WAƘAR CORONAVIRUS 01


WAƘAR CORONAVIRUS 01

 Bissmillahi da sunan rabbana
 Haiman ayau zan fara batuna
Tsira da amincin Allah ga adali Manzona
Da Sahabbai da Tabi’ai da ma malamaina
Allah ka kawo mana sauƙi da ni da duk 'yan uwana. 

Mun wayi gari a yanzu kowa na ɓuya
Babu babba babu yaro babu ko mai talla akan hanya
Cutar Corona na kashe yara har da manya
Ƙare dangi ta ke ta yi a ko' ina ba sanya
Ya ku jama'a ku mu gane dujal yana kan hanya.

Ƙarshen duniya ya matso alamu na ta bayyana
Mutuwa dai tana zuwa gareku har ma guna
Ko ka gudu ko ka tsaya ko kana gida ko gona
Mutuwa za ta iske ka aboki da 'yan uwana
Kuma ba wanda zai rage tun da har ta ɗau Manzona.

Mu daina dariya da nishaɗi da yi wa juna barka
Da cewa ai fa da saura a cikin rayuwarka
Mu roƙi Allah dare da rana kar mu je gun boka
Kuma kar tsoro ya sa mu je mu faɗa shirka
Kawai mu koma ga Allah zai mana maganin duk wata cuta.

Zan ɗan tsaya anan wajen don na sarara
Allah tsare mu da mugun gani irin na asara
Da mugun ji ko gida ko da can a sahara
Ka tsare mu da ga dukkanin taɓara
Kai ke da ikon komai Allah Jalla tabara

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

Aaraha Hoon! 
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive