MUWADDAT 03

💗💗💗💗💗💗
      MUWADDAT
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗             ~NA~ *AYSHA A BAGUDO*     ~DEDICATED TO~   
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
     _(UMMIN KADUNA )_


WARNING!!! 

FOR THE FIRST TIME !!!! I WILL LIKE TO SAY," DON'TS READ THIS NOVEL ,IF YOU KNOW YOU ARE NOT MARRIED... ❌❌❌COZ THIS BOOK CONTAINS ONLY FOR MATURE PEOPLE , IF YOU READ IT, IS FOR YOUR OWN RISK ...... 


WATTPAD @HAUESH

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM 


Page 3


......Tun da alhj Mahamud yasoma sanyawa mukarama albarka ,murmushi yaki 'bacewa a fuskarta ,hajara ta du'beta a sukwane tace "kai duniya mukarama ko kunya baki ji ,ana zance aurenki kina guri , sai wani nishad'i da annashuwa kikeyi ..


Wani sabon murmushi mukarama ta sake yi "bil hakki da gaske mugun son ishaq ya kamata sosai tun kwanaki ma na lura da rawar kafar da takeyi akansa ,kalli ma yanzu kaga rawar jikin da take ,barin in taji yazo gidan ta dinga 'bare 'bare kenan tana hanzari zuwa gaidashi ,wata sabuwar kunya ta kama mukarama ta tashi da sauri zata fice daga d'akin tana dariya ,alhj Mahmoud ya dakatar daita "kinga dawo kiyi zamanki in dai tsiyar hajara ce kin saba daita ,tunda tayi baki neman take ta bud'e bakin kowa ta karfi da yaji.

Mukarama tace 'kai ma yaya kayi mata kishiya kawai mu huta da halinta hajara ta kwashe da dariya ahayyeeeeee yau zan ga had'in kai acikin gidan nan, to Dan kince yayi min amarya sai me ?

Ince ba'a kaina aka fara ba sannan kuma ba akaina zata zauna ba ita shegiyar kishiyar, tazo Dan ubanta ...


"Duk dadin baki yayanki yake miki Dan yaga zaki yi auri abokinsa yanzu da wani ne da watakilla ya rungumi transformer Amman shi Da kansa yasan mijin mace daya ne ..


Alhj Mahmoud yace " yarinya karki cika baki in kika zugani gobe gobe sai ,naje na biya sadakin wata yarinya da take mutuwar sona in ga tsiya"

Mukarama ta kwashe da dariya, har da yiwa hajara gwalo, hajara tace" lallai mukarama wai ni kike kwayewa baya agaban yayanki bari ?

"La yaya kalli kaga daga jin zancen kishiya har idanun hajara ya raina fata ..sukayi Dariya gabadayansu har hajara wace cikin dariya tace "zan miki mummunar addu'a kema kina shiga gidan ahmed da wata biyu ya gano wata ,tunda dai zuga shi kike yi ayi min kishiya ,wace Sam sunanta ma bai da dadin fad'a .

*******

Byn Sati biyu ishaq ya sake zuwa gurin mukarama byn sun gaisa suka zarce da hira, wannan karon yaji dadi sosai da yadda ta sake dashi har suka tautauna sosai da kanshi yace "na ji dadin irin kar'buwar Dana samu duk da dai har yanzu baki furta min cewar kina sona ba ,Amman dai na gamsu dari bisa dari sannan na gamsu da bayyani da yayanki yayi min kuma hausawa sunce labarin zuciya a tambayi fuska ,ina ga tun da mun rigada mun amincewa juna ai ba sai an d'auki dogon lokaci ba ,abin nan tuwona maina ne zan so ace mun yanke lokaci kinga tun daga yanzu mu fara shirye shirye Dan tun Dana sheidawa hjyta batunki ta kasa zaune ta kasa tsaye, domin burinta arayuwa bai wuce taga na ajiye iyali ba Amman me kika gani?


Ta D'an dubeshi cikin murmushi tace "ina ganin wannan maganar zaifi kyau kuyita tsakaninka da yayana "eh na San da haka ,Amman shi Mahmood ya sheida min, in dai ina bukatar aurenki ko gobe ma zai iya d'aura mana aure ,shi yasa nake ganin nida ke yakamata mu zauna mu tsara lokacin da muke bukata .


Ta janyo ajiyar zuciya da kyar ta fesar saboda yadda maganarsa ke shiga jikinta kana tace " to kai kmr wani lokaci kake ganin ya dace ?

"Yauwa zuciyar ishaq ni dai idan kin amince zuwa karshen shekarar nan yayi min ,nan da wata biyu kenan sai ayi komai cikin gaugawa a d'aura aure tare da biki, ta D'an fad'ad'a murmushinta tana kallonshi tmkr yau ce rana ta farko data soma sanyashi acikin idanunta .

ahankali muryata ta fito still kwayar idanunta na cikin nashi tace "haba dai nan da wata biyu ina ma laifin wata uku .

Yayi saurin ware mata matsakaitan idanunsa ,"wani irin wata uku idan dai baso kike labarin mutuwata ta riskeki ba ,ko na dibo kayana na dawo gidanku da zama ba,ki San ko irin yadda nake jinki a zuciyata? 

"In aka kai watanin uku ba'a shafa fatiha ba,ai sai na fara sanbatu ,mgnr yabasu dariya gabadaya 


"in dai ba wani babban uzuri gareki ba ,gaskiya bana son a dau lokacin domin ina son muje aikin haji tare InshaAllahu,dan alkwari nayiwa kaina bazanje aikin hajji ba sai da matata saboda zanfi jin dadin tafiya tare da iyalina, Amman ban sani ba watani uku da kika ambata ko akwai wani tanadi na musamman da za'a yi domina ?

"sai in hakura har zuwa wani lokaci kinsa ku mata bakwai rabo da daburu da hikimomi. 
"Ta sunkuyar da kanta kasa "babu wani shiri da zanyi daman gani nake kafin lokacin mun Dan dada fahimtar juna "ai babu wata fahimtar data wuce kaunar da take cikin zukatanmu kin Riga kin San ina sonki ,kema ko baki fad'a ba nasan kina sona batun yau ba na gane akwai kaunata a zuciyarki .

A kunyace ta rufe fuskarta tana dry "kinga kuwa fahimtar juna bazata yi wahala ba ,yanzu dai kin amince min karshen watan nan nake son na turo kayan aurena kuma in kin tashi tarewa banason yayanki yayi wahalar siyan komai domin babu abinda ban zuba acikin sabon gidana ba ,komai akwai ke kawai suke jira .

Cikin murmushi tace "bakasan yadda yaya ya fika d'aukin wannan auren ba ,domin tunda yaji ka furta maganar auren yayi oder a kamfan, hatta kayan kitchen ya gama siya ..


Ishaq yayi D'an murmushi "ina ruwan mutumina ai naga alamar yafi kowa doki auren nan, to tun da yake ya rigada ya siya miki kayan d'aki babu komai asasu a extara room's.

 kanta a sunkuye tace "shikenan Allah ya nuna mana ya kara budi Amman ni dai Dan Allah karkace zakayi wata hidima kayan aure komai na yafe, ya D'an dubeta cike da fara'a a zahiri gsky yaji dadin kalamanta "GSKY sai dai kiyi hakuri Dan koni bance zanyi ba dole dangina suyi bare kuma allah ya horemun abinda zan miki dole nayi komai da'akewa matashiyar budurwa kmr ki, kisawa ranki duk abinda ake yi na hidimar aure zan miki ,ni ko banason mace zanyi mata hidimar aure balle ke da zuciyata take kwakwa tayi murmushi "to ai ni nace na yafe ko?


Cikin murmushi ya tsura mata ido yana dubanta salon maganarta da komai na Burgesa "zuciyar ishaq ya fad'a yana sake tsareta da idanunsa "ki duba kanki da kyau ,kiga irin baiwar halittar da Allah yayi miki ai jikinki ya wuce irin macen dazatace ta yafe kayan aure ,kuma ya yafu din.


Ta rufe fuskarta tana dry saboda kunya "dadina dake kin fiyye kunya da yawa wallahi yanzu haka zamuyi zaman aure kina jin kunyata? 

"Kayi hakuri zan D'an rage in naje gidanka "gsky yakamata Dan nasoma jin tsoron wannan kunyar Dan hka tun daga waje yakamata ki soma ragewa kinga idan na kaiki gidana na zamo abokin rayuwarki, kinga maganar kunya ma bata taso ba ,kunyar nan ki kawar daita domin mu had'u mu ingata rayuwar aurenmu.

" ni zama abokin wasanki ,abokin nishadinki, abokin Hirarki ,abokin barkwancinki ,kinga ni mutun ne mai son nishadi don hk nake bukatar cire wannan kunyar ,ko tun yanzu ni na cireta da kaina ya kai hannunsa zai ta 'bata tayi saurin dojewa da sauri zuciyarta na bugawa domin tunda taso arayuwata babu nmj daya ta'ba d'aura hannunsa ajikinta "babu abinda zan miki ,domin Sam bakiyi kama da tsagairan mata ba ,akwai cikar Kamala atare dake ,hankalinki da tunaninki tare da natsuwarki yasa nake kyautata kyakkyawan zato acikin rayuwar aurenmu ,Dan haka ina fatan zaki cire kunyar nan kiyi masa babban ma'aji agidan yayanki domin ishaq a yunwace yake dake ,ba zai iya da wannan kunyar ba "ki yi min akwarin cire kunyar ko na soma cirewa da kaina ?


Muryarta a matukar sanyaye tace "karkaji komai nayi maka alkwarin InshaAllahu zan cire ,tun yanxu ma na fara cirewa ...duk yadda taso kauce masa sai daya matsota sosai tmkr zai shige jikinta yana narke mata har yayi nasarar kamo fuskarta ya daidaita da nashi suna shakar numfashin juna ..

Wata irin soyayya ishaq yake nuna wa mukarama mai tsuma zuciya sai dai duk yadda yaso ya dinga romancing dinta taki yarda ,ta dinga nuna masa hkn haramu ne ya bari har sanda zasu mallaki juna .

Ishaq ya turo iyayensa aka kawo komai na aure tare da tsaida lokacin wanda bai wuce wata biyu kamar yadda ya bukata .
**********

Anyi biki lafiya amarya ta tare agidan angonta ishaq ba k'aramin shirya mata gida yayi ba ,gida kmr aljannar duniya komai yaji ban da tsiya babu abinda babu acikin gidan duk wani kayan jin dadi da more rayuwa an zuba mata takowani bangare ,gidan kam sai Wanda yagani ya had'u karshen had'uwa ,kai daga ganin gidan kasan naira ta zauna ,gabadaya mukarama ta tsinke da alamarin ishaq duk da tasan wani kusan attajiri ne ,Amman shigowarta gidansa tasan ya taka matsayin mai girma wajen dukiya.

 byn 'yan kawo amarya sun watse mukarama ta sake sabuwar kwaliya saboda shirin tarbar miji duk da yadda zuciyarta ke luguden bugu, ta saka wani ratsetsen blue less ,Wanda tsayawa fad'ar kudinsa 'bata baki ne, ga zinarin da yayanta ya sai mata hannu da wuya sai sheki take irin turarrukan da tayi amfani dasu ita kanta bazata iya lisafasu ba, gabadaya gidan ya d'auki kamshi a haka ango yashigo ya sameta zaune a bakin gado lullube da mayafi ya D'an sa hannu ya yaye mayafin data rufe jikinta dashi yana mata dry.

Tsura mata kyawawan idanunsa yayi yana kallonta hk nan yaji amarya tasa tafi kowace mace kyau a duniya yasan gwanar Ado ce Amman na yau yafita daban kodan ya had'e Dana amarci ne, bai sani ba ,kallonta yake yana kallon halittar Allah irin kallon kurulla ,sai ta D'an sunkuyar da kanta tana murmushi habarta ya d'ago yasanya kwayar idanunsa cikin sannan yace "zuciyar ishaq duk yadda akayi kinyi kuka ko?
Ta D'an dubeshi kawai kana tace "me kagani ?

"Naga idanunki sun canza sunyi ja, kin tuna wani abu daya Sosa miki zuciya ne ?
Tayi murmushin tana neman wayancewa ,in har ta sanar dashi dalilin kukanta zatayi tace mishi me ?
Kmr yashiga zuciyarta yace "kiyi hakuri zuciyata ko baki fad'a ba ni nasan abu daya zai iya sakaki kuka a irin wannan lokacin bai wuce kin tuna da innarki ba, musamman idan mace tayi auren fari Amman ki kwantar da hankalinki ishaq zai rikieki amana, zai zame miki komai ,kani yaya dangi da komai nayi alkwarin kyautata miki InshaAllahu, daga yau bazaki sake kukan mutuwarta ba, komai runtsi zanyi k'ok'arin sanyaya miki zuciya ,zan rikeki amana zan kula da maraicinki, zan kyautata miki, San jiyar dake dadin dake cikin duniya gwargwadon ikona, zan soki, zan kaunaceki, Zan faranta miki bazaki ta'ba nadamar aurena ba, ta 'dan murmusa cike da jin dadin kalamansa sannan tace "nagode da alkwarin daka d'auka zan tayaka da addua Allah yabaka iko sauke nauyi dake kanka "amen. 

 Ka fad'i komai bakayi mgn akan cigaban karatuna da yayana ya kwallafa rai akansa ba ...ya tsinkayi muryata cikin dodon kunnenshi ya d'ago ahankali ya tsareta da ido kawai sai dry ta subuce mata aiko suka sa dariya gabadayansu ya kamo hannuta cikin nasa "ban manta ba ina sane zakiyi karatu har sai kin gaji matukar kina tare dani, domin ni kaina mai son yin karatu ne ..
 Yanzu kin gaji dayawa saboda hidimar biki ,a yanzu Hutu kike bukata ba zance wani karatu ba, Dan hk nake son ki biyoni muje d'akina Muje ki kwanta ki huta..


Batare da mutsu ba ta Mike ta yafa mayafinta ya d'aukar mata sabuwar rigar bacci suka fito tare da kansa ya rufo bangarenta suka fito suka nufi bangarensa suna shiga yace "ina ganin kafin bacci yakamata mu fara gabatar da sallah nafila kmr yadda Manzon rahma ya Umarci ma'auratan da suka yi sabon aure suyi ,Dan neman zaman lfy da samun zuria na gari.....


Mmn sudais

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive