Skip to main content

Posts

Showing posts from May, 2020

SHARHIN FIM ƊIN BIGIL

SHARHIN FIM ƊIN BIGIL 

Bigil fim ɗin India ne da ya fita a cikin shekara ta 2019. Shiri ne da aka shirya shi a cikin harshen Tamil kuma yana ƙunshe ne da faɗa tare kuma da wasan ƙwallon ƙafa. An sanar da tabbacin cewa za'a yi wannan shiri ne a ranar 14 ga watan Nuwambar shekara ta 2018 inda a wancan lokaci ake wa shirin take da Thalapathy 63. Haka kuma shirin shi ne shiri na uku da jarumi Vijay yayi da mai bada umurni Atlee bayan Theri da kuma Mersal. 
An fara ɗaukar wannan shiri ne a ranar 21 ga watan Janairu 2019 a garin Chennei, yayinda kuma aka kammala a ranar 10 ga watan Agustan wannan shekara. Haka kuma an sanar da sunan shirin ne a ranar 22 ga watan Yuni na 2019 tare da hoton farko na shirin. Ma'anar Bigil dai shi ne fito. 
An fassara wannan shiri tare da sakinsa a cikin harshen Kannada da sunansa na asali, yayin da aka fitar da shi a harshen Telugu da sunan Whistle. Fim ɗin ya samu yabo kuma ya samu suka a lokacin fitarsa. Sai dai kuma ya samu nasara sosai a harkar kasuwa…

FASSARAR WAƘAR HUM MAR JAAYENGE

Fassarar Waƙar Hum Mar Jayenge
Waƙa: Hum Mar Jayenge
Fim: Aashiqui 2
Harshe: Hausa 
Shekara: 2013
Sauti: Mithoon, Jeet Ganguly
Rubutawa: Irshad Kamil, Sandeep Nath
Kamfani: T-Series
Rerawa: Arjit Singh & Tulsi Kumar 
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Apni aankhein khaali kar de
Ka goge idanuwanka. 
• Kaash tu meri aankhein bhar de (x2)
Ina ma za ka cika idanuwana (da hawayenka) 
• Mere yaara tere gham agar paayenge
Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 
• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge
Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa. 
• Ho... Mere yaara tere gham agar paayenge
Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 
• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge
Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa. 
• Do yeh saugaat tum, to zamaane ki hum (x2)
Idan har ka bani wannan kyautar, to zan... 
• Har khushi se mukar jaayenge
Ce a'a wa dukkan farincikin duniya. 
• Hum mar jaayenge ho...
Mutuwa zan yi. 
• Hum mar jaayenge ho...
Mutuwa zan yi. 
• Mere yaara tere gham agar paayenge
Abokin t…

ALHAJI DA HAJIYA

Alhaji da HajiyaGata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
A wani gida a wani gari, akwai alhaji da hajiya a gidan, kuma akwai wani ɓarawo yana da sunaye da yawa, sai ya je gurin mai gadin gidan. Da mai gadi ya gan shi sai ya tambaye shi sunansa, sai ɓarawo ya ce sunansa salati, sai mai gadi ya tambaye shi gurin wanda ya zo, sai ya ce gurin alhaji ya zo, sai ya ce da shi ya wuce.
Da ɓarawo ya shiga gurin alhaji sai alhaji ya tambaye shi gurin wanda ya zo, sai ya ce gurin hajiya ya zo. Sai alhaji ya tambaye shi sunansa, sai ɓarawo ya ce sunansa Alanta, sai alhaji ya ce da shi ya wuce. Daga nan kuma sai ya wuce gurin hajiya. Da ya isa gurin hajiya sai ta tambaye shi sunansa, sai ya ce da ita sunansa dambu, sai ta ce da shi gurin wa ka zo? Sai ya ce da ita gurinki na zo, sai ta ce da shi “me ka zo yi”, sai ya ce “sarƙar wuyanki zan sace”. Sai ya shaƙe mata wuya zai ƙwace sarƙar, sai ita kuma ta fara kururuwa tana cewa, “alhaji dambu ya shaƙe ni”. Sai alhaji ya ce da ita “kora da ruwa”, har sai …

JATAU DA MUTUWA

JATAU DA MUTUWAWai wata rana Mutuwa ta zo wa Jatau tace masa lokacinka yayi, sai Jatau yace gashi kuwa ban shirya ba, Mutuwa tace ko baka shirya ba lallai yau tafiya zaka yi, don sunanka ne na farko a saman takardata, jatau yayi rarrashin duniya akan mutuwa ta kyaleshi mutuwa taki.
Da ya fahimci mutuwar ba zata kyaleshi ba sai dabara ta fado masa sai yace wa mutuwa to me zai hana ki bari in dan kawo maki abinci ki ci kafin mu tafi? Mutuwa ta zauna Jatau ya tafi kawo mata abinci.
Da yaje wurin dauko abincin sai yasa maganin bacci cikin abincin ya kawo wa mutuwa, da mutuwa ta ci abincin sai ta kama bacci, da jatau yaga tayi bacci sai ya dauko takardar da sunayen mutane suke sai ya goge sunansa daga saman takardar ya rubuta a kasan takardar.
Da mutuwa ta farka daga bacci sai tace wa jatau saboda jin dadin karramawarda kayi mini da kuma dadin abincinka da naji har nayi bacci, ba zan fara sunayen mutane daga saman takardar ba zan faro daga kasan takardar. Jin haka sai Jatau ya fadi sumamme.
Da…

HANKAKA DA KURTATTAKI

Hankaka Da Kurtattaki Wata rana kurtattaki na koto a gonar wani bakauye, suna tone shukar da ya yi suna cinyewa, sai ga hankaka ya zo zai wuce. Ya ce musu, “Na hore ku da ku tone abin da manomin nan ke shukawa duka ku cinye.”
Sai suka tambaye shi me yake shukawa. Hankaka ya amsa musu, “Irin rama.”
Kurtattaki suka kada fiffike suna yi wa hankaka dariya, “Me za mu yi da irin rama ga dawa da gero.”
Kwanci tashi rama ta fito har ta girma. Manomi ya cire ta ya kware bawon ya yi zare. Da zaren rama ya tufka raga wadda ya kafa tarko cikin gonarsa, kurtattakin nan duka suka fada cikin tarkon. Suna cikin kici-kicin yadda za su yi su kubuta sai ga hankaka. Ya dube su ya ce, “Ashe ban gaya muku ku tone irin ramar nan ba tun kafin ya fito? Ga abin da nake yi muku gudu nan!”
Manomi ya kama kurtattaki ya kashe, da ma sun addabe shi da barna. Hankaka ya wuce yana cewa, “KU KAWAR DA MUGUN IRI, KO YA GIRMA YA KAWAR DA KU!”

TATSUNIYAR DISKIN DA RIƊI

Tatsuniyar Daskindaridi 
Gata nan Gata nan Ku...
A wani gari da akwai wasu 'yan mata wanda suke zaune tare a gida daya. Da alkama, shinkafa, dawa, da kuma daddawa.
Sun tsani daddawa kamar me. Komai ba'a yi da ita. Sai watarana aka yi shela a gari cewa duk 'yan matan gari su hadu a wani fili za'a yi gasa. Ita wannan gasar za’a chanki sunan dan sarki ne! duk wanda ya chanka zai aure dan sarkin.
Su alkama, dawa, da suransu suke ta murna za'a tafi filin gasa. Ranar gasar ta zo duk 'yan matan suka ci kwaliyya banda daddawa saboda bata da abun sakawa! kuma sauran 'yan matan suna ta yi mata dariya.
Haka suka shirya suka tafi ba tare da daddawa ba. Abun tausayi daddawa ta saka 'yan kayanta wadanda take ji dasu ta kama hanyar filin gasa.
A hanya, sai 'yan matan nan suka hadu da wata tsohuwa tana wanka a rafi. Sai tsohuwar tace da Allah su taya ta wanke bayan ta sai yan matan suka ce lallai ma iya baki ganin na ci kwaliyya ki ce wani na wanke maki baya! sannu ma. D…

SOYAYYAR ZAMANI 1

*DA'AWA WOMEN GROUP* 🎤🎤🎤💞 *SOYAYYAR ZAMANI {1}* 💞

Dan taqaitaccen rubutu akan halin da samari da yan mata suka tsinci kansu da sunan *soyayya.* 
Allah ya kawo mu wani *zamani* da sai dai ace innalilahi wa'inna ilaihir raji'un, yanda samari da yan mata suke holewa san ransu da sunan soyayya abin yayi muni. 
A zahirin gaskiya a yanxu yanda mutuwar aure da rigingimu tsakanin ma'aurata suke qara yawaita... wani aurenma ko wata baya qarasawa sai ace an rabu. to irin wannan auren meye amfaninsa, ina qaunar? ina soyayyar da akeyi kamar za a cinye juna? duk ta tafi a banxa kenan?
Wannan yana faruwa ne sakamakon tun kafin auren an gama debe albarkarsa an gama sabawa Allah da take dokokinsa, an qulla alaqar ba don Allah ba, an ginata ba akan doron gaskiya ba, sai kuma uwa uba an gama taba jikin juna tas tun kafin auren,duk wadan nan su suke haduwa suke haifar da matsaloli bayan aure. 
Sai dai galibin mutanen da hakan take faruwa dasu basu fahimtar ai ga abin da suka aikata…

JAN HANKALI GA SABUWAR AMARYA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Zaman Aure: Jan Hankali Ga Sabuwar Amarya_*
Zaman auren kusan ya fi kowanne zama dadi, haka kuma ya fi komi wuya, domin Hausawa ma suna fadar zo-mu-zauna-zo-mu-saba! Aure idan zamansa ya yi dadi za ka ga ana jin dadi, ana sam barka tsakanin amarya da ango da mahaifan ango da mahaifan amarya. Har ma ana gasa wurin kyautata wa kowane bangare, kowa zai rika kokarin ganin ya kyautata wa wani bangare domin nuna masa jin dadinsa da godiya a kan diyaucin da aka nuna masa. A wannan lokacin za ka sami ango yana wani haske, yana ciccika, yana kasaita tamkar wani basarake, ko wata agwagwa. Yayin da ita kuma amarya za ka ga tana sheki da wani irin kumbura tamkar kazar Turawa. Haka za ka ga tana wani irin annuri da sakin fuska. A wannan lokacin ko iska ta kada sai ta yi masa dariya, to, balantana wani ya yi mata magana ta wasa ko ta zolaya. Shi ango kada ma ka tona bangarensa, domin shi kam wannan zarafin ya koma wani dan karamin tauraro ko kuma ya koma tamkar mota kirar sa…

TSIMIN KWARJINI

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Yadda Ake Hada Tsimin Mai Haifar Ma Mace Kwarjini Da Kima_*
Wannan tsimi ne wanda yake da matukar mahimmanci musamman ga matayen da mazajensu suke yawan kuka na rashin jin dadi yayin saduwa ko kuma ita kanta sai taji kamar ana tusa ma mata ice a gaba, to yar uwa ga maganin matsalarki yar uwa.
 Wannan tsimi yana Karawa mace kwarjini da kima a wajen mijinta.
Zaki nemi wadannan abubuwan kamar haka; * Yan shila guda biyu. * Albasa fara. * Gyadar mata. * Furen zogale. * Idon zakara. * Kayan qanshi. *Bayani;* Zaki dafa wannan ‘yan shila da wadannan da duk kayayaki zaki zuba a cikin tukunya da kike dafa yan shila, kuma wannan hadin shi akesu a fara karyawa da shi da safe kafin mutum ya ci abinci, Yana matuqar kara kwarjini da kima da kuma ni’ima ga ya mace. domin yana daga cikin abinda yake taka rawa muhimmiya ga ma’aurata.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Mace…

AMFANIN RUWAN ƊUMI GA 'YA MACE

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Amfanin Ruwan Dumi Ga Ya Mace;_*
Mafi yawan mata ba su damu da yin amfani da ruwan dumi ba, to lallai daga yau ki sani cewa ruwan dimi na da matukar mahimmanci ga jikinki. Ruwan dumi yana kara wa mace lafiya a jikinta fiye da jikin da namiji. Idan da baki yin amfani da ruwan dumi a jikinki, to daga yau ki fara za ki sha mamakin yadda jikinki zai koma.
*1. Ruwan dumi:* yana taimaka wa mace wajen kashe mata wasu kwayoyin cuta idan tana tsarki da shi. Yana kuma kara mata ni’ima a matsayinta na matar aure.
*2. Ruwan dumi:* yana zama kariya ga mace wurin kamuwa da cututtuka idan tana yin wanka da shi. yana kuma gyara wa mace fata ta yi kyalli ba tare da kin yi bilicin ba.
*3. Ruwan dumi:* yana mikar da hanjin ciki lokacin da suka tattari sakamakon yunwa ko kuma an yi azumi. Ina bukatar idan mutum ya dade bai ci abinci ba, to idan ya zo zai ci ya fara da abu mai zafi domin ya mikar da hanjinsa kafin wani abincin da bai da zafi.
*4. Ruwan dumi:* yana kara dankon zamanta…

KIYAYE ABINDA YAKE DAIDAI SHI NE MAFI WAHALA A WANNAN ZAMANI

*KIYAYE ABIN DA YAKE DAIDAI SHINE MAFI WAHALA A WANNAN ZAMANI!*

Abu ne mai sauki mutum ya ya ɓata dare baki ɗaya yana kallo da chartings da downloadings da sauraron waƙoƙi. Amma abu ne ami wahala a gare shi ya ya tashi yayi sallar tahajjud a daya biya ukun dare, balle yaje sallar asuba.
Abu ne mai sauki a wajen 'yan matan yanzu da burgewa su saka kaya matsattsu da fidda tsiraicinsu da shapes din jikinsu. Amma abu ne mai matukar wahala a wajensu su saka hijjabi da niqabi su rufe jikinsu da kyau.
Abu ne mai sauki a wannan zamanin ƙawata alfasha da yi mata kwaskwarima da daukanta wayewa da burgewa wajen yadawa acikin mutane da kuma koya musu ita, ta hanyar mace ta dinga rawa a gaban mijinta ko suna rungumar juna da sunan wai soyayya, amma abune mai wahala a wajen irin wannan mutanen yin Umarni da kyakkyawa ta hanyar da ya dace da koyarwar addinin islama! 
Abu ne mai sauki yanzu ayi gulma a ci naman wani wanda yayi daidai ko akasin haka. Amma abu ne mai wahala wajen kare da tsare mutuncin…

YADDA ƊAKIN MA'AURATA YA KAMATA YA KASANCE A LOKACIN SADUWA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Yadda Ya Kamata Dakin Ma'aurta Ya Kasance A Lokacin Saduwa_*
Ya kamata dakin ma'aurata ya kasance kamar haka; A duk yayin da suka nufi saduwa da junansu a cikin dare ne ko rana. Kamar yadda sunnar Manzon Allah ta tsara kamar haka;
1. Dakin ya kasance babu wani mutum a cikin ko da yaro ne.
2. Daki ya kasance a lokacin mai nutsuwa.
3. A samu karancin mutane a kusa da wajen.
4. Dakin ya kasance a kulle yake.
5. Sannan a kashe fitilar cikin dakin.
6. Abin kwanciyar ya kasance ba mai motsi ba.
7. Dakin da abin kwanciyar su kasance mafi dadin kamshi.
8. Ma'aurata su kwanta a tube ba tare da tufafi ba, amma ba laifi ba ne in sun kwanta da kaya a jikinsu.
9. Su kwanta a cikin mayafi guda daya, amma ba laifi ba ne in sun kwanta a mayafi daban-daban.
10. Su ambaci sunan Allah kafin su fara saduwa.
11. Daki ya kasance ba hayaniya.
Wabillahi Taufiq. Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shig…

TAMBAYA TA 145

TAMBAYA 1,724Assalamu alaikum, Malam idda Wata nawa ne mace takeyi tagama? AMSA Idda shine lokaci da Allah ya ɗebawa mace ta jirashi kamin yin aure bayan rabuwa da mijinta, ko mutuwarsa sannan Allah ya ɗaurawa mace idda ne saboda dalili kamar haka: 1. Kuɓutar da mahaifarta saboda kada ruwan maniyyi maza sama da biyu su haɗu akan yaro ɗaya 2. Domin nuna darajar aure 3. A baiwa mijin da yayi saki lokaci mai yuwa ya gane amfanin matarsa ko kuskurensa ko ita sannan idan sunyi nadama su nemi su koma 4. Bin dokar Allah kan bayinsa, saboda mace ta zauna wajen sauƙe haƙƙin mijinta da Allah yayi mata umarni daidai yake da Allah tayi wa biyayya *NOU'O'IN IDDA* 1. sakakkiyar da mijin ya tara da ita wannan iddanta jini uku ne saboda faɗin Allah cikin suratul baƙara aya ta 228 ((sakakkun mata zasu zauna ga kawunansu jini uku)) 2. Sakakkiyar da bata idda saboda ƙarancin shekaru ko tsufa wannan kuma iddanta wata uku ne saboda faɗin Allah cikin suratul Ɗalaƙ aya ta 4 ((wanda suke ɗebe tsammani daga a…

ILLAR RASHIN TSAFTA A GIDAJEN MATAN AURE

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Illar Rashin Tsafta A Gidajen Matan Aure_*
Akwai abubuwan da yakamata mu lura da su, mu inganta su a wurin gina tsaftarmu. Misali wanka, wanki, wanke kai, goge dattin kunnuwa, wanke baki, wanke hannu, yankan farce, da sauransu.
A nan ina so mata su gane cewa muna da daraja da kima dole sai mun tsaya mun lura da abubuwa a cikin zamantakewar aure sannan gidanmu zai gyaru, mu kwato wa kawunanmu ‘yancinmu a hannunmu domin addinin musulunci ya fi kowane addini tausaya wa mace a tarihin dan adam.
Amma abin da ke ban mamaki sai ka shiga gidan mace ka ganshi kaca-kaca, babu sha’awa, kazanta ta tare tun daga tsakar gidanta da dakunanta da ban-daki har ita kanta. Ga tulin kayan wanki da wanke- wanke kuda suna bi ko kayan wanki a jibge, yara kuwa sai ka gan su dukun-dukun, hanci dagaje- dagaje da majina. Idan ma girki take yi sai ka gan shi a bude ko an bude murfi an bar shi a kasa ana face majina, wannan yana daga cikin abin da maza suka tsana. Kuma koma wane ne ransa ba…

MACEN DA TA KE ƘAUNAR MIJINTA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Macen Da Take Kaunar Mijinta_*
Ita ce Wanda a har kullum burinta bai wuce ya zata sa mijinta farin ciki.
Ita ce wanda koyan nau'ikan girki don natsuwan mijinta.
Itace mai kwalliya don ta kawar ma mijinta hankali daga matan banza.
Tana sadaukar da lokacinta don faranta ma mijinta rai.
Tana kawar da duk wani abu wanda tasan mijin baya so.
Itace wanda takeyin komai don gamsar da mijinta a shimfida.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Me Ake Nufi Da Soyayyar Gaskiya?

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Me Ake Nufi Da Soyayyar Gaskiya?_* Kowane mai rai na bukatar Soyayyar gaskiya, sai dai mutane kadan ne ke sa’ar gamuwa da masoyan gaskiya a cikin dan kankanin lokaci.
Ya zaka bayyana soyayyar gaskiya?.. Soyayar gaskiya aba ce da tafi komi dadi da kuma faranta ma dan adam rai a lokacin da mutum ke cikin soyayya.
Dan kawai ka hadu da wani ko wata waddan kake kauna ba shine soyayayyar gaskiya ba, ko da wanda kake so ma najin irin yadda kake ji ba lallai son gaskiya ne ba.
Amma bincike ya nuna hakan shine mataki na farkon soyayyar gaskiya.
A cikin mataki na farko akwai yadda, domin kuwa babu soyayyar da zata kai labari idan babu yadda a tsakanin masoyan.
Idan yadda ta shiga tsakanin masoya, to lallai babu sauran wata damuwa ko tunani na daban akan abokin soyayya.
Amma idan yaddar bata zo daidai ba, to ana iya samun matsala ko kuma rabuwa.
Soyayyar gaskiya abuta ce tsakanin saurayi da budurwa ko mace da namiji mai karfin gaske, saboda idan kana matukar so da kaunar masoyi…

YORUBA PEOPLE

YORUBAAAAAAAAYoruba people can't correct someone without adding insult as a suffix. (1) do it like this, ode. (2) press the red button, oponu. (3) hold it for me, didirin! (4) you can't greet person, alaileko. (5) give it to your brother, agbaya. (6) Go and take your bath, obun. (7) Go and do your assignment, Olodo. (8) you better wake up, oloorun iya. (9) Yago lona funmi joor, arindin. (10) iwo ni moun pe......aditi. (11) where are you coming from, onirin kuri? (12) Stop writing on the wall, Baseje! (13) you forgot what I just told you now, alakogbagbe. (14) So the one you ate is not enough, oloun je iya. (15) who put your mouth there, saliu elenu gboro? (16) Is that where I asked you to put it, abunu. (17) I know you are laughing now..... oni yeye. (18) Shaa forward it to others, amebo. 😂😂😂😂😂😂. Don't laugh alone put a smile on someone's face by SHARING to them. okay ooo Pass it to everyone in Messenger and see hw much they love u 😭0%... 😪10%... 😁20%... 😔30%... 😛40%... 😃50%... 😮60%…

RUFE MASALLATAI SABODA ANNOBAR CORONAVIRUS

RUFE MASALLATAI SABODA ANNOBAR KORONA
Rubutawar Abdulmajid Muhammad Umar
22/Ramdana/1441 Birnin Madina, KSA Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin kai. GABATARWA Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad SAW da alayensa da sahabbansa gaba daya. Bayan haka, hakika duniya ta samu kanta a wani yanayi wanda ya canja abubuwa da yawa; na addini da rayuwa. Duk da cewa malamai a wannan zamani sunyi sabani akan hukucin rufe masallatai, hakan bai hana a yi rubutu kan hukucin hakan a ilmance.
KAFIN NA TSUNDUMA CIKIN AINIHIN BAYANI KAN RUFE MASALLATAI, AKWAI WASU MUHIMMAN GINSHIKAN DA YA KAMATA MAI KARATU YA SANI; Allah Ya kara mana fahimta, Ya ba mu kirji mai yalwa, Ya kara mana sani a addini, Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.
Na Farko: A Musulunci akwai hukunce-hukunce da suke banbanta tsakanin daidaikun mutane ko wani bangare na mutane da kuma gaba daya al’uman gari ko kauye; misali:  Misali Na Farko: Kira…

WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI 5

WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI
Kabir Abubakar Asgar
Fitowa ta Biyar
D. KO TARIHI NA MAIMAITA KANSHI?
Fadin cewa ‘tarihi na maimaita kanshi’ magana ce shahariyya a bakin mutane. Abu ne mai sauki a fahimci cewa maganar ta dade kuma ta shiga cikin al’ummomi mabambamta da yarurruka dabam-dabam.
Abin da maganar take nufi shine duk abin da kake gani yana faruwa a rayuwa ta fuskar siyasa da tattali da yaqe-yaqe da daukakar dauloli ko faduwarsu da samuwar damuwoyi dabam-dabam a al’ummar dan adam ko cututtuka ko annoba ko fari da yunwa da kuma fadi-tashin da dan adam yake yi don raya qasa da gyara ta da inganata rayuwarsa a bayan qasa da gwagwarmayar neman ‘yanci ko mulki ko faruwar rikici tsakanin qasashe ko tsakanin ra’ayoyi dabam-dabam da sauransu to ba wanda ba a taba ganin makamancinsa ba a can baya.
Fadin haka ya samo asali ne daga kasancewar dabi’ar dan adam ba ta canzawa, shi ya sa ake samun maimaituwar abubuwan da ke faruwa a kodayaushe. Masana da yawa na iqirarin cewa su gano cew…

FASSARAR WAƘAR CHINTA TA TA

FASSARAR WAƘAR CHINTA TA TA CHITA CHITA 
Waƙa: Chinta Ta Ta Chita Chita
Fim: Rowdy Rathore
Harshe: Hausa
 Shekara: 2012
Sauti: Sajid-Wajid
Rubutawa: Sameer Anjaan
Kamfani: UTV
Rerawa: Mika Singh & Wajid 
Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Duniya chale pichadi
Da ace duniya za ta koma baya. 
• Toh main chalu agaadi
To ni gaba zan yi. 
• Sab khel jaanta hoon
Na san duk wasannin. 
• Main hoon bada khiladi
Ni babban ɗan wasa ne. 
• Oh ho..Duniya chale pichadi
Da ace duniya za ta koma baya. 
• Toh main chalu agaadi
To ni gaba zan yi. 
• Sab khel jaanta hoon
Na san duk wasannin. 
• Main hoon bada khiladi
Ni babban ɗan wasa ne.
• Simti mein leke jaaun
Dukkan su zan kaisu kusurwa ɗaya. 
• Aur sab ko main sikhaun
In koya musu dukkan su. 
• Kya?
mene? 
Chinta ta ta chita chita Chinta ta taa.. Chinta ta ta chita chita Chinta ta taa.. Chinta ta ta chita chita Chinta ta taa.. Chinta ta ta chita chita Chinta ta taa..
• Duniya chale pichadi
Da ace duniya za ta koma baya. 
• Toh main chalu agaadi
To ni gaba zan yi. 
• Sab khel jaanta hoon
Na…

VERSE OF THE DAY

Brothers and sisters in Islam we will continue with our last topic from the book of *AL-QUR'AN* which I bring to you every two days, with me your presenter *_Abu 'qatada Muhammad Bashir Ibrahim Illela_* have a nice reading.
[Quran 4:120] He [Shaitan (Satan)] makes promises to them, and arouses in them false desires; and Shaitan's (Satan) promises are nothing but deceptions.
[Quran 22:65] See you not that Allâh has subjected to you (mankind) all that is on the earth, and the ships that sail through the sea by His Command? He withholds the heaven from falling on the earth except by His Leave. Verily, Allâh is, for mankind, full of Kindness, Most Merciful. 
_*We will stop from here and we will continue in our next lesson by Allaah's willing*_

TRUST

TRUST 
In The Name Of Allah, The Most Gracious, The Most Merciful.
Brothers and sisters in Islam, our daily reminder today is going to talk about trust.
Trust is very important aspect of man's responsibility. A good Muslim must keep trust and not betray it. If one is the head of a place, those under him are to put in him trust, he should therefore treat them well for Allah shall ask how he has treated them. The same applies to one's wife and children, they are put in one's care and must be taken care of. If a teacher keeps some money for the care of a student, the student should not say that the money is lost, it is trust (Amanah). One may be appointed a trustee of an orphan's property until he grows up, he should carry out his responsibility to the best of his ability because it is amanah which must be discharged. Positions of responsibilities are a trust which must not be abused.
Allah says in the Holy Qur'an: 
──────⊹⊱✫⊰⊹────── Surah Al-Ma'idah
Verse 1 ──────⊹⊱✫⊰⊹──…

HADITH OF THE DAY

عَنْ حُمْرَانَ، رَأَيْتُ عُثْمَانَ ـ رضى الله عنه ـ تَوَضَّأَ، فَأَفْرَغَ عَلَى يَدَيْهِ ثَلاَثًا، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْثَرَ، ثُمَّ غَسَلَ وَجْهَهُ ثَلاَثًا، ثُمَّ غَسَلَ يَدَهُ الْيُمْنَى إِلَى الْمَرْفِقِ ثَلاَثًا، ثُمَّ غَسَلَ يَدَهُ الْيُسْرَى إِلَى الْمَرْفِقِ ثَلاَثًا، ثُمَّ مَسَحَ بِرَأْسِهِ، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَهُ الْيُمْنَى ثَلاَثًا، ثُمَّ الْيُسْرَى ثَلاَثًا، ثُمَّ قَالَ رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم تَوَضَّأَ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا، ثُمَّ قَالَ ‏"‏ مَنْ تَوَضَّأَ وُضُوئِي هَذَا، ثُمَّ يُصَلِّي رَكْعَتَيْنِ، لاَ يُحَدِّثُ نَفْسَهُ فِيهِمَا بِشَىْءٍ، إِلاَّ غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ ‏"‏‏.‏Narrated Humran: I saw `Uthman performing ablution; he washed his hands thrice, rinsed his mouth and then washed his nose, by putting water in it and then blowing it out, and washed his face thrice, and then washed his right forearm up to the elbow thrice, and then the left-forearm up to the elbow thrice, then smeared his head with water, wa…