SHETTY POLICE UNIVERSE: THE INDIAN AVENGERS?

Shetty Police Universe: The Indian Avengers?

An daɗe ana tunanin cewa za'a wayi gari watarana Masana'antar Fina-Finai ta Indiya za ta fitar da wani shiri da zai ƙunshi manyan jarumai kwatankwacin na shirin kamfanin marvel watau Avengers. Wanda in ban manta ba, a shekarun baya har an fara maganar ƙila Fina-Finai irin su Krrish, Ra.one, Robot, Kick da makamantansu za su share fagen faruwar wannan al'amari, sai dai har izuwa wannan lokaci 'yan kallo ba su samu damar ganin wannan mafarki nasu a zahiri ba. Dalili mafi ƙarfi kuwa shi ne: fina-finan ba na kamfani ɗaya bane kuma ba mutum ɗaya ya bada umurninsu ba. 

To ga alama dai mai bada umurni watau Rohit Shetty ya zama mutum na farko a ƙasar Indiya da ya fara share wannan fage a ƙasar ta Indiya tun bayan da shirya fim ɗin Singham, Singham Returns da kuma Simmba. A bisa bayanan da suka bayyana da kuma abinda ya bayyana daga tallar shirin da aka saki, 'yan kallo za su ga jarumi Akshay Kumar a matsayin Jami'in ɗan sanda ne mai suna Veer Sooryavanshi wanda yake yaƙi da ta'addanci. Sai dai a cikin shirin, za mu ga jarumi Ajay Devgn hallau a matsayin Bajirao Singham wanda shima wani ɗan sanda ne da ya fito a cikin wani fim na daban wanda Rohit Shetty ne ya bada umurninsa. Hallau kuma dai, za mu ga jarumi RANVEER SINGH a cikin shirin a matsayin Sangram Simmba Bhalerao wanda shi ma wani ɗan sanda ne mai hali irin na sauran guda biyun kuma daga wani shirin can na daban. Duk a cikin wannan shiri.

A gefe kuma, akwai raɗe-raɗen cewa jaruma Rani, wacce ta fito a matsayin jarumar 'yar sanda mai suna Shivani Shivaji Roy a cikin shirin Mardani ita ma za ta fito a cikin wannan shiri mai suna Sooryavanshi. Wanda idan muka lura da waɗancan jarumai maza guda uku, su kaɗai kawai haɗa su a cikin fim ɗaya ba ƙaramin ƙoƙari bane, sannan haɗa su a irin yadda aka haɗa su a cikin shirin wani abu ne da Bollywood ba ta taɓa ganin irinsa ba. Amma kawo jaruma Rani a cikin shirin, wannan kuma wani abu ne da ya ma fi ƙarfin tunani, domin kuwa ba Rohit Shetty bane ya bada umurnin shirin. 

To sai dai kuma fa abin bai tsaya ga nan ba, wasu rahotanni da ba su da sahihanci suna bayyana cewa idan wannan shiri ya karɓu, to lallai Rohit Shetty zai iya tara wasu manyan jaruman 'yan sanda a cikin shirinsa na gaba watau Singham 3. Rahoton kuma ya ce, matuƙar Rani ta fito a cikin shirin, to akwai yiwuwar cewa Jarumi Salman Khan shima zai iya shigowa cikin tawagar a matsayin Chulbul Pandey daga cikin shirin Dabang, Yayinda Aamir Khan kuma ake tunanin zai iya shigowa a matsayin Surjan Singh Shekhawat daga fim ɗin Taalash.

Sai dai kuma, ba lallai bane hakan ya yiwu bisa duba da banbancin ra'ayi da kuma kamfanoni da masu bada umurnin shirye-shiryen. To amma Rohit Shetty mutum ne mai basira sosai, zai iya shirya sabbin shirye-shirye wa jaruma daban-daban akan 'yan sandan domin ya ƙara faɗaɗa duniyar tasa ta Shetty Police Universe.

Fatan nasara.

Aarahi hai Police

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 

Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive