TSAYIN GASHI


💆🏻💇🏻 *GYARA SHINE MACE* 👸🏻

 _TSAYIN GASHI_ 🧝🏻‍♀
Sister idan nace miki gashinki zai qara tsayi kizama yalasha a sati biyu ta hanyar amfani da abubuwa natural wanda ko Naira dubu daya bazaki kasheba a hadasu🥰

 *Abubuwan bukata* 
Coconut oil 1 cup.
Albasa medium 1
Aloevera 2 small

 *Method* :
Sister kisamu albasa medium size guda daya ki gurzata da grater saiki dinga diba kina sakawa a rariya kina matse ruwa daga cikinta acikin bowl. Ki ajiye ruwan albasar agefe, Ki dauko Aloevera qanana guda biyu ko babba guda daya saiki yimusu yanka qanana,kisamu tukunya qarama kizuba coconut oil kofi 1 saiki Dora akan wuta kizuba aloe Vera dakika yanka aciki kibarshi ya tafasa kamar minti 15 saiki sauke,kibarshi ya huce, saiki samu roba mai spray kisaka bututu ki tsiyaya man kwakwa mai Aloevera aciki yadda man kadaine zai shiga cikin robar saiki dauko ruwan Albasa shima kizubashi aciki,saiki rufe robar ki fesa shi a gashinki wanda yake a tsefe, kina fesawa kina saka yatsunki kina shigarda man cikin gashin sosai. Saiki bashi mintuna 40, kafin ki wanke. Zaki maimaita wannan sau biyu a sati. Idan kikayi 14 days kina haka,hmmm ai sister waqa a bakin mai ita tafi dadi.

✍🏻 *MRS KABEER*
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive