KAWAR DA KAI


KAWAR DA KAI
DABI'A CE TA MANYAN MUTANE MASU KARAMCI

Ibn Athir R.h yake cewa, yana bada labarin Salahuddin al-ayyubi R.h barden musulunci, wanda ya kwato masallacin Al-Aqsa (qudus) daga hannun arna ya kafa daular musulunci cewa; Ya kasance mai juriya Mai kyawawan dabi'u, Mai 'kaskantar da kai, Mai hak'uri akan duk abinda yake k'i (idan an yi masa abinda baya so, se ya yi hakuri) na kasa dashi zasu yi masa laifi amma se ya yi kamar ma ba'a yi masa ba, zai ji wani ya fada masa mummunan kalma, amma ba zai ce masa abinda ka yi baka kyauta mun ba, sannan ba zai canza ba wajen yi masa mu'amala.

Wata Rana yana zaune ga mutane tattare da shi, bayi da suke zaune a wajen suna jefe-jefe, se wani ya dauki takalmi ya jefi d'an uwansa dashi, se takalmin ya kuskure ya tafi inda Salahuddin yake, shikuma lokacin shine (Amirul mu'minina)fa! Cikin ikon Allah se takalmin ya kauce masa ya fad'a wani guri(bangare daban), to, don ma kada wannan bawan ya ji yayi laifi (k'ila sarki zai masa uk'uba) an jefo takalmin ta damansa kuma yaga takalmin inda ya fad'i se ya waiwaya hagunsa yana cewa (abokin zaman sa) don Allah ina ma zamu je idan anjima? Wai don karma bawan nan ya d'auka ya yi wani laifi (domin ya kawar da kai daga wancan wautar da bawan nan ya yi masa)

Allah ya jikan Malam Ja'afar Mahmud, shi naji ya kawo wannan, cikin wani Nasihan sa (kyawawan dabi'u).

Halin magabata na kwarai kenan abin koyi, abinda ake ga mumini na kwarai ya siffantu da kyawawan halaye na girma da karamci

Allah ka bamu Kawaici, ka jik'an Salahuddin DA Malam Ja'afar, da iyayen mu da musulmi baki daya (Amin)

# Zaurenfisabilillah 

Facebook: https://www.facebook.com/FISABILILLAH-2169310043281726/

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive