Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

DAGA ZUCIYATA 01


DAGA ZUCIYATA 01

Da sunan Allah Rabba
Ba wa'azi zan yi muku ba 
Ba nasiha zan yi muku ba 
Ba damunku nake son yi ba 
Zance ne daga zuciyata zan furta. 

Damuwa ta aure ni 
Damuwa ta kama ni
Damuwa ta dame ni 
Damuwa ta kayar da ni 
Na bi duk na dagule a tunanin zuciyata. 

Ban san fa mai ya sa haka ba
Ban san fa mai na yi musu ba
Ban san yaya suke so ba
Ban san ya suke so na yi ba
Ban san menene yasa suke ƙina ba. 

Wai ni ba dogo ne ba
Wai ni ba siriri ba
Wai ni ai ban waye ba
Wai ni ban san komai ba
Wai shin sai yaushe ne za ku bar gaba?

So suke wai in yi kaza 
So suke wai in bar kaza 
So suke in je wuri kaza 
So suke in bar gu kaza 
So suke dai in zamo kamar banza. 

Sun ce min ɓarawon kaza 
Sun ce wai na saci reza 
Sun ce wai ai na yi kaza 
Sun ce wai ai nace kaza
Sun ce wai ni na zamo kamar geza. 

Saboda na ƙi zama wawa 
Saboda na gaza duƙawa
Saboda na gaza dainawa 
Saboda na gaza kasawa 
Saboda na zama wanda ya ƙi lalacewa. 

Shi ya sa basa sona 
Shi ya sa fa suke ƙina 
Shi ya sa suke tsorona 
Shi yasa suke ta guduna 
Shi ya sa suke min hassada a aikina. 

Ko da dai kun cuce ni
Ko da dai kun zalunce ni
Ko da dai kun tauye ni
Ko da dai kun fa tsane ni
Ko da ba kwa son gani na dai gani.

Zan ci gaba...

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR WAƘAR HUM MAR JAAYENGEFassarar Waƙar Hum Mar Jayenge

Waƙa: Hum Mar Jayenge

Fim: Aashiqui 2

Harshe: Hausa 

Shekara: 2013

Sauti: Mithoon, Jeet Ganguly

Rubutawa: Irshad Kamil, Sandeep Nath

Kamfani: T-Series

Rerawa: Arjit Singh & Tulsi Kumar 

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 


• Apni aankhein khaali kar de

Ka goge idanuwanka. 

• Kaash tu meri aankhein bhar de (x2)

Ina ma za ka cika idanuwana (da hawayenka) 

• Mere yaara tere gham agar paayenge

Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 

• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge

Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa. 

• Ho... Mere yaara tere gham agar paayenge

Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 

• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge

Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa. 

• Do yeh saugaat tum, to zamaane ki hum (x2)

Idan har ka bani wannan kyautar, to zan... 

• Har khushi se mukar jaayenge

Ce a'a wa dukkan farincikin duniya. 

• Hum mar jaayenge ho...

Mutuwa zan yi. 

• Hum mar jaayenge ho...

Mutuwa zan yi. 

• Mere yaara tere gham agar paayenge

Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 

• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge

Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa. 

• Tere kaandhe se hi lag ke yaara beete umar saari

Fatan dukkan rayuwata ta ƙare ina kusa da kafaɗunka. 

• Socho kaisi hogi kismat hua yun to phir hamaari

Ka yi tunanin irin sa'ar da zan yi in hakan ya faru. 

• Saare aansoo to hon tere aur aankhein hon hamaari

Fatan duk hawayen su zama naka, idanuwan su zama nawa. 

• Tere dard hamein jo mile pyaar mein (x2)

Da zan samu raɗaɗinka a so. 

• Hum khushi se yun bhar jaayenge...

Da na cika maƙil da farinciki. 

• Hum mar jaayenge ho...

Mutuwa zan yi. 

• Hum mar jaayenge ho...

Mutuwa zan yi. 

• Mere yaara tere gham agar paayenge

Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 

• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge

Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa. 

• Chaahe dukh ho, chaahe sukh ho

Ko damuwa ce ko murna ne. 

• Dil ne tujhko hi pukaara

Zuciyata ke kawai ta ke kira. 

• Tune humko hai banaaya

Ke ce kika samar da ni. 

• Tune humko hai sanwaara

Kin ƙawata ni. 

• Jahaan ko to rab ka hai hamein tera hai sahaara

Ubangiji shi ke tallafawa duniya, ni kuma ke ce ke taimako na. 

• Bas tera saath ho chaahe jo baat ho (x2)

Wanzuwarki kawai na ke buƙata, koma menene.

• Tere kehne se kar jaayenge

Zan aikata in har kika umurce ni. 

• Hum mar jaayenge ho...

Mutuwa zan yi. 

• Hum mar jaayenge ho...

Mutuwa zan yi. 

• Mere yaara tere gham agar paayenge

Abokiyar tarayya ta, idan na samu damuwarki. 

• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge

Na yi rantsuwa a gareki, zan ji ni kamar sabo. 

• Mere yaara tere gham agar paayenge

Abokin tarayya ta, idan na samu damuwarka. 

• Hamein teri hai kasam hum sanwar jaayenge

Na yi rantsuwa a gareka, zan ji ni kamar sabuwa.


ƘARIN HASKE: Lallai Allah shi ne mahaliccin kowa da komai, kuma shi ne wanda ake nufa da buƙata domin shi ne mai biya wa kowa buƙatarsa, ba a neman taimakon kowa sai Allah. Allah ya shiryar da mu. Amin. 

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
Share:

FASSARAR WAƘAR DHOOM MACHALE DHOOMFASSARAR WAƘAR Dhoom MACHALE DHOOM 

Waƙa: Dhoom Machale Dhoom

Fim: Dhoom 3

Harshe: Hausa

Shekara: 2013

Sauti: Pritam

Rubutawa: Sameer Anjaan

Kamfani: YRF Music

Rerawa: Aditi Singh Sharma

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
 
• You Know That Thing Must Be A Hundred Years Old

Kun san wannan abun fa dole zai iya kaiwa tsawon shekaru ɗari. 

Dhoom Dhoom 

• Sar Chadhi Hai Dhoom Dhoom

Haniya ta hau kawunanmu.

• Bekhudi Hai Dhoom Dhoom

Shagali ya samu yin maye. 

• Isme Gum Ho Ja…

Kawai mu ɓace a cikin wannan.

Dhoom Dhoom

• Khalbali Hai Dhoom Dhoom

Hayaniya ta jawo hargitsi. 

• Har Gali Hai Dhoom Dhoom

Shagali na tashi a dukkan tituna. 

• Isme Tu Kho Ja…

Ɓace kawai a cikinsa. 

• Dhoom Nasha Hai, Dhoom Junoon Hai

Hayaniya maye ne, shagali soyayya ce. 

• Dhoom Hai Hulchul, Dhoom Sukoon Hai

Hayaniya na jawo sace-sace, shagali na jawo lumana. 

• Aaj Tu Sab Kuch Bhula Ke Jhoom…

Manta da komai kawai a yi ta rawa. 

• Dhoom Machale…

A tada hayaniya! 

• We Rock It, We Roll It, So Come On You People!

Mu ke yi, mu ke damawa, don haka jama'a mu je! 

 • Dhoom Machale…x6

A tada hayaniya! 

Dhoom…

 • Dhoom Machale…x6

A tada hayaniya! 

Dhoom…

Dhoom Dhoom 

• Jism-O-Jaan Mein Dhoom Dhoom

Akwai shagali a jiki da ruhina. 

• Ho Jahaan Mein Dhoom Dhoom

Fatan a samu shagali a cikin wannan duniyar. 

• Josh Wo Bhar Ja…

A zuba shi yadda ya kamata. 

Dhoom Dhoom 

• Har Zubaan Pe Dhoom Dhoom

Akwai shagali a bakin kowa. 

• Zikr Tera Dhoom Dhoom

Ambatonka ma kaɗai ya isa ya tada hayaniya. 

• Aise Kuch Kar Ja…

Yi wani abu mai kama da haka. 

• Dhoom Sharara, Dhoom Ishara

Hayaniya tartsatsi ce, shagali kuma alama ce. 

• Dhoom Ho Yaara, Dhoom Dobara

Ya aboki, ina ma a ce za'a ƙara samun shagali? 

• Aaja Dil Se Dil Mila Ke Jhoom

Zo mana, ku haɗa zukatanku ku yi rawa. 

• Dhoom Machale…

A tada hayaniya! 

• We Rock It, We Roll It, You Ready To Party

Mu ke yi, mu ke damawa, kun shirya wa bikin? 

 • Dhoom Machale…x6

A tada hayaniya! 

Dhoom…

 • Dhoom Machale…x6

A tada hayaniya! 

• Kar Na Fikar Tu Kal 

Kada ku damu da gobe. 

• Lutf Le Aaj Ka

Ku ji daɗin yau bakin iyawarku.

• Zindagi Hai Bas Do Pal Ki

Rayuwa ba wani tsayi ne da ita ba. 

• Ek Ek Pal Chura

Ku saci kowacce daƙiƙa (domin ku rayu) 

• Jee Bhar Ke Jee Le Jee Le

Rayu yadda zuciya ke so. 

• Gham Dhuen Mein Uda

Sha hayaƙi ya kauda damuwa. 

• Dhoom Macha, Macha, Macha, Macha, Macha, Macha…

Tada hayaniya.

• It’s Time Now For A Big Big Dhoom!

Lokaci ya yi na babbar hayaniya 

• Dhoom Machale…x6

A tada hayaniya! 

Dhoom…

 • Dhoom Machale…x6

A tada hayaniya! 

Dhoom…

ƘARIN HASKE: wato ita kalmar ‘Dhoom’ da su ke ta amfani da ita a cikin wannan waƙa, tana da ma'anoni guda biyu Hayaniya da kuma shagali. Don haka sun yi amfani da duka ma'anonin a cikin wannan waƙa. Nagode

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176

Share:

FASSARAR WAƘAR BOLE CHUDIYAN


FASSARAR WAƘAR BOLE CHUDIYAN 

Waƙa: Bole Chudiyan

Fim: Kabhi Khushi Kabhie Gham...

Harshe: Hausa

Shekara: 2001

Sauti: Jatin Lalit

Rubutawa: Sameer

Kamfani: Sony Music

Rerawa: Kavita K. Subramanium, Alka Yagnik, Amit Kumar, Udit Narayan & Sonu Nigam

Fasaarawa: Jamilu Abdurrahman 


+• Bole chudiyan, bole kangna

Awarwaro na cewa, mundaye na cewa. 

+• Haai main ho gayi teri saajna

Na zamo taka masoyi

+• Tere bin jiyo naiyo lag da main te margaiya

Ba zan iya rayuwa babu kai ba, mutuwa zan yi. 

+• Le jaa le jaa, dil le jaa le jaa

Tafi da zuciyar kawai, tafi da ita. 

+• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa 

Tafi da ita, masoyi tafi da ita kawai. 

-+• Le jaa le jaa, dil le jaa le jaa

Tafi da zuciyar kawai, tafi da ita. 

-+• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa 

Tafi da ita, masoyi tafi da ita kawai. 

Aah aah aah aah, aah aah aah

+• Bole chudiyan, bole kangna

Awarwaro na cewa, mundaye na cewa. 

+• Haai main ho gayi teri saajna

Na zamo taka masoyi

+• Bole chudiyan, bole kangna

Awarwaro na cewa, mundaye na cewa. 

+• Haai main ho gayi teri saajna

Na zamo taka masoyi

+• Tere bin jiyo naiyo lag da main te margaiya

Ba zan iya rayuwa babu kai ba, mutuwa zan yi. 

+• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa 

Tafi da ita, masoyi tafi da ita kawai. 

+• Dil le jaa le jaa, ho

Ka tafi da zuciyata. 

-• Bole chudiyan, bole kangna

Mundaye da awarwaronki na cewa. 

-• Haai main ho gaya tera saajna

Na zamo naki masoyiya. 

-• Tere bin jiyo naiyo lag da main te margaiya

Ba zan iya rayuwa babu kai ba, mutuwa zan yi. 

-• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa

Tafi da zuciyata, masoyiya tafi da ita kawai. 

-• Dil le jaa le jaa, ho

Tafi da zuciyata kawai. 

+• Haai haai main marjaawa marjaawa tere bin

Zan mutu, mutuwa zan yi in babu kai. 

+• Ab to meri raatein kat ti taare gin gin

Yanzu ina tafiyar da dararena ne ta hanyar ƙirga taurari. 

+• Bas tujhko pukaara kare, meri bindiya ishaara kare

Ni kaɗai ke kiran ka, ɗigon goshi na zai maka alama. 

-• Hoye, lashkaara lashkaara teri bindiya ka lashkaara

Wannan ƙyallin na ɗigon goshinki 

-• Aise chamke jaise chamke chaand ke paas sitaara

Ya na sheƙi kamar tauraro a kusa da wata. 

Oh oh, oh oh oh, oh oh oh oh oh

+• Meri paayal bulaaye tujhe, jo roothe manaaye tujhe

Awarwaron ƙafata suna kiranka, za su kawar da damuwarka. 

+• O sajan ji, haan sajan ji

Ya masoyina, Eh Masoyina. 

+• Kuch socho, kuch samjho meri baat ko

Ka ɗan yi tunani kaɗan ka fahimci zancena. 

-• Bole chudiyan, bole kangna

Mundaye da awarwaronki na cewa. 

-• Haai main ho gaya tera saajna

Na zamo naki masoyiya. 

-• Tere bin jiyo naiyo lag da main te margaiya

Ba zan iya rayuwa babu kai ba, mutuwa zan yi. 

-• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa

Tafi da zuciyata, masoyiya tafi da ita kawai. 

-• Dil le jaa le jaa, ho

Tafi da zuciyata kawai. 

+• Apni maang suhaagan ho

Fatan tsagun gashin kaina a koda yaushe zai kasance da kalar shi. 

+• Sang hameshaa saajan ho

Fatan masoyina ya kasance tare da ni har abada. 

+• Aake meri duniya mein vaapas na jaana

Yanzu tun da ka shigo cikin duniyata, kada ka taɓa barin ta. 

+• Sehra baandhke maahi tu mere ghar aana

Ka shigo gidana sanye da Sehra 

-• Oye soni kitti soni aaj tu lagdi ve

Kai amma fa kin yi kyau yau. 

-• Bas mere saath yeh jodi teri sajdi ve

Da ace ni abokin tarayyar ki ne, to da haɗuwar tamu ta yi daidai. 

-• Roop aisa suhaana tera, chaand bhi hai deewana tera

Kyawunki sai ƙyalli ya ke yi har ma sa wata hauka ya ke yi. 

+• Jaa re jaa oh jhoothe teri galla hum na maane

Ci gaba, maƙaryaci, ba zan yarda da kurantawarka ba. 

+• Kyoon taarife karta hai tu humko sab kuch jaane

Ka da ka zuzuta, kana ɓata rawarka da tsalle ne fa. 

Ho, oh oh oh, oh oh oh oh oh, ho oh oh oh oh

-• Mere dil ki duaa yeh kahe, teri jodi salaamat rahe

Zuciyata na addu'ar wannan haɗin yayi albarka. 

+• O sajan ji, haan sajan ji

Wayyo masoyina, Eh masoyina. 

+• Yunhi beete saara jeevan saath mein

Fatan rayuwar mu ta ci gaba da wanzuwa har abada a haka. 

-• Bole chudiyan, bole kangna

Mundaye da awarwaronki na cewa. 

-• Haai main ho gaya tera saajna

Na zamo naki masoyiya.

+• Tere bin jiyo naiyo lag da main te margaiya

Ba zan iya rayuwa babu kai ba, mutuwa zan yi. 

-+• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa

Tafi da zuciyata, masoyiya tafi da ita kawai. 

-+• Dil le jaa le jaa, ho

Tafi da zuciyata kawai. 

-+• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa

Tafi da zuciyata, masoyiya tafi da ita kawai. 

-+• Dil le jaa le jaa, ho

Tafi da zuciyata kawai. 

-• Aaja heeriye

Zo, kyakkywa. 

+• Oh, jaa jaa ranjhna

Jeka, Jeka, yaro ɗan soyayya. 

-• Aaja heeriye

Zo, kyakkywa. 

+• Oh, jaa jaa ranjhna

Jeka, Jeka, yaro ɗan soyayya. 

-• Le jaa le jaa, dil le jaa le jaa

Tafi da zuciyar kawai, tafi da ita. 

-• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa 

Tafi da ita, masoyi tafi da ita kawai

-+• Le jaa le jaa, dil le jaa le jaa

Tafi da zuciyar kawai, tafi da ita. 

-• Le jaa le jaa, soniye le jaa le jaa 

Tafi da ita, masoyi tafi da ita kawai

+• Aa aa aa aa aa aa, kabhi khushi kabhi gham

A lokacin farin ciki ko lokacin baƙin ciki. 

+• Na judaa honge hum, kabhi khushi kabhi gham

Ba za mu rabu ba, ko a lokacin farin ciki ne ko kuma a lokacin baƙin ciki. 

ƘARIN HASKE: 'Sehra' wani mayafi ne mai kama da gyale wanda maza ke yafawa kafin a ɗaura musu aure a al'adance. Shi kuma kalar ja da Mata kan sa a tsagin gashin kansu, alama ce da ke nuna cewa matar tana da aure kuma mijinta na raye. Nagode

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
Share:

FASSARAR WAƘAR CHAORO

Fassarar Waƙar Chaoro (Lori)


Waƙa: Chaoro (Lori)

Fim: Mary Kom

Harshe: Hausa

Shekara: 2014

Sauti: Shashi Suman

Rubutawa: Sandeep Singh

Kamfani: Zee Music Company

Rerawa: Priyanka Chopra

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
 

• Teri Main Balayein Loon

Ina so in kauda dukkan damuwarka. 

• Tujhe Main Duaayein Doon

Ina addu'a a gareka. 

• Tujhko Main, Khushiyon Ke Saaye Doon

Zan samar maka da Inuwa mai cike da farinciki. 

• Khwabon Ko Sajaaye Tu

Fatan za ka ƙawata mafarkai.

• Aankhon Mein Basaaye Tu

Ka kuma wanzar da su a idanuwanka. 

• Tujhko Main, Doon Sab Jo Chaahe Tu…

Zan ba ka dukkan abinda kake so. 

• Saari Raat Ye Pehra Kare

Su tsare ka tsawon dare. 

• Keh Doon Chand Taaron Ko…

Zan faɗa wa rana da wata haka. 

• Chaoro, Chaoro, Icha Paari Chaoro (x2)

Ka girma, ka girma, ɗa na, ka girma. 

• Jaag Jaaye Na Tu, Jaagu Raaton 
Main

Saboda kada ka yi ta tashi cikin dare. 

• Jhoole Jhoola Tu Mere Haathon Mein

Zan yi ta juya ka kamar hannaye na. 

• Teri Chumoon Aankhein Main Baith Sirhaane

Zan sumbaci idanuwanka zaune a kusa da kai.

• Saari Raat Ye Pehra Kare

Su tsare ka tsawon dare. 

• Keh Doon Chand Taaron Ko…

Zan faɗa wa rana da wata haka. 

• Chaoro, Chaoro, Icha Paari Chaoro (x2)

Ka girma, ka girma, ɗa na, ka girma. 

Hmm… Haa… Haa… Hmm… Haa…


•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
 

Share:

FASSARAR WAƘAR AAJ ZID


FASSARAR WAƘAR AAJ ZID 


Waƙa: Aaj Zid

Fim: Aksar 2

Harshe: Hausa 

Shekara: 2017

Sauti: Mithoon

Rubutawa: Sayeed Quadri

Kamfani: T-Series

Rerawa: Arijit Singh

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 


• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil (x2)

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

• Karna Hai Bas Tujhe Haasil

Ke kawai ta ke so ta samu. 

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

• Ho... Mujh Mein Tu Ho Bhi Ja Shaamil

Ki zo ki haɗa kai da ni. 

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

Hoo Ooo… Hoo Ooo….

• Kahin Khudko Mujh Main Tu Chhodh Jaa, Chhodh Jaa

Ki bar min kanki a wani wuri.

• Tere Saath Mujhko Tu, Jod Jaa Jod Jaa

Ki ki kasance tare da ni. 

• Ye Jo Kaanch Ke Jaisi Ek Deewar Hai

Wannan gilashin ya zama shinge a tsakaninmu. 

• Meri Baahon Mein Usse Tod Jaa Tod Ja

Zo ki rungume ni ki fasa shi. 

• Yeh Jo Ek Adhurapan Hai

Rashin cikar da ya wanzu.

• Ek Doosre Se Bhar De

Ki yaye shi da wanzuwarki. 

• Jise Umr Bhar Na Bhule

Waɗannan da zan iya mantawa da su a rayuwata ba. 

• Woh Lamhe Mil Jaaye

Ki bani waɗannan lokutan. 

• Maan Le Mujhe Tere Kaabil

Ki ɗauke ni a matsayin wanda ya cancance ki. 

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

• Ho... Mujh Mein Tu Ho Bhi Ja Shaamil

Ki zo ki haɗa kai da ni. 

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

• Aaj Zid…

Tawaye ta ke yi (yau) 

• Bepanah Tujhpe Fida Hoon

Na yi hauka akan ki babu iyaka (adadi) 

• Bepanah Tujhe Chaahta Hoon

So nake miki babu iyaka/adadi. 

• Bepanah Tujhe Maanta Hoon

Na Aminta da ke ba tare da iyaka ba. 

• Bepanah Bepanah

Babu iyaka, babu iyaka.

• Tu Nasha Tu Khumaar, Tera Junoon Sar Pe Sawaar

Kece na bugu/yi maye akan ki, soyayyar ki tana buga ni. 

• Aaj Tu Khud Ko Mere Yaar, De Pila, De Pila

Ki barni in shanye ki kawai masoyiyata. 

• Mujhe Sirf Teri Lagan Hai, Usse Mil Ke Poora Karde

Begen ki kawai na ke yi, ki tadda ni ki gusar min da wannan sha'awar. 

• Meri Itni Si Hai Khwaahish, Tera Pyar Mil Jaaye

Burina kawai shi ne in samu soyayyar ki. 

• Ban Bhi Ja Tu Meri Manzil

Don Allah ki zamo bigirena. 

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

• Ho... Mujh Mein Tu Ho Bhi Ja Shaamil

Ki zo ki haɗa kai da ni. 

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

Hmm… Ooo… Oo…

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

Hmm… Ooo… Oo…

• Aaj Zid Kar Raha Hai Dil 

Yau zuciyata tawaye ta ke yi. 

• Aaj Zid… Aaj Zid… Aaj Zid…

Tawaye ta ke yi (yau)

ƘARIN HASKE: Mai karatu ko ba a faɗa maka ba dai na san za ka iya fahimtar ɗirkaniyar da ke cikin wannan waƙa, don haka sai in ce Allah ya kiyaye.

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176 

Share:

HANYOYI GYARAN JIKI


(HANYOYIN GYARAN JIKI)

Idan ana Saura wata daya bikinki to ki rage shiga rana idan da halima kidena shiga rana koda yake zaki iya amfanida nikaf domin kiyaye fuskarki idan kuma saura mako biyi (2wek) saiki samu
 kurkum, 
madara
  kwai 
 dilka 
 xuma 
 lemon tsami 
da kuma turaren gaf gaff 
 Ki hada Kurkum da madara da kwai ki shafe duk jikinki dashi ki barshi yayi sa oi hudu (2hours) sai ki samu kyalle me kyau ki samu ruwa ki goge face dinki ahankali saiki shiga wanka da ruwan dumi ba soso ba sabulu, in kin fito saiki hada dilka da lemon tsami da xuma da ruwan zafi ya narke ki shafe duk jikinki da shi sai kiyi turaren gafgaf xuwa mintuna talatin (30minutus) ki shiga wanka da sabulu ba soso, haka xaki dinga yi kullum har sati daya
Wannan shine gyaran jiki na musamman


HASKEN MA AURATA
littafin auwal azare
Share:

RAGE GIRMAN NONO


(RAGE GIRMAN NONO)


to Abinda zaki fara lura dashi shine ya yanayin jikinki yake? sannan yaya nononki yake?
Idan kinada kiba sannan nononki irin Wanda yakeda tsayine to gaskiya akwai wahala ace maganin rage nono yayi miki aiki
Amma nononda yakeda girma koda bashida tsayi amma be kwantaba shi wannan yana iya raguwa da wuri kuma hakan yana kara masa kyau..

Kisamu Ganyen lemun
zaki sai garin Buhuru sudaniya.Ki hada ki dakasu ki dinga shafawa a nonon zai ragu amma ki rage shan madara da kunun aya da yougut Ki dinga soya hanta da kitsen akuya kina ci zasu ragu kuma bazasuyi bacci baHASKEN MA AURATA
littafin auwal azare
Share:

IYA MAGANA DA MIJI


SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

IYA MAGANA DA MIJI

Da yawa daga ciki mata ba sa kula da yadda zasu furtawa mazajensu magana, wata macen idan tana magana da mijinta, to har makota sai sun jiyota don haka sai a kula da yadda zaki yiwa mijinki magana, ki yi masa magana cikin tatausan lafazi ko da kuwa ke ce da gaskiya, domin dai hausawa suna fada cewar, durkusawa wada ba gajiyawa ba ne. 

Saboda haka dole ne ki sani fa yana sama da ke, ba ke ce sama dashi ba, sai ki dage idan kin iya ki cigaba dayi, idan ba ki iya ba ki koya, iya tafiya gaban maigida, iya kallo, iya murmushi duk ire-iren wadannan salon shi ne matan banza ke yi amfani da su wajen kwace zukantan dubban mazaje a waje.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)


Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.
Share:

SHAWARA GA MATAN AURE


SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

Shawara Ga Matan Aure

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta a dakin aure a wannan zamanin da muke ciki yanzu, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba za ta ga wasu ‘yan mata irin ta, sun fi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu ba su samu mijin aure ba.

Don haka zai fi alkairi a gareki ki kudurce a cikin zuciyarki cewa gidan mijinki nan ne wajen neman aljannarki, idan kika bi mijinki sauda kafa to za ki yi samun aljanna cikin sauki, idan kuma kika sabawa mijinki to ki sani za ki hadu da fushin Allah.

Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar muhallinku.
Kuma ki zama ko yaushe a shirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.
Ki kiyaye mugwayen kawaye wanda ba za su rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji su kuwa ba su samu ba dole su yi miki hassada. Don haka sai ki kula da irin sawarwari da za su iya baki.

Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa, musamman ma kawayenki za su so su ji abin da yake faruwa don haka kar ki gaya musu.

Idan kuna da ‘ya’ya to ki kula da su, ki kula da tsaftarsu idan ma ‘ya’yan kishiyarki ne, to ki kula da su kamar yadda za ki kula da ‘ya’yanki.

Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki musamman ma iyayensa da ‘yan uwansa da dukiyarsa domin duka Allah zai tambaye ki.

Matan aure ku sani Aaljannarku yana tafin kafar mazajanku, idan kun yi masu biyayya to za ku samu aljanna cikin sauki. Allah ka sa maza da mata mu yi aiki da wannan shawarwari domin mu gudu tare kuma mu tsira tare.
 
Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.
Share:

ƘARIN HIPS


KARIN HIPS (DUWAWU)

(1) Kisamu dankali na hausa ko na turawa ki dafashi saiki yanyankashi sannan ki dakashi ki zuba acikin nono ko madara peak sannan ki zuba zuma ki gaurayashi sosai kisha zaki iyayinsa sau3 Akowanne sati tabbas wannan hadin har ni ima yana karawa mace

(2) ko kuma ki samu kankana ki yanyankata da gwanda itama ki fereta sai kabewa itama ki yankata kokumba (gurji) shima haka da tumatur ki yanyankashi ki wankeshi duk kiyi markadensu waje daya ki tace ruwan kinasha sau2 a rana
Shima wannan yana kara hips sannan yana karawa mace ni ima...
KARIN HIPS (DUWAWU)


budurwa ko matar aure kike zaki iya jarraba wannan hadin wato Abarba da Ayaba, da Gwanda da Kankana ki markadasu ki tace ruwan sannan ki zuba Zuma da Madara peak ki ajiyeshi inda bazai baciba ki wuni kinasha kuma kowane lokaci zaki iyasha babu adadi amma anaso kisha da safe kafin kici komai


Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe,
ki hada da ganyen Alayahu, ki
zuba Tumatiri da Albasa, ki yi
kwadonsu da kuli ki rika ci shima wanan yana karawa mace hips ...


HASKEN MA AURATA
littafin auwal azare
Share:

FASSARAR WAƘAR AWARI

FASSARAR WAƘAR AWARI 

Waƙa: Awari

Fim: Ek Villain

Harshe: Hausa

Shekara: 2014

Sauti: Rabbi Ahmed, Adnan Dhool (Soch)

Rubutawa: Rabbi Ahmed, Adnan Dhool (Soch)

Kamfani: T-Series 

Rerawa: Adnan Dhool, Momina Mustehsan

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
 

• Teri Baahon Mein Jo Sakoon Tha Mila…

Salamar da na samu a hannayenki. 

• Maine Dhunda Bahut Par… Phir Na Mila...

Na ke ta nema, amma na gaza samunta a ko'ina. 

Aaa… Na Na Na Na Na Na…

• Duniya Chhoona Chaahe Mujhko Yun

Duniya ta na so ta taɓa ni ta yadda.

• Jaise Unki Saari Ki Saari Main

Kai ka ce ni mallakinsu ce. 

• Duniya Dekhe Roop Mera

Duniya kyawuna kawai su ke kallo. 

• Koi Na Jaane Bechari Main...

Ba su san tashin hankalin da nake ciki ba. 

• Haaye Tooti Saari Ki Saari Main

Gaba ɗaya a karye nake. 

• Tere Ishq Mein Hui Aawari… Main...

Na zamo almajira a ƙaunarka. 

• Haaye Tooti Saari Ki Saari Main

Gaba ɗaya a karye nake. 

• Tere Ishq Mein Hui Aawari… Main...

Na zamo almajira a ƙaunarka. 

• Koi Shaam Bulaaye

Wasu kan kira ni da yammaci. 

• Koi Daam Lagaaye

Wasu kuma kan ɗaura farashi a kaina. 

• Main Bhi Upar Se Hansti…

Na kan yi murmushi a fili . 

• Par Andar Se Haaye…

Amma abin na damuna daga ciki. 

• Kyun Dard Chuppaye Baithi Hai…

Me ya sa ki ke ɓoye damuwarki? 

• Kyun Tu Mujhse Kehti Hai

Me ya sa ki ke faɗa min hakan? 

• Main Toh Khud Hi Bikhra Hua…

Bayan ni kaina a karye nake. 

• Haaye Andar Andar Se Toota Main…

A karye nake daga ciki. 

• Tere Ishq Mein Khud Hi Se Rootha… Main…

Kasantuwana a cikin ƙaunarki, ina fushi da kaina. 

• Haaye Andar Andar Se Toota Main…

A karye nake daga ciki. 

• Tere Ishq Mein Khud Hi Se Rootha… Main…

Kasantuwana a cikin ƙaunarki, ina fushi da kaina. 

• Main Jee Bharke Ro Loon

Barni in yi kuka ma'ishi. 

• Teri Baahon Mein So Loon

Bari na yi a hannuwanki. 

• Aa Phir Se Mujhe Mil

Ki so mu sake haɗuwa. 

• Main Tujhse Yeh Bolun

Bari na faɗa miki wannan. 

• Tu Anmol Thi…

Ke ta daban ce. 

• Pal Pal Bolti Thi…

A da ki kan yi magana koda yaushe. 

• Aisi Chup Tu Laga Ke Gayi

Amma yanzu kin yi shiru. 

• Saari Khushiyaan Kha Ke Gayi…

Kin tafi da dukkan farincikin. 

• Haaye Andar Andar Se Toota Main…

A karye nake daga ciki. 

• Tere Ishq Mein Khud Hi Se Rootha… Main…

Kasantuwana a cikin ƙaunarki, ina fushi da kaina. 

• Haaye Tooti Saari Ki Saari Main

Gaba ɗaya a karye nake. 

• Tere Ishq Mein Hui Aawari… Main...

Na zamo almajira a ƙaunarka. 

• Par Tere Liye Bazaari Main…

Amma ni ƙwarƙwararka ce. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

CATCH THEM YOUNG


Catch them young!!! 
We always hear this words but we never put the meaning into hands
But today i really got the meaning 
A young girl of 4 years reciting quran off hand without a single mistake really got me astonished 
Same thing goes to azkar is as if the whole citadel is on her head
Did you know when she start all this memorization?
During this lockdown period subhanallah She started from suratu naas now she is in suratu buruuj Ma sha Allah with the help of her elder sister and her mum but what amazed most people is that she doesn't know the alphabet yet she memorized all this by heart
Now a challenge to us 
Let's ponder on this what did our children gain in this lockdown period? What positive change happen to our children this period 
Is it that from morning to night they are always watching television hoping to watch the next cartoon they will play or they are busy going from one friend's house to another playing around?  
Lets plan their time for them because they never know the meaning of it now. Let's catch them young
May Allah make our children a righteous muslim and muslimah
And bless those who seeking for such.
 
Fatimah Ademola 
(Umm Attiyah)
28 june 2020
Share:

SO MANY PEOPLE


SO MANY PEOPLE CAN BE RESPONSIBLE FOR YOUR SUCCESS BUT YOU ARE RESPONSIBLE FOR YOUR FAILURE!

The training you expose and give your mind and body to is what they respond to. 

However, the training of your spirit is of utmost importance. 

Give yourself training through the Spirit by the Word. 

Teach yourself how and what to think. 

Until you come to understand the connection between your outer experiences and your inner thoughts, you will be a victim of life. 

You must focus your mind; discipline and channel your mind in the direction of your purpose. 

Use your tongue to direct your mind. 

You own your mind, your mind doesn't own you. 

You have to change your relationship to your mind. 

Remember that you are the thinker of your thoughts. 

Be the thinker, not the thought. 

The power is with the thinker, not the thought. Be the one to give your thoughts what to dwell upon.
Share:

BUDURCI

BUDURCI

Wannan kalmar bata barin yan mata hankalinsu ya kwanta koda kuwa Mace tanada tabbacin bata taba aikata wani abu Wanda zai rabata da budurcintaba
Yan mata an dade ana tsoratasu da wannan kalmar harma wasu suna ganin raina musu hankali akeyi domin kowa da irin bayaninda zaiyi akan yanda budurcin mace yake

Shidai budurci ajikin mace masana ilimin jima i sun kasashi gida hudu

(1) kashi na farko sunce fatarda take tsakiyar farjin mace wacce ta toshe kofar farjin itace take fashewa kuma tana fashewane ta hanyoyi da yawa musamman kamar saduwa da namiji ko bude kafa ko hawa wani abu ko gudu da dai sauransu amma kuma dolene idan ta fashe aga jini

(2) wasu kuma sukace budurcin mace wani ruwane me kamada na ni ima kuma kowacce mace tana dashi yana zuwane alokacinda ta fara saduwa da namiji kuma namiji zaiji wani irin dadi saboda duk jikin mace wannan ruwan yafi komai dadi amma ita kuma zafi takeji lokacinda yake fita kuma ruwan farine amma akwai alamar jini ajikinsa to wannan shine ruwan budurci kuma kowacce mace sau daya yake fita to ta wannan hanyar ake ganewa mace ta taba saduwa da wani

(3) wadannan kuma sukace budurcin mace yar wata karamar tsokace a saman farji Wanda kuma don an saka yatsa ko azzakarin namiji baya fashewa saidai idan haifuwa tayi abinda suke nufi anan duk abinda shiga yayi ba fitaba baya fasashi duk dadewar mace tana saduwa da namiji matukar bata haifuba to yana nan amma daga ta haifu zai fashe kofar ta bude dole sai anyi yan dabaru zai koma

(4) na hudu kuma cewa sukayi sun yarda budurcin mace yar.fatace a tsakiyar farji amma saduwa da ita baya fasa matashi saboda shi kansa saduwa da mace kala ukune
(1)Akwai Wanda za a sadu da ita tana budurwa ta balaga kuma tanaso to wannan budurcinta baya fashewa saboda sha awarta ta motsa kuma idan mace Sha awarta ta motsa ruwa yana taruwa a farjinta kuma yana budewa sannan fatar budurcin tana dagawa
(2)Akwai kuma Wanda za ayi bataso ma ana da karfi za ayi mata to wannan shi zai iya fasa budurcin saboda Sha awarta bata motsaba 
(3) sai kuma Wanda za ayi mace tana karama wannan bata balagaba shima budurcin yana fashewa koda kuwa tanaso akayi ko bataso..

YAYA MACE ZATAYI MATSI IDAN TA RASA BUDURCINTA?

ga yanda zakiyi Ki daka Garin zogale ki tankadeshi

Kisamu man kadanya (ana samu awajen masu islamic medicine)

Kisamu man zogale (ana samu awajen masu Islamic cemest)

Kisamu Qwaro shine Wanda ake tawada dashin kuma ana wanke hula dashi (ana samunsa awajen masu kayan bakar koli)

Kisamu man shanu (ana samunsa awajen masu sayarda nono)

Duk ki hadasu waje daya ki kwabasu suyi kamar sa o i5 wato 5hours zakiga sun hade sai kiyi matsi dashi kuma zaki iya rabashi kashi3 wato kiyi matsi dashi sau uku acikin sati biyu

To abin tambaya anan tayaya budurwa zata gane ta rasa budurcinta kuma tanada tabbacin bata taba saduwa da namijiba?

1 Lokcinda kika tsuguna toilet ko mummunan zama zakiji iska tana shigarki
2 Zaki saka yatsarki daya ko biyu su shige 
wadannan sune manyan hanyoyin ganewa akwai kananan hanyoyi masu yawa wanda babu hikimar fadarsu

HASKEN MA AURATA
littafin auwal azare

Share:

AUREN BAREWA DA MUTUM


 

Auren Barewa da Mutum

Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wata barewa da ta rikiɗe da zama mace mai kyawun gaske; son-kowa ƙin-wanda ya rasa. Wata rana sai ta ɗauki akushinta (kwatashi) ta kai shi tsakiyar karofi ta ajiye. Sai ta ce da mutanen da ke wurin, “duk wanda ya ɗauki tsakuwa, ya jefa ta daga nan (ta tsaya a daidai wani guri), ta buɗe wannan akushi, to shi zai zama mijina”.

Da mutane suka ji haka, sai suka yi ta jefa tsakuwa. Wannan ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa bai buɗe, sai can daga ƙarshe aka samu wani ya yi sa’a ya jefa, akushin ya buɗe.

Sai wannan barewa ta ce, “yawwa, yanzu na samu miji”. Saboda haka sai suka rankaya tare da wannan mutum zuwa garinsu dan a ɗaura musu aure da wannan mutum. Bayan an ɗaura aure, sai ta tare a gidan mijinta.

Duk sanda ranar girkinta ta zagayo, akan tura ta gonad an ciro kuvewar miya. Idan ta je gonar sai ta yi birgima a ƙasa, ta rikiɗe ta koma barewa, ta kira ‘yan’uwanta ta hanyar rera waƙa kamar haka:

Cinkalkalkal, cinkalin kalaya
Turmin ‘yankale ya yi furen ceɗiya
Tudu na korar tudu da ƙaho
Ban da kwatsa-kwatsa
Ban da ƙanana.

Idan ‘yan’uwanta suka ji haka sai su fito, su zo su taru, su cinye kuɓewar da take gonar. Sai su yi bankwana da ita su koma gida. Ita kuma sai ta yi birgima ta koma mutum, ta ɗauki zanenta ta ɗaura, ta koma gida tana cewa, “ai dama da gangan aka tura ni ciro kuvewar nan, gashi nan na je ban samo komai ba”.

Da mijin nata ya ga haka, wata rana sai ya bi bayanta bata sani ba. Da isarsa gona sai yaga tana birgima. Bayan ta gama birgima sai ya ga ta koma barewa. Daga nan kuma sai ya ji tana waƙa, bayan gama waƙartata, sai ya ga bareyi sun fito suna cin kuɓewar da take gonar. Shi kuma da ya ga haka sai ya fasa su. A lokacin da yake fasa su, ya ga matar tasa ita ma ta gan shi. Daga nan sai ya dawo gida.

Da barewar nan ta ga abin da ya faru, sai ta yi wuf, ta yi birgima ta koma mutum ta ɗebi kuɓewa ta nufi gidan mijin nata. Da isar ta gida sai mijin ya ce:

Miji: “Wacece wannan?”
Barewa: “ni ce”.
Miji: “ina za ki?”
Barewa: “ɗaki”.
Miji: “a’a, koma daji”.
Barewa: “na ƙi”.

Daga nan sai ya ɗauki sanda ya bita da gudu, ya kora ta daji. Tun daga wannan lokaci bata sake koma masa gida ba.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

 
Share:

RASHIN SHA'AWA


RASHIN SHA'AWA

akwai matanda basayin sha'awa ko basa jin dadin saduwa ko ni'imarsu ta dauke, to yanda za'a magance wannan matsala shine sai kisamu

zangarniyar zogale,da ya'yanta gadaya
karanfani
citta
masoro
kinba
sai ki dakesu guri daya su zama gari,sai ki rinka shan wannan hadi a shayi safe da yamma,ki gwada ki gani, yana kara dadin da mai gida zai gamsu sannan kuma zaki rinka cin dabino(ajuwa) mai kyau tare da kwakwa zaki sha mamaki.

👆🏽👏🏽masu wannan matsalar saikuyi, 
Sirri na 4
Share:

GIDA NAGARI

SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

Gida Na Gari

* Kaunar juna a tsakanin ma'aurata.

* Wasa a tsakanin ma'aurata don debe ma juna kewa.

* Masu ilmantar da yayansu ga abubuwa kamar su; Addini, zamantakewa, girmama nagaba, hakuri da juna, gudun haramun, gudun abin duniya da sauransu.

* Masu lura da matsalan dayan su.

* Ware lokaci don tattauna al'amura kamar su; addini, waye da sauransu.

* Tausayawa a tsakanin ma'aurata idan daya na cikin damuwa.

* Karban laifi idan daya yayi wa daya laifi.

* Neman afuwa a tsakanin ma'aurata.

Wabillahi Taufia.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.

Share:

TSAFTAR JIKINKI


SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

TSAFTAR JIKINKI

Ya kamata akalla mace ta yi wanka sau biyu a rana, ta sauya kaya sau biyu, kadaki ce zaki saka kaya har su kwana biyu a jikinki, ki kula da tsaftace bakinki, da akwai wasu wurare da suka kasance matattarar datti ne a jikin yan ya mace, kwauri, hammata,cibiya,kasar mama,(nono), tsakanin cinyoyi.

Don haka dole sai mace ta kula da tsaftace wadannan guraren, rashin kula da su yana haddasa warin jiki, yin askin gashin hammata da mara a duk bayan wani dan lokaci shi ne maganin warin.

Tsaftar yaranki, ki kula datsaftar jikinsu da ta kayansu, ki tabbatar kin yi musu wanka kafin babansu ya dawo, ki samu wankakku kaya ki saka musu, hakan zai sanya mijinki ya ji dadi a zuciyarshi, ke kuma ki kara samun matsayi a gurinsa.

Ta bangaren sanya kaya kuwa idan muka koma ta wannan bangaren akwai kalar kayan da ya kamata ta sanya daddare.

Saboda da rana akwai yawan zirga zirgar jama'a zaki iya amfani da kaya wadanda ba zasu nuna tsiraicinki ba sosai ba, amma da dare ya yi ana so ki sanya kaya wadanda suke masu bayyanar da surorin jikinki ne, domin kuwa kada ki dauki I zumbuleliyar riga mai kama da ta sanyi ki saka, ki ga ko idan har kika yi haka babu abin da zai hana idan maigida ya shigo ya kalle ki ya yi tsaki.

Saboada haka sai ki yi kokari ki zama mace ta gari wadda idan mijinta ya kalle ta sai ya ji ranshi ya yi masa fari, ko kuma idan yana cikin bacin rai da ya kalleki ya ji duj wani kunci da yake cikin ranshi an tafiyar masa dashi.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)


Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.
Share:

GIZO DA BOTORAMI


Gizo da Botorami
Ga ta nan ga ta nan ku.

Ta zo mu ji ta.

 Gizo ne da Botorami. Sai ran nan Botorami zai yi tafiya, sai ya ce, “To Gizo, tsaya - ga amfanin gonata nan, zan yi tafiya ƙauye. Ga shin nan amana duk abin da ya yi ka kwashe mini ka kai mini gari”. Sai Gizo ya ce, To, “sai ka dawo”, daman da Botorami sai ya tafi sai ya ce, Shi ke nan, sai Gizo ya noma gonar sa amfanin gonar yayi kyau. Shi kuma Botorami hatsinsa bai yi kyau ba ya fara lalacewa. Sai Gizo ya yanke masa ya je ya ajiye. Wadanda suka danyi kyau ya saka su a saman damin marasa kyau kuma ya saka a kasa. Haka ya samu audugarsa ma duk bat yi ba, sai ya sa ta. Wacce ta isa ya yayyaɗa a sama ya ɗaure. Gero haka, dawa haka, maiwa haka, duk dai. Shi ke nan sai ya kai rumbu sai ya ajiye. Gizo kuma nasa ya yi shar-shar, ya yi kore shar abin sha’awa. Sai ya kai rumbu sai ya ajiye. Sai ran nan Botorami ya dawo. Sai ya ce da Gizo. Au! Har ka gyara kayan amfanin gonar. Sai ya ce, eh. Sai ya ce, To shi ke nan. Sai Botorami sai ya je ya ga ta sama mai kyau. Sai ya ce, ìTo na ga amfanin gona, na gode, na gode, madalla, madalla. Sai ya ce, ìTo shi ke nan.íí Sai ran ran gidan Botorami zaía yi girki. Da ya je ya buɗe dawa sai ya ga duk ba ta yi ba, ta sama ce ta yi kyau. Ya buɗe gero haka, ya buɗe dawa haka, ya buɗe gyaɗa haka. Sai ran sa ya baci bai ji dadi ba.         

  Sai ya ɗebe mai kyan, marar kyan sai ya bar ta a rumbu sai ya bunka wa runbun wuta. Shi ke nan sai ya je ya fara kuka, ya ce, Lailaha illallahu, Gizo ba ka san abin da ya same ni ba.

 Sai ya ce, Ban sani ba. Ya ce, To duk kayan nan nawa mai kyau duk sun ƙone, na yi gobara. Sai ya ce, To shi ke nan, Allah ya kiyaye, Allah ya tsayar nan. Da safiya ta yi sai ya ce, To, a je a duba amfanin daya kone. Sai ya ce, To shi ke nan. Dama kuma Botorami ya zuba kuɗi a cikin rumbun daya kone. A tona, sai kuɗi. A tona, sai kuɗi, a tona, sai kuɗi. Sai Gizo ma sai ya ce, To ni ma bara na ƙone nawa ko ni ma zan samu kuɗi. Duk sai ya ƙone nasa mai kyan, da ya ƙone nasa mai kyan, sai ya je ya sa wa Botorami kuka. Ya ce, Ni ma na yi irin taka. Sai Botorami ya ce, To Allah ya kiyaye. Ya ce, To sai a je a duba amfanin gona. Shi ke nan, aka je aka dudduba duk ba a samu kuɗi ba sai toka. Sai Gizo ya sa kuka.

Kurunkus kan dan bera  

 
Share:

ABIN FA NA YI NE


ABIN FA NA YI NE


Oh yanzu ace kafin ƙiftawa da bismillah sai caccakar mutum ake yi daga kowane ɓangare?

Ashe za a iya yiwa mutum irin wannan bore haka kamar bai taɓa aikin kirki ba?

Ashe za a wayi gari mutumin da indiyawa suka fi so shi kuma za a koma a fi tsana?

Oh! Jama'a kun taɓa jin an rera wa wani jarumi a Bollywood waƙar tsinuwa da zagi?

Wai yanzu kenan ba shi da damar yin magana sai a lauya ta ko?

Yanzu hawa online ma fa zuluminsa yake yi ko?

A'aha, to amma wai na ji masu wani shirinsa ma na cewa za su canja shi, to me yayi zafi?

Yanzu in bincike ya nuna ba shi da laifi me zai faru?

In kuma ta tabbata yana da laifin me zai faru?

Shin in har jarumi babba irin wannan zai iya aikata zargin kenan me Bollywood take so ta zama?

In kuma matsalar a wajen Bollywood take amma aka liƙa mata fa?

To ku yanzu masoyansa in aka gano yana da laifi ya za ku yi?

Da fa za a gano cewa ba shi da laifi sai ku yi ta kuri cika baki ko?

Ta yiwu ma har shagali za ku yi ko?

Hmmmmm wannan abu dai akwai jimirɗa.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

BANZA TA KORI WOFI


Banza Ta Kori Wofi

Wani saurayi ne da gidansu ke kusa da makabarta, kullum idan ya hawo mota ko babur baya biya, ana zuwa daidai makabartar nan sai ya ce a sauke shi, ana sauke shi sai ya nuna ai shima mataccene, fatalwa ya yi ya fito yawon shakatawa, kawai sai ya shige makabartar.

Ana cikin haka ne wata rana ya hawo babur din wani dan achaba me shegen naci, bayan sun zo daidai makabartar sai saurayin nan yace, “Tsaya na sauka anan” yana sauka sai yai kokarin shiga makabarta kamar yadda ya saba, amma sai Dan achaba ya rike shi ya ce ya ba shi kudinsa, to anan ne saurayin nan ya ce da shi shi fa fatalw ne ba me rai bane kuma gida ya kawoshi (wato makabarta).

Nan take Dan achaba ya ce to su shiga ya ba shi kudinsa. Haka kuwa aka yi, suna shiga abokin namu ya je kan wani kabari yace, “Danlami bani naira tamanin (#80) na ba wa wannan Dan achaban kudinsa”, ai kafin ya gama rufe baki kawai sai suka ga wani hannu ya bullo da naira dari (#100) yace, “Karbi wannan ka ba shi, ya ba mu chanji, ni ma ragowar kudina ke nan.”

Ai da Saurayin nan da Dan achaba sai kowa ya cika rigarsa da iska yayi takansa. Ashe wani Mahaukaci ne yazo ya kwanta a ciki, banza ta kori wofi ke nan.

A ganinku, tsakanin saurayin da Dan achaba wa zai fi wani gudu?
Share:

SHARHIN FIM ƊIN BLACK PANTHER


SHARHIN FIM ƊIN BLACK PANTHER 

Black Panther fim ɗin jarumta ne da aka fitar a shekara ta 2018 a ƙasar Amurka, kuma labarin ya samo asali ne daga Litattafan almara na Marvel Comics. Black Panther shi ne fim na goma sha takwas daga cikin jerangiyar fina-finan duniyar Marvel wato (MCU). 

An sanar da tabbacin yin fim ɗin Black Panther a watan Oktoba na2014, yayin da daga baya Chadwick Boseman ya fito da wannan matsayi a cikin shirin Captain America: Civil War. 
Black Panther shi ne fim na farko da kamfanin Marvel suka yi wanda mafi yawancin mutanen cikinsa baƙaƙen fata ne. An fara ɗaukar wannan shiri ne a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun shekara ta 2017 a EUE/Screen Gems Studios da ke Atlanta da kuma Busan, South Korea.

An saki shirin Black Panther a birnin Los Angeles a ranar 29 ga watan Janairu 2018, yayin da kuma aka sake shi a ko'ina cikin ƙasar Amurka a ranar 16 ga watan Fabrairu na wannan shekara a matsayin ɗaya daga cikin fage na uku daga cikin fagagen fina-finan kamfanin Marvel. Fim ɗin ya samu yabo sosai daga masu sharhi musamman ga mai bada umurni, 'yan wasan, kayan sawa, na'urorin da aka yi amfani da su da dai sauransu. Mutane da dama sun yarda cewa wannan shiri yana ɗaya daga cikin fina-finan kamfanin Marvel mafi kyau, har ma an sanar da cewa yana daga cikin fina-finai goma da suka fi kowanne kyau a duniya a cikin shekara ta 2018. Haka kuma fim ɗin ya kawo kuɗi sama da dala biliyan uku a harkar kasuwancinsa na duniya baki ɗaya tare da kafa tarihi iri daban-daban a box-office ciki kuwa har da zama da yayi fim ɗin da baƙar fata ya bada umurni da yafi kowanne kawo kuɗi a duniya. Haka kuma shirin ya zamo shi ne shi ne shiri na tara da yafi kowanne kawo kuɗi a duniya baki ɗaya, shiri na uku da yafi kowanne kawo kuɗi a Amurka da Canada, kuma shiri na biyu da yafi kowanne kawo kuɗi a 2018 gaba ɗaya. 

Shin ya samu lambobin yabo da kuma damar shiga gasanni da dama, cikinsu har da Best Picture, Best Costume Design, Best Original Score , da kuma Production Design. Black Panther shi ne fim ɗin jarumta na farko da ya fara samun shiga gurbin gasar Best Picture, kuma shi ne fim ɗin MCU na farko da ya fara lashe gasar Academy Award. 

MA'AIKATAN SHIRIN 

• Bada umurni - Ryan Coogler
• Ɗaukar nauyi - Kevin Feige
• Rubutawa da tsarawa - Ryan Coogler & Joe Robert Cole
• Asalin labari - daga Black Panther wanda Stan Lee da 
Jack Kirby suka rubuta 
• Sautin Shiri - Ludwig Göransson
• Horas da 'yan wasa - Rachel Morrison
• Tacewa - Michael P. Shawver & 
Debbie Berman
• Kamfanin da ya shirya - Marvel Studios
• kamfanin da ya yaɗa - Walt Disney Studios
Motion Pictures
• Ranar Fita - 29, January 2018 ( Dolby Theatre )
February 16, 2018 (United States)
• tsawon Shiri - mintuna 134 
• Ƙasa - United States
• Harshe - English
• Kasafi - $200 million 
• kasuwancin Box-office $1.347 billion

LABARIN SHIRIN 

Dubunnan shekaru da suka gabata, wasu ƙabilu guda biyar a yankin Afirka sun kasance suna yaƙar junansu akan wani dutse mai daraja da faɗo daga sama wanda yake ɗauke da sinadarin Vibranium. Ɗaya daga cikin mayaƙan sai ya sha wani tsuro mai siffar zuciya wanda Wannan sinadarin ƙarfe ya taɓa. Hakan ne yasa ya samu gagarumin ƙarfi, daga nan ne ya zama Black Panther na farko. Wannan jarumi ya haɗa kan dukkan sauran ƙabilun baki ɗaya inda suka kafa ƙasar Wakanda, amma ƙabilar Jabari sai suka yi tawaye suka koma rayuwa a cikin tsaunuka. Kwanci tashi sai mutanen Wakanda suka dinga amfani da sinadarin Vibranium wajen ƙere-ƙere na gaban kwatance, amma sai suka ɓoye kansu a matsayin ƙasa mai ƙaramin ƙarfi wacce yanzu take tasowa. 


 A shekara ta 1992, sarkin Wakanda na wancan lokacin wato sarki T'Chaka ya ziyarci ɗan uwansa me suna N'Jobu wanda yake yi musu leƙen asiri a Oakland, California. T'Chaka sai ya zargi N'Jobu da laifin yin harƙallar makamai da wani mai harkar makamai me suna Ulysses Klaue ta hanyar nuna masa yadda zai yi ya saci Vibranium daga Wakanda. Abokin harƙallar N'Jobu sai ya bayyana cewa sunan shi Zuri, kuma shima ɗan leƙen asirin Wakanda ne, kuma ya tabbatar wa da T'Chaka zargin da yake yi gaskiya ne. 

A yanzu kuma, bayan mutuwar sarki T'Chaka, ɗansa wato T'Challa sai ya dawo Wakanda domin ya hau karagar mulki. Shi da Okoye, wacce ita ce shugabar masu tsaron sarki da ake kira da Dora Milaje sai suka ɗauko tsohuwar budurwar T'Challa me suna Nakia daga wani aikin sirri da ta je yi a dajin sambisa. 

Da aka zo bikin naɗin sarautar, sai shugaban ƙabilar Jabari da ake kira da M'Baku ya ƙalubalanci T'Challa da su gwabza domin neman karagar. T'Challa yayi nasara akan M'Baku kuma ya shawarce shi da ya miƙa wuya a maimakon ya kashe shi. 

Sanda Klaue da abokin aikinsa Erik Stevens suka saci wani kayan tarihi da ya fito daga Wakanda a London, sai abokin T'Challa kuma saurayin Okoye wato W'Kabi ya roƙe shi da ya dawo da Klaue a raye. Daga nan sai T'Challa, Okoye, da Nakia suka tafi Busan , South Korea, domin a can ne Klaue ya shirya siyarwa da jami'in hukumar CIA Everett K. Ross wannan sinadari na Vibranium. Anan ne faɗa ya ɓarke har dai T'Challa ya kama Klaue, inda da ƙyar ya barshi a hannun Ross domin ya bincike shi. Klaue sai ya faɗa wa Ross cewa yadda ake tunanin Wakanda a duniya fa ba haka take ba. Ana cikin haka ne sai ga Erik ya zo tare da abokansa inda suka ƙwace Klaue yayin da shi kuma Ross ya samu mummunan rauni wajen taimakon Nakia. Maimakon ya bi Klaue, sai T'Challa ya ɗauki Ross ya tafi da shi Wakanda, domin a can suna da fasahar da za su iya ceto ransa da ita. 

Yayinda Shuri ke ƙoƙarin warkar da Ross, T'Challa sai ya tunkari Zuri dangane da N'Jobu. Zuri sai ya bayyana mishi cewa N'Jobu ya shirya raba raba kayan ƙere-ƙeren Wakanda ne tare da sauran baƙaƙen fata na duniya domin ya taimaka musu su yaƙi masu yaƙarsu. Yayin da sarki T'Chaka ya kama N'Jobu, sai ya yi yunƙurin hallaka Zuri wanda hakan yasa T'Chaka ya kashe shi. T'Chaka shi ne ya umurci Zuri da ya yi ƙaryar cewa N'Jobu ya ɓace, kuma ya bar ɗansa domin hakan shi zai tabbatar da ƙaryar. Wannan yaro shi ne ya girma ya zama Soja Stevens a ƙasar Amurka wanda ya ɗauki inkiyar "Killmonger" a matsayin sunansa. 

Ana cikin haka ne kuma, sai Killmonger ya kashe Klaue ya kuma tafi da gawarsa Wakanda. Bayan an kawo shi gaban tsofaffin birnin, sai ya bayyana asalinsa a matsayin N'Jadaka kuma ya buƙaci a bashi damar hawa karagar mulki. Daga nan sai Killmonger ya ƙalubalanci T'Challa da su yi faɗa domin a tantance. To a garin hakane ya kashe Zuri kuma yayi galaba akan T'Challa ya jefa shi cikin ruwa. Bayan Killmonger ya sha ɗan wannan tsiro, sai ya umurce su da su ƙona sauran gaba ɗaya, amma Nakia ta samu damar ɗaukar guda ɗaya kafin su ƙone. Killmonger, tare da goyon bayan W'Kabi tare da mayaƙansa sai suka shirya rarraba makamai zuwa sauran sassan duniya. 

Nakia, Shuri, Ramonda, da Ross sai suka gudu zuwa ga ƙabilar Jabari domin neman mafaka. A can ne suka iske T'Challa a sandare cikin dusar ƙanƙara, ashe sun tsinto shi ne daga ƙasan Kogin da ya faɗa shi ne suka cece shi domin su biya bashin halaccin da ya yi wa M'Baku's life. Bayan Nakia ta bashi wannan ɗan tsuro, sai T'Challa ya warke, kuma ƙarfinsa ya dawo. Don haka sai ya tunkari Killmonger wanda shi ma ya sanya tasa rigar ta Black Panther. W'Kabi tare da mayaƙansa sai suka fara yaƙar Shuri, Nakia, da kuma mayaƙan Dora Milaje, yayin shi kuma Ross ya ke ƙoƙarin kaɓo jiragen da ke ƙoƙarin fita da makaman. M'Baku da mayaƙan Jabari suma sai ga su sun kawo wa T'Challa ɗauki. Yayinda Okoye ta tunkari W'Kabi, sai shi da mayaƙansa suka miƙa wuya. Su kuma T'Challa da Killmonger a ɓangaren nasu faɗan, T'Challa ya samu damar caka masa wuƙa wanda hakan ya yi masa mummunan rauni. Duk da cewa T'Challa ya bashi shawarar ya miƙa wuya ya bari a warkar da shi, Killmonger sai ya ƙi amincewa tare da bayyana cewa ya yarda ya mutu a matsayin mutum mai 'yanci. 

Bayan mutuwarsa, sai T'Challa ya gina gidauniyar taimako a inda N'Jobu ya mutu tare da bayyana Nakia da Shuri a matsayin waɗanda za su tafiyar da wannan wuri. A ƙarshe dai an nuno T'Challa ya bayyana a taron majalisar ɗinkin duniya domin bayyanawa kowa asalin yadda Wakanda take. A wata nunowa ta ƙarshe kuma, an nuno Shuri tana taimakawa Bucky Barnes dangane da jinyar da yake yi. 

JARUMAN SHIRIN 

• Chadwick Boseman - T'Challa / Black Panther 
• Ashton Tyler - T'Challa yana ƙarami 
• Michael B. Jordan - N'Jadaka / Erik "Killmonger" 
• Seth Carr - Erik Yana ƙarami 
• Lupita Nyong'o - Nakia
• Danai Gurira - Okoye 
• Martin Freeman - Everett K. Ross
•Daniel Kaluuya - W'Kabi 
• Letitia Wright - Shuri
• Winston Duke - M'Baku
• Angela Bassett - Ramonda 
• Forest Whitaker - Zuri :
• Andy Serkis - Ulysses Klaue
• John Kani - T'Chaka 
• Florence Kasumba - Ayo 
• Sterling K. Brown - N'Jobu
• Isaach de Bankolé 
• Connie Chiume 
• Dorothy Steel 
• Danny Sapani 
• Sydelle Noel 
• Marija Abney,
• Janeshia Adams-Ginyard
• Maria Hippolyte
• Marie Mouroum
• Jénel Stevens
• Zola Williams
• Christine Hollingsworth
• Shaunette Renée Wilson 
• Sebastian Stan 

NASARORI DA GURBIN GASANNI DA SHIRIN YA SHIGA 

1. American Music Award (won)
 2. BET Awards (winning two)
 3. ONE Billboard Music Award
 4. ONE British Academy Film Award (won)
 5. TWELVE Critics' Choice Movie Awards (winning three)
 6. Golden Globe Awards
 7. EIGHT Grammy Awards (winning two)
 8. SEVEN MTV Movie & TV Awards (winning four)
 9. ONE MTV Video Music Award (won)
10. SIXTEEN NAACP Image Awards (winning ten)
11. FIVE People's Choice Awards (winning two)
12. FOURTEEN Saturn Awards (winning five)
13. TWO Screen Actors Guild Awards (winning both)
14. ELEVEN Teen Choice Awards (winning three)
15. Academy Award for Best Picture
16. Golden Globe Award for Best Motion Picture – Drama

Ana sa ran kashi na biyun wannan shiri zai fita a 2022
Share:

KATRINA KAIF


KATRINA KAIF

Katrina abar ƙauna
Katrina mai daɗin suna
Kyakkywa ce ita Katrina
Kallonki na sanyaya mini raina
Murmushinki na ƙawata raina
Ƙwarewarki ta shanye tunanina
Juriyarki ta haye hashena
Jajircewarki ta ruɗa mafarkaina
Kafiyarki ta sani cikin ƙauna
Wayyo Wayyo Katrina mai kyau abar ƙauna.

Wajen rawa Katrina tana burge kowa
Wajen iya soyayya tana nishaɗantar da kowa
Gashi ta ƙware a dambe da kokawa
Tana da masoya a cikin Indiyawa
Tana da masoya a cikin Larabawa
Tana da masoya a cikin Amurkawa
Tana da masoya a cikin Hausawa
Tana da masoya a cikin Japanawa
Tana da masoya a cikin farisawa
Katrina tana da masoya har ma cikin yarbawa.

Kallon idonta kan sani cikin shauƙi
Kalmanta na da zaƙi
Murmushinta kan sani shiga yanayi
Kai da ganin sifarta ka godewa buwayi 
Dariyarta kan sani jin nishaɗi
Muryarta a koyaushe tana da daɗi 
Wannan mace gaskiya ta ko'ina ta yi 
Duniya ta sanda ke ake yayi 
Maƙiyanki ko da gardama sun yi 
Da sun gane ki sai su koma wasu bayi. 

Ni ne Masoyinki Jamilu Abdurrahman 
Fatan ƙaunarki ko kaɗan za ki sammin 
Ko da ragowa ce na yarda abar min 
Don Allah murmushinki nake so ki ɗan min
Don Allah dariyar ki nake so ki ɗan min 
Don Allah tafiyarki nake so ki ɗan min 
Don Allah ɗan farin nan naki ki yi min 
Ko da murguɗa baki ne ma duk ki yi min 
Ko ma duka ne duka na yarda ki yi min 
Koma menene na yarda ki yi min. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com  
 27 June 2020 
Share:

KHANS OF BOLLYWOOD


Khans of Bollywood ......


Amjad Khan – also director
Arbaaz Khan – Salman Khan's brother, also a director and producer
Ayub Khan – Nasir Khan's son and Dilip Kumar's nephew, also an Indian television actor
Faisal Khan – Aamir Khan's brother
Fardeen Khan – Feroz Khan's son
Feroz Khan – Fardeen Khan's father, also a
film director and producer
Imran Khan – Aamir Khan's nephew
Jayant (actor) – Amjad Khan's father
Kader Khan – Indian-Canadian film actor, comedian, script and dialogue writer, as well as director
Mazhar Khan – Zeenat Amaan's Husband
Mehboob Khan – best known as a director and producer, also writer
Nasir Khan – Dilip Kumar's brother
Nazir Ahmed Khan – director and producer in British India and then Pakistan after
partition of India , brother-in-law of filmmaker
K. Asif
Riyaz Khan – predominantly South Indian actor
Salim Khan – Salman Khan's father, best known as a screenwriter , as part of screenwriting duo Salim-Javed (along with
Javed Akhtar )
Sanjay Khan – Zayed Khan's father, also a director and producer
Shadaab Khan – Amjad Khan's son
Shahbaz Khan – also a television actor
Sohail Khan – Salman Khan's brother, also a director and producer
Tariq Khan – Aamir Khan's cousin, Nasir Hussain's nephew
Zain Khan Durrani – also a model
Zayed Khan – Sanjay Khan's son, also a producer
Zuber Khan – also a television actor
Female actresses
Sharmila Tagore (Ayesha Sultana Khan) – actress, model , Central Board of Film Certification chairperson, mother of Saif Ali Khan
Farah Khan – best known as a dance
choreographer , director and producer
Gauhar Khan – also a model
Jiah Khan – British-American actress who worked in Bollywood
Kareena Kapoor Khan – Saif Ali Khan's wife, Karishma Kapoor's sister, part of Kapoor family , daughter of actor Randhir Kapoor and actress Babita
Krutika Desai Khan – actress working in film, television and theater
Soha Ali Khan – Saif Ali Khan's sister, daughter of actress Sharmila Tagore
Sana Khan – also a model and dancer
Sara Ali Khan – Saif Ali Khan's daughter
Zareen Khan – Bollywood actress who has also appeared in Tamil and Punjabi films
Others
Alvira Khan Agnihotri – film producer and
fashion designer, Salman Khan's sister and Salim Khan's daughter
Gauri Khan – producer, interior designer,
costume designer, Shah Rukh Khan's wife
Kabir Khan – director, screenwriter, cinematographer
Mansoor Khan – director, producer, screenwriter, Nasir Hussain's son, Aamir Khan's cousin
Nasir Hussain (Nasir Hussain Khan) – director, producer, screenwriter, Aamir Khan's uncle
Nikhat Khan – film producer, Aamir Khan's sister
Parvati Khan – Indo-Trinidadian singer and model who worked in Bollywood
Tahir Hussain (Tahir Hussain Khan) – director, producer, Aamir Khan's father
Faraaz Khan - television actor, son of Yusuf Khan.
Share:

POUSE AND PONDER


PAUSE AND PONDER!

How would you talk to your brother if you knew that would be your last time of hearing from him?

How would you treat your sister if you are certain you would never see her again?

What kind of words would you use on your mother or your father if you would be speaking to any of them for the last time in your life?

What would be your last word before you hang the phone finally on a friend if he or she was going to die the next hour?

What's going to be your attitude on that person you call an enemy if his or her life was about to end?

How will you be addressing the world if you were to make your last and final speech today?

What would be the urgent amendment you would make today in your life if this was to be your last opportunity?

What prayers would you be praying if you were to say your last prayers this minute?

Can't you see we would treat one another better, kinder and with more understanding if we should consider these questions more critically?

Can't you see that our world would be a better place to live in if we would be more merciful to one another, less judgemental and more helpful to our neighbors?

Please, let's us all check our selves on a regular basis....

God bless you all


Enjoy the rest of the evening.
Share:

GYARAN GASHI


GYARAN GASHI

abunda ya shafi gyaran gashi kasancewar anasamun mayika masu gyarawa mace gashi shiyasa bamu cika kawowa na Islamic ba amma kasancewar wasu suna bukatar na Islamic insha allahu zamu rinkayi koda atakaicene

 hulba da man kwakwa babu abinda ya kaisu gyaran gashi kusan duk wani sinadarin gyaran gashi idan kayi bincike zaka samu akwai daya daga ciki idan kika samu garin hulba kika hadashi da man kwakwa zaki iya hadawa da man ridi saiki shafa agashinki bayan kamar sa.a daya (1hour) saiki wankeshi anaso kiyi sau biyu ko uku a sati daya kuma kiyi har zuwa wata daya 
wannan zai gyara miki gashi kuma yayi laushi musamman masu fama da karyewar gashi

shikuma man zaitun ana dafashi bayan anyi wanka ana shafawa akayi yana saka gashi yayi baki yayi sheki...


HASKEN MA AURATA
littafin auwal azare
Share:

AALIA BHATT


AALIA BHAT

Kyakkywa Aalia 
Tauraruwa Aalia 
Kina burge ni Aalia 
Mace mai kama da taliya 
Ga kyawun gani Aalia 
Ga murmushin so ga Aalia 
Ga nutsuwa gun Aalia 
Jarumar ƙasar India. 

Shararrun matan duniya 
Masu tashe a wanga duniya 
Tabbas da ke ciki Aalia 
Ga ki dai ƙarama ce Aalia 
Amma da aikin manya Aalia 
Ga farin jini a gun Aalia 
Kin zamo abar so ga duniya 
Wayyo jaruma Aalia. 

Aalia sanyin idaniya 
Mai sanyaya zafin zuciya 
Tauraruwar nahiyar Indiya 
Mai murmushin kaɗa duniya 
Kin zamo madubin soyayya 
Kin zamo wa mata rariya 
Ke ce mai kyawun wuya 
Aalia abar son duniya. 

Jamilu ne ni kin jiya 
Daga nan cikin Nijeriya 
Masoyin kafcen Indiya 
Saboda ke baitukan ga na shirya 
Fatana in wasa Mashahuriya
Fitacciyar Jaruma Aalia 
Mai haskaka ruhi Aalia 
Ina gaisheki gudaliya. 

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176 

26 June 2020

Share:

DEEPIKA PADUKONE

DEEPIKA PADUKONE

Jinjina ga Deepika 'ya a wajen Padukone
Wace kyawunta ke wuta da kanta ta ƙone
Mutum ko da ma shi wanene
Ba shi da zarrar ƙin 'yar Padukone
Ga jarumarata Deepika me kyawun kunne
Sannu sannu Deepika 'yar Padukone.

Kin fi su kyau da kuɗi jarumar mata
Kin fi matsayi su ɗin duka 'yan mata
Kin fi su sa'a da ƙwarewa duka mata
Ke ce fitilarsu Deepika ƙawata
Ke ce kika hasken dukka duhun mata
Sannu Deepika tauraruwar mata.

Kin cinye Indiya kin lashe su gaba ɗaya,
Kin cinye birnin Sin duk ke ɗaya
Kin ci galabar zukatan Amurkawa baki ɗaya
Kin mallake zuciyar mutanen Nijeriya
Ke ce kika karɓe zukatan mutanen Somaliya
A taƙaice dai Deepika ta mamaye duniya.

Fatan alheri da ke da mai gidanki 
Da iyayenki har ma da ƙawayenki 
Cikinsu haɗa duka harda 'yan uwanki 
Ki tuna ciki duka har da abokanki 
Allah yasa watarana mu ga 'ya'yanki 
In muna da rai ma wataƙila da jikokinki. 

Ni ne Jamilu katibin nan na Kaduna 
Me rattabe babu dare ko kuma rana 
Ko da da iska ko ruwa ko zafin rana, 
Na yi miki baituka domin son raina 
Da ƙwarewa a batuna na cikin magana 
Gashi waƙa na rera ta cikin hikima. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI 03


JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI


࿐࿐࿐࿐࿐࿐
FITOWA TA 03
࿐࿐࿐࿐࿐࿐

21. Aarahi hoon - Ga ni nan zuwa (mace)

22. Aaraha hai - Ga mu nan zuwa (maza)

23. Aarahi hai - Ga mu nan zuwa (mata)

24. Ab Rooh Se Juda Na Ho

Ka da ki rabu da ruhina. 

25. Bhool gaya - ya manta 

26. Bhool gayi - ta manta 

27. Aap kaha seh? - Daga ina kake?/kike? 

28. Yeh mera gari hai - wannan mota ta ce.

29. Yeh khon banaugi? - wa ya haɗa wannan? 

30. Woh Dekha - kalli nan 

Zan ci gaba in shaa Allah

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook:
https://m.facebook.com/JamiluWriter/
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Telegram: https://t.me/Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b882118
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com
──────⊹⊱✫⊰⊹────── 
Share:

FASSARAR WAƘAR TERI MERI

FASSARAR WAƘAR TERI MERI 

Waƙa: Teri Meri

Fim: Bodyguard

Harshe: Hausa 

Shekara: 2011

Sauti: Himesh Reshammiya

Rubutawa: Neelesh Misra

Kamfani: T-Series

Rerawa: Shreya Goshal & Rahat Fateh Ali Khan

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

Aa ..

• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil

Naka da nawa, nawa da naka, labarin soyayyar mu tattaura ne. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Ik Ladka, Ik Ladki Ki Yeh Kahani Hai Nayi

Wannan wani sabon labari ne akan Saurayi da budurwa. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil

Naki da nawa, nawa da naki, labarin soyayyar mu tattaura ne. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Ik Dooje Se Hue Judaa, Jab Ik Dooje Ke Liye Bane

A rabe mu ke da juna, duk kuwa da cewa an halicce mu ne domin juna. 

• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil

Naki da nawa, nawa da naki, labarin soyayyar mu tattaura ne. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

Aa ..

• Tumse Dil Jo Lagaya, Toh Jahaan Maine Paaya

Yayinda na baki zuciyata, sai na samu duniya a madadinta. 

• Kabhi Socha Na Tha Yun, Meelon Door Hoga Saaya

Sai dai ban taɓa tunanin cewa ko da inuwar ki za ta nisan mil ba 

• Kyun Khuda Tune Mujhe Aisa Khwaab Dikhaya

Ya Ubangiji! Me ya sa ka bani irin wannan mafarkin? 

• Jab Haqeeqat Mein Usse Todna Tha

Saboda na san tabbas zai faru a zahirance. 

Aa ..

• Ik Dooje Se Hue Judaa, Jab Ik Dooje Ke Liye Bane

A rabe mu ke da juna, duk kuwa da cewa an halicce mu ne domin juna. 

• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil

Naka da nawa, nawa da naka, labarin soyayyar mu tattaura ne. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Teri Meri Baaton Ka Har Lamha Sab Se Anjaana

Babu wani wanda ya san lokacin hirarrakinmu. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Har Ehsaas Mein Tu Hai, Har Ik Yaad Mein Tera Afsaana

Kina cikin kowane yanayi (da na ke ji) kina cikin kowane tunani nawa. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

Aa ..

• Saara Din Bit Jaaye, Saari Raat Jagaaye

Yini gaba ɗayansa ya shuɗe, dare kuma ya barni a farke. 

• Bas Khayal Tumhara, Lamha Lamha Tadpaaye

Tunaninki kaɗai kan tayar min da hankali a koyaushe. 

• Yeh Tadap Keh Rahi Hai Mit Jaaye Faasle

Wannan ƙuncin muradin naki yana so ya ƙare duk wani nisa. 

• Yeh Tere Mere Darmeyaan Hai Jo Saare

Da ya yake tsakanin mu. 

• Ik Dooje Se Hue Judaa, Jab Ik Dooje Ke Liye Bane

A rabe mu ke da juna, duk kuwa da cewa an halicce mu ne domin juna. 

• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil

Naka da nawa, nawa da naka, labarin soyayyar mu tattaura ne. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Har Ehsaas Mein Tu Hai, Har Ik Yaad Mein Tera Afsaana

Ka na cikin kowane yanayi (da na ke ji) ka na cikin kowane tunani nawa. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba. 

• Teri Meri, Meri Teri Prem Kahani Hai Mushkil

Naki da nawa, nawa da naki, labarin soyayyar mu tattaura ne. 

• Do Lafzon Mein Yeh Bayaan Na Ho Paaye

Ba zai yiwu a iya bayyana shi a 'yan layuka ba.

ƘARIN HASKE: Wannan waƙa ce ta soyayya tsantsa wacce ko sautinta kawai mutum ya ji na san zai iya fahimtar hakan. Sai dai kuma ita ma an yi kuskure a cikinta inda ya ke tambayar Allah dalilin da yasa sa ya yi mafarkin da ya yi. Haƙiƙa mun yarda cewa babu wani mahaluƙi da ya isa ya tambayi ko ya tuhumi hukuncin Allah. Muna fata Allah ya yafe mana kura-kuran mu, Aameen. Nagode

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Twitter: @jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Instagram: Jamiluwriter 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Facebook:
https://m.facebook.com/JamiluWriter/
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Tumblr: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman 
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Telegram: https://t.me/Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b882118
──────⊹⊱✫⊰⊹──────
Haimanraees@gmail.com
──────⊹⊱✫⊰⊹────── 

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form