe, tarmanamana Zakara: In yi muku ɗan kiɗa ku ji? Tamagun-tamagun, muƙut sai ya haɗiye matan suma.
Da jama’ar gar…

YARINYA DA ƘAWAYENTA

Yarinya da ƘawayentaGata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
Wata ce dai, wata ce dai, za su tafi wasan kalangu wani gari mai suna Dahira da ita da ƙawayenta. Sai ta je gurin ummarta, ta ce da ita ta bata zaninta za su je wasa. Sai ummar tata ta ce ba zan ba ki ba sai kin samo min ‘ya’yan ɓaure. Shike nan sai ta tafi daji, ta je gidindin ɓaure ta ce da shi:
Yarinya: Ɓaure, ɓaure gareka na zo. Ɓaure: In ba ki me? Yarinya: Ka ba ni ‘ya’ya. Ɓaure: Ki kai wa? Yarinya: In kai wa inna. Ɓaure: Ta ba ki me? Yarinya: Ta ban zani na, mu je mu wasa a Dahira.
Da ɓaure ya ji abin da yarinya ta ce, sai shi ma ya ce ba zai bata ba sai ta kawo masa kashin shanu, ta zuba masa taki. Daga nan sai ta tafi garke. Ta je ta samu shanu ta ce da su:
Yarinya: Shanu, shanu gurinku na zo. Shanu: Mu ba ki me? Yarinya: Ku ba ni kashi. Shanu: Ki kai wa wa? Yarinya: In kai wa ɓaure, ya ba ni ‘ya’ya na kai wa inna, ta ban zani na mu je mu wasa a Dahira.
Sai suma shanu s…

SIRRIN GANYEN GASAYA

SIRRIN GANYEN GASAYA

bayan kin wankeshi saiki dakashi sannan ki debo kamar cokali biyu ki hada da zuma me kyau cokali daya

sannan saiki zuba akan farin kyalle me tsafta ki zuba akayi

saiki nadeshi kamar yanda ake nade laya
to ana bukatar kisamu wando (pant) me tsafta ki saka aciki amma idan kin lura da photon anaso wajenda yake naso ya zama shine a gabanki

bayan kin saka wandon anaso yakai kamar sa o i goma ko fiyeda haka to saiki cire ki wanke wajen da ruwan dumi shikenan kin gama saiki jira haduwa da oga kiga sumbatu ranar dandanonki daban yake wannan saikin gwada kinji


HASKEN MA AURATA littafin auwal azare

HANYAR DA ZA KI GYARA JIKINKI

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Hanyar Da Zaki Gyara Jikinki, laushi da Haske_*
Yar uwa gyara jiki wani abu ne mai mahimmanci ga mace domin yana haifar mata da hasken jiki da kuma gamshi a jikinta don nishadantar da abokin zama.
Abubuwan da zaki nema sune kamar haka;
* Sabulun salo * Sabulun ghana * Lemun tsami * Kur kur *Bayani;* Sai ki hada sabulan wuri guda da kur kur din sai ki juya kadan sai ki dauko lemun tsaminki sai ki matsa a ciki kar yai yawa sai ki cigaba da juyawa har sai ya hade sai ki dunga wanka da shi, bayan kin fito wanka sai ki sami man ridi ki dunga shafawa, da yardan Allah zaki ga yadda zai gyara miki jiki, fatanki ta rinka sheki da sulbi.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*