TSAKANIN ƊAN BOKO AƘIDA DA CORONAVIRUS


TSAKANIN DAN BOKO AQIDA DA ANNABOR CORONA

Dan Boko Aqida yana ta cin zarafin Malamai don sun fadakar ga yin riga-kafi a kan annobar Corona, yana ganin bai kamata Malamai su saka baki a harkar lafiya ba, saboda shi a wajensa Addinin Muslunci bai shafi fagagen rayuwa ba, kawai aiyukan ibadu kadai ya shafa. Alhali Muslunci ya shafi dukkan rayuwar mutane gaba daya, lafiyarsu da rashin lafiyarsu. Don haka Malamai suna da ta cewa yadda ya kamata a harkar kiyon lafiya.

Har aka samu wasu suna taya su 'Yan Boko Aqidar da sunan malumta, -wai- ai magani shi ne gaba da yin addu'a. To ta yaya za ka wulakanta lamarin addu'a, alhali yanzu a matakin riga kafi ake, ba a kai ga matakin shan maganin ba?
Kuma ai duk mai imani da Allah ya san cewa; komai a hanun Allah yake, shi yake kaddara alheri da sharri, hatta maganin sai Allah ya ga dama ya yi tasiri. Saboda haka addu'a tare da imani da kaddara da tawakkali ga Allah shi ne gaba da komai har shan maganin cutar.

Bayan haka dan boko Aqida yana ta murna an kulle Masallatai don gudun yaduwar wannar annoba. Saboda da ma shi ba a sonsa ake tsayar da wadannan sha'a'ir na Addini ba.

Dan Boko Aqida bai tsaya nan ba, har cewa yake yi; -wai- Malamai sun buya sun dena wa'azi da karantarwa, an kulle Masallatai amma Duniya ba ta yi hasaran komai ba. Amma in an isa a ce Likitoci su buya su dena aiki, kuma a kulle asibitoci a ga abin da zai faru, a ga irin hasarar da Duniya za ta yi?!

To ka ga wannan tunani ne na maras tunani, saboda ai ba Masallatai kawai ake ta rufewa ba, an kulle makarantu, an kulle ma'aikatu da kasuwanni da filayen jirage, da wuraren tarurruka da filayen wasanni da wuraren shakatawa. Kai, hatta zirga-zirga sun takaita a manyan biranen Duniya kowa ya lazimci gidansa.
To duka wannan da ya faru, me Duniya ta yi hasara?

Shi wannan Dan Boko Aqida maras tunani, ma'aunin hasara da nasara a wajensa shi ne abubuwa na zahiri a rayuwa (Matter) kadai, alhali duk mai hankali ya san cewa; ma'aunin hasara ko nasara bai takaita a kan abubuwa na Zahiri kadai ba, a'a, sun hada da bangaren Ruhi da jin dadin rai da samun nitsuwarta wanda hakan yake samuwa ta hanyar imani da bautar Allah da rokonsa da yin addu'a. Haka kuma ta bangaren halaye da kyawawan dabi'u, na gaskiya da rikon amana da kyautata wa mutane da rashin cutar da su a magana ko aiki.
Haka ta bangaren Lahira, ta hanyar samun yardar Allah da samun Aljanna da samun tsira daga fushin Allah da azabarsa a wuta. Duka wadannan suna cikin ma'aunai na nasara a rayuwa, akasinsu kuma ma'auni ne na hasara, ba kawai abubuwa na zahiri ne ma'auni kadai ba.

Kuma shi mai wannan tunani, gani yake yi akwai cin karo tsakanin Malamai da Likitoci, da tsakanin Masallatai da Asibitoci, alhali sam ba cin karo tsakaninsu, kowa da fagensa, kuma duka Muslunci yana bukatarsu. Samun Malami a cikin al'umma Farilla ne na Kifaya kamar yadda samun Likita ma haka yake. Haka kamar yadda samar da Masallatai yake larura ta Addini, haka samar da Asibiti ma yake larura ce a Shari'a. Kowanne yana aikinsa ne a fagensa, daya ba ya hana daya, kai hasali ma taimakekeniya ne a tsakaninsu. Shi ya sa za ka samu Masallaci a cikin kowane Asibiti.

Kamar yadda mutane suke bukatar Malamai masu nuna musu hanya a Addini da rayuwarsu haka suke bukatar Likitoci a harkar lafiyarsu. Kamar yadda Likitoci suke kula da lafiyar jiki, haka Malamai suke likitoci ga ruhi da zuciya.

Saboda haka rufe Masallatai ya janyo wa Duniya hasara mai girman gaske ta bangaren Ruhi da Halaye da Sakamakon Lahira. An rasa rayuwar ruhi da zukata irin wanda ake samu a bauta a Masallaci. An rasa karuwar imani da ake samu a ibada a cikin Masallaci. An rasa kyawawan dabi'u da ake samu a dalilin haduwar mutane a Masallaci. Kai, an yi hasara mai yawa da aka dena zuwa Masallaci saboda wannan uzuri na wannar annoba a bangaren ruhi da karuwar imani da raya zukata.

Saboda haka rashin kyakkyawan ma'aunin auna nasara da hasarar abubuwa ne zai sa ka ce Duniya ba ta yi hasarar komai ba da aka kulle Masallatai ya kai Dan Boko Aqida.

Dr. Aliyu Muh'd Sani
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive