Barka da warhaka

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2


Bissmillahi Jallah sarki
Rabbana Sarki gurina
Za na fara da sunan ka
Rabbana mahaliccina
Za na yi waƙe akan Corona
Wacce ta zagaye duk garina
Babu sarki sai Allah a wajena
Annabina baban Fatima
Shi ne manzo a guna.

Duniya dukka ta jigata babu sauran watayawa,
Rayuwa yau ta wahalta ba batu na mai darawa,
Hatta jakin da ya ke cin harawa,
Ya san duniya ta sauya tunda babu sukunin yawatawa, 
Bar batun baƙin fata ko baturen yammatawa,
Ƙyale zancen mutan Kaduna ko mutane na Kanawa,
Duniya kaf tana ta kuka da zuwan cutar Corona,
Rabbana mun yi nadama a gare ka mu ke ta tuba.

Mun yi tuba a gare ka ubangijina sarki kai ke da kowa,
Mun yi tawassili da ƙur'ani magani ga komai,
Mun yi sujjada gare ka Rabbana kai ke da kowa,
Muna ta roƙo a gareka rabbi kai ne ka ke da komai,
Ka yafe mana laifukanmu kar ka bar mu da wayonmu,
Domin in ko ka bar mu da wayonmu babu sauƙin da za mu samu.

Mun yi roƙo zuwa gare ka babu shakka ko gadara,
Mun yi tuba zuwa gareka babu ɗa babu maraya,
Mun koma zuwa gareka Rabbana ka kawo mana sauƙi,


Gamu nan yau muna ta kuka ba baƙauye babu na birni,
Babu yaro ba wani babba ba mace ba jinsi na,
Wahala ta yi mana tsauri Rabbana ga mu mun tuba ka yafe mana Allah.

Cutar nan ta Corona Rabbana ka kiyaye mu,
Ka tsare mu ubangijinmu da mu da iyalanmu,
Ka yaye mana ita a gida har ma garinmu,
Da maƙwabta da duniyar mu don mu samu zaman lumana.

Rabbana albarkar watan Ramadana ka sa cutar nan ta bar mu,
Rabbana ka sa ta tafi don mu samu shiga garinmu,
Ka sa ta zamo labari a kunnuwanmu, 
Watarana mu yo zance da tunanin ta a rayuwar mu,
Ta zamo mana tarihi abin tunawa a tsakanin mu da juna.

Aameen.

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------

    +23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Facebook
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹───── ─m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76• 
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form