Barka da warhaka

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 26


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*

 ```//26 ```

KAI NE FARKO

In har za mu nemo hanyar cin nasara a rayuwa kai ne farko, domin kai ne za ka fara laluben inda take ka hau hanyar nemanta, wasu cikinmu suna ganin cewa in ka ji ana maganar nasara to a neman aure ne ko wasan motsa jiki, tabbas an fi samun nasara idan akwai gasa, amma wace gasa ce ta wuce mutum ya sami abinda yake so a rayuwa? Duk masu qoqarin cin nasarannan da kake ji kowa haqilonsa shi ne ya sami abinda yake so a rayuwa, na zauna da wanda bai da wani zance sai ya zama mai kudi, ma'aikacin gwamnati ne, ya qi komawa makaranta ya qaro karatu, arziqin mahaifinsa ya karye bare a yi maganar gado, baida sana'a bare mu ga nau'in sana'ar da kuma gudunta wurin isa ga nasarar da yake nema.
.
Akwai qananan sana'o'i wadanda masu kudinmu na yau duk sun yi su, amma sun yi sana'o'i da yawa a bayansu, na ga wani mai arziqi aka ce wanki-da-guga ne silar arziqinsa, da na bincika sai na ji ya yi wasu sana'o'in barkatai a tsakiya, na ga wani matashin dakta a ilimi da na tambaye shi yadda aka yi ya isa wannan matsayin, sai ya fara ba ni tarihinsa wanda na ji har qasashen maqwabtammu ya zaga don neman nasara a rayuwa, ya sheda min cewa burodi yake sari yana sayarwa, ya yi wasu sana'o'in kafin ya dawo ya riqi karatun da yake dogoro a kansa yanzu?
.
Kai dai ka lura wace sana'a ce za ka fara don ta zama maka gada wurin isa inda nasara take? In ka tara masu kudi kowa za ka ji hanyar arziqinsa saban ce, akwai shahararrun mawaqa da na gani suka ce daga almajirci suka zarce, ka ga dai kamata ya yi a ce sun zama malaman Qur'ani, to ba su kadai ba, na ma ga wasu masu abin hannunsu, arziqi ya kankama kuma suka ce daga almajirci suka fara, kowa kuma ya san almajirci ba sana'a ba ne bare a fara tunanin yana kawo arziqi ko bai kawowa, uwayensu kan turo su ne sai yadda hali ya yi, ko karatu ko wani abin, duk abinda yaro ya fara bude ido da shi to shi ne zai zama mafarin tafiyarsa da zai riqa takawa yana hango nasara da shi.
.
1) Yanzu dai a matakin farko ka fara amincewa kana son ka dogara da kanka, ba wai jira kake a raba gado ka samu a sama ba, ko hakan ne ma ka sani in har aka ba ka kasonka dole ka riqa ririta shi kana qara yawansa, qoqarin da za ka yi wurin ba wa dukiyar kariya ta rurin qara yawanta ya fi wanda za ka yi a lokacin da kake neman na kanka wahala, don haka yi qoqari ka kama sana'a, fitar da burin cewa za ka gaji kudi, ko tsammanin wani zai taimake ka, yi qoqari neman na kanka ya zama maka jiki kafin ka riqe wata dukiya da za ta shigo maka daga baya, da za ka riqe kantinka da ka habbaka shi shi cikin shekara 17, ka miqa shi ga wanda mai san kan sana'ar ba, ka ba shi shekara daya tal ka dawo ka ga inda ya kai.
.
Yi qoqari ka gano inda ka fi rauni, in ba ka son abokanka su riqa ganinka kana qananan sana'o'i to ka nemi irin sana'ar da za ka zauna wuri guda kamar tela, tsaron kanti da sauransu, kar ka dauki kabu-kabu ko yaron mota ko sayar da gwanjo wuri -wuri, ka amince wa kanka tabbas kana son sana'ar, kuma za ka iya yin alfahari da shi a ko'ina ne, in mace ce kake nema ka gamsar da zuciyarka cewa da sana'ar za ka ciyar da ita, daganan sai tsarin yadda za ka tafiyar sana'ar ba tare da tsoron komai ko kowa ba.
.
In ka fara sana'ar za ka ga wasu matsaloli a tsakiya kar ka damu, ka sami qarfin gwiwa kawai, ina yaro na yi sha'awar bara yadda na ga sa'o'ina yara suna neman na kansu kuma suna iya yi wa kawunansu wasu abubuwan duk da cewa suna nesa da mahaifansu, mu kuwa muna gaban uwayen ba iya tsinana komai, ranar farko da na fita aka kama ni a gida na ji jiki, bayan wasu lukuta kuma na yanke zama yaron mota, har na sami wanda zan riqa bi, amma da yaron gidansa ya zo haka ya ce min na sauka, daganan na karaya na koma gida, banda wannan ma na taba zuwa gona na siyo rake na je kasuwa, don in sayar in sami na rufin asiri, amma ni da kaina na saka rakennan a gaba na shanye kayana, wanda na sayar kuma na cinye kudin, shi ma dai ban ci nasara ba.
.
Bayan na qara wasu 'yan shekaru sai na fahimci da a ce na sauko da kaina qasa na bi dayan abokaina da yake dayan sana'o'in da na yi dinnan, na koyi aikin sosai, na kuma san yadda zan yi manejin rayuwa qila da hakan bai faru ba, amma duk da haka na gode wa Allah, domin na yi karatun rayuwa, wajen fadi tashina na sami wurin da na maqale har na kawo matsayin da nake ciki yanzu, akwai wani yaro da ya yi rayuwa kusan irin tawa amma ya fi ni natsuwa, ban san sana'o'in da ya yi a baya ba, amma na fara ganinsa da 'yan faya-fayen bidiyo na wasan Hausa yana yawo da shi, da yake yana samun ciniki a kasuwar unguwarmu sai ya yi wani dan shago dan mitsili wanda ko shi bai iya shiga, sai dai ya jera faya-fayen in za a saya ya ciro wa mutum ya ba shi.
.
A hankali ya fara kawo man shafawa da 'yan turarurrukan mata yana sayarwa, maganar da muke yi, ya kama shago a daya hannun ya maqare shi da nau'ukan turare, yana kan hanyar nasara, akwai wata mata da na san ta auri wani mutum, mu a waje muna kallon soyayyar da suke sha kuma tsuna burge mu, amma a cikin gida auren na lilo yana qoqarin balgacewa, ba abinda ta rasa na ci da sha da sutura, kudi kuma sai dai ta ba wasu, komai take so gashinan, sai dai tana da matsalar shimfida, 'yan uwanta ba su ganin wannan wani abu ne, na ce ita ce da kanta za ta fara nemo wa kanta hanyar nasara.

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

WaΖ™ar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waΖ™e ak...

Contact form