SHARHIN FIM ƊIN I

SHARHIN FIM ƊIN I 

I fim ɗin India ne da aka fitar da shi a cikin shekarar 2015 a harshen Tamil. Shirin ya ƙunshi abubuwa da dama kama daga soyayya, tausayi, cutarwa, nishaɗi da kuma dambe. 

MA'AIKATAN SHIRI 

Umurni: Shankar

Shiryawa: V Ravichandran

D. Ramesh Babu

Tsarawa: Subha (kalamai)

Rubutawa da tsara labari: Shankar

Sauti: A. R. Rahman

Jami'in Shiri: P. C. Sreeram

Tacewa: Anthony

Kamfanin da ya shirya: Aascar Film

Yaɗawa: Aascar Film 

Global United Media (Kerala)


Ranar fita: 14 January 2015

Tsawon Shirin: minti 188
 
Ƙasa: India

Harshe: Tamil


Kasafi: est. ₹100 crore


Kasuwanci: est. ₹240 crore

 An fara ɗaukar wannan shiri ne tun a ranar 15 July 2012, amma sai da aka yi shekara biyu da wata takwas kafin aka kammala aiminsa. Mafi yawancin shirin a ƙasar Sin aka ɗauke shi. Sai dai an ɗauki wasu ɓangori muhimmai a Chennai, Bangkok, Jodhpur, Kodaikanal, Pollachi, Bangalore da kumaMysore. A yayin fitar shirin, an fassara shi izuwa harshen Telugu da Hindi, yayinda daga baya kuma aka fassara shi izuwa harshen Hausa. 

 Masana da masu sharhi akan fina-finai sun yabi irin rawar da jarumi Vikram ya taka a shirin, kuma sun yabi kayan aikin da aka yi amfani da su tare da sautin shirin da Waƙoƙinsa tare da kayan kwalliyar da aka yi amfani da su a cikin shirin. Sai dai sun caccaki yanayin tsarin labarin da kuma tsawonsa. Sai dai hakan bai hana shirin kawo maƙudan kuɗade a harkar kasuwancinsa ba, domin kuwa sai da ya kawo kimanin dala miliyan talatin da biyu a harkar kasuwancinsa na duniya baki ɗaya, watau (US$32 million) worldwide. Hakan ya sa shirin ya zama fim ɗin Telugu da ya fi kowanne kawo kuɗi a wancan lokaci kuma ya zama fim ɗin Vikram da yafi kowanne kawo kuɗi a wancan lokacin. Hallau kuma dai, shirin ya samar wa jarumin lambar yabo ta gwarzon jarumin shekara na FILMFARE watau Filmfare Award for Best Actor – Tamil. 

LABARIN SHIRIN 

Lingesan wani mai motsa jiki tare da tara ƙwanji ne daga Chennai wanda babban burinsa shi ne ya zama na ɗaya a Indiya, watau dai yana so ya kai matakin Mr. India. Cikin sa'a kuwa sai ya lashe gasar Mr. Tamil Nadu watau gwarzon yankinsa, wanda kuma hakan ya bashi damar shiga gasar lashe kambun Mr. India. 

Kwatsam sai ya kamu da son wata kyakkyawar 'yar tallar gidan talabijin mai suna Diya. Ba su daɗe da haɗuwa ba, sai Diya ta faɗa cikin matsala, domin kuwa abokin aikinta mai suna John ya tsula mata tsiya ta hanyar daƙile mata hanyoyin kasuwancinta saboda ta ƙi yarda yayi lalata da ita. 

A yunƙurinta na ganin cewa ta dawo da martabar aikinta, Diya sai ta yanke shawarar maye gurbin John da Lingesan a wata ɗaukar talla da za ta yi. Ɗaukar za'a yi ta ne a birnin Sin a daidai lokacin da za'a yi gasar Mr. India, amma sai Lingesan ya amince ya sadaukar da burinsa domin faranta mata. 

Kafin ƙiftawa-da-bismillah sai ga Lingesan ya canja nan da nan sakamakon kulawar da wata masaniyar salon Diya watau Osma Jasmine ta yi masa, wanda ita wannan osma ɗin irin matan nan ne da aka sauya wa halitta izuwa rabi namiji rabi mace. Da fari aikin ya ƙi musu kan gado saboda kunyar Diya da Lingesan ya ke ji, hakan ya sa mai bada umurnin ɗaukar ya baiwa Diya shawarar ta yi kamar ta kamu da son Lingesan domin ya zage ya bada abinda ake so. Hakan kuwa aka yi, kuma nan da nan aiki yayi kyau. Sai dai kuma ba'a daɗe ba Diya ta bayyana wa Lingesan gaskiyar magana. Jin haushin hakan ya sa ya maida hankalinsa kan aikin tallace-tallacen gidan talabijin ya ƙyale ta. A hankali kuwa sai gashi sun samu nasara sosai, har ya zama in dai za'a haɗa mace da namiji a talla, to su ne zaɓin farko ga kowa. Da sannu dai, sai Diya ita ma ta kamu da Lingesan har ma aka yi musu baiko. 

A kan harkarsa ta gina jiki gami da tara ƙwanji da kuma talla a talabijin, Lingesan ya samu maƙiya da dama, cikin su akwai John wanda tun daga lokacin da ya shigo harkar shi kuma lamura su ka kwaɓe mishi, har ta kai shi ga yin ƙananan tallace-tallace domin tsira da mutuncinsa. Akwai kuma Osma wacce ta kamu da son Lingesan har ta bayyana masa amma sai ya ƙi amincewa. Akwai kuma ɗan kasuwa Indrakumar wanda kamfaninsa ya samu giɓi sosai sakamakon ƙin yi musu talla da Lingesan yayi saboda rahotanni sun nuna akwai maganin ƙwari a ciki. A gefe kuma can a kwai Ravi wanda shima ya shiga gasar Mr. Tamil Nadu amma sai Lingesan ya yi nasara a kansa. Waɗannan mutum huɗun sai su ka shirya yadda za su ɗauki fansa akan Lingesan. 

A a saura kwana biyu a ɗaura aurensu, sai gashi da haƙoran Lingesan su ka fara zubewa a hankali yayin da fatarsa ita ma ta fara lalacewa. Hakan ya sa shi ya tuntuɓi abokinsa Vasudevan wanda likita ne kuma shi ne mai kula da ahalin su Diya. Vasudevan sai ya bayyana mishi cewa ya kama da wata mummunar cuta ce da ba'a san asalinta ba kuma ba ta da magani. Kamar wasa fa dai, abu sai ƙara gaba yake yi, fuskarsa da jikinsa duk suka fara lalacewa har dai ta kai ga ya koma mai ƙusumbi. A wannan hali, sai Lingesan ya yanke shawarar ɓacewa daga idon duniya tare da rayuwar Diya, ya cimma hakan ta hanyar ƙaryar cewa ya mutu, abokinsa Babu ne kawai da Vasudevan su ka san cewa bai mutu ba. 

 Lingesan sai ya roƙi Vasudevan cewa ya auri Diya, domin shi kaɗai ne ya san halinta kuma ya fahimceta, Vasudevan sai ya amince, inda aka sa ranar biki. 

A ranar bikin Diya sai wani likita mai suna Thiruvengadam ya bayyanawa Lingesan cewa, duk da abinda likita Vasudevan ya faɗa, a zahiri yana fama ne da mura irin ta H4N2 influenza wacce cutar "I"the virus ce ta samar da ita. A ta kuwa cutar ba'a taɓa samunta a ko'ina face in allurarta aka yi wa mutum. Lingesan sai ya fahimci cewa John, Osma, Indrakumar, Ravi da kuma Vasudevan su ne suka haɗa kai su ka yi masa allurar cutar. Ashe Vasudevan yana matuƙar ƙaunar Diya tun tana ƙarama. Kuma ya harzuƙa matuƙa da ya ji ta zaɓi wani a madadinsa, wannan ya sa ya haɗa kai da maƙiyan Lingesan su ka haɗa tuggun lalata masa rayuwa. 

Daga nan sai su ka zane Lingesan kuma suka ɗaure shi, amma ya samu sa'a ya fece. Jin haushin irin wannan yaudara da aka yi masa, sai Lingesan ya sace Diya a ranar ɗaurin auren ya ajiye ta a wani keɓaɓɓen gida ba tare da ya bayyana mata ko wanene shi ba. 

Tare da taimakon Babu, Lingesan sai ya yanke shawarar ɗaukar fansa a kansu ba tare da kisa ba. Da fari ta kan Ravi ya fara, inda ya yi sanadin da ya samu mummunar ƙuna. Daga nan kuma sai ya haɗa wani mai na musamman ya ajiyewa Osma ta shafa ba tare da ta sani ba. Hakan ya sa gashi ya firfito mata a jiki. Na gaba kuma shi ne Indrakumar, wanda ya sha harbi daga zuma. 

A ƙarshe kuma sai yayi faɗa da John akan wani jirgin ƙasa mai gudu inda a haka ya je ya lahanta kanshi. Daga nan kuma sai ya yi wa Vasudevan wayo shima ya yi wa kansa allurar cutar ta "I". Bayan ya cimma burinsa na ɗaukar fansa, sai Lingesan ya bayyanawa Diya halin da ake ciki. Duk da cewa da ji daban, ta bayyana mishi tana son shi duk da irin halin da yake ciki, kuma daga nan su ka yanke shawarar ci gaba da yin rayuwarsu a ɓoye. A ƙarshe dai Lingesan ya koma daidai bayan ya bi wani tsari na samun lafiya. 

JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SHIRIN 

Vikram - Lingesan

Amy Jackson - Diya

Suresh Gopi - Vasudevan

Santhanam - Babu

Upen Patel - John

Ramkumar Ganesan - Indrakumar

Ojas Rajani - Osma Jasmine

M. Kamaraj - Ravi

Mahru Sheikh - Maman Diya

Azhagu - Mahaifin Lingesan 

T. K. Kala - Mahaifiyar Lingesan

Mohan Kapoor - Sushil

Srinivasan - Keerthivasan

Yogi Babu 

 
<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive