Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2020

ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 5

*05→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*
11. Cikin zina akwai kamancecceniya da dabbobi, saboda mazinaci ba ya daukar nauyin abin da zai biyo bayan lalatarsa, kamar yadda dabba ba ruwanta da abin da ke biyo bayan saduwarta da ’yar uwarta, na kula da mai ciki da tufatar da ita da rainon abin da aka haifa da yi masa tarbiyya. Ka ga ke nan mazinata rayuwar dabbobi suke yi. Allah Ya kiyaye mu.
12. Zina tana kawo kisan kai a cikin al’umma. Sau da dama fada kan faru tsakanin masu neman mata a wajen yawon banzarsu; wani ya kashe wani, kamar yadda yawancin yaran da ake yarwa, ko ake kashewa ’ya’yan zina ne. Haka yawancin cikin da ake zubarwa cikin zina ne, wanda duk wannan kisan kai ne da Allah ba Zai kyale wanda ya yi shi ba.
13. Zina tana lalata al’umma, ta ruguza rayuwa gaba daya, ta hanyar samar da ’ya’yan da ba su da tarbiyya, ba sa ganin girman kowa. Kai, suna jin haushin al’umma, lura da hanyar da suka zo, abin da da dama yakan sa su zamo ’yan daba da fashi da sauran miyagun ayyuka, su bata r…

ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 4

*04→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*
5. Zina tana kawo kiyayya da gaba a tsakanin masu yin ta da sauran mutane. Allah Madaukakin Sarki Yana cire kwarjininsu da girma daga idon mutane, saboda haka ne za ka ga karamin yaro yana fada da sa’an kakansa a wurin neman mata, saboda ba ya kaunarsa, ballantana ya girmama shi.
6. Zina tana jawo rashin amincewa da mai yin ta. Kowa yana yi masa kallon maha’inci, mayaudari.
7. Zina tana haifar da wari daga jikin mai yin ta. Ba wanda yake jin wannan wari sai mutanen kwarai.
8. Zina tana jawo azaba mai tsanani ga mai yin ta idan bai tuba ba a duniya da Lahira. A duniya jefewa ko bulala da bakuntarwa; a Lahira kuwa makomarsa wuta. Allah Ya kare mu.
9. Zina tana kawo rugujewar gida da daidaicewar iyali, sannan tana kawo lalacewar tarbiyya.
10. A cikin zina akwai tozartar da dangantaka da sanya cin dukiyar mutane ba da hakki ba, domin kuwa duk dan da aka samu ta hanyar zina, abin da zai gada ba hakkinsa ba ne.

Zamu kwana a nan, a dakacemu 
Rubutawa:- Dr, M…

ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 3

*03→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*
*Illolin zina:*
Babu ko shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wadanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba daya. Ga wasu daga cikin illolinta:

1. Zubar da mutunci da jawo wa kai kaskanci: Duk matar da ta yi zina, to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar musu da mutumci a idon duniya. Idan har ta samu ciki ta haihu, sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne, to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.

2. Zina ta hada dukkan sharri gaba daya: Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah; rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika alkawari; karya da butulci da sauransu. Duk kuwa wadannan munanan halaye ne a Musulunci.

3. Zina tana haifar da cututtuka da mutuwar zuciya da sanya…

ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 2

*02→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*
*Hukuncin zina:*
Zina haramun ce a addinin Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Ya haramta ta inda Yake cewa : “Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna.” (Isra’i:32). Malamai suna cewa, fadin Allah “kada ku kusanci zina,” kai matuka ne wajen hana ta, don ya fi a ce “kada ku yi zina.” Sheikh Abdur-Rahman Assa’idiy yana cewa: “Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuka a kan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya hada hana dukkan yin abubuwan da suke gabatar ta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge, to ko yana daf da fadawa cikinsa, musamman ma a kan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna dauke da abin da yake sawa a afka masa. 

Sannan Allah Ya siffata zina da cewa alfasha ce. Ma’ana zina wata aba ce da shari’a da hankali suke ganin muninta, saboda keta alfarmar Ubangiji ce da shiga hakkin macen da hakkin danginta da mijinta, kuma bata wa miji shimfidarsa ne da cakuda dangantaka …

ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 1

*01→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*
Gabatarwa:--- 
Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.
 Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa.
 Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari’ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan Gida mai albarka ( *miftahul ilmi*) don amfanin jama’a. 
Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane musulmi...
Shimfida
Ma’anar zina da hukuncinta: Lafazin zina a shari’ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idan…

MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 3

_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(3)
MA’ANAR ZAKKA: DAKUMA DALILAN WAJABCINTA:
 Ma’anar Zakka a harshen Larabci shi ne Karuwa da tsarkaka.
Amma ma’anarta a shari’a kuwa, 
ita ce:  Fitar da haKKin da ya wajaba daga dukiya yayin da ta kai nisabi ga wadanda suka cancanta.
 Zakka rukuni ce daga cikin rukunan Addinin Musulunci kamar yadda ya zo a Hadisi:
"بني الإسلام على خمس شهادة أن لا إلـه إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلوة وإيتاء الزكاة وحج البيت وصوم رمضان" رواه البخاري ومسلم.
“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar;  shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,  kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne,  da tsai da Salla da ba da Zakka  da ziyartar Dakin Allah (Aikin Hajji)  da azumtar watan Ramadan”  (Bukhari da Muslim).
Zakka rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar. Zakka ta kasu zuwa kaso biyu:
1-Zakka ta jiki (Wato zakkar fidda kai), bayaninta zai zo a nan gaba.
2-Zakkar dukiya.
DALILAN WAJABCINTA:
Zakka wajibi ce da nassin AlKur’ani, kamar yadda Alla…

MALAMAI KU GAYA WA SHUGABANNI GASKIYA

MALAMAI KUGAYAWA SHUGABANNI GASKIYA SUGUJI MAYARDA CORONA INJIN BUGA KUDI SUNA KASHE ADDINI DA TATTALIN ARZIKIN KASA DA AL'UMMA‼️
Tabbas babu tantama CORONA-VIROS annobace mai muni kuma akwaita➖ Ammafa cutarda tafita muni shine👉 SON DUNIYA DA KIN MUTUWA‼️
Anya bamu fada cutarda tafi CORONAN ba⁉️
Shin da muka kukkulle masallatan mukabar sallar jam'in CORONAN raguwa tayi ko karuwa⁉️
Shin idan za'a bawa kasuwa dama a mako sau daya ko biyu dubun dubatan mutane sushiga lokaci guda suna turereniya suna haki suna sayan kaya a tsawon yini guda wato kusan mintuna 500➖To donme bazamu bawa ALLAH Mahaliccinmu mintuna 30 a mako sau daya don muyi sallar juma'a ba⁉️
Jihohinda akasa kofi an halattawa mutane yin komai da rana banda dare amma kun hanasu sallar jam'i➖shin Ayane ko Hadisi ko binciken likitoci yace a sai a Masallaci za'a harbu da CORONA⁉️
Ko kuma rena ALLAH mukayi⁉️ Ko kuma takalar ALLAH mukeyi⁉️ Ko kuma cutar SON DUNIYAR da KIN MUTUWARNE⁉️ Ko kuma a hakan an fasa mutuwarne…

LADUBBAN MAI AZUMI: CI GABA

LADUBBAN MAI AZUMI
A yau zamu cigaba da bayani ne a inda muka tsaya bayan mun tattauna akan cewa wanda yake Azumi ya bayar da muhimmancin yin Sahur a koda yaushe, kuma mukaji cewa Sahur yana da albarka matuka kwarai da gaske, abunda ake cewa albarka shine: Alkhairi mai tarin yawa kuma mai faɗi wanda baya gushewa, don haka Sahur yana da albarka, lokacin mai albarka ne abincin mai albarka ne, bayan nan sai kuma mukaji bayanai akan Asuwaki yana daga cikin Sunnonin Annabi bayan haka ma yana da fa’idoji masu yawa, to yau zamu cigaba Insha Allahu.
LADABI NA UKU: NESANTAR DUK ABUBUWAN DA SUKE KORE DALILIN DA YASA AKE YIN AZUMI
Allah madaukaki yace: (Ya ku waɗanda kukayi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi ga waɗanda suka gabace ku don kuji tsoron Allah) Suratul Bakara: 183.
Babban Malamin Tafseerin nan Al-Imamu Ibn Katheer yace: “Allah yana mai Magana da Muminai na wannan Al’umma, kuma yana umurtar su da yin Azumi, shine: kamewa daga barin cin abinci, da abun sha, da kuma yi…

LADUBBAN MAI AZUMI: GAGGAUTA BUƊA BAƘI

*DAY 07*  ```RAMADAN ARTICLES``` 
 *LADABI NA HUDU: GAGGAUTA BUƊA BAKI*  Ya kai dan uwana Musulmi ka gagaguta buda-baki da zaran Rana ta fadi, domin yin haka tsantsanta biyayya ce ga Sunnar Manzon ka (SAW) wanda Allah yace maka shine kyakkyawan abun koyin ka, kuma gaggauta buda bakin sabawa ne ga Yahudu da Nasara, domin su suna jinkirtawa ne jinkintawar su kuma tana da lokaci, wato bayyanar taurari, kuma a cikin bin hanyar Manzon Allah (SAW) akwai bayyana alamomin Addini, dad a tinkaho da abunda muke kai na shiriya wanda muke kaunar mutane da Aljanu su hadu a kansa, daga cikin fadar Annabi (SAW):  “An Karbo Hadisin Ingantacce daga Sahal ɗan Sa'ad (Allah ya kara masa yarda) Lallai Manzon Allah ﷺ yana cewa:
 ```“Mutane basu gushewa suna cikin alkhairi, matukar suna gaggauta buɗa baki”```  [Bukhaariy da Muslim] Idan rana ta faɗi mai Azumi ya yi buɗa baki, jinkirta buda baki har duhu yayi yin haka bidi'a ce, kamar yadda muka ji Manzon Allah ﷺ ya fadakar damu gaggauta buda bakin yana dag…

HADITH OF THE

*HADITH OF THE DAY IS ABOUT JANNAT* 
Narrated Ibn `Umar: Allah's Messenger (peace be upon him) said, "When the people of Paradise have entered Paradise and the people of the Fire have entered the Fire, death will be brought and will be placed between the Fire and Paradise, and then it will be slaughtered, and a call will be made (that), 'O people of Paradise, no more death! O people of the Fire, no more death! 'So the people of Paradise will have happiness added to their previous happiness, and the people of the Fire will have sorrow added to their previous sorrow."
 *SOURCE:* Sahih al-Bukhari, Vol. 8, Book 81, Hadith 135.

A COMPELLING LESSON

A COMPELLING LESSON FROM THE GREAT PLAGUE OF MARSEILLES FRANCE
In 1720, a ship was quarantined at the port in Marseille because of a strange infection was killing people on the ship.
Deputy Mayor of Marseille lifted the quarantine to “help economy”. Over 100,000 people died. More than half of Marseille died. This was the Great Plague of Marseille.
The govt of Marseille felt they could not afford to lose all the valuable goods on the ship as it will destroy the economy. As they lifted the quarantine and moved the goods into the city of Marseille, they moved in the infection. More than half of Marseille citizens died.
Marseille is a major port city in the south of France. Just as Lagos is in the south of Nigeria.
By the end of the Great Plague of Marseille, the city of Marseille had 50,000 dead people (out of a total 90,000 population back then).
That is like 10 million people dying in Lagos.
The ship left Sidon in Lebanon, picked up people at Tripoli, and Cyprus which already had infection out…

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2


Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe akan Corona Wacce ta zagaye duk garina Babu sarki sai Allah a wajena Annabina baban Fatima Shi ne manzo a guna.
Duniya dukka ta jigata babu sauran watayawa, Rayuwa yau ta wahalta ba batu na mai darawa, Hatta jakin da ya ke cin harawa, Ya san duniya ta sauya tunda babu sukunin yawatawa,  Bar batun baƙin fata ko baturen yammatawa, Ƙyale zancen mutan Kaduna ko mutane na Kanawa, Duniya kaf tana ta kuka da zuwan cutar Corona, Rabbana mun yi nadama a gare ka mu ke ta tuba.
Mun yi tuba a gare ka ubangijina sarki kai ke da kowa, Mun yi tawassili da ƙur'ani magani ga komai, Mun yi sujjada gare ka Rabbana kai ke da kowa, Muna ta roƙo a gareka rabbi kai ne ka ke da komai, Ka yafe mana laifukanmu kar ka bar mu da wayonmu, Domin in ko ka bar mu da wayonmu babu sauƙin da za mu samu.
Mun yi roƙo zuwa gare ka babu shakka ko gadara, Mun yi tuba zuwa gareka babu ɗa babu maraya, Mun koma zuwa gareka Rabb…

TAMBAYA TA 81

*TAMBAYA*

Assalamu alaikum. Malam Barka da warhaka. Tambaya ta shine: Menene hukuncin lockdown a mahangar shari'a, da hakan yajawo rasa ran mutane da dama da karyewan kasuwancin wasu. Don Allah Ina neman qarin bayani. 

*Amsa*
_Daga bakin👇🏼_ ⚖ ```Mai Shari'a Malam Kabir Sulaiman```

*_Do Allah a daure a saurara Malam yayi bayani mai shiga jiki tareda nasiha wa shuwagabanni_*

```(ZAUREN FATAWA A MUSULUNCI📖)```
      👇🏼👇🏼👇🏼

THE OBLIGATORY CONDITIONS FOR AN ISLAMIC HIJAB

The Obligatory Conditions for an Islamic Hijab – Dr. Saleh as-Saleh.
WOMEN BEAUTIFICATION , WOMEN DRESS (HIJAAB)                             (PART TWO)
(3) THE HIJAB MUST NOT BE TRANSPARENT The purpose must be achieved. In order for the Hijab to be a cover, it must not be made of transparent material making the woman covered only by name(!) while in reality she is naked. The Prophet ( ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠّٰﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢ ) said: “In the latest part of my Ummah (nation of Muslims) there shall be women who would be naked in spite of being dressed, they have hair high like the humps of the Bukht camel, curse them, for they are cursed” (42). He ( ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠّٰﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢ ) added in another hadeeth: “They will not enter Al-Jannah and would not perceive its odor, although its fragrance can be perceived from such and such distance .(43) This indicates that a woman could cause herself a grave and destructive sin if she puts on a garment that is thin and transparent and which clearly shapes her body’…

BENEFITS OF RAMADAN 4

*Benefits of Ramadhaan= 04*
_Abu Uwais Abdullah Alee_

Any other Ramadhaan do what you will. But my sincere advice to you is, this Ramadhaan worry about yourself. Am I backbiting? Am I slandering? Am I committing fahishah? Am I committing gheebah? Am I committing Nameemah (tale-carrying)? Do I have ‘hasad’? Do I have pride (Kibr) ? Am I arrogant? Am I too harsh? Am I unkind? Am I not gentle enough? Am I gentle enough? Question yourself. Was my intention when I said what I said or did what I did for the pleasure of Allaah or to be noticed? When I spoke what I spoke was it for the pleasure of Allaah or to be seen or heard? Was I doing it “Haarisa min Qalbi’— sincerely from my heart or I did it to be known? ‘Khutbath Duroor’ — Loving to be known breaks it.
Be Mukhlis. Be sincere. Be like that servant of Allaah like the Hadith that has been related in the Kitaab al tawheed of the soldier whose head is disheveled, who is bare-footed and dirty.. but he is sincere to Allaah. If he was placed…

MATSAYIN ZAKKA A SHARI'AR MUSULUNCI 2

_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(2)GABATARWAR MARUBUCI,
GABATARWA TA 2
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai Tsarki ya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya bani ikon yin wannan aiki. Allah Kai dadin tsira da aminci ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki daya. Domin shawara ko Karin bayani ka iya tuntuba ta wadannan hanyoyi kamar haka: MIHNA SOFTWARE AND WEB DESIGN No. 12 Dandago Sabontitin Mandawari, Kano +2347033826988, +2348027916518, www.sadiksalihu.com,   abubakarmihna@yahoo.com  abubakarmihna@gmail.com  Naku:  Abubakar Salihu Kabara, _*Zamuci gaba insha Allah!!*_ Rubutawa>>✍🏼 *Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_ _*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽 https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta WhatsApp _*Miftahul ilmi*_ Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽 07036073248

MATSAYIN ZAKKA A SHARI'AR MUSULUNCI 1

_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(1)GABATAR WA TA FARKO!!! Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai Tsarki ya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya bani ikon yin wannan aiki. 
Allah Kai dadin tsira da aminci ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki daya.
Kamar yadda muka gabatar da wani darasin da yagaba wanda yake bayani akan AZUMI,
Toh senaga yadace in kawo wani darasin mai matuqar muhimmanci ga Al'ummar musulimin Duniya wanda suna tafiya tare kafada da kafada da Watan AZUMI,
Wanda mutane dayawa suna Amfani da wan nan dama don gabatar da ZAKKA acikin Watan AZUMin Ramadan, toh insha Allah zamu kawo darasin kamar yadda muka saba kullum,
Muna rokon Allah da ya karba mana yasa dashi muke yakuma bamu ladar sa ranar Alqiyama, Allahumma Ameen yãhayyu-yãQayyum 🤲🏼🤲🏼 _*Zamuci gaba insha Allah!!*_ Rubutawa>>✍🏼 *Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_ _*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽 https://t.me/miftahul…

NO OBSCENE LANGUAGE DURING RAMADAN

🌙🕌Ramadan 1441AH🕌🌙         ✨🌅DAY #6⃣✨
🔰 *No obscene language !!!It is sunnah if someone insults you to respond in a better manner!!*
Abu Hurayrah(RA) narrated:
The Messenger of Allaah (peace and blessings of Allaah be upon him) said: 
"Fasting is a shield🛡 or protection so there should be no obscene or offensive talk or behaviour. If a person fights him or insults him, let him say, *I am fasting, twice*. By the One in Whose hand is my soul, the smell coming from the mouth of the fasting person is better before Allaah then the fragrance of musk. [Allaah says:] He gives up his food, drink and desire for My sake. Fasting is for Me and I will reward for it, and a good deed receives the reward of ten like it''.✔
Reference🔍 : 📚Al-Bukhaari 1894 📚Muslim, 1151.
Pray:🙏🏾 "My Lord! Grant me the power and ability that I may be grateful for Your Favours which You have bestowed on me and on my parents, and that I may do righteous good deeds that will please You, and admit me by…

TAMBAYA TA 80

Assalamu alaikum malan mutumne take gaba dani NA tambayeshi mena yi mashi tayi shiru in anje sallah bai hada sahu dani in Ina limanci bai bina in a main sallama bai amsawa in Ina guri bai zuwa KAI malan had aika mai da sakon yadaina gaba dani yakiya.... To malan idan nadaina binshi sallah NA yanke dukkan hulda dashi nayi laifi
Amsa
Wa'alaikumussalam
Asali shine duk Wanda suke gaba har tsawon kwanaki uku to sallarsu ma da duk wata ibadunsu baza'a karba ba amma idan ya kasance dayane yake gaba dayan kuma ya kulashi yaqi yi masa magana to yayi masa hakan har sau uku idan yaqi seka qyaleshi amma karka qullace shi duk randa yaima magana seka kulashi kuma lefin yana Kansa shi kadai 
Amma matakin da kake shirin dauka Sam Sam ba dedai bane shi idan baya binka salla kai karka dena binsa sallar amma tabbas akwai matsala idan kuka mutu kuna gaba Allah ya tsare mu

TAMBAYA TA 79

Assalamu alaikum warahmatullah  Shin mãlam dagaske ne cewa kiran sallah Badai dai ba yana jawo bala'i a gari har yakan haifar da yawaitar 6eraye ??
Amsa
Wa'alaikumussalam
Allahu a'alam amma dai shi saddiqul manshawi be fadi hakan ba acikin littafinsa me suna KUSKUREN MASALLATA saboda haka ku turje shi Wanda yafada maganar ya gaya muku wajen da yaganta kaga semu qaru baki daya 
Allah yasa mudace.

TAMBAYA TA 78

Assalamu alaikum malm dafatan ansha ruwa lfy Malm Wanda yamanta Zaman tahiya na farko Se bayan yamike se y tuna malm y yakamata Yayi ,wassalamu alamkum warahama  Tullahi wabarakatuhu.
Amsa
Wa'alaikumussalam
Baze dawoba ze jira harse ya idar da sallarsa kawai se yayi sujjada kafin sallama (Sujuda Qabli)
Allahu a'alam

TAMBAYA TA 77

Assalamu alaikum warahamatullahiMalam shin ya halatta mutum yafita Neman kudi a wannan lockdown din?
Amsa
Wa'alaikumussalam
Jiya ma anyi mun makamanciyar wannan tambayar nace wannan fatawace a nemi malamai ba irin mu 'yan kuci ku bamu ba 
To yau din ma haka take Allahu a'alam

TAMBAYA TA 76

Assalamu Alaikum.Malam mutum zai iaya kewar matansa biyu a Dare guda?.
Amsa
Wa'alaikumussalam
Eh tabbas idan har ze iya babu wani Wanda ya hanashi 
Allahu a'alam

TAMBAYA TA 75

Salamu alaikum Malam dangane da ciyarwa da aka ce mai ciki tayi idan baxata Iya axumi ba, shin dole sai a ranar da ta sha xata ciyar ko kuwa xata Iya ciyarwa daga baya, sannan dole Wanda xata bawa yayi buda baki da abincin ko ko daga baya xaka Iya bashi bayan isha haka? Sannan kuma dole shi kadai xai ci ko xasu Iya ci da wasu? Shin xata Iya bada kudi a maimakon abincin ko dole sai abinci
Amsa
Wa'alaikumussalam A dunkule abinda ake buqata kowanna azumi Daya aciyar da mutum daya ya Qoshi kawaiba'a buqatan wani abu sama da haka
Ciyarwa ake nema "Kunada zabin chiyar da mutane 30 arana daya ko kubawa mutum daya na tsawon kwana 30 na abinda ze wadatar dashi, da abinda ze dafa kayan miya da sauran su..."
Ba se lalle a ranan ba "yazama dai bashi akanki, idan kinsamu dama seki sauqe nauyi" Wallahu a,alam

TAMBAYA TA 74

Assalama alaikum,shin zan iyayin alwala in zan kwanta koda banida tsarki?  
Idan mace ta taje kanta wai suman nata da ya fita tana iya jefawa a toilet ko ta binne?

Amsa
Yakamata ku ringa babance mun rashin tsarkin wana iri akwai janaba akwai haila irinsu fitsari sauransu 
To idan haila ce ko janaba zaki iya insha Allah
Batun suma ko gashi idan baki Yar anan ba to ai zefi kyau ki sa masa mai da yaji nasan zeyi dadi sosai a baki musamman idan yaqi maggi 
Allahu a'alam

TAMBAYA TA 73

Assalamu alaikum mlm barkan mu da shan ruwa, mlm tambayata anan shine akwai nafiloli na watan ramadana kamar ace yau daren 6 ga abinda za a karanta akowace raka a
Amsa Wa'alaikumussalam
Gaskiya nidai bansan wasu kebantattu nafiloli ba harma ace wai akwai kebantattun abunda za'a karanta wannan nidai ban sani ba allahu a'alam

TARIHIN BARIN SALLAR JUMU'A DA SALLOLIN FARILLA A MASALLACI SABODA ANNOBA

TARIHIN BARIN SALLAR JUMU’AH DA SALLOLIN FARILLA CIKIN JAM’I A MASALLACI SABODA ANNOBA KOWASU LARURORI Jumu’ah,2 ga watan Sha’aban 1441(27/03/2020)
01
BismillahirRahmaanirRaheem.Alhamdulillah.Wassalaatu wasSalaam alaaRasuulillah, wa Aaalihiwa As’haabihi waman waalah.
Bayan haka,wannan dan takaitaccen bayanine gameda tarihin dakatar da sallar Jumu’ah dayin sallar jam’i a masallaci saboda tsoron yaduwar Annoba ko saboda wasu larurori dasu kahada da ambaliyar ruwa da yaki. Na tattaro bayananne daga wasu makaloli da littafan da wasu masu bincike suka rubuta bayan na bibiyi asalin littafan da sukayi amfani dasu wajen tsara nasu bayanan.
Ina rokon Allah Yakawo mana karshen wannan Annoba ta Corona virus(COVID-19)data addabi Duniya a halin yanzu.
DAKATAR DA SALLAR JUMU’AH DAYIN JAM’IN SALLOLIN FARILLA A MASALLACI SABODA AUKUWAR ANNOBA KO TSORON YADUWAR TA
,A shekarar 18AH(693CE), annoba mai tsanani ta auku a garin Amawaas kuma tamamaye garuruwan Shaam. Annobar tayi sanadiyyar mutuwar Sahabban Manzo…

TAMBAYA TA 72

*WATA TA NEMI IZININA ZATA JEFA MAGANI A RIJIYAR GIDANA......*: DAGA ZAUREN  📘 *HISNUL-MUSLIM*📘 :         *TAMBAYA* Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu  tambayata itace yakasance akwai tsohon rijiya agidan da nake sai wata tazo tace intaimaka mata zata jefa magani ni kuma a sanina sihiri ne kadai ake jefawa a tsohon rijiya to zan iya barinta ta jefa? :      *AMSA* Wa alaikumussalam warahmatullah . Bai halattaba kamata kiyi mata nasiha tareda nuna mata hadarin abun, domin allah s.w.a yana cewa  .  وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ
المائدة (2) Al-Maaida .  Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne. Allah ya karemu ➿➿➿➿➿➿➿ Masu buqatan kasancewa damu ta WhastApp 🔰🔰♻✳🔰🔰 +2348065523065 +2349039510396 〰〰〰〰〰〰〰 🆓facebook.com/hisnullmuslim
http://T.me/hisnulmuslim01
(( ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ…

TAMBAYA TA 71

*YA MATSAYIN KUDIN DA AKA TARA WA MARAR LAFIYA DON NEMAN MAGANI SAI YA RASU?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum warahmatullahi Wa barakatuh. malam Dan Allah a warware mana wannan matsalar..mutum ne ba lafiya aka nema masa taimakon kudi domin dashen qoda,ana cikin haka ba'a kai ga gamawa ba sai yarasu,to wannan kudin nasa ne ma'ana yazama nashi zai shiga gadonshi?ko za'a iya taimakon wani mai tsananin buqata irin wannan larurar.?mun gode jazakumullahu khairan.
*Amsa* Wa'alaykumussalam
Dukiyar da wani ya bayar don mamaci, kafin ko a bayan rasuwar sa ne, ita ma ta na cikin dukiyar gado.
A duba : [FATA'WAL LAJNATID DA'IMA; 16/473]
Wallahu A'alam
*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*
05/04/2020
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

TAMBAYA TA 70

Tambaya: Mene ne hukuncin sallar matar da ba ta rufe duga-duganta ba ko kuma wani sashe na jikinta ya bayyana ta na Sallah? : Amsa: : Abinda ya ke wājibi akan Mace idan zā ta yi Sallah shine, dōle ne ta rufe dukkan jikinta da tufāfi in banda fuskarta da kuma tāfukan hannāyenta, domin ita Mace dukkaninta al'aurace in banda wajen da aka tōgace, idan kuwa har wani ɓangare na jikinta ya bayyana kamar gāshin-kanta, Ƙwabrinta, ko wani sāshe na jikinta, to Sallarta ba ta inganta ba, domin kuwa Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ) Yāce: : "لا يقبل الله صلاة حائض إلا بخمار" MA'ANA Aʟʟāн(ﷻ) bā ya karɓar sallar mātar da (ta balaga ta fāra) Haila sai (in tā lulluɓe kanta da jikinta) da mayāfi, : To amma dangane da abinda ya shāfi hukuncin fitowar dugā-dugan-Mace ko Ƙafāfunta acikin Sallāh anan Mālamai sunyi Saɓāni, Mazhabobin Mālikiyya, Shāfi'iyya, Hanābila da wani sāshe na Mazhabin Hanafiyya tāre da mafi yawa daga cikin Mālamai-Ma'abōta-Ilimi duk sun tafi ne akan cewa wājibi ne Mace ta suturce dugā-du…

YANA DAGA CIKIN SUNNAH RASHIN GAISAWA DA MUTUMIN DA AKE ZA A IYA KAMUWA DA CUTA DAGA GARE SHI

YANA DAGA CIKIN SUNNAH RASHIN GAISAWA DA MUTUMIN DA AKE TUNANIN ZA A IYA KAMUWA DA CUTAR DA TAKE DAMUNSA
Amru bin Sharid Ath-Thaqafiy ya ba da labari daga Mahaifinsa ya ce:-
Qabilar Thaqif sun zo yi wa Manzon Allaah ( صلى الله عليه وسلم ) mubaya'a, ya kasance a cikin su akwai wani mutum kuturu, lokacin da mutumin ya taso zai yi mubaya'a ga Manzon Allaah ( صلى الله عليه وسلم ), sai manzon Allaah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aika masa da saqo cewa:-
 *" Lallai mun yi maka mubaya'a, ka koma inda kake ( ba sai ka qaraso nan ba) "*
Wannan hadisin Imam Muslim ne ya riwaito shi, hadisi mai Namba 4256.
*Ga Matanin hadisin cikin nan* 👇👇 قَالَ الإمام مُسْلمُ رحمه الله:-
4256 حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى ، أَخْبَرَنَا هُشَيْمٌ ، ح وَحَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ ، حَدَّثَنَا شَرِيكُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ ، وَهُشَيْمُ بْنُ بَشِيرٍ ، عَنْ يَعْلَى بْنِ عَطَاءٍ ، عَنْ عَمْرِو بْنِ الشَّرِيدِ ، عَنْ أَبِيهِ ، قَالَ : كَانَ فِي وَفْدِ ثَقِيفٍ رَجُلٌ مَجْذُومٌ ، فَأَرْسَلَ إ…

TAMBAYA TA 69

TAMBAYA========= 👇 Slm malam Dan allah hankalina atashe yake narasa yazanyi kabani shawara Dan allah Dan annabi ni budurwace kuma tunda nake bantaba sanin namijiba inasan aure amman iyayena basaso nayi yanzu Wai sainayi deploma kouma haryanzu bangama secondary ba ina sss 2 haryanzu sai shekara maizuwa zangama masu nemana sunanan dayawa yanzu haka wallahi malam akwai Wanda yake nemana ko yau akace yafito zaizo ashirye yake kuma shi ma aikicine likitane shi babbane yanada gidansa duk abinda ake nema yanadashi amman iyayena sunce saina gama deploma nan da shekara hudu kenan Dan bangama secondary bama haka narasa yazanyi musamman mahaifiyata itace take wannan bain shikuma babana maganarta yakeji kawayena babu Wanda baiyi aureba wasuma suna da yara uku amman saitace kada naje gidansu Dan kada su zigani akan aure narasa yazanyi bansan yazanyiba.   Malam Dan allah kataimkamin kabani shawara.

AMSA ===== 👇  Ba ke Za'a Baiwa Shawara ba. Mahaifanki ya kamata baiwa Shawara akan ya kamata Suyi Mik…

ZAGIN MATACCE

ZAGIN MATACCE....
IKRAMA BIN ABI JAHIL ya nuna qiyayya Mai tsanani ga addinin islama bayan yaqin uhud ya na cikin y'an committee da aka kashewa iyayan su a yaqin uhud, don HAKA ya cutar da muslunci matuqar cutarwa
HAKA Nan Abu ne bayyananne a tarihin muslunci irin cutarwar da Abu jahil yayi wa Annabi Sallallahu alaihi wasallam
Bayan fatahu makka Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace game da mutanen makka duk Wanda ya shiga ka'aba ko gidan Abu Sufyan ya tsira, Amma yace duk inda IKRAMA BIN ABI JAHIL ya shiga a kamo shi a kashe shi, da IKRAMA yaji labarin ya gudu ya bar garin can ya kusa tsallaka gabar kogi, matar IKRAMA BIN ABI JAHIL ta karbi muslunci taje ta roqi Annabi ya yafewa IKRAMA, Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya yafe Masa,  Sannan matar sa ta bi bayan sa ta sanar dashi cewa Annabi ya yafe masa, ya dawo zuwa garin makka ya muslunta  Kafin ya dawo Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace da sahabban sa "IKRAMA ZAI ZO MUKU YANA MUMINI MAI HIJRA , KADA KU ZAGI BABAN SA,…

TAMBAYA TA 68

Tambaya: Menene hukunci akan Jinin-Al'adar da ya ke yiwa Mace wasa sakamakon ta yi amfani da maganin tsarin iyali?? : Amsa : Alal-Haƙiƙa yin amfani da magungunan hana ɗaukan ciki sukan janyowa Mata wasu matsaloli dabam-dabam, kamar rikicewar al'ada wani lokacin sai Mace taga jinin yazo mata kafin lokacin zuwansa yayi, ko kuma taga yayi jinkirin zuwa a kan lokacinsa, to amma Malamai sunyi saɓani a game da hukuncin jinin da ke fitowa Mace a dalilin amfani da wani magani da ta yi, shin wannan jinin shima jinin-haila ne ko kuma jinin-cuta ne? : Wasu daga cikin Malamai sukace Mace za ta duba ne ta gani idan jinin yazo da siffa ne irin ta Jinin-Haila to kawai Jinin-Haila ne, amma idan yazo da wata siffa da ba ta jinin haila ba to ba zai hana ta yin ibadunta ba, : Wasu Malaman kuma sukace a'a kawai Mace za ta je ta tambayi Likita ne idan ya ce mata Jinin-Haila ne to shikenan hukuncin Jinin-Haila yahau kanta kenan, : Amma wasu Malaman suna ganin cewa dukkan wani jini da zai fitowa Mace a dal…

SOYAYYA DOMIN ALLAH

SOYAYYA DOMIN ALLAH. 
Imam Ash-Shaukani Allah ya masa rahama yana cewa "watarana na kwana inata kai komo akan hadisin manzon Allah da yake cewa {lalle maso soyayya domin Allah suna kan wasu minbari na haske wanda Annabawa da shahidai zasuso dama ace sune awannan matsayin}, na kasance inata tinani akan wannan hadisin tayaya soyayya domin Allah zata kasance, yaya take da za'ace har Annabawa da shahidai na kwadayin samunta??       Sai nace; hakika dayawa soyayyar da ake samu ayanzu badan Allah akeyinta ba,  🌹Miiji nason matarsa ba soyayyace domin Allah ba,  🌹 Mata nason mijinta ba soyayyace dan Allah ba,  🌺 Ya'ya nason iyayensu ba soyayyace dan Allah ba,  🌸 Iyaye nason ya'yansu ba soyayyace dan Allah ba.      Hakanan; kanason shugaba, dankasuwa, mai wakiltanka, kanason wane saboda kyansa, ko saboda sautinsa, ko saboda kudinsa.       Da wannan ne nagane cewa ita soyayya domin Allah ita tafi karanci samada Jan kibreet".
الفتح الرباني مجلد التاسع. 
# zaurenfisabilillah https…

SINADARIN MA'AURATA

SINADARIN MA 'AURATA
shi wannan wani sinadarine mai albarka wanda ake yi masa lakabi da sinadarin ma'aurata, kuma yana jimawa a jiki, sannan yana kara kuzari kuma yana karawa mace martaba ga mijinta. zaki samu:
 *furen zogale* *zanjabil*  *habba*  *garin raihan* sai ki dakesu guri daya sudaku dakyau sai rinka diban karamin cokali kina hadawa da zuma kina safe da yamma shima wannan sai mai aure amma idan kin kusa yin aure zaki iya yin wannan hadin. 
👆🏽yanayi shima👏🏽 Sirri na 2

TAMBAYA TA 67

*SHIN KO SHARI'A TA YADDA MUTUN YA KAURACEWA MATAR SA DA SUN SAMU SABANI YA BARTA BA ABINCI BA KWANA A DAKIN TA?*
*Tambaya*
Assalam alykum warahmatullah Mlm ina da makwafciya su biyu ne wajen mijin to da abu yafaru tsakaninsu matan da mijin wdd sukayi rashin jituwar sai yabar dakinta yakoma dakin dayar tace ko kwanan tane bazai shiga ba Mlm tace sai yayi fin sati adaki daya baya kulata bare kudin abinci Mlm haka dayake ya dace da shariar Ubangiji Allah ngd
*Amsa* Wa'alaykumussalam
Haka ba dai dai bane, domin shari'a ta zo da tsayar da adalci... Tayi kokarin tattaunawa dashi cikin lumana don tina masa hakin ta dake kan sa idan ya gyara toh shikenan idan kuma bai gyara ba toh sai ta kai shi gaba (sanar da magabatan sa) domin suyi masa nasiha.
Wallahu A'alam
*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*
05/04/2020
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

YADDA AKE HAƊA PEANUT BOGGER

RAHMAT KITCHEN & MAKE UP 🍝🌶💄👄      PEANUT BOGGAR       Ingredient
* gyada * kwai * sugar * milk * fulawa  * baking powder * gishiri  * mai      METHOD
Zaki sami gyadan ki ki tsinceta ki wankata sannan ki bazata a rana ta bushe bayan ta bushe zaki soya ta kadan ita bata soyu ba kuma ita ba danya ba bayan kin gama se ki dakko kayan hadinki , zaki fasa kwan ki a wuri mai kyau se ki saka sugar acikin ruwan kwan ki zaki yi ta buga shi har se sugar ta narke bayan ta narke se ki dakko madara na gari amma ki zuba akai se ki kara baga shi har su hade jikin su in kika gama se ki dakko fulawan ki da ki ka Riga kika tankade ta se ki saka baking powder dinki da gishiri kadan seki jijjuya su su hade jikin su bayan kin gama se ki dakko gyadar ki se ki zuba hadin ruwan kwan ki kadan se ki jijjuya ta ko ina ya ji bayan kin gama juyawa se ki dakko hadin fulawar ki kina zubawa kina jiwa da sauri-sauri Dan kar ta cure wuri daya in in fulawar taji ko ina se ki kara zuba hadin ruwan kwanki ki kara jiyawa se ku…

THE WISDOM BEHIND FASTING

THE WISDOM BEHIND FASTING
Fasting is a great act of worship the Muslim performs by turning away from his own desires in order to please his Lord, hoping for His reward. Common sense dictates that one would not give up desired things except for the sake of more desirable ones, in this case the pleasure of Allah, which is the most sought after desire.
It is also a means if achieving piety and righteousness. The Prophet صلي الله عليه وسلم said, “ He who does not give up forged speech and evil actions, Allah needs not his refraining from eating or drinking.”(16) In other words, Allah does not accept his fast.
The heart, through fasting, is inclined to maintain its tenderness since the desires are not sought, but rather shunned, and thus the heart tends to be more receptive to the words of Allah.
The rich person will, through fasting, be more appreciative of Allaah’s graces and bounties. He also will suffer the deprivation the poor and needy experience under normal circumstances. Thus he will …

TODAY'S HADITH

Manzon (SAW) yace:
Mutane ba zasu gushe suna cikin alkhairi ba matuƙar suna gaggauta buda baki. -Bukhari
An so gaggauta buɗa baki lokacin da aka tabbatar da faɗuwar rana ta hanyar gani ko kuma ya yi galaba a wajen sa cewa rana ta faɗi ta hanyar jin labari daga amintacce Imma da kiran sallah ko wanin sa.
 Shaikh Saleh Al-Fauzan R.
#Zaurenfisabilillah Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

LADUBBAN DA MAI AZUMI YA KAMATA YA KULA DA SU

Article 005//
LADUBBAN DA MAI AZUMI YA KAMATA YA KULA DASU
Wadannan sune dunkulallun ladubban da nassoshi na Shari’a suka zo dasu kuma suka kwadaitar wa akan su, sai dai a Yau zamu dauke wasu ne daga cikin muyi bayanan su, kuma ya kamata ga kowani mai Azumi ya kula dasu kulawa ta musamman, lokacin da yake dauke da Azumi a bakin shi.
LADABI NA FARKO: KIYAYEWA AKAN SAHUR, TARE DA JINKIRTA SHI
Saboda fadar Annabi ﷺ: “Kuyi Sahur domin shi Sahur acikin sa akwai albarka”. [Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi daga Sahabi Anas ɗan Malik]
Ba hakanan ba kadai, Annabi ﷺ ya sanya cin Sahur yana daga abunda yake bambanta ma’abota Musulunci daga Yahudu da Nasara, sai Annabi ﷺ yace: “Bambancin da yake a tsakanin Azumin mu da Azumin Yahudawa da Nasara, shine cin Sahur”. [Muslim ne ya riwaito shi daga Sahabi Amru ɗan Ass]
Bayan haka kuma, Sahur yana sanya nishaɗi da walwala ga mai Azumi, sannan yana kara Lada da albarkar Azumi, kuma dukkan Annabawan Allah suna yin Sahur, kuma Allah da Mala'ikun Sa sun…

FASTING: THE GREATEST ACT OF WORSHIP 1

*01 ≈ Fasting : The Great Act of Worship*
By:- Shaykh ibn Uthaymeen
بسم الله الرحمن الرحيم
THE VIRTUES OF RAMADHAAN
Abu Hurayrah رضي الله عنه narrated that Allah’s Apostle صلي الله عليه وسلم said, “ When the month of Ramadhaan starts, the gates of Jannah (Paradise) are opened and the gates of Hell are closed, and satans are chained.”(1) The gates of Jannah are opened in this month because a great deat of righteous deeds are performed, and as an encouragement for those who seek Allaah’s reward. The gates of Hell are closed because few sins are committed by believers. The Satans will be chained so that they may noy have the chance they have in other months to whisper into the hearts of the believers and misguide them.
Allaah has prescribed fasting and it obligatory upon all nations. He said :
) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ) (البقرة:183)
O you who believe ! fasting has been prescribed for you as i…

MU SAN AZUMI A SHARI'ANCE 13

_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(13)
*DAREN LAILATUL KADARI*
Ya zo a cikin Hadisi, ana samun Daren Lailatul Kadari a kwanakin mara na goman karshe na watan Azumi a daren ashirin da daya ko ashirin da uku ko ashirin da biyar ko ashirin da bakwai ko ashirin da tara da dare na karshen watan Ramadan.
Nana Aisha (R.A)  ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce:  “Ku nemi Daren Lailatul Kadari a goman karshe.”  (Bukhari ne ya rawaito).
Ana so a yawaita addu’a a Daren Lailatul Kadari.  Nana Aisha (R.A) ta ce, na tambayi Manzon Allah (S.A.W) Na ce, ya Rasulullahi, idan na ga Daren Lailatul Kadari me zan fada a cikinsa? Sai Manzon Allah (S.A.W)  ya ce, ki ce: 
*"اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى."*
“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa’afu anni.” Ma’ana:
 “Ya Ubangiji, hakika, Kai mai afuwa ne, kuma kana kaunar yin afuwa,  ya Allah ka yi min afuwa.”  (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
Kuma ana so a karanta wadannan ayoyi masu yawan lada. 1- آيَةُ الْكُرْسِيُّ  2- آمَنَ …