Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2020

TAMBAYA TA 014

*RAMUWAR AZUMIN FARILLA A SHARI'A*
Salam shin ya alatta mutum ya ringa skiping yayin yin rankon azummi? Misali kana yinshi litinin da alhamis kuma ranko ne.
AMSA
Wa'alaikumussalaam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh. Babu laifi akan hakan shine abin da mafi yawancin mallamai suka tafi a kai wanda yake da ramuwa na azumin Ramadan yayin da zai rama su, ba dole sai ya yi su a jere ba, saboda fadin Allah(SWT):
(فمن كان منكم مريضا أو على سفر فعدة من أيام أخر)
Wanda ya kasance daga cikin ku bashi da lafiya ko a hali na tafiya to sai ya biya adadin a cikin wasu kwanuka na dabam.
-Haka an ruwaito daga Aisha Allah Ya kara mata yadda tace da an saukar da àyar
(فعدة من أيام أخر متتابعات)
Sai aka goge kalmar (متتابعات)
-Haka an ruwaito hadisi daga Abdullahi binu Umar (RTA) Ya ce manzon Allah(SAW) yace: (أن النبي صلى الله عليه وسلم قال في قضاء رمضان إن شاء فرق وإن تابع)سنن الدارقطني.
Manzon Allah(SAW) ya ce: Wanda yake da ramuwa na azumi idan ya so ya yi su a jere idan ya so ya yi su a rarrabe. والله تعالى …

TAMBAYA TA 015

*HUKUNCIN YIN ALKUNUTU SABODA CUTAR CORONA ?*
*Tambaya* Assalamu Alaikum Meye hukunci yin Alkunut saboda Annobar coronavirus ?
*Amsa* Wa alaikum assalam
Babu nassi bayyananne yankakke wanda yake nuna ana yin Alkunutu idan cuta ta yadu a gari, saidai Malaman Shafi'iyya da Kuma wasu daga cikin malaman hanafiyya da Hanabila suna ganin Mustabbi ne yin Alkunutu idan ciwo ko bala'i ya sauka, ya kuma gama gari saboda Annabi (SAW) ya yi Alkunutu ga abokan gaba lokacin da suka kashe makaranta Alqur'ani, ita ma Kuma gama-garin cuta idan ta sauka a gari tana jawo rasa rayuka da dukiyoyi, hakan sai ya nuna hukuncinsu daya. Sannan lokacin da Annabi SAW ya zo Madina ya samu wasu cututtuka a cikinta har wasu Sahabbai ma sun harbu kuma ya yi addu'a Allah ya dauke su, hakan sai ya nuna ana iya yin addu'a saboda neman dauke Musiba, ita Kuma Alkunutu addu'a ce.
Don neman karin bayani duba Almugni (2/115) da Al'ashbahu wan naza'ir na Ibnu Nujaim (372) da Mugni Almuhtaj (1/242) .
Z…

ZUWA GA 'YAR UWA TA

*Zuwa ga 'Yar uwata 🧕🏾*
Haqiqa Allah Maďaukakin Sarki Shi ne Mai azurta bayinsa a dukkan lokacin da Ya so, kuma idan Ya ga dama sai Ya amshi abin sa a dukkan lokacin da Ya so. 
◽Wasu an haife su a gida ko a dangi na talakawa, amma sai Allah Ya azurta su kuma Ya ďaukaka darajarsu. 
◽Wasu kuwa sun fito daga manyan gida, ko sun yi tashen dukiya da ababen duniya, amma lokaci guda Allah Ya amshi dukiyarsa su ka koma marasa komai kuma sunansu ya shuďe a tarihi.  .
To 'yar uwa idan har kin yi imani cewa Allah Shi ke da arziki da talauci, to me zai sa ki damu kanki ko ki qaqaba wa zuciyarki cewa dole sai mai kuďi za ki aura?! Ba ki tunanin cewa koda kin samu mai kuďin Allah Zai iya talauta shi? Ba ki tunanin ki faďa hanun azzalumi mara addini da kyawawan halaye? 
Lallai dai yana da kyau ki zauna ki sake tunani, domin shi aure ibadah ne ba kasuwanci ba, idan mutum ya zo neman aurenki, to abin da ake so ki duba shi ne addininsa da kyawawan ďabi'unsa, kuma ya kasance yana da sana'a k…

GASKIYAR ZANCE

*GASKIYAR ZANCE 👌*
20 Jan, 2019.
Zaune take a gidan iyayenta cikin walwala, lumana da kwanciyar hankali, ba rashin ci babu rashin sha, ba rashin sutura ballantana matsuguni. A koda yaushe tana kallon iyayenta tana kara samun sakewa, tana ganin 'yan uwanta tana samun nishadi, ba ta rasa komai ba na daga kulawa daga wajen iyaye da 'yan uwa, sun ilimantar da ita, sun ba ta tarbiyyar da ya dace gwargwadon iyawarsu. Tun tasowarta ta taso ne a cikin iyayenta da 'yan uwanta, idan ta shiga damuwa za su share mata hawayenta. A lokaci daya ka zo ka kwallafa ranka a kan sai ka aure ta, iyayenta suka yarda suka ba ka ita ba don sun gaji da ita ko don sun rasa abin da za su ci gaba da yi mata hidima ba, ita ma ta amince ta bi ka gidanka ta ci gaba da rayuwa da kai, ta sadaukar da debe kewar iyayenta da 'yan uwanta don saboda ta rayu da kai, ta amince ta zama uwar 'ya'yanka, ta yarda ka san inda babu wanda ya sani a jikinta, ta yarda ta kare rayuwarta a gidanka, ta yarda ta z…

Tambaya ta 013

Is it Not Allowed To Marry in Muharram? – 
Dr Murtaza bin Baksh
Our brother's question is:  My friend is about to get married in [the month of] Muharram. 
His friends and relatives are saying that he shouldn‘t get married in Muharram as it is prohibited. Brother, why shouldn't we get married in Muharram? Dr. Murtza bin Baksh (hafidhahullaah): The individuals that prohibit getting married in Muharram are the Rafidi [extreme] Shi‘a. They don't get married in Muharram and more specifically in the first 10 Days. They are Ahlul-Bid'ah [people of innovation] and deviance. The meaning of Bid'ah is without any textual evidence [from the Book of Allah or the [Authentic] Sunnah] starting a new practice [as a form of worship]. Nikkah [marriage] can be performed at any time of the year. The only exception being when someone is in the state of ihraam [performing Hajj or Umrah] at this time it is Haraam [impermissible to perform a nikkah]. Other than this time, if you wish to get marrie…

JIKIN ƊAN ADAM 04

*بسم الله الرحمن الرحيم**_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 04🍍🍊*
*(Fitowa ta Hudu)*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
Baya ga wadancan azumummuka da suka wajaba ga dan adam masamman ma azumin Ramadan, akwai kuma wadan da ba su zama dole ba, su kam ya danganta ne da neman kusancin mutum ga Ubanjinsa, ta iya yuwuwa na kwana daya ne rak kamar azumin Arfa, ko Tasu'a ko kuma Ashura, ko na kwana biyu a mako, wato Litini da Alhamis, ko na kwanaki uku a wata, ko ranakun da ake farin wata 13, 14, 15, akwai kuma na watanni masu alfarma, hadisai sun tabbata cewa Annabi SAW yã riqa yin azumin Sha'aban sama yadda yake yi a sauran watannin in ba Ramadana ba.  
Ga kuma azumin kwana shida na Shawwal, sai kuma azumin tsallake kwana guda-guda wanda ake yi wa laqabi da azumin Dawoud AS, wannan yana nuna yadda mutum zai iya kasantuwa a cikin azumi koda yaushe domin neman…

ADDU'A GA MAMACI 02

ADDU'A GA MAMACI0⃣2⃣
📘 SHIN ZA'A IYA YIWA MAMACI ADDU'A BADA ABUNDA YAZO A HADISI BA??     Abunda akafiso kuma yafi falala shine yiwa mamaci Addu'a da abunda yazo ahadisi ingantacce, saboda shi manzon Allah anbashi jawami'ul kalim, amma babu laifi mutum ya rokawa mamaci da duk abunda ya sawwaka masa, domin wannan babi yanada yalwa, matukar dai bazaiyi addu'ar da shirka ko zalunci ba, misalin irin wadannan addu'o'in sune kamar  ١. اللهم عامله بما أنت أهله ولا تعامله بما هو أهله ٢. اللهم اجزه عن الإحسان إحسانا وعن الإساءة عفوا وغفرانا ٣. اللهم اجعل قبره روضة من رياض الجنة ولا تجعله حفرة من حفر النار  ٤. اللهم يمن كتابه ويسر حسابه وثقل بالحسنات ميزانه، وثبت على الصراط أقدامه، وأسكنه في أعلى الجنات في جوار نبيك ومصطفاك ٥. اللهم آنسه في وحدته، وآنسه في وحشته وآنسه في غربته Dama wasu makamantar wadannan, duka ya halasta mutum yayi. 
📙 WANDA ZAISA MAMACI ACIKIN KABARINSA MAI ZAICE??      Alokacin da mutum zai kwantar da mamaci acikin kabarinsa abunda Shari'a ta…

ADDU'A GA MAMACI 01

ADDU'A GA MAMACI 0⃣1⃣
Kafin kutsawa kai tsaye ga hukuncin yin add'ua ga mamaci, da kuma abubuwan da suke iya riskar mamaci bayan mutuwarsa na daga aikin bayi, zanso in danyi tsokaci akan wasu hukunce hukunce da suka shafi abubuwan da mara lafiyan da ya cire tsammani zaiyi da abunda masu jinyarsa zasuyi, dama sigar yadda ake ta'aziya da kalan addu'o'in da za'ayiwa mamaci, in sha Allah. Ina rokon Allah ya datar dani. 
📕 WANDA YAJI ALAMAR MUTUWA ME ZAIYI??        Alokacin da mutum yaji alamu na cewa rayuwarsa tazo karshe ko kuma rashin lafiya ya tsananta masa takai ga har yafitar da rai, to yana wajaba akansa da yayiwa iyalansa wasiya da jin tsoron Allah da kuma riko da addinin Allah, da nisantar shirka kamar yadda Annabin Allah yaqub Alaihis salam yayi (Baqara 133). Sannn yayi kokarin hanasu aikata duk wani abu na sabo da yake tinanin zasu iya aikatawa bayan mutuwarsa koma adalilin mutuwarsa.           Sannan bayan nan sai ya shagaltu da ambaton Allah, musamman Kalma…

Tambaya Ta 012

Tambaya :
Slm Dan Allah mlm mene Hukunci wadda take karin gashi

Amsa :
Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala Rasulillah wa'ala ahlihi wasahbihi waman walah. Bayan haka :
Haramun ne yin ƙarin gashi , sabida faɗin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam : ( Allah ya tsinewa Mai ƙara gashi da wadda ta nemi a ƙaramata , da mai yin wushirya da wadda ta nemi ayimata.) Bukhari ya rawaito 
Daga Jabir Radiyallahu anhu yace : ( Manzon Allah ya tsawatar akan waɗanda suke ƙara wani abu a jikin gashinsu ) Muslim ya rawaito.
Kuma koda gashinta ne Wanda ta taje idan ta ƙara ta shiga ƙarƙashin wannnan hukuncin.
Malamai Hanafiyya da Malikiyya da Shafi'iyya sunyi bayani ƙarara akan haka.
" Yin ƙarin gashi da gashin ɗan Adam haramun ne , koda kuwa mutum gashinsa ya ƙara dashi ko gashin wani"  الفتاوى الهندية 5/358 حاشية ابن عابدين 6/372
Malam Adawiy yace : " faɗin Manzon Allah ( Allah ya tsinewa mai ƙarin gashi) yana nufin wadda take ƙara wani akan gashinta , nata ko na wani ..." حاشية على ش…

BURABUSKO

*BURABUSKO*

KAYAN DA ZA KI TANADA
1. Gero  2. Mai  3. Gishiri
YADDA ZA KI HADA Ki sami gero ki wanke shi ki rage domin tsakuwar ta fita, sai ki shanya ya bushe. Idan ya bushe sai ki kai a barzo miki a inji. Ki dora ruwa a kan wuta kamar rabin tukunya, sai ki kawo madambaci ki dora akan tukunyar, ki shimfida buhun algarara ko kuma jarida akan madambacin. Sai ki kawo barzazzan geronki da kika bakace kika fitar da dusar ki zuba a cikin madambacin, ki yayyafa ruwa akai. Idan kina so ma kina iya jika kanwa ‘yar kadan ki yayyafa ruwa akan geron saboda ya yi laushi sosai. Sai ki bar shi ya turaru. Idan ya dauko turaruwa zaki ga ya fara curewa, sai ki sauke daga kan wuta ki zuba mai da gishiri ko magi ki mitststsika domin ya warware. Sai ki rage ruwan daya ke cikin tukunyar ki bar shi dai-dai yadda zai yi miki. Sai ki dauko turarren geronki ki zuba a cikin ruwan, sai ki dan juya kamar kina rude, amma wannan da kauri. Sai ki kawo leda ki rufe, sannan ki kawo murfin tukunyarki ki dora akai. Idan ya y…

PROHIBITION OF DECEIVING OTHERS

Prohibition of Deceiving others 
Abu Hurairah (May Allah be pleased with him) said: The Messenger of Allah صلى الله عليه وسلم said, "He who takes up arms against us is none of us; and he who cheats us is none of us.'' [Muslim]. 
     Another narration of Muslim is: The Messenger of Allah صلى الله عليه وسلم happened to pass by a heap of corn. He thrust his hand in that (heap) and his fingers felt wetness. He said to the owner of that heap of corn, "What is this?'' He replied: "O Messenger of Allah! These have been drenched by rainfall.'' He remarked, "Why did you not place this (the drenched part of the heap) over the corn so that people might see it? He who deceives is not of us.'' 
Commentary: 1. To take arms here signifies to revolt against the Muslim community (and a Muslim government, for that matter) or draw a sword, gun, etc., to kill a Muslim - a common practice in the present-day terrorism. 
2. Forgery and deceit have two different…

SIRRIN SOYAYYA DA BAZAWARI

Mata, Ga Sirrin Soyayya Da Bazawari:
Ita ma macen da take soyayyar aure da bazawarin da yake da mata daya ko fiye a gidansa, macece datafi sauran matan da muka ambata a baya aiki tukuri domin ganin ta samu shiga wajen manemin nata har kuma tayi sa'a amincewarsa ta zama matarsa ta aure.
Duk da yake wasu mata na ganin cewa auren mace mai mata yana da matsala da kuma wuyar gaske, ni kuma anawa ra'ayin da kuma nazarin ba haka abun yake ba, matsalar da mata suke fiskanta dai kwai shine, basusan sirrin soyayya da mazan da suke da mata a lokacin da suka zo neman auren suba. Shi yasa 'yan mata da damar gaske suke daukar cewa maza masu mata basu da dadin soyayya kokuma rashin sanin yaddazaki tafiyar da shi yasa ki rasa shi.
Sirrin duk wani namijin da yake da mace a gida ko yake da mata kuma ya fito yana meman kara wani auren shine, yana da dalilin daya sanya yake sha'awar kara wannan auren kuma yace ke yakeso ki zama matar tasa dai zai kara, to yana da kyau kiyi kokarin sanin dali…

HANYOYIN RAGE ƘARNI A KITCHEN

*Mieererh's Kitchen* 🥙🥗🥬🌮🍲🍝 HANYOYI 1⃣0⃣ MASU SAUKI DA ZASU RAGE MIKI.KARNI A KITCHEN
1⃣Yana da kyau ace mace ta ware roba kara dazata dinga fasa kwai sannan ki ware cokali ma yadda duk sanda zaki abinda ya shafi kwai da ita zaki using 2⃣Ki ware roba babba ta wanke nama ko kifi duk sanda zaki amfani dasu da ita zaki 3⃣Ki ware tukunyar tafasa nama ko kifi ko ganda da kayan ciki ya zamana ta abinci da ta miya daban 4⃣Kisai tukunya ki barta ta dafa shayi karki dafa komai sai shayin saboda gujewa karni Idan anci kifi ko abin karni  5⃣Ki daina sa soso direct kina wanke kwanon zaki zuba omo a kwanon sai kisa hannu a hankali ki fara wankewa 6⃣Ki dinga zubawa ruwan zafi omo kina zuba cokulanki na abinci dukka su jiko hakan yana kashe karni ki dinga yawan yin hakan koda ba abincin zaku ci ba 7⃣Duk sanda zaku sha tea ki matsa lemon tsami da ruwan dumi kisa a cup din ki barshi zuwa wasu mintina kanki gama aiki zakiji cup din in an zuba tea din yana kamshi 8⃣Karki dinga sawa miyar ki kanwa dinga …

MIJINKI A TAFIN HANNUNKI

*MIJINKI A TAFIN HANNUNK*
🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙🖤👙 _*by waleed Ibrahim funtua*_ Wannna matsin dauke yake da magunguna guda shida Wanda kuma sune mafi shahara wajen Mallaka ta hanyar ganyen magani ba tareda sihiriba Idan kun lura akwai

(1)Dan kadafi (2)hana kishiya (3)kafi malam (4)bita zaizai (5)manta uwa (6)Mallaka
Wadannan kusan kowacce mace me hada magani tasansu saidai wajen sarrafasu shine babban aikin domin sahihin mallaka ne ba ruwanki da boka cikin sauki Zaki shawo kan miskilin mijinki matukar yana saduwa dake ko kuma yanacin abincinki domin maganHANNUNKukune na farko akwai Wanda Zaki shafa agabanki lokacinda Zaki sadu da mijinki zaiji babu mace irinki saboda dadinki zaiyi jarabarki sosai Sai kuma Wanda Zaki hada kinasha zai kara miki ni ima ta daban Wanda idan mijinki ya sadu dake shi kadai yasan yanda zaiji

Sannan akwai Wanda ake sakawa acikin abinci Wanda kuma duk irin abincinda kikayi zaiji dadinsa tayanda kullum idan beci abincinkiba bashida kwanciyar hankali To kin…

Tambaya ta 011

Tambaya:

Assalamualaikum malam meye hukuncin wacce namijin Daba muharramin taba yaga hoton gashinta a waya ko a hoto .
Amsa:

Waalaiku mussalam.
Ganin al'aurar mace a hoto hukuncin shi daya da ganinshi a fili wato haramun ne. Duba littafin عبد الله بن عبد العزيز ببن باز التبرج

ATTABARRUJ. Wal-Allahu aalam. .

Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.

🕌Islamic Post WhatsApp.

FASSARAR WAƘAR SAANS (REPRISE)

FASSARAR WAƘAR SAANS (REPRISE) 
Waƙa: Saans (Reprise)
Shiri: Jab Tak Hai Jaan
Shekara: 2012
Sauti: A.R. Rahman
Rubutawa: Gulzar
Kamfani: YRF Music
Rerawa: Shreya Ghoshal
Fassarawa: Haiman Raees 
*. Tumko Dekhke Yoon Lagta Hai Koi Bichda Khwab Aaya Hai
Yayin da na ganka, sai in ji kamar wani ɓataccen mafarki ne ya dawo min. 
*. Barson Lambi Raat Se Guzre Subah Ka Jhonka Laut Aaya Hai
Kamar safiya ce ta zo da ga ƙarshe, bayan dare mai tsawo. 
*. Bahut Derr Jaagi
Afarke nake tsawon lokaci.
*. Bahut Door Aayi
Na zo ne da ga waje mai nisa.
*. Khwab Ne Chodi Na Meri Kalai
Mafarkin ya ƙi rabuwa da hannuwana. 
*. Kab Se Meri Saans Ruki Thi
Numfashi na ya tsaya ba tsawon lokaci. 
*. Mujhe Saans Aayi 3x
Yanzu ina iya yin numfashi. 
*. Saans Mein Teri Saans Mili Tho Mujhe Saans Aayi
Yayin da numfashina ya haɗu da naka, a lokacin ne na ke fara numfashi. 
*. Mujhe Saans Aayi 3x
Yanzu ina iya yin numfashi.
<••••••••••••••••••••••••••••>       Haiman Raees  <••••••••••••••••••••••••••••>
        08185819176
Twitter: …

JIKIN ƊAN ADAM 03

*بسم الله الرحمن الرحيم**_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 03🍍🍊*
*(Fitowa ta Uku)*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
Wasu masana wadan da ba su ma da alaqa da Muslunci sun ce: Azumi yana rage mummunar qibar ga dan adam, ya tsarkake fatarsa, ya yi maganin wani mummunan sinadari na jikin mutum wanda zai riqa yi masa barazana, ya gara tsarin jijiyoyin jiki, ya rage radadin jiki ko kumburi, ya qara wa mutum qarfin tabbatar da abubuwa, ya sauqaqa wa mutum damar gamsar da iyalinsa ta wajen ciyarwa, ya kuma sami isasshen lokacin zama da su, wata qila ma abu mafi girma shi ne mutum ya kyautata tsarin lafiyar jikinsa.
Wannan bincike na su kamar fassarar ayar Qur'ani ce da Allah SW yake cewa: وَأَنْ تَصُومُوا خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُون. In dã kun sani yin azumin shī ne ya fi muku. Don duk abin da kake buqata na tsarkakewa azumi ya tattara shi, kamar ba da …

MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA

MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Assalamu Alaikum warahamatullah Wabarakatuhu.
A cikin 'yan kwanakin nan da mu ke ciki, musamman da ga jiya zuwa yau na fahimci cewa akwai wasu tsirarun mutane da su ke cikin wani irin hali na shauƙi, annashuwa da kuma jin daɗi saboda labari ya isar mu su cewa wasu manyan mutane sun kamu da wannan cuta ta COVID19.
A zahirin gaskiya, yana ɗaukar dabba mafi girman daraja a cikin dabbobi marasa hankali kafin ta yi wa 'yar uwarta dariyar murnar ta kamu da cutar da za ta iya zama ajalinta, ko kuma saboda ta shiga wani hali da zai iya kai ta zuwa ga hakan. Kenan hakan yana ɗaukar mafi girma daga cikin jahilan mutane kafin a ce ya ma bar irin wannan tunanin ya shige shi ballantana ma har ya kai ga bayyana shi a fili. Shin kai da kake murna ta kama waɗancan mutane, tsakani da Allah menene abun murnar? Shin kana tunanin ka fi ƙarfin ta kama ka ne? Ko kana ganin cewa in sun mutu kai za ka tsaya gadin duniyar ne? Shin ko ka san cew…

Tambaya ta 010

*HARAMUN NE KA AURI JIKAR MAHAIFIYARKA TA BANGAREN SHAYARWA !*
*Tambaya* Assalamu alaikum Dr. Yarinya ce tana da saurayi suna son junansu, amma saida aka zo ga6ar aure shi ne sai mahaifiyar saurayin take cewa ta shayar da mahaifiyar yarinyar nono, Malam yanzu don Allah ya matsayin auran na su zai kasance?
*Amsa* Wa alaikum assalam, Babu aure a tsakaninsu, saboda ta zama 'yar 'yar'uwarsa ta bangaren shayarwa, 'yar 'yar'uwa kuma haramun ne a aureta kamar yadda Allah Ya yi bayani a aya ta (23) a Suratun Nisa'i.
Annabi (SAW) Yana cewa "Duk abin da yake haramta ta bangaren Nasaba, to yana haramta a bangaren shayarwa" kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari da Muslim. Ya wajaba iyaye sun dinga taka-tsantsan idan an shayar da yaransu, ko su rubuta su ajiye saboda ko da an yi auren dole a warware shi, kamar yadda ya faru da Ummu Yahya da Ukbah bn Harith a zamanin Manzon Allah (SAW) a hadisin da Bukhari da Muslim suka cimma daidaito wajan fitar da shi.
Allah ne mafi…

FINA FINAN ALGAITA DUKA WAƊANDA SU KA FITO KASUWA

FINA-FINAN ALGAITA DUKA WADANDA SUKA FITO KASUWA
ALL ALGAITA DUBBED MOVIES (FILMS)
ALGAITA DUB STUDIO ^^^^MASUBURBUDAR FASSARA^^^^ . . . 1. YAKI DA RASHIN ADALCHI 2. DAN TAWAYE 3. MUNNA 4. NEMAN DUNIYA 5. DAN BASAJA 6. KO'OHO 7. MAI TABARGAZA 8. RAINA KAMA 9. MASHEKI 10. ZAKIN ZAKUNA 11. HATSABIBI 12. DAMISA 13. BARKONO 14. MAI TAURIN KAI 15. MAI KISHIN KASA 16. SARKA 17. BAKIN RIJIYA 18. MAI GASKIYA 19. MARA TSORO (DABAANG) 20. ZUBAR JINI 21. CHAKWAKIYA 22. IZZAR MULKI 23. BABBAN YARO 24. MARAR TABBAS 25. BABBAN YAYA 26. GIDAN KURKUKU 27. INUWA 28. MASS 29. NINJAN KISA 30. SURYA UBAN DABA 31. KISAN GILLA 32. YAKIN KWATO ƳANCI 33. KARON BATTA 34. DOLAYE UKU 35. GADARA 36. SHUGABA 37. KADDARA 38. ASHOK MADAKIN KATTI 39. KUNAMA 40. NAMIJIN ZAKI 41. BIRNIN MATSAFA 42. TARIHIN ANNABI YUSUF 43. TSOHUWAR GABA 44. GABAR GADO 45. TAKUNKUMI 46. MAI ADDA 47. MAKASHIN MAZA 48. FUSATACCE 49. HANYAR MADARAS 50. SANSANI 51. BOTORAMI 52. TARKO 53. GHAJINI 54. DODON ƳAN GATARI 55. SOYAYYAR BEBAYE 56. SA MAZA GUDU 57. BANZA FALALU 58. HATSARI DA RAI 59. SOJA 60.…

TARIHIN RAYUWAR JARUMA LARA DUTTA

TARIHIN RAYUWAR JARUMA # LARA_DUTTAkamar kowacce larabar tsakiyar mako da muka saba kawo maku shirin mu ,da yake bayani akan jaruman film na bollywood wadanda suka fara harkar film daga 1990s zuwa wannan lokaci ko kuma wadanda tauraruwar su ta haska a wannan zango ,yauma cikin ikon ALLAH mun zo maku dauke da tarihin rayuwar jaruma LARA DUTTA. An haifi jaruma LARA DUTTA ranar 16/04/1978 takasance jarumar fina finan india wacce take fitowa a bangaren bollywood ,sannan takasance mai sanaar tallata kayan kawa wato (modelling) a turance,kuma jarumar tazamo er india ta biyu data sami nasarar lashe kyautar kyau ta MISS UNIVERSE wacce akayi a qasar CYPRUS shekarar 2000. tafara fitowa a filmdin ANDAAZ 2003 tareda da jaruma priyanka chopra da kuma AKSHAY KUMAR filmdin yasamu karbuwa sosai a wajen masu kallo (audience) gami da samun yabo daga bakin masu sharhi (critics),sannan da filmdin tasami nasarar lashe kyautar FILMFARE AWARD Ta sabuwar jaruma mafi nuna hazaqa a shekara wato (filmfare award f…

WA YA KASHE TSOHO?

WAYA KASHE TSOHO wata yarinyace tana xaune a cikin mota bus kusada ita akwai wani tsoho abinka ga yar xamani sai chat take tana murmushi shima tsohon sai leken wayar yake yana kallon abinda take rubutawa shima yana dariya ashe wan nan yarinyar ranta yabaci sai tayi rubutu kamar haka duk wata dukiya tawa aba mamata da babana domin ina cikin mota bus nanda minti daya bom zai tashi koda tsoho yaga abinda yarinya ta rubuta betsaya wata wata ba kawai yabude kofa yafado kasa akayi rashin sa a ya mutu TAMBAYA TSOHO SHENE YAKASHE KANSA KO KASHE SHI AKAYI

INA WACCE MIJINTA BA YA IYA GAMSAR DA ITA?

*****INA WACCE MIJINTA BAYA IYA GAMSAR DA ITA ****Ba qaramar matsala bace ace saidai ke ki gamsar oga ke kuma shuru saikin yi rabi shikuma ya zare bananarsa Mata masu irin wannan matsalar ku gwada wadannan hanyoyin dazan baku 1-wani mijin yanada qarancin Maniyyi shiyasa bai fiya yin abin kirkiba wani kuma saurin kawowa gareshi idan me daya daga cikin wannan matsalar gareki to ba zuramai ido zakiyi kina cutuwaba zata iya yuwuwa shi kunyar neman magani yake tunda dai shi buqatarsa na biya  Ga wasu hadi dazaki riqamar da kanki (a) kisamu albasa guda biyu ki yan yankasu ki soya sai bayan ta soyu sai ki kawo kwai ki zuba amma kada ki bari ya soyu ki sauke kibashi yaci idan kina haka in sha allahu za kiyi mamaki.. (b)- Maza da dama suna bukatar jimawa awajen jima I amma hakan baya samuwa saboda daga sunfara jima I zasuyi idan mijinki irin wannan garesa dayafara tuqi sai mai yaqare toga wani da zakimar don qara masa fuel kisamu garin h/sauda cokali daya sai kisamu kwai guda uku sannan ki hadas…

A TUBA ZUWA GA ALLAH

A TUBA ZUWA GA ALLAH !!!
Allah madaukaki yana cewa : "Babu wata musiba da za ta same ku, face sai ta kasance daga abin da hannunku ya aikata ne" suratush Shurah aya ta 30.
Zunubai suna jawo bala'oi da yawa, wadanda suke cutar da zuciya da jiki, a Duniya da Lahira, ba wanda ya san adadinsu sai Allah, ya kamata mu koma ga Allah mu tuba zuwa gare shi, mu kusance shi da aiyuka nagari, mu dinga umarni da kyakkyawan aiki, muna hani da mummuna, saboda idan bala'i ya zo ba zai takaita kawai akan wadanda suka aikata alfasha ba, domin ba za'a dora maka wani ya dinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da ka aikata, ka san zunubin ko ba ka san shi ba, wani daga cikin magabata ya hadu da wani mutum sai ya aibanta shi, sai ya ce masa : jira ni na shiga gida na fito, sai ya shiga gida yayi sallah ya tuba zuwa ga Allah, bayan ya fito sai mutumin ya ce masa: me ka yi, sai yace : na tuba zuwa ga Allan da ya dora ka akaina.
Rubutawa✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 20/1/2012

HAƘURI A ZAMAN AURE

HAKURI A ZAMAN AURE (‘YAN UWA MATA)
HAKURI yana da matukar riba a rayuwa (bama a zamantakewar aure kadai ba) abun da yake damun wasu ma’auratan shine gaggawa da rashin hakuri, zaka ga mutum yana fadin cewa yana cikin matsala amma kuma abun mamaki shine bazai iya hakuri akan matsalar ba. Musamman a banganen mata ki sani cewa wani abun fah dole take kamawa idan kika kasa hakuri na kankanin lokaci wallahi hakan sai ya jawo miki shiga matsalar da sai kin dauki tsawon lokaci bki fita a ciki ba.
‘YAR UWA kiyi tunani ki gani lokacin da za’a kawo ki gidan ki kowa idan ya gama miki huduba a bun da yake cike hudubar dashi shine a rinqa hakuri, kada kiyi zaton dan su basu samu soyayyar mijinsu bane (su wadanda suke miki nasihar) a’ah wallahi wata a cikinsu soyayyar da mijinta ke gwada mata ke koh rabinta bazaki samu ba, amma da zaki tambaye ta meye jagoran wannan zaman nasu sai tace miki hakuri, haka shima ta bangaren mijin. http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/hakuri-zaman-aure-yan-uwa-mata.…

GIDAN MIJI

*GIDAN MIJI* 👍🏻Rike Kishiyarki tsakani da Allah, idan tacuceki kina zaune zakiga sakayya agun ubangiji👏🏼 wannan nasihace👆🏼
✍🏻 GIDAN MIJI👍🏻 Karki nunawa duniya Ke MOWA ce don randa kika dawo BORA zaki kasa fita duniya, lamarin Aure babu alfahari aciki, nemi yardar Allah ba ta mutaneba👏🏼 wannan nasihace👆🏼

✍🏻 GIDAN MIJI👍🏻 Nemi aljannarki, da yardar mijinki, karki nemi yardar mutane, domun shi dan adan baka iyamasa👎🏼 wannan nasihace👆🏼

✍🏻 GIDAN MIJI👍🏻 Gidan mijinki shine gatanki, ko ke wacece in kika rasa aure kin rasa farin ciki, rike mijinki tsakani da Allah🤝🏼 wannan nasihace👆🏼

✍🏻 GIDAN MIJI👍🏻 Yawaita yi muku addua da mijinki da yayanki da kishiyarki DA abokan zamanki. hakan zaisa zuciyarki gaba da baya tayi Albarka✅ wannan nasihace👆🏼

✍🏻 GIDAN MIJI👍🏻 kula da tarbiyyar yayan kishiyarki, koda kuwa bakya hurda da uwarsu, karki musu mugunta ko sharri, domun shi sharri dan aikene, wataran kan naki yayan zaidawo🙆🏻 wannan nasihace👆🏼

✍🏻 GIDAN MIJI👍🏻 gidan miji gidan hutu😄 Ya A…

Tambaya ta 009

SHIN DOLE NE NA YI WA MIJINA HIDIMA?
Daukacin malaman Musulunci sun tafi akan cewa mustahabbi ne mace ta kula da mijinta wajen yi masa hidima kamar dafa abincinsa da sharar dakinsa da gyara masa makwancinsa da bandakinsa da wankewa da goge masa tufafinsa da sauran abubuwan da a al’adance za a fassara su da sunan kulawa da miji. Malamai suna ganin za ta yi hidimar koda kuwa ta kasance mace ce mai muqami wacce a al’adance ba ta yin sauran ayyukan gidanta da kanta.
Sai dai akwai sabani a tsakanin malamai ta fuskar tantance shin dole ne tai masa hidima din ko kuwa ba dole ba ne? Daukacin malaman mazhabobin Shafi’iyyah da Hanbaliyyah da wasu cikin Malikiyyah sun tafi akan cewa ba dole ba ne mace tai wa mijinta hidima, amma ba laifi in ta yi abin da aka saba a al’adance cewa mace na yi wa mijinta.
Su kuwa malaman mazhabar Hanafiyyah sun doge ne akan cewa, aikin gidan miji dole ne akan matar aure. Yayin da daukacin malaman mazhabar Malikiyyah da Abu Thaurin da Ibn Abi Shaibah da wasunsu suka tafi…

THE END IS NEAR

BREAKING NEWS TO THE MUSLIM UMMAH:     BE WARY, TIGHTEN UP YOUR BELTS AS THE END IS AROUND THE CORNER!!!      YOU WILL FIND THE PIECE ASTONOSHING; DON'T STOP, KEEP ON READING! Assalamualaikum, Did anyone of us imagine how the sun is gonna rise from the west as said by our prophet Muhammad (peace be upon him) 1400 yrs ago..
but now scientists found how it happens..scientists were making researches on MARS for long time....MARS which rotates in the same direction of the EARTH has now started to rotate in the opposite direction...now the sun rises from west in MARS..this is named as RETROGRADE MOTION...and this happens to all planets..amazingly EARTH is next.!!
ALLAH says when the sun rises from the west the doors of FORGIVENESS will be closed..no more dua for repentance will be accepted..it's not too far for this to happen..!!
Let's not waste time on movies, music, parties, etc..spend more time to read and learn QURAN and HADITHS..PRAY five times..and teach our kids on Islam..thes…

Tambaya ta 008

*Tambaya:*
Assalamu Alaikum, malam dan ALLAAH ina neman addu'ar daxanyi da kuma shawara,matar babanmuce tasa magani cikin man shafa,sai taba ƙawata ta saidamn, sai ƙawartawa ta faɗamn, taƙi saidamn ta faɗamn sai taba wata ɗiyar yayan babanmu ta saidamn, da takawon sai nace bansiya. Inaneman shawarwari da kuma addu'ar da xanyi ALLAAH y kuɓutar dani daga sharrinta, kuma malam dan ALLAAH inason nasan yanda ake karya sihiri .
*Amsa:*

Idan sihirine a samu ganyan magarya guda bakwai danyu idan ba'a sami danye ba ayi amfani da busasshe ko garinta wanda masu shago sun fi sanin shi da sidr, a zuba a ruwa me tsarki a karanta wadancan ayoyin, numfashin karatun ya rika shiga cikin ruwan ba tofi za'ayi ba, sai a rika shafawa a jiki safe da yamma har kwana bakwai kuma a rika sha, in sha Allah za'asamu waraka da warwarewar sihirin.  والله اعلم .
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
*🕌Islamic Post WhatsApp.*

THE TRUTH ABOUT JAMB UPGRADING

CORONAVIRUS NA SABON ABU BANE

*Mal. Aminu Ibrahim Daurawa*

CORANAVIRUS BA SABON ABU BANE 
An dade ana gamuwa da ibtila'i da jarrabawa a fadin duniya, kwalara da Annoba da yaduwar cutaka ya dade yana addabar duniya, Kuma ana yi masa farrasa iri iri, kowa gwargwadon abinda yake dauke da shi na akida, ko hankali, ko ilmi ko al'ada, ko surkulle.  Amma mu a mahanda ta addini muna daukar wadananan a matsayin jarrabawa da Jan kunne da Allah yake yiwa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wananan duniya akwai me ita, Kuma yana da iko akanta kuma zai Iya tashin ta duk sadda yaga dama. Domin abubuwan da ake aikatawa a wananan duniya na masha'a sunyi yawa, butulci da kangarewa, da shishigi yayi yawa, wasu ma basu yadda akwai Allah ba, wasu Kuma sun yadda akwai Allah amma sun bashi siffofi irin na mutane, wasu kuma sun yadda da Allah amma sun bijirewa dokokinsa, wasu kuma sun takale shi da fada ta hanyar fada da Annabin sa, da muzantashi, da yiwa addinin sa izgili da baa, Wasu sun shagala da duniya sun m…