Barka da warhaka

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 24


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 24```
.
AIKINKA

Za mu iya kasa qananan ma'aikata zuwa gida biyu, akwai wadanda suke aiki don neman abin sakawa a bakin salati, da kuma wadanda suke yi don tsare dukiya ko tarata, manufar kowa game da aikin akwai bambanci, dagewa da mai da hankali wurin wanda yake aiki don neman abinci bai kai kamar mai yi don tara dukiya ba, shi ya sa ko kyauta za a yi sai ka ga bambanci a tsakaninsu, na taba jin wani babban mutum da na san yana da wani babban kamfani yana ta bala'i a kan Naira hamsin, ya ce in mai kayan ba zai sayar a Naira 500 ba a dawo masa da kudinsa, don me za a qara masa Naira 50?
.
Babban abinda ya kamata mutum ya tsare shi ne aiki koda ba nasa ba ne, kwanannan nake ji wani asibiti sun dauki wata daliba daga gwaji saboda tsabar hazaqarta da dagewarta, na ga wasu lakcarori su ma an dauke su saboda hazaqarsu a dakin karatu, suna gamawa aka dauke su aiki, a duk lokacin da kake aiki ana kallonka, kar ka ce don ba naka ba ne ba za ka wahala ba, in ma naka din ne jajurcewarka wani babban jigo ce da za ta taimaka maka wurin ganin ka isa inda ake buqata.
.
Ba wani ma'aikaci wanda bai sha wahala ba kafin ya kai ga gaci, bari mu dubo wasu 'yan abubuwa ko na ce sharudda wadanda su ne ginshiqan cin nasara masamman a rayuwarmu ta baya-bayannan, duk wani ma'aikaci yana da kyau ya sani cewa ba wani aiki a duniya wanda ake fado masa ta sama, komai yana da farko, in ba ka sani ba kuma kana son cin nasara to ka nemi a nuna maka a matsayinka na sabon ma'aikaci, kar ka yi girman kai, alamun ka shirya aikin kenan, in mutum na neman aiki zai jigata, in ya samu bai nufin yanzu hutu sai ya nade hannu ya ci arziqi, yanzu ya kamata ya fara aiki.
.
Samunka da aiki yana nuna cewa aikin ma ya same ka, in kai ne mai wurin sai ka yi tsayuwar daka wurin ganin ya habaka, kar ka yi zaton shikenan yanzu hutu ya zo, idan kana zama wa wani a kantinsa ne sai yau ya yaye ka, ya bude maka wani dan qwarya-qwaryan kanti kar ka ce "Yauwa 'yanci ya zo, na farko dai sai lokacin da na fito kuma ina da zabi a lokacin da zan koma gida, zan ci abinda nake so, kudin duk da na samu nawa ne sai yadda na yi da su, in ka yi hakan haqiqa ka yi gaggawa, da dan sauran tafiya a gabanka.
.
Wannan wata gada ce da ka tsallake daga dukiyar wani zuwa taka, lokacin da aka mallaka maka kudin gado bayan da kana fama da talauci kar ka taba zaton ka haye, gada ka samu, in ka taka a hankali ka haye, in ka yi gaggawa ka auka ciki, kudin ko shagon da aka ba ka asali na wani ne, za ka dan dauki lokaci kafin ka maida su naka, zan ba ka misali, wani lebura da ya yi aikin wuni tun da safe har maraice kafin ya sami 2,000 a matsayin ladar wahalarsa, kai kuma ka yi rakiya ne a ka miqo maka wannan kudin, cikin sauqi za ka ce a zare maka tsire na dari biyar, shi kuwa ba zai sha wahala tun safe ya kashe dari biyar a kan tsire kacal ba, wanda ya bude shago ya ce ya zama naka, ku ka sami gado, ko ka zama shugaban qaramar hukuma ko kansila za ka dan dauki lokaci kafin ka maida kudin naka, in dan siyasa ne qila sai ya sauka gaba daya kudin sun girgiza kafin ya fara jin cewa nasa ne.
.
Gaggawa ce ke damun mutanenmu, na san wanda ya gaji miliyoyi yanzu ya koma abin tausayi kamar ba shi ne jiya yake fantamawarsa ba, na ga wani dan siyasa wanda ya sami kudi ya yi gidaje ya mallaki kadarori da dama, yanzu ko gidan kansa bai da shi, wani ma gidan ma ya raba biyu ne ya sayar da rabi yadda zai samu ya iya ririta rayuwar, wani bawan Allah ya yi ritaya aka ba shi kudinsa tsibi a hannunsa, ya sami wasu bayin Allah suka ba shi shawarar cewa ya yi shago don kar kudin su qare a banza, ya karbi shawararsu ya fasa daki daya daga cikin dakunansa ya mai da shi shago, ya maqare shi da kaya, kusan komai kake so yana da shi, yanzu aiki ya kamata ya fara tuquru, don ya tabbatar da nasarar da yake ganin ya samu.
.
Sai ya yi kuskure, ba ya iya futowa shagon sai rana ta raba, kafin taran dare kuma ya rufe, sai mutane su zo sayen kaya ba shi, in an aika masa ya ce ba zai fito ba, aka yi ta kukan hakan har aka gaji aka fita harkarsa, da dai ya ga kamar abubuwa na dan ja baya sai ya dauki ma'aikaci, shi ma bai zabo qwararre ba, ya hada irin tarhon kusa dinnan, in an zo sayen kaya sai a buga masa ya fadi kudin, shi ba zai iya zama a shagon ba ya zama babba, ba a jima shagon ya lalace aka rufe shi gaba daya ya koma dakin kwana, na ce ya yi gaggawa ne, na san wanda ya tarairayi abinda ke hannunsa yanzu ana ganinsa a matsayin mai isasshen jari.
.
Idan ka sami jari a rana guda na tsabar kudi wadanda ba ka zata ba, yi qoqari ka zuba su a banki ka manta da su, ka dawo ka fara neman abinda ranka ya natsu da shi kuma yanayin da ake ciki ya karba, sannan ka zauna da wadanda ke cikin harkar ka gani kuma ka tambayi fa'idoji da matsalolin dake cikin harkar, sannan ka qimanta masaniyarka da qoqarinka in zai yuwu ka shiga, sai ka ajiye cewa yanzu ne za ka fara neman nasara ba wai da samun wannan kudin har ka cimmata ne ba, sai ka sanya Allah a gaba ka yi ta roqon ya ci gaba da agaza maka kamar yada ka faro tun farko.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

WaΖ™ar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waΖ™e ak...

Contact form