AKWAI WARAKA TATTARE DA ZUMA


*AKWAI WARAKA TATTARE DA ZUMA 🍯*


Qudan zuma (bee) 🐝 yana sha daga ire-iren ruwa (juices) na furanni da 'ya'yan itace daban daban sai ya samar da zuma (honey) a jikinshi, wanda yake tara shi a cikin kwayoyin kakin zuma (cells of wax). Sai a wasu qarnoni da suka gabata ne mutum ya gane cewa zuma tana fitowa ne daga cikin qudan zuma. Wanda alqur'ani ya tabbatar da hakan tun shekaru dubu ďaya da ďari huďu (1,400years) da suka gabata a wannan ayar 👇 

*”ثُمَّ كُلِى مِن كُلِّ الثَّمَرَٰتِ فَاسلُكِى سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلًا يَخرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٌ مُّختَلِفٌ أَلوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٌ لِّلنَّاسِ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَءَايَةً لِّقَومٍ يَتَفَكَّرُونَ“*

*"Sa´an nan ki ci daga dukkan ´ya´yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinki, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata WARKEWA ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.”* (Suratun Nahl: 69).
.

Yanzu mun fahimci cewa akwai waraka tattare da zuma kuma tana ďauke da magunguna iri-iri. 'Yan qasar Rasha (Russians) sun yi amfani da zuma a yaqin duniya na biyu (World War II) wajen ďaure ciwukan da suka ji a jikinsu. Ciwon ba zai ru6e ba kuma ba zai zaizaye waje ba. Saboda density na zuma, babu wani fumfuna (fungus) ko bacteria da zai yi tsiro a ciwon. 
.

Mutumin da yake fama da mutuwar wani sashi na jikinshi ana ba shi zuma don magance wannan cutar, 

Zuma tana ďauke da sinadarin sugar (fructose) da vitamin K. 
.

Don haka tabbas alqur'ani ya sanar da mu amfanin zuma, kuma likitoci na wannan zamanin sun tabbatar da hakan. 
.

Allah Ya sa mu dace. 
.

Duba Littafin 👇 
*The Qur'an and Modern Science.*

Rubutawa:
*✍🏾Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive