Tambaya ta 001


```Assalamu Alaikum
Allah ya kara wa Malam lafiya, gameda aiki ga matar aure wadanne sharudda ne ya kamata a gaya mata ta kiyaye kamar aikin koyarwa a Makaranta.```


_*ANSWER:*_
**********

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Ya halasta matar aure tana iya fita zuwa aiki, amma a karkashin wasu sharudda. Idan ta cika kuma ta kiyaye wadannan sharruda, toh ya halasta ta fita zuwa aiki. Sharuddan sune kamar haka:

*1.* Wajibi ne ta samu izini da kuma amincewar mijinta game da fita zuwa aiki. 

*2.* Ya kasance tana so tayi aikin ne domin ta samu kudin da zatayi wasu buqatun rayuwar ta wadanda basu sabawa shara'ah ba, kuma mijinta bashida halin yi mata.

*3.* Dole ne aikin ya kasance aiki ne da yadace da mata, kamar likitanci, ungozumanci (nursing and midwifery), karantarwa, dinki, da ire-iren su.

*4.* Dole ne aikin ya kasance a wuri ne na mata kadai. Kuma ya kasance babu cudanya da mazan da ba muharraman ta ba.

*5.* Dole ne ta kasance tana sanya Hijabin Musulunci (Hijabin da shara'ah ta yarda da shi).

*6.* Kuma kar aikin ya zama silar tayi tafiya mai nisa ba tareda muharramin ta ba. Kamar zuwa Seminar a wani gari.

*7.* Fitar ta zuwa wurin aikin kar yasa ta aikata wani aikin zunubi, Misali kamar ta kadaice da direba, ko ta sanya turare a wajen da mazan da ba muharraman ta ba zasuji kamshin sa.

*8.* Kuma ya zamana cewa aikin bai shagaltar da ita ba har takai ga yin sakaci ga ababen da sukafi zama tilas akan ta, kamar Kula da gidan ta, bawa Mijinta kulawa, da kuma kula da 'ya'yanta.

*Shaykh Muhammad Ibn Saleh Al-Uthaymeen (rahimahullah)* yace: Wurin da mace take aiki ya kasance na mata ne kadai, kamar idan tana aikin karantar da yara mata, ko kuma tana aiki a gida na koyar da aikin tela na dinki, da sauran su. Amma yin aiki a fannin da ya kasance na maza ne wannan bai halasta agareta yin aiki anan, saboda aikin zaisa tayi ta'ammuli da maza, Wanda hakan kuma babbar fitina ce kuma dole a kauce wa wannan fitina. Ya tabbata cewa *Manzon Allah (ﷺ)* yace:

مَا تَرَكْتُ بَعْدِي فِتْنَةً أَضَرُّ عَلَى الرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ وَأَنَّ فِتْنَةُ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَانَتْ فِي النِّسَاءِ.

_Ban bar wata fitina a bayana ba, mai cutarwa ga maza da ta wuce mata ba, kuma fitinar banu Israa'ila ta kasance a mata ne._ 

Saboda haka mutum ya tseratar da iyalan sa daga wuraren afkuwar fitina domin tana iya afkuwa ne ta kowace irin siga.
_*(Fataawa Al-mar'atul Muslimah, Mujalladi na 2, Shafi na981).*_
 
Saboda haka Idan mace ta cika wadannan sharudda, toh babu laifi zata iya yin aikin ta inshaa Allah. والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*🕌SAUTUS SUNNAH*_
        +2348034679561
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive