Barka da warhaka

HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 28

*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 28```
.
DA WA KAKE MA'AMALLA?
Idan ka ce ba za ka yi ma'amalla da wane ba to qila ka yi da shi ne a baya ba ka ji dadi ba, ma'ana dole yanzu a kiyaye, ka qaru da ilimi kenan, ba a cewa ba za a yi ma'amalla da mutum ba sai in an yi a baya ba a ji dadi ba, haduwa da mutane mabambanta hanya ce mafi sauqi da za ta qara maka ilimi wurin isa ga inda kake so, in mutum mahauci ne, yana da kyau ya san komai game da kiwon dabbobi, wannan kuma sai a wurin fulani, ta hanyarsu zai san dabbobin da suke da lafiya, da masu kitse ba naman kirki, da lokacin da ya kamata a sayi dabba ko lokacin da bai kamata a yanka nau'i kaza ba.
.
Yana da kyau kuma ya yi mu'amalla da Majema, domin zai riqa sayar musu da fata, tanan ne zai san irin fatun da suke buqata, da kudinsu, da lokacin da aka fi buqatar fatun, zai yi mu'amalla da Yarbawa kasancewarsu ma'abota ganda, suna sayen fatu da yawa su je su gyara suka riqa sayarwa, har ila yau zai yi mu'amalla da masu sana'ar sayar da gasasshen nama, wannan a matsayin misali ne, duk wani mai sana'a za ka taras akwai mutanen dake kewaye da shi wadanda yake amfani da su wurin aiwatar da aikinsa daidai, koda kuwa ma'aikatan gwamnati ne, za ka taras akwai kyakkyawar alaqa ta aiki tsakanin ma'aika kaza da kaza.
.
Ba abin mamaki ba ne ka ga ma'aikatar haraji tana mu'amalla da jami'an tsaro, masamman masu fararen kaya don tabbatar da kowa ya bi doka da oda wajen biyan harajin, idan wasu suka gano cewa ma'aikata kaza ba ta ba da haraji akwai wadanda za su yi bincike mai zurfin gaske a kansu, in an kawo su gaban quliya suka yi biyayya shikenan, to haka ma mutum a qashin kansa da yake neman aure, yana so ya yi nasara a cikin aikinnan, mata wato maqwabtan yarinyan za su taimaka, samarin dake kusa da ita, malaman dake koyar da ita a boko da islmaiyya da wurin sana'anta, in mai yi ce, duk za su iya ba ka abinda kake nema, kenan haduwa da wasu a gefe babban ginshiqi ne da zai taimake ka wajen cika burin ka.
.
Mutumin da yake son ya gwanance kuma ya ci nasara a aikinsa na likitanci yana da buqatar sanin injiniyoyi, kafintoci, ma'aikatan wutar lantarki, malaman makaranta, likitoci da sauransu, duk mutanennan za su amfane shi, injiniyoyin za su nuna masa irin ginin da yake buqata da yadda zai yi ginin ya dauki majinyata da dama a dan wuri kadan, qila a rushe tsohon ginin a sake wani da tsari mai kyau, malaman makaranta za su riqa turo dalibansu bisa wani alqawari ko yarjejeniya da za a yi ta rage kudin, da masu shagunan gwajin jini ko daukar hoton jikin mutum, ba nau'in mutanen da ma'aikaci ba zai amfana da su ba.
.
.
A duk lokacin da ka fara ma'amalla da wasu mutane dole ka koyi wasu abubuwa daga wurinsu, ko dai ka dauki ilimi ko darasi, in Allah ya sa ka yi dace da abinda kake so a wurinsa ka sami ilimi kenan, sai ka natsu ka koyi abubuwa da dama a wurinsa, in kuma akasin haka ne za ka dauki darasi sai ka san yadda za ka guje wa irinsa, ko ya aka yi dai mu'amalla da mabambantan mutane za ta taimaka wa mutum a harkokinsa na yau da kullum.
.
KA SAN MAHIMMANCINKA
Tabbas mun bambanta a rayuwarmu dabi'ummu da ma yadda muka dauki kammu, wannan ya sa wani yake jin cewa ba zai iya hada inuwa da wane ba don shi talaka ne, ko ba zai iya zama da wannan ba don shi mai arziqi ne, har ka ga wani ya shigo dakinka yana qoqarin zama a qasa, sai ka yi tsayuwar daka kafin ya yarda ya zauna a kan kujera, a ganinsa bai kai wannan matsayin ba, to rashin adalcinmu a yau duk matsayin da ka ba wa kanka haka wasu za su dauke ka, mun karanta cewa kowa a ofis dinsa shi ne babba don wurin aikinsa ne, in mai kudi ya kira ka faskare anan kai ne babba in ba ka yi masa ba ba zai iya yin abinda yake buqata ba, amma saboda rashin tsari irin namu ba ma fahimtar hakan.
.
Sai mu dauka tunda muna da kudi sai yadda muke so, in mutum ya ga ba zai yi ba mu canja shi mu kawo wani, muna sane da cewa in makewayin Alhaji ya cika ba zai fito ya tube riga ya kware matsuguninsa ya fara yasa ba, ba zai iya wannan aikin ba, sai dai ya nemo gwanaye a fannin, to idan su ma suna neman kudinka kai ma fa kana neman hidimarsu, kuma kai ka fara buqatarsu kamata ya yi ka ba su wannan girman, anan mun sami matsala ta rashin girmama juna, in mutum ya hau motarka sai ya riqa ji kamar ta gidansu, don zai ba ka kudi, ya manta cewa za ka yi masa hidima, in ya zo shagonka sai ya fado maka duk abinda ya ga dama don zai fidda kudinsa, shi ma fa zai karbi kayanka ya tafi da shi, yanzu an kai ko ofishin 'yan sanda mutum ya shiga in dai mai kudi ne sai ka dauka ba mai laifi ba ne, hankalinsa a kwance.
.
Tunda duniyar ta juya kai ma'aikaci ko mai sana'a ka lallaba kayanka, ban ce ka qasqanta kanka ba, in akwai halin da za ka lalla ba mutum kuma ka jawo hankalinsa a kaikaice zan so ka yi, shi kyakkyawan hali ko mugu yana son sa, matuqar za ka girmama kanka wasu ma za su girmama ka, sai in ka hadu da irin wadancan mutanen sai ka mu'amalance su ta wata fuskar amma kar ka yarda ka yi asararsu, akwai wani mai shago in na zo siyan kayan da ba shi da shi zai bar shagonsa ya sayo min a duk inda zai samu, wani sa'in ko ba ni da kudi zai yi amfani da nasa ya sayo min in na samu in mayar masa, ba fa yaron gidana ba ne ba a kamfanina yake aiki ba, wannan ya sa ba zai yuwu na sayi wani abu a wurin wani ba matuqar yana da shi.


Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

WaΖ™ar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waΖ™e ak...

Contact form