YAYA KI KE TASHIN MIJINKI?


Yaya kike tashin MIJINKI? 

1. Tsarin lallashi na ban baki:

Ki iya tsaro lafuzza da yabo da zakin baki:

Kiyi kalar tausayi

Ki hado da shagwaba

Ki saisaita amon murya

Ki dan gajarta jimlolin

Ki zabi risinar da kwayar idanun ki

Ki kusanto shi - ki sanya hannunki cikin nashi

Sannan ana lallashin a:

2. Lallashi ga waya: 

Da ya kunshi Sarrafa jimlolin da fasahar zance tsakanin yabo da zakin baki ta sigar lallashi, idan baya daukar waya, ki tura text daya mai tsadaddun kalamai kwaya tak takaitacce, bayan sallar asuba. Koh da kuna gida daya a daki daya, gado daya ne.

3. Lallashi a shinfida "Bed room sweets" :

A lokacin kwanciya; bayan kin:

*Zagaye lebunan shi da harshen ki

*Ki side doron hancin shi

Ki lailaye zagayen kunnin shi, ki zira tsinin harshenki cikin kunnin shi sosai:

Ki shiga jikin shi sosai, har ki kunno shi , sai ki saisaita saitin muryarki "with shaking voice" ki fara sarrafo jimlolin lallashi.

4. Lallashin miji a nesa ga gida, wanda yake bukatar iya sarrafa harshe da kirari da ababen da yafi son ayi mashi zakin baki dasu, wanda kowacce mace ta san ta yanda take seta mijinta, se idan ta zamo ballagaza !

5. Lallashi na fuskantar miji, bayan kin dan bashi lokaci ya dan sha iska ya gama cika da batsewa, sannan ki:

Ki yawaita qayatar da kwallia da ababen da suka fi dauke hankalin sa, kamar lalli na qafa da hannu idan kin hardace sirrin oiling na tafunan kafa da hannu:

Sanya kanan kaya a lokutan da kuke ku kadai "If there are no much chances" :

Kamsashewa:

Shariya-dan share shiga sabgar sa, da kin yadda ku hada idanu:

Takaita magana, d.s

Idan kika fahimci ya dan sauko yana nemsn shiri, sai ki fuskance shi, da:

Zagaye wiyan sa da hannayen ki, kwantowa a kafadar sa, ki fara rada masa jimlolin ban hakuri cikin siririyar murya kasa kasa.

5. Lallashi ta hanyar aiwatar da ababen da yake so da barin wanda baya so, da kwantar kanki:

Ba kya ramuwa koh da an miki abin ramuwar:

Ba kya tankawa balantana ayi maki jikakken rashin mutunci:

Ba kya sishshigi idan akayi murabus daga gadon sarautar ki :

Ba kya gaba, sai dai musanyar alkhairi akan gayyar da ake maki domin Allah baya bacci balantana gafala da cutarwar da ake maki.

👌🏼Zamantakewa sai da damara ta hakuri da gyaran kai, da zage damtse, idan baki iyawa, har wa yau bada hanya !

🛡Health Talk 4 Ladies
     +2349077562389
Share:

No comments:

Post a Comment

Total Pageviews

Featured post

WAƘAR CORONAVIRUS 01

WAƘAR CORONAVIRUS 01  Bissmillahi da sunan rabbana  Haiman ayau zan fara batuna Tsira da amincin Allah ga adali Manzona Da Sahabbai da Tabi’...

Blog Archive