YADDA AKE SAI DA SAFE A SHIMFIƊA


YADDA AKE SAI DA SAFE A SHIMFIDA:

Shimfidar Ma'aurata wuri ne da za su kwanta har gari ya waye. Saboda haka akwai bukatar ya zama an gyara shi tsaf. Kuma ba hayaniya , ba haske . Ya zama za a samu natsuwa sosai.

 Mai gida zai dinga taimakawa matarsa. Wato kawo turaren daki harma da wanda za ta sa ajikinta. Zai kuma yi wanka ya sa turare kafin ya kwanta da yin asiwaki.

Matarsa kuma za tabbata ta tsaftace duka Daki. Ta gyara shimfida, ta sa turare. Ta yi ado da bargo yadda zai ba da sha'awa.

Ta yi wanka da wanke ba ki, ta shafe jikinta da Humra mai dadin kamshi. Ta sa kaya masu jan hankali.

*HANYOYIN DA AKE SAI DA SAFE :*
1 - Ma'aurata za su kwanta ne manne da junansu. Mai gida ya rungumeta . Ko kuma ita ta kwanta kan kirjinsa, ko kan kafadarsa. Lalle ya zama jikinsu a hade ya ke.

2 - Idan kawai bacci za ku yi. Sai ki ja mayafi ki lullube ku duka. Ki sumba ce shi. Ki ce : Allah Ya tashe mu lafiya, Ina son ka . Ku yi adduoinku na kwanciya bacci.

3 - Mai gida ya sumbace ta sau uku idan ya na nufin gayyatarta...Ya sumbaci goshinta ya ce : Masoyiya ta. Ya sumbaci kumatunta ya ce : kina cikin raina. Ya sumbaci lebenta ya ce : Ina kaunarki sosai. Shikenan za ta mika wuya. Idan bai yi ba, ke sai ki yi gayyatar. 

A karshe dai , duk Ma'aurata da su ke haka in za su yi bacci. Za su kasance cikin kauna da Begen juna.

Duba rubutun yadda za ka Birge matarka ta zama masoyiyarka.
✍ *Amina Yusuf Gwamna*
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive