ILLAR ZARGI A TSAKANIN MA'AURATA


ILLAR ZARGI TSAKANIN MA'AURATA:

              ・ILLAR ZARGI TSAKANIN MA'AURATA・

Yau zan danyi tsokacine akan zargi. Wannan kalma ta zargi ba kalma ce me dadi ba, sai dai duk da haka mutane a yau sun doru a kai, ba fa mace ba ba ga namiji ba.

Muna cikin wani zamani na rashin yadda yayi yawa cikin al’umma musamman ga ma’aurata ,wadanda su aka fi so su yadda da junansu fiye da kowa a duniya,sai gashi a yau mace bata yadda da mijinta ba miji bai yadda da matarsa ba.Duk macen da za ta kasance me zargi to kuwa dole za ta zama marar wadatar zuci, don a duk lokacin da miji ya yi mata alheri to fa gani za ta yi ya yi wa wata dubunsa, wannan zai sa ba za ta yaba ba balle ta yi godiya. Mu sa ni a mafi yawan lokuta mu ke haddasa wa kanmu matsaloli wanda ba za mu iya shawo kansu ba. Mace ta sa ni mijinta shi ne mutum na farko da zai zamo amintaccenta sai kuma yaranta su biyo baya, haka shi miji wadannan su yakamata ya yarda da su ya kuma amince dasu saboda sune makusantansa fiye da kowa. Aure da yawa sun mutu, wasu sun samu tangarda an warware ,wasu har yanzu ana fuskantar matsala don ba a gano bakin zaren maganar ba duk a dalilin zargi. Mata mu gyara dabi’unmu akan mazajenmu musamman a bangaren abinda ya shafi zargi, duk wata mace rufin asirinta shi ne mijinta, gatanta kuma ya kasance cikin daraja a cikin al’umma, saboda haka mu rage zargi akan mazajenmu, mu kyautata musu zato me kyau a cikin rayuwarsu, hakan zai sa mace ta kasance abin kwatance a cikin al’umma.
 http://sirinrikemiji.blogspot.com/2020/02/illar-zargi-tsakanin-maaurata.html#.XkUMOldQEWU.whatsapp
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive