YADDA IYAYE ZA SU KOYA WA 'YA' YA'YANSU ZAMAN AURE


Yadda Iyaye Za Su Koya Wa ‘Ya’yansu Zaman Aure:


Hakkin iyaye ne su aurar da ‘ya’yansu mata da maza a lokacin da su ka kai munzalin aure, kuma hakki ne a kansu su fayyace mu su yadda a ke yin zaman auren da abin da ya ke cikin auren da yadda a ke yin zaman auren. Tabbasa samari da ‘yan mata sun a zaton aure abu ne na nishadi da holewa da kuma nuna bajinta ba tare da sun san menene auren ba da yadda zaman auren yak e ba.

Dan haka daga an gama hidimar biki an cika gida da kayan alatu sai su yi zaton soyayya kawai za a yi ta yi babu sauran kalubale, ba haka abin ya ke ba kuma a zahiri. Yau da gobe sai Allah, kuma zo mu zauna an ce zo mu saba in ji ma su iya magana.

Aikin uwa mace ne ta zaunar da ‘yar ta ta karanto ma ta duk wani hakkin mijinta da ya ke kanta da kuma yadda za ta zauna da shi da kuma danginsa . Ladabi da biyayya ne akan gaba sai kuma tsafta da iya abinci kuma a dafa akan lokaci ba sai miji ya dawo da yunwa ba sannan za a hau fafutukar dora tukunya.

Haka uba namiji ya zaunar da dansa ya fada ma sa yadda ya kamata ya kula da matarsa, ya sauke hakkin da Allah ya dora ma sa na ciyarwa da tufatarwa da kuma muhalli.
Gaba daya mace da namiji su na da bukatar a fada mu su a sake fada mu su wannan kalma ta ‘hakuri” tabbas zaman aure ba zai taba a yiwuwa ba idan babu hakuri.

Mace-macen aure ya yi yawa a a rewacin Najeriya a sanadiyyar rashin hakuri abu kalilan sai ya jawo saki.

Zawarawa sun yi yawan da har ba a shakka kuma ba a jin nauytin ambaton saki sabo da ya zama ruwan dare.

Abin mamaki kuma sai a samu hannu uwar miji ko uwar mata dumu-dumu wajen ba da gudunmawa aure ya mutu.

Iyaye da yawa su na taka rawa wajen hargitsa zaman auren ‘ya’yansu saboda son abin duniya ko wata manufa ta daban akan burinsu.

Wata uwar ita ta ke kimtsawa ‘yar ta yadda za ta bi da miji ta hanyar gurbatatcciyar hanya dan a kori kishiya ko a hana shi kara aure ko kuma a mallake shi ya guji danginsa da mahaifansa duk abin da ya samu ita kadai da iyayenta zai din ga yiwa. http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/yadda-iyaye-za-su-koya-wa-yayansu-zaman.html#.XloPwEleA6w.whatsapp
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive