TINƘAHON HAWAN JAKI MAI HANINIYA


TINƘAHON HAWAN JAKI MAI HANINIYA

Masu rattabe da makafta barkanmu da sake arangama a cikin wani sabon kafcen wanda ni kafta'u jagoran makafta kan kafto muku loto-loto. A yau dai alƙalamin nawa ya dira ne kan jarumi a-jaye-dogon-yaro. Jarumin da a yanzu yake ƙwambo a masana'antar bulbula soyayya gami da sambaɗe-sambaɗe da ke birnin in-da-yaya. Hakan kuma ya faru ne tun bayan antayowar sabon kafcensa mai suna Tinƙahon-hawan-jaki. Shirin, wanda ya fita a cikin watan jan-ido ya ƙwamuso maƙudan matsabbai daga lalitar 'yan kallo fiye da yadda ake tsammani, wanda hakan ne kuma ya bashi damar ɗarewa kan kujerar tarihi irin wacce jarumin bai taɓa hawa ba. Shirin wanda ya ƙunshi jarumai irin su gaje, sumaila da sauransu, a yanzu shi ne kafcen ɗin da ya fi kowanne ƙwamuso citta a cikin wannan shekara a masusukar surfe citta da ke can ƙasar ta in-da-yaya.

Wannan ya sa na ji wasu na cewa akwai yiwuwar fa nan gaba wannan jarumi da shi da jarumi a-kashe-kunama da kuma Ragon-sin za su iya doke waɗannan jarumai uku da ake ji da su watau Shamharu, Sallau da Kuma Amshi. To ko ina aka baro Hantaru gwanin caskale da suburbuɗa a cikin wannan lissafi, sai ku taya ni duba, wai makaho da ya so gulma. Amma kafin nan, na fece!

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive