HAPPY BIRTHDAY RAANI

HAPPY BIRTHDAY RAANI

Gaisuwa gareki Rani
Sarauniya gareni
Tauraruwar ƙarni
Abar biɗar zamani
Murmushinki na birgeni
Muryarki na ƙayatar da ni
Kafcenki na kafceni
Takunki na ɗasa ni. 

Ni dai komai naki ya min 
Kyautar nishaɗi tuni kin min 
Duk dai ƙusa tuni an min 
Soyayyarki babu mai iya cire min
Ƙwarin gwiwarki ya min 
Nauyin damu ki kan rage min 
Da murmushinki idan kika min 
Ni ke zama ko da matan duniya za su mutumin. 

Allah sarki, kowa ya san ina sonki 
In shirinki zai fito sai in ta ɗoki 
Da kika haihu sai da na ɗanyi biki
Saboda ƙaunar da na ke gareki 
Bana gajiya da kallon shirinki 
Bani ƙosawa da jin Muryarki 
Ji nake kamar Rahul ina na kalli kumatunki 
Kowa ma ya kira ni Raj In har zan ga idanuwanki. 

Happy birthday mai mardani
Fatan nasara gareki mai zamani 
Nasan cewa bakya cin makani
Amma tabbas kina da kyan gani 
Hakan yasa kika sheƙeni 
Kuma na yarda ba batun guna-guni
In kina son wani abu sanar dani 
Zan zamo gareki kamar aljani. 

Asha shagali lafiya 
Allah dai ya ƙara lafiya 
Ya bada sa'ar tafiya 
Ki kame dukka nahiya 
Kowa yace Sarauniya 
Gareki yau mu ke mubaya'a 
Haiman dai tuni yayi niyya 
Zuwa ƙasa ta Indiya 
Domin zuwa gaida gimbiya. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 


Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive