Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2020

WATA MATA TA KASHE MIJINTA A MALUNFASHI

Da dumi duminsa jami'an yansanda dake karamar Hukumar malunfashi a jahar katsina sun damke wata mata yar shekara 19 da laifin kashe mijinta har lahira. Matar mai suna rabi Shamsudeen ta kashe mijnnatane mai suna Shamsudeen salisu dan shekara 25 da misalin karfe 4:00am na safiyar litinin tahanyar daba masa wuka. Lamarin yafarune a wani kauye mai suna danjaku dake karamar Hukumar malunfashi. Mai magana dayawun yansandan jahar katsina ne malam SP Gambo musa ne ya bayyana hakan a yayin ganawar shi da manema labarai Yace a biciken da sukayi basukai ga gano dalilin dayasa ita mai laifin ta aikata kisanba amma dai zasuyi bincike. Makwaftan Shamsudeen nedai suka jiyo ihunsa suka fito suka same shi rike da cikinsa yana Cewa ku taimake ni a YAYINDA ita kuma rabi take rike da wuka da jini a hannun ta to Allah ya kiyaye ya kumasa mufi karfin zuciyoyinmu. Ameen

KO DA GASKE ZA A ZARTAR DA HUKUNCIN RATAYE MARYAM SANDA?

SHARHI: Ko Da Gaske Za A Tabbatar Da Hukuncin Rataye Maryam Sanda?
Daga Datti Assalafi
Abinda kowa ya kamata ya fahimta shine kafin a zartarwa Maryam hukunci tana karkashin beli ne, wato ba'a gidan yari take tsare ba, an bayar da belinta, wallahi wasu kwanaki da suka gabata da idona na ga Maryam Sanda da Mahaifiyarta da 'dan da ta haifa, da kanin mijinta marigayi Bilyaminu a wani guri a cikin garin Abuja, har nayi zaton cewa an kammala Shari'ar gaba daya.
Da aka zo zaman kotu a yau, bayan da kotu a matakin Federal High Court ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai alkali ya bayar da umarni a tafi da ita gidan yari kafin ranar rataya ya cika, sai dai dokar gwamnatin Nigeria ya bata damar daukaka kara zuwa Court of Appeal har zuwa Supreme Court.
Hukuncin High Court ba shine karshen al'amari ba a halin da Maryam Sanda take ciki, akwai matakin sake zama a kotuna guda biyu da na fadi a sama, hatta Alkalin da ya zartar mata da hukuncin kisa a yau sai da ya …

NI MUSULMI NE, MATATA HINDU CE, YARANA KUMA INDIA CE

Daga Salim Idris 

"Matata mabiyar addinin Hindu ce, ni musulmi neh, 'ya'yanmu kuma qasarsu INDIA ita ce addininsu" cewar Jarumi Shahrukhan
Jarumin wanda akewa laqabi da KING OF ROMANCE ya jima ba'a ganshi a fim ba tun bayan fitar fim dinsa ZERO wanda AANAND L RAI ya bada umarni. Fim din bai yi abin kirki à kasuwancinsa ba wanda yasa tun daga lokacin Shahrukhan bai fadi fim din da zaiyi nan gaba ba.
An ga jarumin kwanan nan ya fito a wani shiri da akeyi na talabijin mai suna DANCE PLUS 5 yana magana akan addini. Shahrukhan yace basa yin hirarraki akan addini a gida tare da iyalinsa. Ya qara da cewa indai yazo cike gurbin addini a fom din makarantar 'ya'yansa, INDIA yake rubutawa a wajen. 
An sha jin jarumi Shahrukhan à baya yana cewa suna yin bikin kowane addini a gidansa kuma basa banbancewa.  Daga qarshe jarumin yace "Ni ba mai yin sallah biyar a rana bane amma ni musulmi ne. Na yadda da abubuwan da addinin musulunci yake koyarwa kuma na yadda addini ne …

TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYI IBN BATTUTA Kashi na Uku.

TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYI IBN BATTUTA
Kashi na Uku.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
Bayan Ibn Battuta ya kammala aikin Hajjinsa, sai kuma ya ɗaura harami ya shiga cikin wani ayari mai tafiya kasar Iraqi. Daga can kuma bayan ya huta sai ya wuce zuwa Iran, a inda babu jimawa ya sake tattaro kayansa ya biyo ayarin mahajjata, sai gashi a saudiyya.
Daga nan bai zame ko ina ba sai gabashin afirka, inda yayi kara-kaina, ya zagaya kasashen larabawa ta kudu, sannan ya sake ɓulla kasar saudiyya.
A wannan karon ma bai jimaba, sai yabi tawagar wasu matafiya, kwanci tashi sai gashi a Misira. Ya sauka yayi 'yan kwanaki, sannan ya tashi izuwa kasar syria, a inda babu jimawa ya tsallaka babban teku ya dira a Crimea.
Anan ne kuma tafiyar Ibn Battuta ta mika izuwa yankin Asia, inda ya shiga kasashen Khwarizm, Bukhara da Afghanistan, sannan ya tsallaka tsohuwar daular musulunci data kafu a Delhi ɗin kasar India.
Ibn Battuta ya shafe shekaru biyu a Delhi yana rike da mukamin alkalin alkalai. Daga nan yaji taw…