TAMBAYA TA 006


ZA MU IYA BARIN SALLAR JAM'I SABODA CORONAVIRUS ?

Tambaya
Assalamu Alaikum
Malam Dazu a masallacinmu a Abuja an kira meating cewa, za'a rufe masallacinmu daga gobe saboda cutar CoronaVirus, gaskiya abin ya daure min Kai, shi ne nake so na ji matsayarku ?
 
Amsa

Wa'alaikumus sallam
Tabbas akwai nassoshi na Sharia wadanda suke halatta nisantar cakuduwa da mutane saboda gudun daukar cuta, daga ciki akwai fadin Annabi (SAW) "Ka gudu daga Kuturu kamar yadda za ka gudu daga Zaki", sai dai zahirin hadisin Yana nuna ana gudun cuta ne idan ta samu, wannan yake nuna cewa Jahohin da ba'a samu bullar cutar ba, ba su da hujjar barin SALLAR JAM'I saboda bullarta a wasu wuraren.
 Hadisin Abdurrahman Bn Auf a cikin Sahihil Bukhari akan Annoba yana nuna cewa hukunce-hukuncenta suna shafar garin da aka same ta ne kawai, ana gina hukunce-hukuncen Shari'a ne akan abin da yake tabbas ko mafi rinjayan zato.

Galibin Musibu zunubai ne suke kawo su, kamar yadda Allah ya yi bayani a Ayoyi mabambanta a cikin Alqur'ani, dukkan zunuban da aka halakar da Al'umomin baya saboda da su babu wadanda ba ma aikatawa a ciki.

Ya wajaba mu kusanci Allah mu nemi gafara a wajan shi, mu yi salloli kamar yadda ya umarta, ya wajaba Malamai su ji tsoran Allah wajan sassauta in da Sharia ba ta sassauta ba.

Akwai abin mamaki mutane su haramtawa kansu sallar Jam'in da take Sahu-sahu a cikin minti (10) saboda gudun cutar,,,,Corona,,, amma su halattawa kansu zuwa Kasuwannin da suke a cunkushe da ofisoshin da ake samun sama da mutum daya suna wuni a ciki ?

Allah ne mafi Dani

Dr.Jamilu Yusuf Zarewa

22/03/2020
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive