TA YI ABIN KUNYA


TAYI ABIN KUNYA

Wannan labari ya fito daga bakin wata amarya, tace:-
Wata rana a wurin aiki ne na ci wake mai yawa fiye da kima. Da na koma gida sai mijina ya tarbe ni da murna, ya ce mani: “Abar kaunata, yau zan ba ki mamaki da daren nan, a wajen cin abinci.” Don haka sai ya samo kyalle mai
duhu ya daure mani idanuwa, ya jagorance ni zuwa kan kujerar teburin cin abinci, ya zaunar da ni.
MHar ya kama kyallen zai kwance
mani ido, sai wayarsa ta kada. Sai
ya ce bari ya tafi ya amsa wayar,
idan ya dawo zai kwance mani
daurin kyallen idona. Ina zaune sai
cikina ya fara murdawa, domin
kuwa waken da na ci ya bata mani
ciki. A tsammanina, tun da mijina
bai kusa da ni, sai na karkace kafa
daya na burka tusa mai kara kuma
mai dan karen wari. Na dauki
hankici na fara fifita saboda warin
ya kau da sauri, kafin mijina ya
dawo. Cikin nawa ya sake rudewa,
sai na saki jiki na burka tusa har
sau uku kuma masu kara da wari,
fiye da ta farko. Babu abin da
nake sauraro sai muryar mijina
daga nesa yana ta magana a
waya. Ni kuwa domin in samu
sauki sai na yi ta sakin tusa ba
kaukautawa, ina jin dadi sosai,
cikina yana washewa. Da na ji
mijina ya gama magana a waya
kuma yana shirin dawowa wajena,
sai na ci gaba da fifita, domin in
kori warin tusar da na yi ta
burkawa. Da ya dawo sai ya ba ni
hakuri, ya ce mani: “Ina zaton dai
ba ki bude idonki ba tun da na
tafi.” Ni kuwa na ce ban bude ba
ko kadan. Daga nan mijin nawa ya
kwance mini kyallen idona. Abin
mamaki da kunya, sai na ga
abokan mijina su bakwai a
zazzaune a kujerun gaban teburin
abinci. Sun tottoshe hancinansu
da hankici saboda warin tusa ta
hmm hehehehe
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive