DANGANE DA KASHE MUSULMAI DA AKE YI A INDIYA


DANGANE DA KASHE MUSULMAI DA AKE YI A ƘASAR INDIYA

Bissmillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum warahamatullah Wabarakatuhu. 'Yan uwa barkanmu da Warhaka, fatan kowa yana lafiya.

Izuwa yanzu dai na san kusan kowa da ga cikinku ya samu irin ɓarnar da ake yi wa musulmi a ƙasar India, don haka ba sai na ja doguwar magana a wannan fanni ba.

Fannin da zan ɗanyi tsokaci akai shi ne: Wato ɗabi'a ce ta ƙananan ustazai, ko 'yan bana bakwai, ko gama garin mutane waɗanda su ke da ƙarancin fahimta dangane da abubuwan da ke faru na yau da kullum, idan irin wannan al'amari ya faru za ka ga nan da nan kansu yayi zafi, ƙirjinsu kuma ya ɗau ɗumi. Tabbas ko dabba ce aka taɓa mata nata dole ta ji zafi, kuma dole ta ji cewa tana buƙatar ɗaukar fansa. Ballantana mutane masu hankali, don haka abin da aka yi mana ba mu ji daɗinsa ba, kuma mun yi Allaah wadai da shi. To amma me? Wani mataki ya kamata mu ɗauka?

Na ga rubututtuka da dama na abokai da makusanta akan wannan lamari da kuma na waɗanda babu abinda ya haɗa mu. Wasu sun yi kyau wasu kuma ba'a cewa komai. To a ƙarƙashin wannan, zan so mu fahimci cewa wannan abu da ya faru ba komai bane face ɗaya daga cikin alamomin ƙarshen duniya. Kuma haka abin zai ci gaba da kasancewa har sai alƙawarin Allaah ya tabbata a kanmu. 

To, idan irin wannan abu ya faru ne ya kamata mu yi? Akwai masu tunanin kawai a fito mana a gwabza, to in an ce a gwabza kuna da makaman yaƙar maƙiyanku irin wanda ya fi nasu? Shin cewa aka yi a fito a yi surutu, me surutun zai amfanar da mu? Shin in zai mana amfani ma, su ya kamata ace su yi? Ta wace hanya ya kamata ayi? Kai da kake hawa yanar gizo kana wannan ɓaɓatu feesabilillah matakin da ya kamata ka ɗauka kenan? Shin kai da kake ta zage-zage da aibata dukkan mabiyan sauran addinan da suke da alaƙa da lamarin ka na da hujjar da zaka kare kanka in aka rutsa ka ka yi bayani dangane da abubuwan ɓatanci da ka faɗa a kansu? Shin su jaruman Fina-Finai musulmai da kake cewa sun ƙi fitowa su yi magana, tsakani da Allaah maganar su wane irin canji za ta haifar? Shin wai ma musulmanmu na indiyan sun damu da addinin nasu kamar yadda ya kamata da har za su fito su ɗauki matakin da ya dace? Shin ka san irin halin da su kansu jaruman su ke ciki kuwa da har kake neman jawabi daga gare su?

Shin kamata yayi mu ɗauki hanyar gyara aiyukanmu da halayenmu ko kuma kamata yayi mu fito mu yi hargagi kawai a fito a share mu maganar ta wuce? Shin za mu aminta da cewa mun saɓa wa mahaliccinmu ta hanyar kaucewa umurnin Manzonsa mun ɗauki ƙauna mun danƙawa maƙiyanmu wanda hakan yasa yanzu mu ke fuskantar abinda muka shuka ko kuma za mu fake ne da liƙawa wasu laifin ko da hakan ya dace ko bai dace ba?

Shin za mu ci gaba da zargin juna ne da ganin laifin juna ko kuma za mu shiga taitayinmu ne mu yi yunƙurin gyara baki ɗaya?

Ba Za su daina kashe mu ba, ba za su daina tsanar mu ba, ba za su daina ƙoƙarin ganin bayan mu ba. Amma dukkan su ne su ke yi mana hakan? Shin za mu bar zafin rai da mummunar fahimta ta sa mu tsani waɗanda ba su ji ba basu gani ba ne ko kuma za mu miƙe ne mu koma kan tafarkin da ya dace?

Bani da iko da kowa, bani da ikon dakatar da ta'addanci, amma ina da ikon hana kaina ɗaukan nusarin hukuncin da bai dace ba ga waɗanda ba su cancanta ba a kuma lokacinda bai dace ba.

Allaah ya ƙara tsare mu.

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive