Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

FASSARAR WAƘAR DIL BECHARA (TITLE TRACK)


FASSARAR WAƘAR DIL BECHARA (Title Track)


• Waƙa - Dil Bechara(Title Track)

• Shiri - Dil Bechara 

• Harshe - Hindi = Hausa   

• Shekarar Fita - 2020 

• Sauti - A.R. Rahman

• Rubutawa - Amitabh Bhattacharya

• Kamfani - Sony Music

• Rerawa - A.R. Rahman

• Fassarawa - Jamilu Abdurrahman 


• Dil Bechara

Raunannar zuciyata. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• Dil Bechara

Raunannar zuciyata. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• Koi Toh Bata De Kya Karun

Don Allah wani ya faɗa min abin da ya kamata in yi. 

• Koi Toh Bata De Kya Karun

Don Allah wani ya faɗa min abin da ya kamata in yi. 

• Dil Bechara

Raunannar zuciyata. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• L Mein Joda OVE

Na ƙara haruffan ‘OVE’ ga harafin ‘L’

• Maine Toh Love Love Love Hi Kiya

Ko da yaushe ni masoyinki ne. 

• Usne Joda IKE

Amma sai ta ƙara haruffan ‘IKE’ a gaban nata 'L' ɗin. 

• Mere Ko Like Like Like Hi Kiya

Ita kawai yi na take yi. 

• Dil Bechara

Raunannar zuciyata. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• Oh Baby! Yaad Hai Mujhe

Wayyo bebi! Ko da yaushe na kan tuna 

• Tera Birthday Day Day

Zagayowar ranar haihuwarki 

• Tera Birthday Day Day Day Day

Zagayowar ranar haihuwarki

• Tu Har Saal Mera Birthday

A kowace shekara, Zagayowar ranar haihuwata. 

• Bhul Bhul Bhul Jaaye 

Ki kan manta. 

• Roz Tere Call Ki Main Raah Dekhun

Na kan tsumayi kiranki kullum. 

• Tu Sms Bhi Na Kare

Amma ko saƙon waya ba kya aiko min. 

• Tu Mujhe Miss Bhi Na Kare

Ko kewa ta ms ba kya yi. 

• Kyun... Mujhe Miss Bhi Na Kare

Me ya sa ba kya kewa ta? 

• Kyun...

Me ya sa? 

• Dil Bechara

Raunannar zuciyata. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• Dil Bechara

Raunannar zuciyata. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

• Friend Zone Ka Maara

Ta maƙale a bigiren abota. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

GANTALALLIYA


GANTALALLIYA

Da sunan Allah madaukaki nake waƙar Gantalalliya
Allah Rahmanu, Arrahimu mai ikon duka duniya
Ina roƙonka da ka ba musulmai juriya 
Akan irin waƙi'ar da muke fuskanta a duniya 
Albarkacin baban Fati Muhammadu mai son gaskiya. 

A yau zan yo raddi gurin Kangana Wahalalliya
Jaɓa mai dogon baki Jemammiya
Kin taɓo mu ne don haka dole mu yi miki tirjiya
Kuma kin ɗauko hanya ta ɓata Wahalalliya 
Tabbas yanzu kin tabbata ke ce Wawiya. 

A cikin azamarki na son ganin kin zamo Shahararriya 
Kin zamo kunama wacce bata da sabo ko ɗaya 
Kin ci zarafin kowa kuma kin ɓata rawarki gaba ɗaya 
Hakan yasa ayau ki ka zamo gantalalliya
Baki nan ba ki can ko ina gudunki ake yi Mujiya. 

Allah ga baiwarka ta taɓo Addinin gaskiya 
Idan tana da niyyar tuba ka sa ta samu shiriya 
Idon bata da shi ka sa ta zamo Watsatstsiya 
A bita a layi ko'ina ana ga bushiya 
Kuma cikin gaggawa ka sa ta zamo taɓaɓɓiya. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR BHARAT ANE NENU: THEA SONG OF BHARAT


FASSARAR WAƘAR BHARAT ANE NENU (THE SONG OF BHARAT)


• Waƙa - Bharat Ane Nenu (The Song of Bharat) 

• Shiri - Bharat Ane Nenu

• Shekarar Fita - 2018

• Harshe - Telugu = Hausa 

• Sauti - Devi Sri Prasad

• Rubutawa - Ramajogayya Sastry

• Rerawa - David Simon

• Fassarawa - Jamilu Abdurrahman


• Virachistha nedey navasakam

Zan fara gina sabon zamani daga yau. 

• Ninadistha nithyam janahitham

Zan yi aiki domin jin daɗin jama'a a koda yaushe. 

• Naluperugani sevey abhimatham

Manufar ita ce yi wa jama'a aiki ba tare da cuta ba. 

• Kashtam edaina samatham

Kowane irin tserereniya ta yi min. 

• Bharat ane nenu haami isthunannu

Ni ne Bharat kuma ina mai ba ku kalma ta. 

• Baadhyunnai untanu… Of the people, for the people, by the people prathinidhiga

Zan yi aiki a matsayin wakilin demokuraɗiyya, Mulkin mutane, wa mutane kuma domin mutane. 

• This is me, this is me |2|

Ni ne wannan. 

• Paalinche prabhuvunu kaanani… Sevinche bantunu nenani

Ni ba sarki bane da yake mulki... Ni soja ne da yake hidima. 

• Adhikaaram ardham idi ani…telisela chestha naa pani

Zan yi aiki ta yadda mutane za su fahimci abin da ake nufi da iko. 

• Bharat ane nenu haami isthunannu

Ni ne Bharat kuma ina mai ba ku kalma ta. 

• Baadhyunnai untanu… Of the people, for the people, by the people prathinidhiga

Zan yi aiki a matsayin wakilin demokuraɗiyya, Mulkin mutane, wa mutane kuma domin mutane. 

• This is me, this is me |2|

Ni ne wannan. 

• Maaticchaa nenee pudamiki… Paatisthaa praanam chivariki

Na bada kalma ta wa wannan ƙasar... Zan kuma tsaya akan kalmar tawa har in mutu. 

• Attaduguna nalige kalalaki…Balamivvani padavulu deniki

Menene amfanin waɗannan membobin matuƙar ba za su iya bayyana mafarkan da aka danne ba? 

• Bharat ane nenu haami isthunannu

Ni ne Bharat kuma ina mai ba ku kalma ta. 

• Baadhyunnai untanu… Of the people, for the people, by the people prathinidhiga

Zan yi aiki a matsayin wakilin demokuraɗiyya, Mulkin mutane, wa mutane kuma domin mutane. 

• This is me, this is me |2|

Ni ne wannan. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

MATSAYA TA DANGANE DA JARUMA KANGANA RANAUTMATSAYA TA DANGANE DA KANGANA RANAUT

Izuwa yanzu dai kusan kowa ya samu labarin irin maganar da jaruma Kangana Ranaut ta yi akan jarumi Aamir Khan wanda kuma hakan bai yi wa mutane da dama daɗi ba, ciki kuwa har da ni. Don haka bana buƙatar komawa kan wannan batu. Magana ta gaskiya ita ce, Kangana Ranaut ba Aamir Khan ta taɓa ba, Addinin Musulunci ta taɓa, ni kuwa duk iya yadda na kai da sonka a raina in ka taɓa min addinina to fa sai inda ƙarfina ya ƙare. Don haka, tun da Kangana ta taɓo addinina daga yau babu ni babu ita, babu ruwana da duk wani abu da ya shafeta, sannan kuma daga yau mun ƙulla ƙaƙƙarfan gaba a tsakaninmu da ita wacce ba za ta taɓa gushewa ba har sai ta janye maganarta. A ƙarƙashin haka, ina mata mugun fata, Allah ya tsine wa Kangana albarka, Allah ya tozartata ya kuma wulaƙantata albarkacin annabi da ƙur'ani.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

SHARHIN FIM ƊIN RACHA


SHARHIN FIM ƊIN RACHA

Racha fim ɗin faɗaIndia ne da aka fitar a cikin shekara ta 2012 cikin harshen Telugu. Wannan shi ne shiri na farko da jarumi Telugu Ajmal Ameer yayi a Telugu. 

• Bada Umurni - Sampath Nandi
• Ɗaukar Nauyi - R. B. 
N. V. Prasad
Paras Jain
• Rubutawa - Sampath Nandi
Paruchuri Brothers
• Taken Shiri - Mani Sharma
• Horaswa - Sameer Reddy
• Tacewa - Gautham Raju
• Shiryawa - Megaa Super Good Films
• Ranar Fita - 5 April 2012
• Tsayin shiri - Mintuna 144 
• Ƙasa - India
• Harshe - Telugu 

A lokacin da aka fitar da wannan shiri ya samu yabo sosai. Shirin ya samu shiga guraben gasar Filmfare har guda 4 a bikin gasar na 60 inda ya lashe kyautar ɗaya wato kyautar Best choreography. Haka kuma shirin ya samu shiga guraben gasar 2nd South Indian International Movie Awards har sau biyar, amma bai ci ko ɗaya ba. An fassara wannan shiri zuwa harshen Hausa inda aka sa masa suna Hatsabibi. 


Labarin Shirin.

Raj wani ɗan cacar gasa ne da ke zaune a garin Hyderabad tare da iyayensa na riƙo. Watarana sai mariƙinsa ya kwanta rashin lafiya sakamakon ciwon shan giyar da yake yawan yi ta lalata masa hanta. Raj yana buƙatar kuɗaɗe kimanin ₹20 lakhs domin a yi wannan aikin wanda ya zama dole a yi shi cikin wata ɗaya ko kuma tsoho ya mutu. 

Ana cikin haka, sai ga abokin adawarsa wato James ya zo masa da wata cacar gasa. James ya ƙalubalanci Raj da ya sa Chaitra ta kware masa a cikin kwanaki talatin. Ita kuwa wannan budurwa, babanta wani mugun ɗan daba ne kuma hamshaƙin ɗan kasuwa da ake kira da Bellary. 

Idan har Raj ya lashe wannan gasa kafin 31 December 2011, James zai bashi kuɗin da yake buƙata domin yin wannan aiki. Idan kuma bai yi nasara ba, to zai yi bankwana da cacar gasa baki ɗaya. Saboda tsananin buƙatar kuɗi da yake yi, Raj sai ya karɓi wannan tayi inda ya fara ƙoƙarin shawo kan Chaitra. Ba da jimawa ba kuwa sai Chaitra ta kware masa. Sai dai Bellary ya gano abin da ke tsakaninsu, hakan ta sa ya aika yaransa da nufin su kashe su a daren 31 December. Sai dai Raj da Chaitra sun samu nasarar guduwa inda suka faɗa dajin Srisailam. Daga nan sai Bellary, Minista Baireddanna da kuma ɗansa suka fara farautarsu a cikin wannan daji na Srisailam, James ya taimaka musu sun kuɓuta daga sharrin Bellary, sai dai ya samu mummunan rauni. Bayan ɗan gidan Minista ya sace Chaitra, sai James ya bayyanawa Raj gaskiyar abin da ya faru a baya. 

Mahaifin Raj wato Suryanarayana wani kamilin mutum ne da ake girmamawa a garin Rayadurg, to yana da wani aboki attajiri mai suna Ramamurthy wanda shi ne mahaifin Chaitra. Chaitra da Raj dama abokai ne tun suna yara. Shi kuma Bellary, surukin Ramamurthy ne, yayin da ya gano cewa akwai tuwon ƙarfe a ƙarƙashin ƙasar filin Ramamurthy, sai shi da Baireddanna suka shirya makircin yadda za su amfana da wannan dukiya. Su kuma Suryanarayana da Ramamurthy sai suka nuna ƙin amincewarsu. Hakan ya sa su Bellary hallaka ahalinsu baki ɗaya, Raj da Chaitra ne kaɗai suka rayu. Shi ne sai Bellary ya riƙi Chaitra da nufin cewa da zarar ta kai munzalin budurtaka zai kashe ta ya mallake filin. 

Ita kuma Chaitra, saboda ta san halin Raj na shiga cacar gasa, shi ne sai ta sa abokinta na yarinta wato James ya sa shi cikin gasar domin kawar da Bellary da kuma Baireddanna. Raj sai ya sha alwashin ɗaukar fansar ran mahaifinsa inda ya kashe Bellary, Baireddanna da kuma ɗansa a Rayadurg. Sannan kuma ya ceci Chaitra tare da raba filayen Ramamurthy wa mutanen ƙauyen bayan ya aure ta. 

Jaruman Shirin 

• Ram Charan - Raj

• Tamannaah - Chaitra

• Ajmal Ameer - James

• Mukesh Rishi - Bellary

• Dev Gill - Ɗan Baireddanna

• Kota Srinivasa Rao - Baireddanna

• Nassar - Ramamurthy

• R. Parthiepan - Suryanarayana

• Brahmanandam - Dr. Rangeela

• Ali - Papa Rao

• Diksha Panth - Basanthi, Budurwar Papa Rao

• Paruchuri Venkateswara Rao - Mahaifin James 

• Jaya Prakash Reddy - S.I Krishna Varm

• Geetha - matar Bellary

• Venu Madhav 

• Srinivasa Reddy 

• Thagubothu Ramesh - Bobby

• M. S. Narayana - Mariƙin Raj 

• Ravi Babu 

• Mukhtar Khan - Police Officer

• Krishna Bhagavaan

Fish Venkat - Venkat

• Jhansi

• Chatrapathi Sekhar

• Lisa Haydon - Fitowa ta musamman. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

TAMBAƊAƊIYA


TAMBAƊAƊIYA

• Har yanzu ina nan ina zance kan Mujiya. 
• Kangana ko kuce Firgitacciya. 
• Mai sukar Addininmu ita ce la'ananniya. 
• Ga ta 'yar ƙyamas kama an ɗaura zane ga Muciya. 
• Kin yi asara yar bayan gari Makauniya. 

• Maras hankali kai kuce mata Mahaukaciya. 
• 'Yar bala'i ku kira ta Masifaffiya.
• Ja'ira mai ja'irci 'yar jagaliya.
• Allah ya watsa lamarinki ki zamo Tambaɗaɗɗiya. 
• 'Yar maye mai shisshigi Makakkiya. 

• Shagiɗaɗɗiya mara kunya Karkatacciya. 
• Sai zare ido kamar ana yi wa Mujiya tsargiya. 
• Jemammiya, 'yar bishiya Lanƙwasashiya. 
• Allahu kasa wanga baiwa taka ta gane gaskiya. 
• Ta shiryu ta dawo hanyar Muhammadu mai son gaskiya. 

• Ta daina ƙwafa da makirci ta gane gaskiya. 
• In kuma ba ta da rabo ka sa ta zamo Wulaƙantacciya. 
• A koma gudun ta tun da ta zamo Annamimiya. 
• A wayi gari ta yo mushe ta zamo Sheƙaƙƙiya. 
• Busashiya, mara tsari Wahalalliya. 

• Jamilu ne na Kaduna ke waƙar raddi a gurin Watsatstsiya. 
• Ɗan Abdurrahman na Gadan nan mai bawa musulunci Kariya. 
• Makafcin zamani mai rattabe da ƙafiya. 
• jariri marubuta, neman ƙarin sani bai ɗaya 
• Ina muku sallama, Allah ya ƙare mu da lafiya. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA


FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA

An jima da fara kallon fina-finan Indiya a ƙasar Hausa wanda shi ne tubalin da ya gina masana'antar fina-finan arewacin Nijeriya da aka fi sani da Kannywood. To amma, da shekaru takwas zuwa goma da suka gabata izuwa yanzu, masana'antun fina-finan Indiya (Musamman Bollywood da Tollywood) sun ƙara samun mabiya a ƙasar Hausa fiye da da, wannan kuwa ya biyo bayan fassara fina-finansu ne da aka fara yi a cikin harshen Hausa.

Duk cewa an ɗauki tsawon shekaru kusan 50 ana kallon fina-finan Indiya a ƙasar Hausa, mafi yawancin makallatan suna wannan kallo ne ba tare da sanin ko da kalma guda ta harshen Hindi ba. Yayin da wasu kuma ke amfani "Subtitles" wajen fahimtar saƙon da fina-finan ke ɗauke da su. To amma duk da wannan ƙarancin fahimtar yare da ake samu, hakan bai hana a ci gaba da kallon fina-finan ba, musamman irin yadda mafi yawancin saƙonnin fina-finan ke kamanceceniya da halaye da kuma ɗabi'un muatenen ƙasar Hausa. A hankali kuma sai aka fara samun zaƙaƙuran matasa a ƙasar Hausa waɗanda sha'awar fina-finan ta sa suka fara bibiyar al'amuran yau da kullum da suka shafi masana'antun fina-finan ƙasar Indiya, wannan shi ne ya haifar da samuwar nagartattu kuma Ingantattun bayanai da suka shafi jarumai, fina-finai da sauran al'amuran da suka jiɓincin harkar baki ɗaya.

Abun bai tsaya a nan ba, domin kuwa ba tare da wani jinkiri ba sai aka fara samun masu nazartar yaren Hindi tare kuma da ƙoƙarin ganin sun koyar da wasu wannan yare. Wannan ya haifar da samuwar ƙungiyoyin da suke ɗabbaƙa al'adu da kuma sauran al'amuran da suka shafi masana'antun fina-finan Indiya. Daga nan sai taruka suka fara samuwa da kuma bukukuwan sallah inda akan haɗu a yi zumunci a yi nishaɗi tare da ƙarawa juna sani dangane da harkar baki ɗaya. A dalilin haka an samu abota da dama wasu ma har ta kai su ga yin aure. Samuwar masu gabatar da shirye-shiryen da suka jiɓinci fina-finan Indiya a gidajen Talabijin da kuma gidajen Rediyo a arewacin Nijeriya sai ya zama ya ƙara hura wutar soyayyar da ake yi wa jarumai da kuma fina-finan Indiya a yankin ƙasar Hausa. Wannan ya sa aka ƙara samun haɗuwar kai da kuma yaɗuwar sabbin ƙungiyoyi majiɓantan harkar.

Zuwan shafukan sada zumunta irin su Facebook, Twitter da kuma Whatsapp sai ya bawa masu sha'awar wannan harka ta fina-finan Indiya damar haɗuwa da juna kai tsaye tare kuma da samun bayanai akan jarumansu da kuma sauran al'amuran da suka shafe su kai tsaye. A yayin da duk wannan ci gaba ke samuwa kada mai karatu ya manta cewa; masoyan wannan harkar ne ke ci gaba da kawo waɗannan ci gaba wanda hakan shi kuma ya haifar da ƙarin mabiya.

Ana cikin wannan ne kwatsam kuma sai ga harkar fassarar fina-finai izuwa harshen Hausa ta samu a cikin harshen Hausa kuma daga Hausawa 'yan asalin yankin ƙasar Hausa. Hakan yasa nan take mabiya wannan harka ta Indiya suka ninku daga biyar zuwa talatin cikin dare ɗaya, domin kuwa da yawansu suna son fina-finan ko da basa fahimtar abin da ake cewa yanzu kuwa da suka fara fahimtar saƙon, sai soyayyar da suke yi wa fina-finan ta ƙaru. Saboda ƙaruwa da fina-finan Indiya suka samu a fannin masoya da kuma masu bibiyar harkar, sai da ya zamana masana'antar fina-finan Kannywood da kanta ta girgiza. Domin kuwa hakan ya jawo samun ƙarancin kasuwancin fina-finansu a kasuwa, har sai da ta kai cewa masu sarin fina-finan sun gwammace su sari fina-finan fassara akan su sari fina-finan da Hausawan suka shirya.


Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

मियां भाई की डेटिंग 
Share:

BARKA SALMAN KHANBARKA SALMAN KHAN

A yau ne jarumi Salman Khan yake cika shekaru 32 da shigowa masana'antar shirya fina-finan Indiya. To sanin kowa ne dai cewa ni ba fan ɗin Salman Khan bane, amma ina son shi saboda shi ɗan uwana ne musulmi, wannan kuwa ya isa komai. Bugu da ƙari, jarumi Salman Khan gwani ne da duniya ma ta aminta da gwanintarsa, shahararre ne wanda duniya ta yarda da shahararsa kuma ya kai matsayinta da ko ba a so dole a girmamashi in dai a harkar fim ne. Don haka ina taya shi murnar zagayowar wannan rana, haƙiƙa salman abun alfahari ne a wajenmu. Ko da yake ban aminta da mafi yawancin tsare-tsaren rayuwarsa ba, na aminta da nagartar aikinsa. Ko da yake yana da matsaloli da dama a rayuwarsa, nima ai ina da nawa mas'alolin. Ko da yake yana aikata kura-kurai da dama a raywarsa, nima ai ina aikata kura-kuran. In kuwa har haka ne, to kowa ya ji da nashi, sai a zauna lafiya.

Fatan alheri wa salman da masoyansa, Allah ya ƙara masa ƙarfin imani, Allah ya ƙara gyara masa al'amuransa, ya bashi mata ta gari, ya bashi sa'a akan fina-finansa na gaba kuma ya kare shi daga sharrin maƙiya. Nagode

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

Yi Haƙuri


YI HAƘURI

Daga Phisio Tim YouTube channel video 

Fassarawa

 Jamilu Abdurrahman 


Yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin mutane masu girman kai. Zamanin da mutanensa kan iya yarda su rasa alaƙar da suka yi shekara ɗaya zuwa uku suna ginawa, kawai saboda yi haƙuri!

Zamanin mutanen da mace ta gwammace ta kwashe kayanta daga gidan mijinta ta koma gidan iyayenta a maimakon ta ce: yi haƙuri!

Zamanin da namiji ya gwammace ya rasa iyalinsa matuƙar zai samu jin cewa shi ya fi wani. 

Barka da zuwa zamanin da mutanensa kowa akan dai-dai yake. Zamanin da mutanensa ba sa taɓa yarda sun yi kuskure, zamanin da mutanensa suka san komai. Zamanin da mutanensa su ke ganin cewa sun isa, alhali sun jahilci yadda za su jure zama da juna. 

Zamanin da mutanensa suka gwammace su yi ta gardama na tsawon shekaru a maimakon su furta kalmar yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin da mutanensa suke ɗaura wa wasu laifukansu. Zamanin da mutanensa ke ganin su ke kan dai-dai a koyaushe kuma suke ƙoƙarin yi wa wasu hukunci.

Zamanin da mutanensa ke ganin rashin dai-dai a tattare da wasu kawai banda kawunansu. Zamanin da mutanensa suka gwammace su yi ta gardama a maimakon su ce: yi haƙuri!

Barka da zuwa zamanin da mutanensa ke taƙama da son kai. Zamanin da mutanen cikinsa ke so ko da yaushe mutane su ke basu haƙuri. Zamanin da mutanensa saboda ganin mutuncin kawunansu suka gwammace su ci gaba da rayuwa ba tare da wasu da Allah ya turo musu ba, maimakon su yi sulhu da abokan zaman su. 

Zamanin da mutanen cikinsa suka gwammace su yi baran-baran da abokansu da masu taimakonsu a maimakon su ce yi haƙuri ka manta da aibu na. 

Zamanin mutane masu ji-ji-da-kai. Zamanin da mutanensa ke ganin sun sha ƙarfin su ce: yi haƙuri! 

 Ku saurari labarai ku ji kuma ku ga yadda mutane da dama ke kashe masoyansu, aure ya mutu kuma ahalin da a da yake cike da farinciki yau ya koma mahauta, saboda muna jin cewa bai cancanta ace mu ce yi haƙuri ba

Shin ko za ku iya min wata alfarma ku furta kalmar Yi haƙuri?

Ya kuka ji da kuka furta kalmar?

Shin sunanku ya canja ne? Shin kalar fatarku ko tsayinku sun canja ne? Shin gyaran gashin da kuka yi ko kwalliya sun canja ne? Shin da kuka furta kalmar asusun bankinku ya yi ƙasa ne? Shin jinannakin ku sun rage ne yayin da kuka furta kalmar? Ko kuma kun kamu da Covid19 ne da kuka furta kalmar? 

Hmm, to mai yasa ku ka zaɓi ku rasa wannan kyakkywar budurwar ko saurayin saboda girman kai? Mai yasa ku ka zaɓi ku rasa wannan tarayyar mai ban mamaki, abota da kuma waɗanda ubangiji ya aiko domin su taimake ku a rayuwa? 

Kada ku manta fa shi girman kai rawanin tsiya ne. Wasun mu da dama sun rasa abokan zamansu saboda ya zama mana abu mai wahala mu ce: yi haƙuri! 

Shin ko kun san cewa kalmar yi haƙuri ka iya canja rayuwarku har abada? Kawai ku dinga faɗarta akai-akai, ku yarda da ni babu wani mummunan abu da zai faru. 

A duk sanda kuka furta kalmar sai dai fa a samu sulhu, za a sake samun zaman lafiya da lumana. Abota za ta sake ginuwa yayin da sabbin al'amuran ban mamaki za su ci gaba da wanzuwa.

Ku yi haƙuri, in har wannan saƙon ya saɓa muku. Na zo da salama ne. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

FASSARAR WAƘAR AAP MUJHE ACHCHE LAGNE LAGEFASSARAR WAƘAR AAP MUJHE ACHCHE LAGNE LAGE 

Waƙa: Aap Mujhe Achche Lagne Lage 

Fim: Aap Mujhe Achche Lagne Lage 

Harshe: Hausa 

Shekara: 2000 

Sauti: Rajesh Roshan 

Rubutawa: Ibrahim ashq

Rerawa: Abhijeet Bhattacharya & 
Alka Yagnik

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Mohabbat ki haseen shuruaat ho gayi x2

Farkon soyayya me daɗi ya faru. 

• Meri duniya mere sapne ab sajne lage 

Duniyata da mafarkaina sun fara ƙawatuwa. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage x3

Na ara son ka.

• Manzilen hai nayi, raaste hai naye x2

Bigirorin da hanyoyin sababbi ne. 

• Hum zameen se aasman tak ab udne lage

 Na fara tashi daga ƙasa zuwa sama. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage x3

 Na fara son ki. 

• Raaz kya hai zindagi ka, khul gaya khul gaya x2

Sirrin soyayya ya bayyana. 

• Dil ka aaina khushi se, dhul gaya dhul gaya 

Madubin zuciya ya wanku da farinciki. 

• Hum bhi apni ek duniya rakhne lage

Har na fara ma ajiye duniyata ta kaina.  

• Ke aap mujhe achche lagne lage

Fara son ka.

• Ke aap mujhe achche lagne lage

 Na fara son ki. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage

Fara son ka.

• Sochi samjhi yeh mulaqatein nahi, ji nahi x2

Wannan haɗuwar ta kwatsam ce.

• Haan aadmi ke bas ki yeh baatein nahi, ji nahi
Tabbas, waɗannan abubuwa (ne) da babu wanda ya ke da iko da su. 

• Rab ne chaha toh yeh dil yoon milne lage
Idan har Allah ya so, zukatan nan za su kasance a tare. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage

 Na fara son ki. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage

 Na fara son ki. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage

 Na fara son ki. 

• Mohabbat ki haseen shuruaat ho gayi

Farkon soyayya me daɗi ya faru. 

• Meri duniya mere sapne ab sajne lage 

Duniyata da mafarkaina sun fara ƙawatuwa. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage x3

Fara son ka.

• Manzilen hai nayi, raaste hai naye 

Bigirorin da hanyoyin sababbi ne. 

• Hum zameen se aasman tak ab udne lage

 Na fara tashi daga ƙasa zuwa sama. 

• Ke aap mujhe achche lagne lage x3

 Na fara son ki/ka

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR WAƘAR HOORFassarar Waƙar Hoor

Waƙa: Hoor

Fim: Hindi Medium

Harshe: Hausa

Shekara: 2017

Sauti: Sachin-Jigar

Rubutawa: Priya Saraiya

Kamfani: YRF

Rerawa: Atif Aslam

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
 

Hmm… Mmm…

Hmm Mmm…

• Lafzon Ke Haseen Dhaagon Mein Kahin

A cikin kyakyawan ƙullin kalamaina. 

• Piro Raha Hoon Kabse Main Huzoor

Na ke ta ƙoƙarin saƙa ki, ya ke kyakkywa. 

• Koshishein Zara Hai Nigaahon Ki

Idanuwana ƙoƙari su ke yi. 

• Tujhe Dekhne Ki Ho Khata Zaroor

Su yi kuskuren kallon ki. 

• Deewangi Kahun Isse Ya Hai Mera Fitoor

Shin wannan hauka ne ko taurin ra'ayi? 

• Koi Hoor… Jaise Tu (x2)

Ke tamkar mala'ika ce. 

• Bheege Mausam Ki Bheegi Subah Ka Hai Noor…

Ke ce hasken safiyar damina. 

• Kaise Door… Tujhse Main Rahoon…

Ta yaya zan iya ci gaba da kasancewa nesa da ke? 

• Khamoshiyan Jo Sun Le Meri

Da za ki saurari shiru na. 

• Inmein Tera Hi Zikr Hai

Za ki ji ambatonki a ciki. 

Hmm.. Hmmm 

• Khamoshiyan Jo Sun Le Meri

Da za ki saurari shiru na. 

• Inmein Tera Hi Zikr Hai

Za ki ji ambatonki a ciki. 

• Khwaabon Mein Jo Tu Dekhe Mere

Da za ki kalli mafarkaina. 

• Tujhse Hi Hota Ishq Hai

Za ki ga cewa ke kaɗai nake ƙauna. 

• Ulfat Kaho Isse Meri, Na Kaho Hai Mera Kasoor

Ki kira wannan da ƙaunata amma kada ki kira shi da laifina. 

• Koi Hoor… Jaise Tu (x2)

Ke tamkar mala'ika ce. 

• Bheege Mausam Ki Bheegi Subah Ka Hai Noor…

Ke ce hasken safiyar damina.


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KICK


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KICK

Shekarar Fita - 2014

Fassarawa - Jamilu Abdurrahman

• Pehda toh main bhi sharif hua tha ... par sharafat se apni kabhi nahi bani

Nima kaina da gaskiya aka haife ni... Amma na kasa ci gaba da rayuwa da gaskiyar. 

Nawazuddin Siddiqui

• Mere bare mein itna mat sochna ... dil mein aata hoon ... samajh mein nahi

Kada ki yi tunani a kaina... A cikin zuciya nake... Amma ina da wuyar fahimta. 

Salman Khan

• Rishtey ko mazboot hona chahiye ... majboor nahi

Kamata ya yi ace alaƙa ta zama abu mai ƙarfi... Ba abinda za a kasa taimakawa ba. 

Salman Khan

• Ek ek paisa gin lena thook laga ke ... yeh ho na ho hum toh traditional kaminey log hai
Count every note with your 

Ka ƙirga kuɗin da yawu... Ta yiwu shi ba haka yake ba, amma mu 'yan iskan gargajiya ne. 

Nawazuddin Siddiqui

• Machli chahe kitni bhi tezz ho ... ek baar kaante mein phas jaye toh kilo ke bhav bikti hai

Komai hanzarin kifi... Da zarar ya shiga ƙugiya, to a kilo za a siyar da shi. 

Randeep Hooda

• Izzat, zillat, shohrat aur maut ... upar waale ke haath mein hai

Daraja, tozarci, arziƙi da mutuwa... Duk a hannun ubangiji suke. 

Mithun Chakraborty

• Aap devil ke peeche, devil aapke peeche ... too much fun

Kana Bayan shaiɗan, shaiɗan na bayanka... Nishaɗin ya yawaita. 

Salman Khan

• Mujhse joh dushmani modh leta hai ... uspe uparwaala reham toh kar deta hai, magar main nahi

Wanda duk ya zama maƙiyina... Ubangiji na iya yafe masa... Amma ba ni ba. 

Salman Khan

• Koi umeed bar nahi aati, koi soorat nazar nahi aati ... maut toh ek din moiyan hai, neend raat bhar kyun nahi aati ... pehle aati thi haal-e-dil pe hassi, ab kisi baat pe nahi aati

Babu wata fata da za a yi, babu kuma wani sulhu da za a samu... Mutuwa ƙaddara ce da sai ta zo watarana,amma me ya sa na kasa bacci tsawon dare... Da fari dariya nake yi akan damuwar zuciyata, amma yanzu kuma na kasa dariya akan komai. 

Nawazuddin Siddiqui

• Main case aur face kabhi nahi bhoolta hoon

Ba na manta taƙaddama da kuma fuska. 

Randeep Hooda

• Jisse zindagi ki parvah hoti hai ... maa kasam maarne ka mazaa us hi ko aata hai

Irin masu damuwa da rayuwa ɗin nan ko... Na rantse da mahaifiyata kashe su akwai daɗi. 

Nawazuddin Siddiqui

• Chehre par gussa, mann mein gaali ... goli bhi chalali ... phir bhi dono haath khali

Akwai fushi a fuskarka, tsinuwa kuma a cikin zuciyarka... Har ma ka harba harsashi... Amma duka hannayenka fayau suke. 

Salman Khan

• Meri vardi pe medal bahut lage hai ... par daag sirf ek

Akwai lambobin girmamawa da yawa a jikin kakina... Da kuma datti guda ɗaya. 

Randeep Hooda

• Dawai aur shaadi mein badi similarity hoti hai ... dono agar time pe na mile na, bahut mushkil ho jaati hai

Akwai babban kamanceceniya a tsakanin magani da kuma aure... Idan har ba ka same su akan lokaci ba, to za ka fuskanci gagarumar matsala. 

Saurabh Shukla

• Woh jeena bhi koi jeena hai jis mein kick na ho

Rayuwar duk da babu nishaɗi a cikinta ba rayuwa bace. 

Salman Khan

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DIL TO PAGAL HAI


FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DIL TO PAGAL HAI

Shekarar Fita - 1997

Fassarawa - Jamilu Abdurrahman 

• Rahul, naam toh suna hoga?

Rahul, na san kin taɓa jin sunan ko? 

Shah Rukh Khan 

• Rahul, naam toh yaad rahega na?

Rahul, shin za ki tuna da sunana? 

Shah Rukh Khan 

• Hamare sapno ka saathi aur hamara jeevan saathi ... kabhi ek nahi hota

Abokan tarayyarmu a mafarki da na zahiri... Ba sa taɓa zamowa ɗaya. 

• Main usse bahut pyar karti hoon ... ek din ke liye nahi ... ek pal ke liye nahi ... zindagi bhar ke liye

Ina son shi sosai... Ba wai na rana ɗaya ba... Ba wai na wani ɗan lokaci ba... Face na dukkan rayuwa baki ɗayanta. 

Madhuri Dixit

• Main kisi ladki wadki se pyar nahi karta ... sirf ladkiya mujhse pyar karti hai

Ni ba na faɗawa soyayya da 'yan mata...'yan mata ne kawai suke faɗawa soyayya da ni. 

Shah Rukh Khan

• Kahin na kahin, koi na koi mere liye banaya gaya hai ... aur kabhi na kabhi main usse zaroor milongi

A wani waje, an halicci wani saboda ni... Kuma watarana tabbas zan haɗu da shi. 

Madhuri Dixit

• Pyar bahut baar ho jaata hai ... lekin mohabbat sirf ek baar hoti hai. 

Akan iya faɗawa soyayya sau da dama... Amma tsunduma cikin ƙauna yana faruwa sau ɗaya ne kawai. 

Aruna Irani

• Kehdo ki tumhe nahi lagta ki hum dono ek doosre ke liye bane hai ... kehdo ki jab main tumse door jata hoon, tum mujhe palat kar nahi dekhti ... kehdo ki jab main tumhe choota hoon, tumhe kuch nahi hota ... kehdo ki is waqt tum meri baahon mein nahi aana chahti ... ek baar meri aankhon mein dekho aur aakhri baar kehdo ki tum mujhse pyar nahi karti

Ki faɗa min ba kya jin an halicce mu ne domin juna... Ki faɗa min in na yi nesa da ke, ba kya waigawa ki ganni... Ki faɗa min a duk sanda na taɓa ki, ba kya jin komai... Ki faɗa min ba kya son zuwa cikin hannayena a yanzun nan... Ki kalli idanuwana kuma ki faɗa min a karo na ƙarshe cewa ba kya so na. 

Shah Rukh Khan

• Kisi ko pyar karna aur ussi se pyar paana ... bahut kam logon ko naseeb hota hai

Ka so wani mutum kuma ka samu soyayya daga wannan mutumin... Mutane ƙalilan ne ke da sa'ar samun hakan. 

Karisma Kapoor

• Kya tumne kabhi bhi ... ek din ke liye bhi ... ek pal ke liye bhi ... mujhse pyar kiya tha?

Shin kin taɓa jin... Ko da na yini ɗaya ne... Ko da na ɗan wani lokaci ne... Cewa kina so na? 

Shah Rukh Khan


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN BAAHUBALI: THE BEGINNING

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN BAAHUBALI THE BEGINNING

Shekarar Fita - 2015

Fassarawa - Jamilu Abdurrahman

• Is rajya mein sirf do log uska naam lete hai ... tum aur main ... tum ki apni maut se pehle usse aakhri baar dekh pao ... main taa ki ek baar aur usse apne haathon se maar paon

A wannan jahar mutane biyu ne kawai ke ambaton sunansa... Ke da ni... Ke saboda ki sake ganinsa a karo na ƙarshe kafin ki mutu... Ni kuma saboda in sake kashe shi da hannaye na. 

Rana Daggubati

• Balwan ko aur balwan karo ... isse chalaaki nahi, rajneeti kehte hai

Mayar da masu ƙarfi mafiya ƙarfi... Wannan shi ake kira siyasa ba wayo ba. 

Nassar

• Ek raja ka dharam sirf shatru ko maarna hi nahi hota ... praja ko bachana bhi hota hai

Aikin sarki ba kashe maƙiya bane kawai... Harda kare mutanensa. 

Ramya Krishnan

• Kayarta ke vikul hai mere yeh aasoon aur peedha ke toh bilkul bhi nahi ... yeh mera rakht hai joh ghoolkar bhav ban gaya aur meri aankhon se behne laga

Hawayena na barranta daga dolanci ne ba na jin raɗaɗi ba... Wannan jinina ne ya rikiɗa daga yadda nake ji yake fitowa ta cikin idanuwana. 

Tamannaah Bhatia

• Yudh mein saikadon ko maarne waala nayak hai ... lekin joh kisi ek ke bhi pran bachaye woh devta hai

Wanda ya kashe mutane da dama a filin daga shi ake kira da jarumi... Amma wanda ya ceci rayuwa ko da guda ɗaya ne shi ubangiji ne. 

Ramya Krishnan

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

FASSARAR WAƘAR JAANA VE

Fassarar Waƙar Jaana Ve

Waƙa: Jaana Ve

FIM : Aksar 2

Harshe: Hausa

Shekara: 2017

Sauti: Mithoon

Rubutawa: Sayeed Quadri

Kamfani: Tips Music

Rerawa: Arijit Singh

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 


• Mohabbat, Ibaadat, Shikayat Main Jis Se Karoon

Wacce nake ƙauna, wacce na ke yi wa bauta, wacce ita na ke kaiwa kukana. 

• Woh Tum Ho, Tumhi Ho Jaan-E-Jaan

Ke ce wannan, ke ce ya masoyiyar rayuwata. 

• Guzarish Ya Khwaahish Farmaiash Main Jis Se Karoon

Wacce na roƙa, wacce na ke muradi, wacce na ke marari. 

• Woh Tum Ho, Tumhi Ho Saathiya

Ke ce wannan, ke ce ya abokiyar tarayya ta. 

• Chehra Tera Maange Aakhein Meri O Jaana

Idanuwana suna muradin ganinki ya abar ƙauna. 

• Teri Justjoo Mein Kat Ta Har Din Mera

Kowane yini nawa yana tafiya ne wajen neman ki. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 


Ooo Hooo Ooo…

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 

Ooo Hooo Ooo…

• Khayalon Mein Maine Tujhko Buna Thha

Na saƙa ki a cikin mafarkai na. 

• Haqeeqat Mein Mujhko Tu Mil Gaya

Gashi yanzu na same ki a farke. 

• Yahi Soch Ke Main Khud Hairaan Hoon

Ni kaina da na ga hakan sai da na gigice. 

• Rab Ko Yeh Kaise Pata Chal Gaya

Ta yaya ubangiji ya san muradi na? 

• Likhi Thhi Muqaddar Mein Chaahat Teri Oh Jaana

Samun soyayyar ki a rubuce yake a cikin ƙaddara ta. 

• Ke Tu Jahaan Mein Mera Ho Hi Gaya

Kamar yadda a duk faɗin duniya kika zamo tawa. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 

Ooo Hooo Ooo…

• Teri Aarzoo Mein Kabse Jee Raha Thha

Tun tuni ina rayuwa ne a cikin muradinki. 

• Teri Justjoo Thhi Mujhe Bepanah

Ina neman ki ba tare da iyakancewa ba. 

• Nigahon Se Meri Tu Door Na Jaana

Kada ki ɓacewa gani na. 

• Baahon Mein Meri Ghar Hai Tera

Gidanki yana nan a cikin hannuwana. 

• Meri Har Tamanna Hai Poori Hui Oh Jaana

Dukkan burikana sun cika ya masoyiya ta. 

• Mehka Hua Hai Har Lamha Mera

Kowace daƙiƙa tawa ta zamo mai ƙamshi. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 

• Jaana Ve, Jaana Ve, Mohabbat Karte Rehna Re

Abar ƙaunata, ki ci gaba da sona. 

• Ho Mausam Chaahe Kaisa Bhi, Hamesha Mera Rehna Re

Koma menene dalilin, ki ci gaba da zama tawa a koyaushe. 


Ooo Hooo Ooo…

• Jaana Ve… Jaana Ve… Jaana Ve…

Ya abar ƙaunata! 


ƘARIN HASKE: a cikin wannan waƙa an nuna makauniyar soyayya wacce har ta sa shi jarumin ya ɓige da ɗaukar masoyiyarsa a matsayin abar bautarsa. Wannan ba dai dai bane gaskiya domin an shiga hurumin Allah, kuma yin hakan kafirci ne. Allah ya shiryar da mu. Amin, Nagode 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

NAYANTHARA

NAYANTHARA 


Sarauniyar Kudanci Nayanthara
Samun kamar tabbas sai an tona
A can kudanci ta tabbata ba ki da tsara
Ko a cikin mafarki zan so ki zam amarya guna
Da ke ake yi tun da har yau Nayanthara
Wa ke ta zomo idan ana batun su ɓauna
Ni ke na hango a sama babu gadara
Idanuwanki kan sa shauƙi a raina
Balo-balon so a zuciyata tuni kin hura 
Wuta ta bege a ruhina tuni kin kunna 
Goron ɗaurin auren mu na gani ashe tuni kin ɓara 
Ko za ki zaneni na yarda ki zamo mata gunaaa... 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

FASSARAR WAƘAR SHAYADFASSARAR WAƘAR SHAYAD 

Waƙa: Shayad

Fim: Love Aaj Kal (2020) 

Harshe: Hausa

Shekara: 2020

Sauti: Pritam

Rubutawa: Irshad Kamil

Kamfani: Sony Music

Rerawa: Arijit Singh

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman
 

• Shayad Kabhi Na Keh Sakoon Main Tumko

Wataƙila ba zan iya bayyana miki kaina ba wataran. 

• Kahe Bina Samajh Lo Tum Shayad

Wataƙila kin fahimci yadda na ke ji duk da cewa ban furta komai ba. 

• Shayad Mere Khayal Mein Tum Ek Din

Wataƙila a tunani/mafarkaina watarana. 

• Milo Mujhe Kahin Pe Gum Shayad

Zan haɗu da ke wataƙila. 

• Jo Tum Na Ho... Rahenge Hum Nahin (x2)

Matuƙar ba kya tare da ni, ba zan iya wanzuwa ba. 

• Na Chahiye Kuch Tum Se Zyada, Tum Se Kam Nahin

Ba na son komai ko wani abu ƙasa da ke.

• Jo Tum Na Ho... Toh Hum Bhi Hum Nahi (x2)

In babu ke, to ba zan iya zamowa kaina ba. 

• Na Chahiye Kuch Tum Se Zyada, Tum Se Kam Nahin

Ba na son komai ko wani abu ƙasa da ke.

• Aankhon Ko Khwaab Dena

Na ba wa idanuwana mafarkai. 

• Khud Hi Sawaal Karke

(tare da) sanya tambayoyi wa ke a kwatance na. 

• Khud Hi Jawaab Dena Teri Taraf Se

Sannan in amsa (tambayar) daga ɓangaren ki kuma. 

• Bin Kaam Kaam Karna

(Ina) aiki duk da cewa bani da aiki. 

• Jaana Kahin Ho Chaahe

Ko da na so zuwa wani wajen. 

• Har Baar Hi Guzarna Teri Taraf Se...

Na kan wuce ta inda kike koyaushe. 

• Ye Koshishein... Toh Hongi Kam Nahin (x2)

Waɗannan ƙoƙarin samun naki fa ba za su taɓa tsayawa ba. 

• Na Chahiye Kuch Tum Se Zyada, Tum Se Kam Nahin

Ba na son komai ko wani abu ƙasa da ke.

• Jo Tum Na Ho... Rahenge Hum Nahin 

Matuƙar ba kya tare da ni, ba zan iya wanzuwa ba. 

• Jo Tum Na Ho... Toh Hum Bhi Hum Nahi 

In babu ke, to ba zan iya zamowa kaina ba. 

• Na Chahiye Kuch Tum Se Zyada, Tum Se Kam Nahin

Ba na son komai ko wani abu ƙasa da ke.

• Jo Tum Na Ho... O...

In babu ke... 

• Jo Tum Na Ho... Ooo...

In babu ke... 

• Jo Tum Na Ho...

In babu ke... 


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

SHARHIN FIM ƊIN SRIMANTHUDU


SHARHIN FIM ƊIN SRIMANTHUDU 


Srimanthudu fim ɗin kudanci India ne da aka fitar a shekara ta 2015. Fim ne da ƙunshi abubuwa da dama waɗanda in muka shiga cikin sharhin da kyau za ku fahimci hakan. 

Bada Umurni - Koratala Siva

Ɗaukar Nauyi - Y. Naveen, Y. Ravi Shankar, C. V. Mohan & 
Mahesh Babu

Rubutawa - Koratala Siva

Sautin shiri - Devi Sri Prasad

Horas da 'Yan Wasa - R. Madhi

Tacewa - Kotagiri Venkateswara Rao

Kamfanin da ya shirya - G. Mahesh Babu Entertainment Pvt. Ltd & Mythri Movie Makers

Yaɗawa - Eros International

Ranar Fita - 7 August 2015

Tsawon Shiri - 158 minutes 

Ƙasa - India

Harshe - Telugu

Kasafi - ₹400—700 million 

Kasuwancin Box office - ₹1.4—2.0 billion 

Da fari an shirya cewa fim ɗin Srimanthudu zai samu shiryawa ne a ƙarƙashin kamfanin UTV Motion Pictures, amma daga baya sai kamfanin ya cire hannunsa daga aikin saboda banbancin ra'ayi aka samu. An fara ɗaukar wannan shiri ne a ranar 11 ga watan Agustan 2014 a Ramanaidu Studios da ke Hyderabad. Ko da yake mafi yawancin fim ɗin an ɗauke shi ne a Hyderabad, wasu sassan shirin an ɗauke su ne a Pune, Tamil Nadu da kuma Malaysia.

Srimanthudu da kuma fassarar shi da aka yi da harshen Tamil mai suna Selvandhan duka an sake su ne a rana guda a duniya baki ɗaya. Masana da masu sharhi sun yabi wannan shiri sosai, yayin da su ma 'yan kallo suka yaba wa fim ɗin ta hanyar ci gaba da kallonsa har sai da ya zama fim ɗin Telugu na uku da ya fi kowanne kawo kuɗi. 

Bayan fitar wannan fim, Jarumai, ma'aikata da 'yan siyasa sun bayyana tsari da burin taimakawa ƙauyuka tare da taimakon mutanen ƙauyen da ke yankin Telangana da Andhra Pradesh. An fassara wannan fim izuwa harshen Hausa da sunan Mai Arziƙi. 

Labarin Shirin 


Harsha Vardhan shi kaɗai ne ɗa kuma magajin kamfanin kasuwancin mahaifinsa Ravikanth wanda ya kai kimar biliyan ₹250. Bayan ya haɗu da Charuseela a bikin zagayowar ranar haihuwar abokinsa Apparao, sai ya shiga jami'a inda ya fara koyon ilimin haɓaka ƙauyuka. Burin Charuseela shi ne ta hi amfani da kimiyya da fasaha wajen taimakawa ƙauyen Devarakota da ke Uttarandhra wanda can ne tsatsonta. Da fari dai abota ce ta shiga tsakaninsu da Harsha, amma da tafiya ta yi nisa kuma sai abin ya koma soyayya. 

Baki ɗayan albarkatun ƙauyen Devarakota suna ƙarƙashin ikon wani tantiri ne mai suna Sashi, wanda ya kasance ɗan uwa ne ga Ministan tsakiya wato Venkata Ratnam wanda shi kuma zaluncinsa ya sa 'yan ƙauyen da dama yin hijira zuwa birni domin samun sauƙin rayuwa. 
Sai dai duk da haka, shugaban wannan ƙauye wato Narayana Rao ya kasance mai fata tare da burin ganin ci gaban wannan ƙauye da mutanen cikinsa. A gefe guda kuma ɗan Ratnam wato Radha ya yi barazanar cin zarafi da mutunci ga ahalin Ravikanth matuƙar bai janye daga neman wata ƙwangilar gina hanya ba. Ashe ɗan ƙanwar Ravikanth wato Karthik, wanda ke burin ganin ya gaji Ravikanth shi ne ya ba wa Radha muhimman bayanan kwangilar, amma sai Harsha ya gano hakan. Bayan ya yi wa Ratnam gargaɗi akan hakan, sai Harsha ya shigar da takardar neman wannan kwangila a sirrance ba tare da mahaifinsa ya sani ba kuma aka samu kwangilar. 

Yayin da Charuseela ta fahimci cewa Harsha ɗan Ravikanth ne, sai ta fara Ja baya da shi. Da ya tambaye ta dalili, sai ta ke bashi labarin cewa mahaifinsa ɗan asalin ƙauyen Devarakota ne da ya shigo birni domin ya tara dukiya, ba kamar mahaifinta ba wato Narayana Rao wanda ya zauna a ƙauyen domin ya taimaka musu. Daga nan sai ta yi masa bankwana ta tafi. 

Bayan ya nemi dogon hutu a wajen mahaifinsa kafin fara shiga ofishinsa, sai Harsha ya tafi ƙauyen Devarakota ba tare da sanin mahaifinsa ba. A ƙauyen Devarakota ne ya haɗu da Rao inda ya gabatar da kansa a matsayin ɗalibi mai karantar hanyoyin haɓaka ƙauyuka kuma ya zo ƙauyen ne domin yayi nazari akansa. Bayan ya nazarci ƙauyen Devarakota da kuma irin zaluncin Sashi da kyau, sai Harsha ya bayyana cewa zai ɗauki nauyin ƙauyen tare da haɓaka shi. A dai-dai lokacin da yake ƙoƙarin haɓaka ƙauyen ne kuma sai Ratnam ya umurci Sashi da ya haɓaka ƙauyen saboda su samu cin zaɓe, amma sai ya yi biris bisa tunanin cewa ya za a yi kura da shan bugu gardi kuma da kwashe kuɗi? 

 A dai-dai wannan lokaci ne kuma Harsha ya gano cewa a lokacin da Ravikanth yake matashi shima ya so ya haɓaka wannan ƙauye kamar yadda Harsha ke yi a yanzu. Amma sai Ratnam da Sashi suka ƙulla makaircin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, inda hakan yasa aka ci mutuncinsa kuma aka kama shi. Wannan dalili ne ma ya sa ya bar ƙauyen ya koma birni har ya zama attajiri. 

Yayin da Charuseela ta dawo ƙauyen Devarakota ta ga aikin da Harsha yake yi, sai ta yi tunanin cewa ya zo ne domin ya shawo kanta da na iyayenta domin ya aure ta. Amma a hankali sai ta ji ya burge ta bayan ya magance wata matsala da ta taso a cikin gidan. Daga baya sai Harsha da Charuseela suka fahimci cewa Ratnam yana shirin mallake dukkan filaye da gonakin ƙauyen saboda wata harƙallar siyasa da ya sa a gaba. Hakan ya sa Harsha ya je ya ja masa kunne akan ya fita daga harkar aikin da yake yi a wannan ƙauye. 

Harsha kuma sai ya kai ziyara zuwa wata ma'aikata ruwan kwalba wanda bayan samar da giya da suke yi a sirrance, suna kuma kwashe kaso mafi tsoka na ruwan wannan ƙauye wanda shi ne mutanen ƙauyen ke amfani da shi. Da yayi ƙoƙarin rufe shi, sai yaran sashi suka kawo masa farmaki inda har suka ji masa rauni aka kai shi asibiti. 

Shi kuma Ravikanth, da yake an bashi labarin aikin da Harsha ya fara a wannan ƙauye na Devarakota, sai ya yi ƙoƙari ya dawo da Harsha Hyderabad, inda ya shiga ofishinsa bayan ya warke. 
A wata zazzafar tattaunawa da suka yi ne dai Ravikanth ya amince wa Harsha da komawa ƙauyen Devarakota, wanda hakan ya sa ya samu soyayyar Harsha, abinda ya daɗe yana nema. Harsha sai ya miƙa ragamar kasuwancin baki ɗaya wa Karthik daga nan ya tafi. 

A ƙauyen Devarakota, Harsha ya kashe Ratnam da Sashi a wata ma'aikata amma sai ya tsara abin a matsayin tsautsayi ne kamar yadda suka yi wa mahaifinsa. Fim ɗin dai ya ƙare ne a yayin da aka nuno Ravikanth da ahalinsa sun kai ziyara wa Rao a bikin 
Sankranthi inda Harsha da Charuseela suke zaune a matsayin mata da miji. 

Jaruman Shirin. 

Mahesh Babu - Harsha Vardhan

Shruti Haasan - Charuseela

Jagapathi Babu - Ravikanth

Rajendra Prasad - Narayana Rao

Sukanya - mahaifiyar Harsha 

Sithara - mahaifiyar Charuseela 

Mukesh Rishi - Venkata Ratnam

Sampath Raj - Sashi

Harish Uthaman - Radha

Vennela Kishore - Apparao

Sriram Edida - Ɗan uwan Narayana Rao

Tulasi - Surikar Narayana Rao

Subbaraju - Ɗan uwan Ravikanth

Rahul Ravindran - Karthik

Ali - Rajaratnam

Sravan - 

Sivaji Raja - Suryam

Ravi Prakash - Dr. Ganesh

Surya - 

Tejaswi Madivada - Yarinyar Venkata Ratnam

Surekha Vani - Sumathi

Anand -

Sanam Shetty - Meghna

Angana Roy - 

Ravi Varma - 

Nikkita Anil Kumar -

Poorna - fitowa ta musamman 

Waƙoƙin Shirin 

1. "Rama Rama" 
2. "Jatha Kalise" 
3. "Charuseela"
4. "Srimanthuda" 
5. "Jaago" 
6. "Dhimmathirigae"


©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

FASSARAR WAƘAR TERE LIYE

FASSARAR WAƘAR TERE LIYE 

Waƙa: Tere Liye

Fim: Veer-Zaara

Harshe: Hausa

Shekara: 2004

Sauti: The Late Madan Mohan yayin da Sanjeev Kohli kuma ya sabunta. 

Rubutawa: Javed Akhtar

Kamfani: Yash Raj Music

Rerawa : Lata Mangeshkar & Roop Kumar Rathod

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Tere liye, ham hain jiye, honton ko siye

Wa ke, na rayu, laɓɓana suka rufe. 

• Tere liye, ham hain jiye, har aansoo piye

Wa kai, na rayu, na haɗiye hawayena. 

• Dil mein magar, jalte rahe, chaahat ke diye

Amma a cikin zuciyata, fitilar soyayyar mu na ci gaba da ci. 

• Tere liye, tere liye
Wa ke, wa ke! 

• Tere liye, ham hain jiye, har aansoo piye

Wa kai, na rayu, na haɗiye hawayena. 

• Tere liye, ham hain jiye, honton ko siye

Wa ke, na rayu, laɓɓana suka rufe. 

• Dil mein magar, jalte rahe, chaahat ke diye

Amma a cikin zuciyata, fitilar soyayyar mu na ci gaba da ci.

• Tere liye, tere liye

Wa kai, wa kai! 

Aa......

• Zindagi, le ke aayi hai, beete dinon ki kitaab(x2)

Rayuwa ta taho da daɗin kwanakin da suka gabata. 

• Gher hain, ab hamein, yaadein be-hisaab

Zagaye nake da ababen tunawa masu tarin yawa. 

• Bina poochhe, mile mujhe, kitne saare jawaab

Na samu amsoshi da dama ba tare da na tambaya ba. 

• Chaaha tha kya, paaya hai kya, humne dekhiye

Dubi abin da na yi muradi, da kuma abin da na samu a sakamakon hakan. 

• Dil mein magar, jalte rahe, chaahat ke diye

Amma a cikin zuciyata, fitilar soyayyar mu na ci gaba da ci.

-• Tere liye, tere liye
Wa ke, wa ke! 

• Kya kahoon, duniya ne kiya, mujh se kaisa bair(x2)

Me zan ce? Rayuwa ta yaudare ni ta wata hanya. 

• Hukum tha, main jiyun, lekin tere bagair

An umurce ni da in ci gaba da rayuwa, amma ba tare da kai ba. 

• Naadaan hai woh, kehte hain jo, mere liye tum ho gair

Wane irin jahilci ne ke tattare da waɗanda ke cewa ke baƙuwa ce a gare ni? 

• Kitne sitam, humpe sanam, logon ne kiye

Kurakurai nawa mutane suka aikata a kan mu? 

• Dil mein magar, jalte rahe, chaahat ke diye

Amma a cikin zuciyata, fitilar soyayyar mu na ci gaba da ci.

• Tere liye, tere liye

Wa kai, wa kai!

• Tere liye, ham hain jiye, honton ko siye

Wa ke, na rayu, laɓɓana suka rufe. 

• Tere liye, ham hain jiye, har aansoo piye

Wa kai, na rayu, na haɗiye hawayena. 

• Dil mein magar, jalte rahe, chaahat ke diye

Amma a cikin zuciyata, fitilar soyayyar mu na ci gaba da ci.

• Tere liye, tere liye
Wa ke, wa ke! 

• Tere liye, tere liye
Wa ke, wa ke! 

• Tere liye, tere liye

Wa kai, wa kai!

• Tere liye, tere liye
Wa ke, wa ke! 

• Tere liye, tere liye

Wa kai, wa kai!

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

FASSARAR WAƘAR TU HI TU (MALE)FASSARAR WAƘAR TU HI TU 


Waƙ: Tu Hi Tu

Fim: Kick 

Harshe: Hausa 

Shekara: 2014 

Sauti: Himesh Reshammiya

Rubutawa: Mayur Puri

Kamfani: T-Series 

Rerawa: Mohd. Irfan

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

 
• Tu Hi Tu Har Jagah, Aaj Kal Kyun Hai (x2)

Me ya sa na ke ganin ki a ko'ina ne cikin kwanakin nan? 

• Raaste Har Dafa, Sirf Tera Pata

Hanyoyin, a kowane lokaci, adireshin ki.. 

• Mujhse Pooche Bhala, Kyun Hai

(suke) Tambaye ta, ban san me ya sa ba.

• Na Main Apna Raha, Na Kisi Aur Ka

Ba zan iya zama mallakina ko na wata ba. 

• Aisa Mere Khuda Kyun Hai

Ya Ubangiji, me ya sa hakane? 

• Tu Hi Tu Har Jagah, Aaj Kal Kyun Hai (x2)

Me ya sa na ke ganin ki a ko'ina ne cikin kwanakin nan? 

• Raaste Har Dafa, Sirf Tera Pata

Hanyoyin, a kowane lokaci, adireshin ki.. 

• Mujhse Pooche Bhala, Kyun Hai

(suke) Tambaye ta, ban san me ya sa ba.

• Na Main Apna Raha, Na Kisi Aur Ka

Ba zan iya zama mallakina ko na wata ba. 

• Aisa Mere Khuda Kyun Hai

Ya Ubangiji, me ya sa hakane? 

• Dheeemi Dheemi Aanch Pe Jaise

Kamar akan bakin wuta. 

• Dheere Dheere Jalta Hai Dil

Zuciya ta ke ƙonewa a hankali. 

• Ye Beqaraari, Kyun Hai

Me ya sa wannan rashin sukunin ya ke anan ne? 

• Ye Khumaari, Kyun Hai 

Me ya kawo wannan irin mayen haka? 

• Awaargi, Kyun Hai Har Mod Par

Me ya sa wannan haukar ta wanzu a kowane layi ne? 

• Na Main Apna Raha, Na Kisi Aur Ka

Ba zan iya zama mallakina ko na wata ba. 

• Aisa Mere Khuda Kyun Hai

Ya Ubangiji, me ya sa hakane? 
O... O… O…

• Tu Hi Tu Har Jagah, Aaj Kal Kyun Hai (x2)

Me ya sa na ke ganin ki a ko'ina ne cikin kwanakin nan? 

• Raaste Har Dafa, Sirf Tera Pata

Hanyoyin, a kowane lokaci, adireshin ki.. 

• Mujhse Pooche Bhala, Kyun Hai

(suke) Tambaye ta, ban san me ya sa ba.

• Hua Nahi Pehle Kabhi Yeh

Hakan bai taɓa faruwa ba. 

• Chhua Nahi Dil Ko Kisi Ne

Babu wadda ta taɓa taɓa min zuciyata irin haka. 

• Har Aarzoo, Tu Hi

Ke ce muradina. 

• Chain-O-Sukoon, Tu Hi

Ke ce hutu kuma zaman lafiya na. 

• Main Toh Kahun, Tu Hi Hai Zindagi

Na amintu da cewa ke ce rayuwata. 

• Na Main Apna Raha, Na Kisi Aur Ka

Ba zan iya zama mallakina ko na wata ba. 

• Aisa Mere Khuda Kyun Hai

Ya Ubangiji, me ya sa hakane? 

O... O… O…

• Tu Hi Tu Har Jagah, Aaj Kal Kyun Hai (x2)

Me ya sa na ke ganin ki a ko'ina ne cikin kwanakin nan? 

• Raaste Har Dafa, Sirf Tera Pata

Hanyoyin, a kowane lokaci, adireshin ki.. 

• Mujhse Pooche Bhala, Kyun Hai

(suke) Tambaye ta, ban san me ya sa ba.

• Na Main Apna Raha, Na Kisi Aur Ka

Ba zan iya zama mallakina ko na wata ba. 

• Aisa Mere Khuda Kyun Hai

Ya Ubangiji, me ya sa hakane? 

O... O… O…


ƘARIN HASKE: Wannan waƙa ce ta soyayya, kewa da kuma damuwa. Sai dai kuma an yi kuskure a cikin waƙar a inda mawaƙin ke tambayar/tuhumar ubangiji kan cewa menene dalilin da ya sa wani abu ya kasance tare da shi. Dalili kuwa shi ne, babu wani wanda ya isa ya tuhumi Allah a bisa wani abu da ya ƙaddara ya faru domin shi ne kaɗai ke da cikakken iko akan kowa da komai. Ku tuntuɓi malaman Tauhidi/Aƙida domin samun cikakken bayani. Nagode ©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

FASSARAR WAƘAR UDI UDI JAAYE

FASSARAR WAƘAR UDI UDI JAYE 


Waƙa: Udi Udi Jaye

Fim: Raees 

Harshe: Hausa

Shekara: 2017 

Sauti: Ram Sampath

Rubutawa: Javed Akhtar

Kamfani: Zee Music Company

Rerawa: Sukhwinder Singh, Bhoomi Trivedi & Karsan Sagathia

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 
 

• Arre Udi Udi Udi Udi Udi Udi… Udi Jaaye…

Yana tashi sama,Yana tashi sama.

• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Dil Ki Patang Dekho Udi Udi Jaaye

Kalli, jirgin ledan zuciyata yana tashi sama. 

• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Dil Ki Patang Dekho Udi Udi Jaaye

Kalli, jirgin ledan zuciyata yana tashi sama. 

• Kehne Ko Toh Khel Hai Yeh Tera Mera Saanjha

Kamar yadda yake, wasa ne kawai a wajenmu masoyi. 

• Par Mera Dil Hai Patang Aur Teri Nazar Manjha

Sai dai zuciyata kamar jirgin Leda take, kallonka kuma kamar zare yake. 

• Manjhe Se Lipti Yeh Patang Judi Judi Jaaye

Wannan jirgin ledan a hankali sai ƙara sarƙewa yake yi a jikin zaren. 

• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Dil Ki Patang Dekho Udi Udi Jaaye

Kalli, jirgin ledan zuciyata yana tashi sama. 

• Do Dil Ude, Do Dil Ude

Zukata biyu na tashi sama. 

• Oonche Aasmaanon Mein Jude

Kuma suna haɗewa a samaniya. 

• Do Dil Ude, Do Dil Ude

Zukata biyu na tashi sama. 

• Oonche Aasmaanon Mein Jude

Kuma suna haɗewa a samaniya. 

• Udi Udi Jaaye…

Yana tashi sama. 

• Mujhe Kab Thha Pata Iska

Ba ni da masaniyar.

• Tere Prem Ka Iktaara

Cewa tsirkiyar soyayyarki. 

• Mann Mein Yun Pal Pal Baajega

Za ta samar da sauti a cikin zuciyata koyaushe. 

• Mujhe Kab Thhi Khabar Iski

Ban ankare ba. 

• Mere Mann Ke Singhaasan Par Tu

Cewa a karagar zuciyata. 

• Sada Ko Yun Tu Birajega…

Za ka zauna har abada. 

• Koi Bhi Kathinayi Ho Ya Koi Ho Majboori

Babu damuwa don akwai wuya ko tilastawa. 

• Teri Meri Ek Bhi Pal Hove Nahi Doori

Babu wani lokaci da zai zama ba ma tare. 

• Manjhe Se Lipti Yeh Patang Judi Judi Jaaye

Da sannu dai wannan jirgin ledan na ta ƙara sarƙewa a jikin zaren. 

• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Dil Ki Patang Dekho Udi Udi Jaaye

Kalli, jirgin ledan zuciyata yana tashi sama. 

• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Dil Ki Patang Dekho Udi Udi Jaaye

Kalli, jirgin ledan zuciyata yana tashi sama. 

Aaa… Hoo…

• Tarnetar No Medo Jaamyo

Kasuwar baje kolin Tarnetar ta fara ci. 

• Jaamyo Het No Hudo

Kowa na ta rawar hudo zukatansu cike da ƙauna. 

• Tarnetar No Medo Jaamyo

Kasuwar baje kolin Tarnetar ta fara ci. 

• Jaamyo Het No Hudo

Kowa na ta rawar hudo zukatansu cike da ƙauna. 

• Haal Ne Gori Rami Laiye (x2)

yarinya mu je can mu yi rawa. 

• Medo Thaase Puro

Kafin baje kolin ya ƙarƙare. 

• Tarnetar No Medo Jaamyo

Kasuwar baje kolin Tarnetar ta fara ci. 

• Jaamyo Het No Hudo

Kowa na ta rawar hudo zukatansu cike da ƙauna. 

• Tarnetar No Medo Jaamyo

Kasuwar baje kolin Tarnetar ta fara ci. 

• Jaamyo Het No Hudo

Kowa na ta rawar hudo zukatansu cike da ƙauna. 

• Mere Jeevan Ke Galle Mein

A ma'adanar rayuwata.  

• Tera Pyaar Hi Toh Mera Dhan Hai

Son ki shi kaɗai ne dukiyar da na mallaka. 

• Tu Hai Toh Dhanwaan Hoon Main

Ni mai arziƙi ne matuƙar kina tare da ni. 

• Hooo… Prem Ke Iss Mohalle Mein

A wannan yankin soyayyar. 

• Mera Ghar Tera Hi Toh Yeh Mann Hai

Zuciyarka ita ce gidana. 

Ki Teri Mehmaan Hoon Main, Haan…

Kamar yadda nake baƙuwar ka. 

• Jaise Sugandh Phool Ke Sang, Chaand Ke Sang Kiran

Kamar yadda ƙamshi ke fitowa daga fure, kamar yadda haske ke fitowa daga wata. 

• Jaise Rasa Daaru Ke Sang Balm Ke Sang Ragan

Kamar yadda maye ke samuwa daga giya, kamar yadda nutsuwa ke samuwa daga balsam. (haka mu ke) 

• Manjhe Se Lipti Yeh Patang Judi Judi Jaaye

Da sannu dai wannan jirgin ledan na ta ƙara sarƙewa a jikin zaren. 

• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Dil Ki Patang Dekho Udi Udi Jaaye

Kalli, jirgin ledan zuciyata yana tashi sama. 

• Yeh Jo Patang Hai Tere Hi Sang Hai

Wannan jirgin ledar nawa da kai kawai yake tare. 

• Teri Hi Ore Dekh Mudi Mudi Jaaye

Kalli yana tahowa gare ka. 

• Do Dil Ude, Do Dil Ude

Zukata biyu na tashi sama. 

• Oonche Aasmaanon Mein Jude

Kuma suna haɗewa a samaniya. 

• Do Dil Ude, Do Dil Ude

Zukata biyu na tashi sama. 

• Oonche Aasmaanon Mein Jude

Kuma suna haɗewa a samaniya. 

• Arre -• Udi Udi Jaaye, Udi Udi Jaaye

Yana tashi sama,

• Hooo… Udi Udi Jaaye…

Yana tashi sama. 
 

ƘARIN HASKE: Tarnetar wata Kasuwar baje koli ce da ke ci a kowace shekara a yankin Gujarat da keIndia, su na kiranta da suna Trinetreshwar Mahadev Mela. Kasuwar tana jawo hankalin 'yan kasuwa da sauran mutane da ga kowane yanki, kuma aƙalla tana ɗaukar adadin mutane kimanin 100,000 people. Wai an ce wannan Kasuwar ta fara ci ne tun gabanin zuwan Annabi Isah. 

Hudo kuma wata irin rawa ce da yara da matasa ke yi a yankin Gujarat. Rawar ta samo asali ne daga ƙabilar Bharwad, su kuma wasu makiyaya ne da ke zaune a yankin na Gujarat. Sannan fasahar yin rawar ta samu ne daga faɗan raguna ko shanu, don haka in kana kallon wannan rawa za ka ga mutanen suna abubuwa irin wannan. 

Balsam kuma wata bishiya ce wacce ake amfani da ita wajen haɗa abubuwa da yau, tun daga magani har irin su mayukan zafin da mu ke amfani da su (Chinese balm d.s). Nagode

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI


JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI

࿐࿐࿐࿐࿐࿐
FITOWA TA 16
࿐࿐࿐࿐࿐࿐

151. Lautunga Yahaan Tere Paas Main Haan - Zan dawo zuwa gare ki.
152. Bahut jhankaar beat aadmi hai woh - Wannan fa ƙasurgumin mahaukaci ne.
153. Teri Muskurahatein Hain Taaqat Meri - Murmushinki shi ne ƙarfina. 
154. Swagat nahi karoge aap hamara? - Ba za ka/ki marabce ni bane?
155. Waada Hai Mera Mar Bhi Jaaun Kahin - Wannan shi ne alƙawarina ko da bana raye.
156. Maa ki jhooti kasam nahi khaate hai - Bai Kamata Mutum ya yi ƙarya yayin amsa tambaya akan Mahaifiyarsa ba.
157. Ek Sawaal Ke Sau Jawaab Hain - Tambaya ta na da amsoshi ɗari. 
158. Har din ek dua maangti hoon ... ke shayad ek din tum mujhe maaf kardo - A Kowace rana Fatar Abu daya nake yi... Cewa Watarana zaki yafe min. 
159. Ho Jaane Dilon Ka Yeh Sauda Parakhna - Ku san yadda za ku kula da zuciya.
160. Main criminals se baat nahin karta - Bana magana da 'Yan Jagaliya. 

Zan ci gaba in sha Allah. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI 15

JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI

࿐࿐࿐࿐࿐࿐
FITOWA TA 15
࿐࿐࿐࿐࿐࿐

141. Maine sirf Musa se baat karna hai - Da Musa kaɗai zan yi magana.
142. Main yahan hoon - Ga ni nan/ ga ni a nan.
143. Maryam Aisha se bari hai - Maryam ta girmi Aisha.
144. Aap khati rahin - sai kake ta yi/ sai ci kike ta yi. 
145. Mere Maa Kaduna se aana hai - mahaifiyata za ta zo daga daga Kaduna.
146. Aake moh se lipat le -Taho ka/ki rungume ni.
147. Khuda ki kasam mein tujhe nahi chaoungi - na rantse da Allah ba zan taɓa barinka ba. 
148. Hum mar jaayenge - Mutuwa zan yi. 
149. Log achcha insaan bano, Mar jate hai, magar unka anchayi zinda rake ga - mutanen kirki ko da sun mutu, sukan bar abinda za a dinga tunawa da su. 
150. Dhokha mere saath hua hai ... joh karna hai main hi karoonga - An riga an cuce ni... Duk abinda ya dace inyi, zan yi shi. 

Zan ci gaba in sha Allah. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Share:

JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI 14


JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI

࿐࿐࿐࿐࿐࿐
FITOWA TA 14
࿐࿐࿐࿐࿐࿐

131. Aur chawal lijiye - ƙara shinkafar.
132. Yehi hai zindagi - rayuwa kenan.

133. Aap bhejtī rahin - kana/kina ta ci gaba da turowa. 

134. Chandni Raat, Taron Ki Baaraat Hai - Dare ne mai cike da farin wata, akwai yiwuwar bayyanar taurari. 

135. mere kapde saaf hain - kayana a tsaftace suke. 
136. paisa vasool - iya kuɗinka 

137. Thappad se darr nahi lagta, pyar se lagta hai - Bana jin tsoron Mari, amma ina jin tsoron soyayya. 

138. Ek Anek Mein Kaisi Yaari - Babu abota a tsakanin halittu biyu mabanbanta.

139. Bandar ek admi ka jaisa hai - Biri ya yi kama da mutum. 

140. Har ishq ka ek waqt hota hai, woh hamara waqt nahi tha, par iska yeh matlab nahi ki woh ishq nahi tha - Kowacce soyayya tana da nata lokacin, wancan lokacin ba namu bane, Sai dai fa hakan baya nufin son ba ya nan. 

Zan ci gaba in sha Allah. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 


Share:

JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI 13


JUMLOLI DUBU ƊARI DA HARSHEN HINDI

࿐࿐࿐࿐࿐࿐
FITOWA TA 13
࿐࿐࿐࿐࿐࿐

121. Kahan ho tum? - kana ina ne?/kina ina ne?

122. Kya hal hai? - ya ake ciki ne?

123. Kya chal raha hai? - me ke faruwa ne?

124. Aap se mil ke khushi hui - na yi farin cikin haɗuwa da kai/ke. 

125. Aap se mil ke accha laga - na ji daɗin haɗuwa da kai/ke.

126. Kripya Padhāriye - Don zauna mana.

127. Alvida - sai anjima

128. Kya main yahan bait sakti hoon? - zan iya zama a nan? (mace) 

129. Kya main yahan bait sakta hoon? - zan iya zama a nan? (namiji)

130. Koi dua mat maangna, sirf pyar karna mujhe - Kada ki yi min addu'a, ki so ni kawai.

Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Share:

ISLAMIC STUDIES 17

ASOF 2020

ISLAMIC STUDIES

DARASI NA 17

GABATARWAR-ABDULRASHID ABDULLAHI, KANO

(Adultery and fornication)
Zina da fasikanci

الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُمْ بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَائِفَةٌ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
Mazinãciya da mazinãci,(1) to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu. (Qur'an 24:2)

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya.
                     (Alkur’ani 17:32)


An ruwaito daga ibn Abba cewa manzon Allah ya ce: kada wanda ya kusaci saduwa da mace Bata hanyar aure ba 

1- Zina larabci kalmar larabci ce Zina tana nuna ma'anar jima'i na son rai a wajen aure ba tare da la’akari da bangarorin da abin ya shafa suna da aure ko kuma suna da wasu abokan wannan ba, wannan ya hada da sharuddan zina da fasikanci a cikin harshen Ingilishi Wanda yana magana ne ga masu yin aure da kuma masu laifin masu aure bi da bi.

Na biyu: sakamakon zina akan aure da dangi
Aure da dangi muhimmaci tsari ne a cikin musuluncin wannan saboda su ne tushen rayuwar jama'a da kuma filin koyarwa na gaba

3 - Azabar Musulunci ga Zina
daga tattaunawar da aka yi a sama game da mummunan tasirin zina ana iya ganin hakan ba kawai laifin sirri bane amma laifi ne ga al'umma kamar sata ko kisan kai saboda haka ana ɗaukarsa ba zunubi bane kawai amma laifin doka ne wanda ake masa hukunci a ƙarƙashin shari'ar ' a
An wajabta hukuncin bulala 100 a cikin Alqur’ani ga namiji da mace idan bai taba yin aure ba dangane da idan kuma ya tabayin aure Koh Ta tabayin aure haka ana iya amfani da hukuncin kisan ta hanyar jifa bisa ga sunnar manzo Allah S A A 

abdulrashidabdullahimusa@gmail.com
Whatapp:09067298607


Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form