BUSHARA GA WANDA YA ZAUNA A GIDA LOKACIN ANNOBA


BUSHARA GA WANDA YA ZAUNA A GIDANSA LOKACIN ANNOBA

An ruwaito daga Ummuna Aisha (RA) ta ce: "Na tambayi Manzon Allah (SAW) game da "Annoba", sai ya bani labarin cewa shi azaba ne da Allah ya ke aikowa ga wanda ya ga dama, kuma Allah ya sanyashi ya zama rahama ga muminai, kuma babu wani mutum da Annoba za ta auku sai ya zauna(a gidansa), yana mai hakuri da neman lada, kuma yana mai sanin cewa babu abin da zai sameshi face abin da Allah ya rubuto/kaddara masa, face ya kasance yana da kwatankwacin ladan shahidi". Ahmad ya ruwaito da isnadi ingantacce 26780

تغريد شيخ صالح العصيمي التميمي2020/3/21

#Coronavirus #Covid19
#Zaurandalibanilimi
📖https://t.me/Zaurandalibanilimi
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive