MUWADDAT 02


💗💗💗💗💗💗
      MUWADDAT
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗             ~NA~ *AYSHA A BAGUDO*
     ~DEDICATED TO~   

_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
     _(UMMIN KADUNA )_

~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~

alhamdullahi am back again.

warning!!! 

for the first time !!!! i will like to say," don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people, if you read it ,is for your own risk. 

WATTPAD @HAUESH 

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM 

page 2

..tana hawa benen mahaifinta, ta d'an zuge kofar glass din parlour'n tashiga bakinta d'auke da sallama, sai alokacin gaanta ya fad'i sakamakon tunawa datayi da kanta babu d'ankwali ,daga ita sai wata hadaddiyar doguwar rigar, yar saudiyya wacce ta sha stone work ,amman kanta babu komai ,hakan ne yasa dogon gashinta data had'a ta tufke da ribbon suka bayyana .

har ta shiga parlour'n tana fargaban fad'an da dad dinta zai yi mata idan yaga kanta babu dankwali,
jikinta a sanyaye ta k'arasa gaban dad ta d'an durkusa ta gayar dashi kana tace" dady gani .

alhaji muhamud mai agogo ne zaune cikin tangameman parlour'n shakatawarsa, wani d'an k'aramin table ne agabansa, cike da kayayyakin motsa baki iri iri.. 
alhaji Muhamud ya d'an d'ago ya dubi yarsa muwaddat cike da fara'a da sakin fuska, sannan yace "muwaddat me kike yi acikin gidan nan tun safe baki lekoni ba .

tsadadden murmushinta tayi sannan tace dady babu abinda nake kawai a kwance nake, ina d'an hutawa, jira nake sai ka sauko sai na gaisheka.

" ok babu damuwa ince duk kanen naki sun tafi makaranta ne? 
"eh sun tafi har ma direba ya dawo "to mai maman taku takeyi da bata zo ta kwashe wad'an kayan abinci ba?
 
"dady wanka tashiga, amman nasan zuwa yanzu ta fito"
yace" yanzu hk baki ci abinci ba ,kika je kika kwanta ,maza ga abinci nan ki zauna kici "dady bana jin yunwa ,ni bama yanzu zanci abinci ba .


"anya muwaddat kina kyautawa rayuwarki tunda kika xo gidan nan kullun sai ayi miki fad'a akan cin abinci amman bakya ji, wai ke yar gayu ko ?
tayi murmushi kawai, shi kuma yaciga da mgn "ina kika ta'ba ganin ana gayu ciki babu komai. 
ta sake yin murmushi sannan ta mika hannunta ta d'auki apple guda d'aya ta kai bakinta ta gutsura tana niyyar tashi yace "ba tafiya zakiyi ba, ki zauna ina son muyi magana dake"
ta mike cikin natsuwa ta koma kan d'aya daga cikin kujerun na alfarma dake zagaye da parloun ta zauna tana jiran abinda zai gaya mata.

 ya dubeta kana yace "muwaddat me yasa baki son d'aura d'ankwali?
" wato kin fi son kullun sai na miki fad'a akanshi ko? 
"tace dady kayi hakuri wallahi mantawa nayi kuma kaina tsantsi garesa idan na d'aura d'ankwali baya zama sai yayita zamewa yace "zaki san gashinki mai tsantsi ne duk ranar dana saka aka aske miki kan na gata gayu.. 

muwaddat ta d'an langwa'be kai a kujerar tana dry yake, tasan fad'a kawai yake bazai iya aikata hakan ba.. 

"au gani kike da wasa nake yi, shi yasa har kike dry ko? 
cikin shagwaba tace "to dady to ita umminah tana ina da har zata bari a aske min gashi? 
"ai tunda bakijin magana daga ke har ummin taki na daina saurara muku tunda bata iya kwa'barki komai kike so sai ta biye miki, nan gaba in kuka yi wasa agaban ummin taki zan sa bulala in zaneki in ga yadda zatayi "a'a d'an Allah dady kayi hakuri na tuba bazan sake ba , in dai kan d'ankwali ne daga yau zan dinga d'aurawa "

sukayi 'yar dariya gabad'aya sannan yace "wai kuwa kinsan ma abinda nake shirin yi miki magana akai ? 
ta girgiza masa kai "bansani ba daddy "yace to karatu nake son na samar miki a jamiar United Kingdom ...

muwaddat tayi saurin dafe daidai saitin zuciyarta dataji yayi wani irin mahaukacin bugu da karfin gaske, saboda tsanar karatun da tayi ,a tsarinta sam tafi bukatar yin aure akan wani karatu, ta girma da muradin son yi aure da wuri saboda yanayin halittarta ,sai dai tsawon lokacin nan bata samu wanda yadace daita ba kmr kaninta auwal wanda take ganin da wuya ta mallakesa arayuwarta, tunda ta kammala karatunta na diploma ,ta cire rai da wani karatu, nest budget dinta shine aure,ita aure take so ba karatu ba. sai dai ahankali zantuttuka mahaifinta ke shiga cikin kunneta kafin daga baya tace "wani irin karatu kuma dady ? 
"nifa banida muradin tsanata karatu mai zurfi"

 "kin ci gidanku dole kiyi karatu mai zurfi domin shine burin mu iyayenki, na asali da iyayen goyonki ,guda nawa kike yanzu da zakice baki da muradin karatu idan bakiyi karatu a halin yanzu ba uwar me zakiyi? 
aranta tace "aure mana daddy ......

" yanzu ne daidai ki natsu ki tsaya kiyi karatu amatsayinki na yarinya yar shekara ashirin da haihuwa "daddy ni dai banason karatun nan yanxu kabarni kawai iya dilomar ma dana ta isheni .. "


"haba muwaddat ni fa nafi son kiyi karatu mai zurfi Allah yasani, "to da kika nace baki son karatu,aure kike so ko me ?

muwaddat ta d'an noke kai ala'mun jin kunyar mgnrsa tana dry "kinga nifa Allah yayoni da mugun son karatun boko bansani ba kodan nasan dadin karatun ne? 
"ki taimaki rayuwata dataki ki cigaba da karatu, kafin muwaddat tace wani abu hjy hajara tashigo parlour'n wanda tun kafin ta k'arasa shigowa parlour'n take jin yadda alhj yake jaddawa muwaddat zance karatu mai zurfi yake son tayi.

da sallama tashigo parlour'n tana "cewa ka rabu da wannan yarinya mara wayo kawai ,in da kai ya waye da karatu nan ,shine ita take cewa bazatayi ba, tasamu guri ta zauna tunda bataso "idan bakiyi karatu ba uwar mezakiyi uhmmmmm? 

"ki duba kiga yadda mata suka samu cigaba a dalilin karatu mai zurfi, ita kanta ummin taki tafison kiyi karatu mai zurfi kafin aure,amman shine dan iya shege kike cewa baki son karatu?
 "baki son karatu sai me?
 
muwaddat tayi shiru tana jin kmr fito ta sanarwa da iyayenta burin zuciyarta, amman kunya tattare da fargaba ya hanata "ki dai gaya mata gsky karatu na da mutukar mahimmanci agurinta bari ummintata takaraso muji mai zatace, alhj muhamud
 na gama fad'ar hk ya mike tsaye ya sa kai ya fice yana takaicin rashin son karatun da muwaddat take yi... 

a harabar gidan yaci karo da motar dataje d'auko kanwarta da suke ciki daya, direban gidan na k'ok'arin daidaita tsayuwar motar yana ganinta ya fad'ad'a faraarsa sannan yaja ya tsaya yana jiran fitowarta, hjy mukarama ta fito a natse tana sanye cikin shiga ta alfarma doguwar riga ce har kasa sanye ajikinta da madaidaicin hijab, amman kallo daya zaka mata kasan cewar akwai gidan rana da tsantsar gogewa irinta 'yan boko atattare daita.

ta k'araso ahankali inda d'an'uwanta yaja ya tsaya yana jiran k'arasowarta "kar dai fita zakayi Yaya ?
"eh fita zan yi wai kafin ki karaso,dama wacan 'yar taki ta nemi 'bata min lokaci da tuni na bar gidan "

"me kuma baby muwaddat tayi ?
"da ita kullun bata wuce laifi agurinku shiyasa sam bata son zuwanta garin nan amman nake matsa mata "

"ai duk ke kike d'aure mata gindi amman nasan yanxu idan kika ji abinda tayi sai ranki yafi namu 'baci yadda nasan kike da kulafucin son tayi karatu.. "au akan karatu ne? 

"akan shine mana wai yanxu nake mata maganar sai cewa tayi ita bata da muradin cigaba da karatu"

hajiya mukarama tayi murmushi tace "manta da wannn shirmen nata karatu d'an ada tayi sa, dan ma inaji tsoron gur'bacewar da rayuwa tayi yanxu ,ai da tare aka had'asu da bunayya "

"nima abinda naso kenan amman naga kamar ita bada raayin ma yin karatu, ni dai zan fita idan kin shiga kinsan yadda zakiyi daita "

"ai tafiya ma zamuyi zaman shirun ya isheni ni kad'ai a gidan daman itace abokiyar hirar tawa sukayi sallama yayi hanyar waje ita kuma ta k'arasa cikin gidan 

*********
alhaji mahamud shine asalin mahaifin muwaddat, sai dai ba a hannunsa ta taso ba, ta girma ne a hannun k'anwanrsa da suke uwa daya uba daya , wato hjy mukarama da mijinta alhj ishaq , hjy mukarama da mijinta suna mugun son muwaddat ,babu irin kulawar da gatan da basu nuna mata ba , ko d'an cikinsu albarka .

 su biyu kawai iyayensu suka haifa suka mutu suka bari a duniya, mahaifinsu tun mukarama na k'arama ya rasu ,suka cigaba da rayuwarsu da mahaifiyarsu, sun sha gwagwamaryar rayuwa kafin daga baya mahamud ya isa munzali mutun, d'an ma mahaifiyarsu jaruma mace ce ,ta iya sana'oi iri iri ,da hk ta raini ya'yanta , sai dai shi mahammud bai samu damar karatun boko mai zurfi ba asanadin matsananciyar rayuwar da suka riski kansu a wancan lokaci ,iyakarsa secondary school kawai ya tsaya wanda yayi a karamar hukumar koko ,
domin alokacin primary school kad'ai ce a kauyen nasu babu secondary, sai dai akai mutun wani gari, sai dai hkn bai hanashi jajircewa na ganin kanwarsa tasamu karatun ta kowani bangare ba.

bayan mahammud ya gama makarantar gaba da primary, ahankali ahankali yake sanarsa ta kwadago ta hanyar kasuwanci,da farko dai gyaran agogo yake har Allah yasanya masa albarka ya bunkasa arzikinsa ya zamo wani abu ..
adalilin wannan sana'ar tasa yasa yayi suna ciki da wajen kauyen har ake kiransa da muhamud mai gyaran agogo, wanda duk inda zaka shiga a fad'in kauyen nemansa, matukar baka sanya lakaninsa ba ,sai dai ka gama karad'e kauyen babu mai ce maka yasanshi. 

bayan wani lokaci sai mahaifiyarsu ta kamu da ciwo ajali ta sha jinya sosai ,suka rasa yadda zasuyi, gashi ciki da wajen kauyensu babu asibiti sai anjen wani gari mai kuruna dake makwabta taka da kauyensu ,idan akace za'a kai mutun asibin ma zai iya yiwuwa ya rayu domin kafin akarasa mararrabar garin mutun zai iya mutuwa , nawa nawa akayi akan idanunsu suka gani ,dan haka addua suke kullun Allah ya kawo musu d'auki daga gwanati mai ci alokacin data tallafi rayukansu ta gina musu asibiti da makarantar gaba da primary . 

 tunda mahaifiyarsu ta fara ciwon take barwa d'anta wasiyya a kullun bakinta baya shiru da mgnr diyarta mukarama ta kance "mahamud ko na mutu dan Allah ka kular min da 'yar'uwarka kaga bata da kowa sai kai," kai ne uwarta kaine ubanta domin zan tafi na barta acikin lisafi na kurciya Muhammad ka rike zumunci ,mukarama amana ce a hannunka ina son ka kaunaceta fiyye da komai ka kula da maraicinta da rayuwarta karka bari ta zubda hawayenta akan damuwa kowace iri ce .. 


duk sanda mahaifiyarsu ta tasa shi gaba tana bar masa wasiyya ya kan share hawaye yace "ki daina furta wannan kalmar inna cuta ba mutuwa ba,sannan ba'a san inda rai yake ba, babu wanda yasan gawar fari ban da Allah, baki sani ba ko mune zamu rigaki mutuwa. 


"kayya d'an nan dayake hk take kiransa kasancewarsa d'an fari , "wannan ciwon bana tashi bane, ni kaina ban sa ran zan warke ba har in tashi ba, domin wannan ciwon bai kamani da wasa ba, ni dai fatana ko na tafi na barku ka rike 'yar'uwarka da daraja kada ka auri macen da zata shiga tsakaninku, duk abinda, zata maka kayi hakuri kamata uziri, ku had'e kanku ka aurar daita ga mutumin da kasan zai riketa da daraja sannan ka inganta rayuwarta da karatun addini dana boko tak'arasa mgnr tana janyo numfashi da kyar wasu zafafan hawayen tausayin ya'yanta yashiga gangarowa bisa kuncinta. 

haka ma duk sanda mukarama ta kunsantota mgnrta kenan "mukarama ki rike d'anuwanki, ki rufa masa asiri a duk sanda hkn takasance, ki d'auke shi matsayin uba, domin hausawa sunce babban wa uba ne, ku rike zumunci atsakaninku, duk abinda kika samu nashi ne hk shima, ku zamo tsintsiya mad'aurinku daya Allah yayi muku albarka. 


tunda inna ta kwanta ciwo bakinta baya shr da barwa mahmamud da mukarama wasiyya da amanar junansu ,su rike junansu , ciwon dai na ajali ne rana daya zazzabin ya tashi zanga zanga suka nufi asibiti Daita ,akan hanya kmr ko wani lokaci Allah ya amshi rayuwarta batare dataga auren ya'yanta ba. 

bayan rasuwar mahaifiyarsu sun shiga damuwa kwarai da gaske kar ma dai mahamud yaji labari musamman idan yaga mukarama tana yawon kukan mutuwar innarsu ,duk sai tausayinta ya kamashi domin yasan dole kewar inna ta dameta, wani lokacin da kansa yake bata umarnin tashiga gidan mukotansu gurin hajara .

hajara kawar mukarama ce tare suka taso tun innarsu tana da rai, basa rabuwa tare suke al'amurasu tare sukayi makarantar boko haka islamiyya ,idan bakaga mukarama ba tana gurin hajara akwai sabo da shakuwa mai tsananin atsakaninsu dama kuma can iyayensu aminan juna ne, byn rasuwar mahaifinyarsu, mahaifin
hajara na d'aya daga cikin wanda ya taimakawa rayuwarsu dan haka shima mahamud lokacin daya samu rufin asiri bai manta dasu ba hatta karatu hajara shi yake biya musu kudi tare da kanwarsa ,komai ya tashi yiwa mukarama ya kan had'a da hajara yayi musu tare irin karar dayake musu , yasa iyayen hajara suke matukar jin dadi sosai, kullun cikin yabonsa suke.


wata rana mahamud na gida yana wanke mashin dinsa sai kuwa hajara tashigo gidan da gudu tana huci ,sauran kiris tayi karo da machine dinsa, ganin mahamad tsaye yana kallonta sai tayi saurin komawa da wani gudun a kunyace ,ya kwalla mata Kira ta dawo da baya yace "zo nan sai kin gaya min dalilin gudun naki, bana hanaku irin wannan guge gujen ba, hajara tasa hannuwanta duka ta rufe fuskarta dashi tana dariya shima diriyar yayi kana yace "wai hajara in tambayeki shin me yasa kike jin kunyata ne? 
tayi shiru kanta a sunkuye yace "ko nayi miki kama da surukinki ne?
 nan ma shr tayi yace "ni na lura duk sanda kika shigo gidan nan bakya sakewa ko kuma tsorona kike ji.? 

   hajara ta girgiza kai yace "to me yasa bakya iya kar'bar abu agurina sai dai mukarama ta kar'ba muku? 
nan ma shiru tayi mukarama ce ta fito daga cikin d'akin tana dry,mahamud ya kalli mukarama, sannan yace"wai me ya sa kawarki take jin kunyata? 

mukarama tace "inajin kodan taji goggo tace.... ya d'an dubeta da sauri yace "me goggon tace ? 
mukarama tayi shr tana kallon hajara tana dry kuma taki k'arasawa, dayake yasan halin shirmensu kurun sai ya rabu dasu yace "ku wuce kubani guri Allah yasa na sake ganin kuna irin wannan guje gujen sai kace wasu kanan nan yara. 

ranar wata litinin da safe mahamud yashiga gidansu hajara domin ya gaida su, hajara najin muryarsa taki fitowa daga cikin d'akin, byn sun gama gaisawa da mutanen gidan baban hajara yace"wai shin mahamud kai har yanzu baka fara tunanin aure ba ne? 
tunda Allah ya amshi ran mahaifiyarku ,ai sai ka d'aure ka nemi abokiyar zama kodan ka ragewa 'yaruwarka kewar innarku data rasa. 


yace "wallahi baba nima nayi wannan tunanin to sai dai ina kan dudubawa in samo wacce ta mallaki kanta, baba yace "naso ace ina da 'ya babba da zan kulla zumunta atsakaninmu amman tunda banida ita ga hajara nan na baka, sai a wanketa akai maka.
 
abin yabawa mahamud mamaki ya danyi driya kana yace "lallai baba kanason ka had'a rigima kasan kuwa yadda hajara take tsananin jin tsorona ?
bama haka ba baba yaushe za'a ce za'a yiwa hajara aure yarinyar da sai ma yanzu zasu kare primary, nima kuma dakake ganina karatu zan koma.

 mahaifin hajara yayi dry sannan yace" duk wannan bawani abu bane in dai kana sonta tunda kana son bokon itama sai ka barta tayi karatu agidanka. 
mahamud ya sake yin dry"amman baba baka ganin irin shirmen da zasu ta min acikin gida.

"duk babu komai sai ka jure har zuwa lokacin da zasu yi hankali mahamud ya d'an dubi babar hajara yace "kin dai ji goggo ,baba yana neman ya had'ani da rigima.
 cikin murmushi tace "to idan haka ne ai nice na fara furtawa kai dai tunda ance anbaka ba sai kayi fatan alkhairi Allah ya tayaka riko ba, babu yadda mahamud ya iya dan haka yace shikenan goggo na karba Allah ya rika min .

a daidai wannan lokacin mahamud yasamu gurbin karatu a jamiar d'an fodio dake jahar sokoto inda zai karanci kasuwanci.

zance aurensa kuwa da hajara abu kmr wasa, abu ya kankama yana da shekara biyu a jimi'a aka soma shirye shiryen aure cikin kankanin lokaci aka saka hajara lalle agama biki aka kaiwa mahamud amaryarsa .
 ba k'aramin raino mahamud yayi ba ,kafin hajara ta zama cikakkiyar mace ba, ya dai sha shirmensu ita da mukarama, haka nan ya dage da kyautata musu kullun yana tsaye akansu komai suke bukata zai siyo ya kawo musu da yake yara ne masu hankali da natsuwa sukayi zamansu lafiya su fad'i tare su tashi tare suna harkarsu su duka suna jin dadi zama da junansu ahankali ahankali rayuwarsu ta cigaba da gudana cikin jin dadi har sanda mukarama tasamu karatu a makaranta kwana dake aleiro government girl's comprehensive secondary school aleiro, yayinda hajara kuma ya samammata makaranta anan cikin garinsu, dan Allah ya tallafisu ya amshi rokonsu yasa aka bud'e musu jeka ka dawo.

 kullun zata makaranta idan ta tashi ta dawo gidan mijinta, tayi girki da sauransu hidimomi gida, rayuwarsu dai gwanin sha'awa in kaga yadda mahamud yake tattalin hajara sai ka rantse wata shararriya soyayya sukayi kafin aurensu. 

shi dai mahamud mutun ne mai son mace taji dadi gashi da busha sha, ga sakin fuska da saukin kai ,hajara dai ta samu soyayya da kulawa agurin mijinta, kullun babanta na saka masa albakar saboda ya rike amanar da'aka bashi kuma gashi da zumunci domin mahamud ya maida iyayen hajara tamkar nasa komai zaiyi ya kan nemi shawararsu haka suka cigaba da rayuwa ganin sha'awa .

ta bangarensa karatunsa ma bashi da wata matsala komai na tafiyar masa yadda yakamata idan ya dawo hutu kuwa zai kama kasuwancinsa na siye da siyar, sannan ya bud'e k'aramin shago a kofar gidansu wanda yake gyara agogo. 

******
lokaci zuwa lokaci idan mukarama tazo hutu hk samari ke yi mata caaaa amman sam mahamud ya kekashe kasa yace "bai san da wannan zance ba, karatu zatayi duk wanda yaji zai iya jiranta to ya jira ,wanda ba zai iya ba, ya k'ara gaba ya nemi matarsa, cikin haka ya kammala da karatunsa 
,kasuwancinsa ya k'ara bukasa, komai yana gara masa domin zuwa yanzu ya fantsana cikin duniya neman arziki, dan har sun bar kauyensu zuwa cikin birnin ilorin state .

byn wani kankanin lokaci sai gashi ya zama matashi attajiri dake da mallakin gidaje, ya sayi motaci baya ga yaran kauyensu daya Diba suke karkashinsa.
 zuwa lokacin yana da yaro daya mai sunan Ibrahim ,suna kiransa da akram da yake sunan mahaifinsa garesa ..

mukarama ta tagama karatunta na gaba da primary, ta zama cikakkiyar budurwa sosai gata da kyau da gogewa da iya tsara kwalliya ,cikin wannan lokacin ishaq abokin Muhammad wanda ya kasance abokin kasuwancinsa ne ya dawo daga kasar maleshia akan harkan kasuwanci da karatunsa .

ishaq hadadden matashi saurayi ne tsayaye mai zati da haiba uwa uba naira ta zauna ajikinsa asalinsa dan Kano ne amman babu inda baya shiga adalilin kasuwanci. 

wata rana ya kawowa Muhammad ziyara,inda Muhammad yace "mukarama ta kawowa abokinsa abun motsa baki,tashigo parlour'n cike da natsuwa da kamewa uwa uba kunya, ai kuwa ishaq yana d'aura idanunsa akanta yarasa tsukuni amman dayayi wani tunani sai yayi saurin kawar da abinda yaji akanta, ta ajiye tire ishaq yace "ga leda nan ta wuce dashi tsarabarsu ce aciki, sam mukarama taki d'auka, ya d'auka ya mika mata nan ma taki amsa yace" haba kanwarmu ina ganinki mai kalar wayyayu, a wannan zamanin yaushe ake kunya hk?
 mukarama ta juya akunyace zata fice daga parlour'n, 'yar drya Muhammad yayi yace "to in kin shiga ki turomin hajara kawai ,tana fita ishaq yace "amman wannan wani irin kunya ce hk sai kace ba yar zamani ba?

alhj Muhammad yace" ina ruwan mukarama haka Allah yayita komai nata sai ta had'a da kunya yarinya ce mai tsananin kawaici babu ruwanta. 
yace "da kyau hk nake son naga mace nada kawaici da alkunya a dukkanin al'amuranta da ganin kanwar tamu mijinta ya dace kwarai ya fad'i hk saboda tunaninsa ko tana da aure. 

alhj Muhammad yace"kuma ka gani bata da miji har yanzu bata tsaida miji ba karatu take domin ina da burin akanta,ina son na ingata rayuwarta da karatu boko domin a dama wannan duniyar daita, shiyasa duk masu kawo hari nake katse masu hanzari har sai ta gama, yanzu haka tana matakin diploma .

ishaq ya d'an dubesa a razane domin yasan asaninsa mutane karkara haka ,basu fiyye barin yaransu su jima hk batare da yin aure ba ....
"gsky abokina kayi nmj k'ok'arin gurin ingata rayuwarta ,yanzu dai kace babu kowa akasa masu neman aurenta? 

"babu kowa ina suka ga fuska, ai sai sunga fuska tukun zasu zo, ni dai burina tayi karatu mai zurfi ta yadda zata taimaki al'umma da ita kanta, nan dai suka bar zance suka shiga hirar kasuwanci dayake daman harkar kasuwamci ne ta had'asu har suka zama abokai, acikinsu duk wanda wata harka tashigo hannunsa daya san za'a samu alheri y kan janyo dan'uwansa ciki, su samu alkhairi tare kasancewar dukansu ba masu kyashi ko bakinciki bane ,kowa yana k'aruwa da kowa suna harkar arziki tare gwanin sha'awa. 

tunda ishaq yakoma gida sai ya kasa samun sukunin zuciya duk yadda ya runtse idanunsa mukarama yake gani tana yi masa gizo ,haka nan abin mamaki jiyayi gbdy ya tsinci kanshi da matsanancin kaunar mukarama ,ganin dayayi mata ya gigita kwalkwaluwarsa ,sosai yarinyar ta rikitashi ,ya rikice akanta har tunaninta na neman hanashi sukuni yin barci, shi kansa sai juya al'amarin yake aransa yadda farat daya ya gigice akanta gashi dan'uwanta na da buri akanta, dan hk ya danne abun aransa yacigaba da hakuri ,haka soyayar mukarama yayita cinsa arai har sai da aka samu wasu yan watani. 

************
 ran nan dai ishaq ya kasa hakuri adalilin soyayyar mukarama da kullun take sake huda kahon zuciyarsa, dan hk a zaunen da yake agaban mahamud yasoma maganar yadda yake son mukarama.
mahamud yayi shr yana sauraron abokinsa har yagama zayyana masa irin kaunar dayake yiwa mukarama,Muhammad yace "naji dadi kwarai kuma ina matukar farinciki da wannan bayani naka ,sanin kanka ne kafi karfin komai agurina ,zai yi wuya ka nemi wani abu a wurina na hanaka, musamman ma irin wannan alfarma ta aure, to amman akwai wani hanzari ba gudu ba kmr yadda kasani, bazan aurawa mukarama mijin da bazai barta tacigaba da karatunta ba, matsawar ka amince zata cigaba da karatunta agidanka shikenan na amince kaje ka nemi yardarta matukar ta amince da kai zan aura maka ita.

ishaq ya sauke naunauyen ajiyar zuciya kana yace "wannan ba wata matsala bace ni kaina har yanzu akan karatu nake kasan da haka ,domin lamarin kasuwancinmu na bukatar ilimi mai zurfi,bugu da kari ilimin mace nada matukar mahimmanci arayuwa.

 "haka ne kam Allah yasa mu dace kana iya turo magabatanka idan ta amince , ishaq yace "ameen had'e dayiwa abokinsa godiya " domin sosai yaji dadin lafazinsa mahamud na gama fadar hk ya bari parlour'n.

 ishaq ya nemi ganawa da mukarama ,byn tashigo parlour'n suka dan yi shru kad'an sannan yakira sunanta "ko kinsan zuwan nawa na yau dominki ne sabanin sauran lokuta?
 ta d'an kalleshi cikin natsuwa, yayinda ta zuba masa idanu tana kallonsa da sauraren abinda zaice dan gabad'aya zuciyarta ta matsu da son jin abinda ke cin ransa akanta, domin itama tana jin wani abu a game dashi .
 yacigaba "hakika mukarama dazaki min alfamar dana dan gutsara miki abinda ke cin raina a game dake, Allah yasamin tsananin kaunarki tun ranar farko dana d'aura idanuna akanki dayake nasan ba aure yayanki zai miki a wannan lokacin ba sai nayi kokarin danne sonki cikin zuciyata har sai yanxu ,a yanzu dai ina gabatar miki da kaina amatsayin wanda yake son aurenki amman menene ra'ayinki akaina ? 

mukarama dai tayi shiru saboda batasan amsar dazata bashi ba, domin mutumin yana yi mata kwarjini ganin bata da niyyar bashi amsa yace "haba mukarama ya kikayi shr ai gara kiyi magana shi sha'anin aure ai ba'a yinsa da wasa zan so jin ta bakinki koda bakya sona barema bana fatan haka nafi son kiyi min alfarma bisa soyayya kar ma ki tsaya duba alaka don ba itace tasani sonki ba.

" kyawawan halaiyenki da dabi'unki na kirki ne suka janyo zazzafar kaunarki ,ki taimawa rayuwar wannan tsohon tuxuron ki aureshi domin idan kika ki aurensa ina tabbatar miki hk zai k'arasa sauran rayuwarsa batare daya ajiye iyali ba. 

mukarama ta cigaba da yin shiru sai dai wannan karon kanta na sunkuye ,murmushi yayi saboda sanin halinta na kunya "haba zuciyar ishaq ki dan yi min magana ko naji dadi "tayi dariya amman batace komai ba yace"kenan dai ana son ishaq ya hakura," mai yiwuwa ina da wani abun da baza a soni dominsa ba? 

sai a lokacin ta girgiza kanta, yace "ni kam muddin ba magana ki kai ba, gani nake ban canci asoni ba ,shi yasa kika barni da kokon barana a hannu, ai sauran maneman ba hk ake musu ba, ko kuma ko dan anga ni babban yaya ne kike ganin nayi miki tsufa? 

maganarsa ta bata dariya har ta sa ta d'ago kanta da sauri suka dubi juna sannan tace "ko kad'an ba haka bane, ni dai aguna baka da wani aibu da kowace irin mace zata kika ,sai dai abunda nake son kagane ban taba yankewa kaina hukunci ba sai dai yayana ya yanke min.

"idan ta wannan bangare ne mugama magana da yayanki har ya amince har ma da sharadinsa nason ki cigaba da karatunki byn aurenmu, na kuma ji na gani na amince da hakan ,saboda ina matsanamcin sonki "duk da haka ni dai nayiwa kaina alkwarin komai zanyi sai da amincewarsa.
  "da kyau kinga wannan biyayyar taki tana daga cikin abubuwan dayasa na kamu da sonki tunda kin tabbatar zabin d'anuwanki shine zabinki, a she dai naci babu hamayya kenan, domin na tabbatar d'anuwanki ba zai iya zaba miki wani fiyye dani ba.

"amman duk da hk xan baki lokaci kije kuyi shawara da matar yayanki tunda itace ta hannun damarki, dan ta abokina shi bana jin komai domin shine yace in nemi soyayya agurinki domin yana son baki cikakkiyar yanci shiyasa nake ganin yanzu shawara ta rage keda hajara babu ruwan aminina ,dan ko yau muka daidaita gobe ma yana iya d'aura mana aure.
   ta dan fad'ad'a murmushinta "shikenan Allah yayi mana zabi mafi alkhari "yauwa masoyayyita abinda nake son ji kenan daga gareki, domin zabin Allah shine mafi alkhairi a gurinmu, gbdy dai ishaq ya gama kashewa mukarama jiki da salon soyayyarsa wanda sukayi tasiri a zuciyarta.

 sosai yasamu matsugunni agurinta ,byn sunyi sallama tare da yi mata alkwarin zai dawo wani sati domin jin shawarar data yanke, kafin su rabu sai da yayi mata alkhairi mai yawa wanda kunya ta hanata kar'ba ,sai daya takurata sosai sannan ta amsa game da yi masa godiya tashige ciki, tana shiga Kai tsaye d'akin hajara tashiga domin ta fesa mata labari da bata ganta cikin parlour'n ba sai ta bita uwar daka ta isketa kwance ita da akram akan lafiyayyen gadonta suna ta sharar bacci cikin nishadi ta dan ja ta tsaya tana jan tsaki .

"ke kam aunty hajara kin cika so baccin tsiya ta fad'i hkn a fii yayinda tasa hannu tana girgizata, ta d'an motsa kadan tare da rungume d'anta ajikinta batare da ta bud'e idanunta ba ta sake komawa bacci abinta .
a hanzarce mukarama ta maka mata duka, hajara a firgice ta d'an bud'e idanunta ganin mukaramaa tsaye akansu tace "kai d'an Allah mukarama in banda d'aukar haki ki barmu muyi baccinmu .
mukarama cikin zolaya tace "mijinki yace na taimaka na tasheki sai nayi laifi? 


hajara da sauri ta watseke tare da tashi, zaune har da d'an murmushinta, mukarama ta kwashe da dry "uhm yar dadi miji daga jin zance miji kin wani wartsetake to karya ne bashine yake nemanki ba ni nake son mgn dake hajara ta d'an kai mata duka "kyaji da karyarki ke daman babu damar kiga mutun yayi bacci sai kin tasheshi .
mukarama tace "ai ina ganin akan shegen baccin nan naki sai nayi miki kishiya in tura amarya d'akin yayana kina nan kina shirgar bacci.

 "haba dan Allah kin isa ai dagani babu kari ai ni nafi karfin amarya. 
"kiyi cika bakinki kigama zanyi maganinki .
suka fashe da drya .
kiyi driyarki ahankali karki tasar min da yaro inji cewar mukarama. 

"ai kuwa babu mai hanani magana, kiyi shru albishir nazo miki kinsamu dankareren suruki idan bakiyi shiru ba wallahi na fasa "hajara tazaro ido "da gaske koda wasa "da gaske mana "to waye surukin nawa? 
"abokin yaya.

 hajara tayi dry har da shewa "gsky in dai shine yayi min, mukarama ta zauna ta zayyene mata yada sukayi sai data gama jin komai tayi murmushi tace "haba ai daman nasan za'a rina shiyasa kika ga ko mamaki banyi ba kinsa ance inkaga kare yana shinshina takalmi d'auka yake son yi ,Allah dai ya tabbatar da alkhari gsky kinyi sa'a more miji d'an gayu d'an boko attajiri kyakkwawa...

 "kinga ba surutu nace ki min ba shawara nazo kibani "hajara tace kawai ki auri abunki tunda mu duk muna sonshi ba wata matsala kuma bashi da wani aibu dan ko mutumin kirki ne gashi attajiri in kika aureshi zakiji dadi mukarama tace"ki ture zance kudi kinsan ni kudi basu dameni ba, ni kawai kwanciyar hankali nake nema atare da namiji.

"karki damu in dai kina sonshi kurum ki aureshi ni dai ina baki goyon baya karma ki tsaya wani hasashe kiyi aurenki kawai da zuciya daya ki shiga gidansa da kyakkyawar niyya Allah ne mai bada zaman lfy bare ma nasan mutumin Nada kirki, zai rikeki amana. 

mukarama tace" shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi in yaya yashigo ki gaya masa na amince hajara tayi dry shikenan ishaq zai d'auke mana ke ,zamuyi kewarki in kin tafi dawa zamuyi hira? 
sai ki dinga yi da mijinki, ni meye zai dameni tunda nasamu nawa abokin hirar.

hajara tace "dadin abun dai baki da baki balle nasa ran zaki yi hira da miji "ki kwantar da hankalinki wannan karon zaki sha mamaki yadda bakina zai bud'e bari dai ayi auren ,ni nasan irin soyayyar da zan nunawa ishaq ,ke ko fita sai naga dama zan barshi suka kyalkyale da dry gabad'aya hajaa tace "kmr gaske "a ture maganar wasa zan dinga tarairayarsa domim karya hango wata. 
hajarra tace "ai shi nmj bakomai bane idan yashiga hannun mace mai wayo, komai girmansa ya kan dawo tmkr yaro in har ya had'u da macen da ta iya kissa sannan ladabi da biyayya ma wani ginshiki ne a cikin zaman aure, amman mu mata hausawa duk bama d'aukar wad'an nan abubuwan da mahimmanci .

mukarama tace "ai kuwa duk kina yi babu laifi kina k'ok'arin kamantawa gashi nan kullun sai k'ara rikita min yayana kike abun bako tausayi "kema ba gashi nan kina shirin zuwa ki rikita yayan wasu ba "
amman ai kinsa ni nafiki kunya bazan dinga irin abinda kike yiwa yayana ba. 

"zauna nan garin jin kunya a je ayi bake, gara ma in zaki cire kunya tun wuri ki cire domin mazan zamani nan basu wani so kunyar nan, ki zage ki tarairayi mijinki, "yanxu ina karuwai suke a gari? 

"babu su domin karuwai na d'akin mazajensu, wallahi wata idan kikaga iskancin datake zubawa mijinta domin gamsar dashi sai kinyi mamaki ,yanzu karuwai babu market kowace takama gabanta.. 
suka fashe da drya a daidai lokacin da Muhammad yashigo ya daga labule d'akin "to gwana kingama mata hudubar? 

kunya duk takama mukarama a zuciyarta tace" Allah dai yasa ba duka hirarsu yaji ba hajara kuwa ta dake tace "kai kace daman la'be kake mana ,ka dai san la'be babu kyau. 

cikin driya yace "ina ruwana da hirar shirmenku, ke din ma yaushe kikayi baki har da zaki koyawa wata yadda zata rikita miji ya zauna a tafin hannuta? 

mukarama tayi saurin cewa "kai yaya bafa hk tace min ba, zancemu ne kurun mukeyi ,"idan haka yaji sai me kissa nake koya miki don abokinsa yazamo a tafin hannunki Muhammad ya dube yana yar dariya "ke din me kika iya balle har ki koyawa wata? 

ta d'an hararesa "haka din da kake rainawa dai ina yi ma ,ina laifi ma da kasamu hk wasu mazan nacan basu samu irin kulawar da nake maka ba. ganin mukarama na gurin yasa yayi saurin wayancewa "karki sake yarda da hudubar wannan kawartaki mallake nmj a tafin hannunki bashine ba ladabi da biyayya shine gaba da komai ,halaiyar kirki ake neman ga mace. 


hajara tace "da kuma me ?
yace "da iya girki ta sake cewa byn nan fa? 
tana kallonsa tana dry "ke mukarama ina ganin , in dai abokina yayi miki shikenan sai ayi magana aure kin dai san ba gurin da za'a tsaya 'bata lokacin bane , in kuma ba kya sonsa gara tun wuri ki gaya min in sanar dashi domin babu wata yaudara atsakaninmu dashi, ko ban fad'a miki ba Kinsa matsayinsa agurina, in kina sonsa komai cikin gaugawa za'a yi agama ba tsayawa za'a yi ana ja masa rai ba ,kinsa ni ban iya kwalo kwalo ba ya fad'a yana kallon mukarama wace tace "yaya ai magana tana hanunka sai abinda kace, ni duk abinda ka yanke daidai ne. 

girgiza kai yayi "haba mukarama ki dai ki fad'i son zuciyarki idan kina so nima ina so, idan kuwa baki so nima banaso "ai ni matsawar kana da rai bazan iya yankewa kaina hukunci ba, sai abinda ka yanke min,. 
ya d'an yi shiru hajara tace "tunda hk ne shikenan aje mun zabi abokinka sai kace ya fito ya d'an washe baki yana murmushin jin dadi "lallai kun kyauta min kuma mukarama ta fiddani kunya in ta aureshi zan fi kowa farinciki saboda abokina mutumin kirki ne nasan bazaki ta'ba nadamar aurensa ba, nagode Allah yayi miki albarka bisa biyayyar da kike min..

mmn sudais ce
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive