Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KARAN ARJUN

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KARAN ARJUN

Shekarar Fita - 1995 


• Paison ke mamle mein main pehdaishi kamina hoon ... dosti aur dushmani ka kya, apno ka khoon bhi pani ki tarah baha deta hoon

Idan ana batun kuɗi to ni cikakken ɗan ƙwal uba ne... Bar ta abokai ma, jinin mutanena ma zubar da shi nake yi kamar ruwa. 

Amrish Puri 

• Main toh budhi ho gayi, meri aankhen kamzor ho gayi ... lekin mera vishvas kamzor nahi hua

Na tsufa, idanuwana sun yi rauni... Amma imanina bai yi rauni ba. 

Rakhee Gulzar

• Main toh samajhta tha ki duniya mein mujhse badkar kamina aur koi nahi hai ... lekin tumne end mauke par aaisa kaminapan dikhaya hai ... ki hum tumhare kaminepan ke ghulam ho gaye hai

A da ina tunanin ni ne babban ɗan iska a duniya... Amma a ƙarshe kun nuna min yadda iskanci yake... Ta yadda har ma na zama bawanku a iskanci. 

Amrish Puri 

• Hum khandani Thakur hai ... hamari ragon mein khoon ke saath saath zid aur ahankaar bhi daudta hai

Ni shugaba ne daga babban ahali... Haɗe da jini, kangara da izza ce ke gudana a cikin jijiyoyina. 

Amrish Puri 

• Bhavnao ki chot jab dil par lagti hai ... toh nafrat ki jwala badakh uthti hai

Yayin da aka baƙantawa mutum... Wutar ƙiyayya ke ruruwa. 

Rakhee Gulzar

• Kiss gaalon pe nahi ... hoton pe kiya jata hai

Ba a kumatu ake sumba ba... A laɓɓa ake yi. 

Shah Rukh Khan

• Tere saare khandaan ki maut ... mere haath ki lakeeron mein likhi hai

Mutuwar ahalinku gaba ɗaya... Rubuce yake a layukan tafin hannuwana. 

Amrish Puri 

• Zindagi mein joh hota hai woh socha nahi hota ... aur joh socha jata hai woh kabhi hota nahi ... aur joh kabhi nahi hota, woh kabhi kabhi ho jata hai

A rayuwa abin da ke faruwa ba shi ake tunani... Kuma abin duk da aka yi tunani ba ya taɓa faruwa... Kuma abin da bai taɓa faruwa ba, wani lokacin shi ke faruwa. 

Kajol 

• Bhudhape mein jism bekaar ho jaate hai ... lekin tune toh apni zindagi hi bekaar kar di

A yayin tsufa jiki kan zama maras amfani... Amma ke rayuwarki kika mayar maras amfani. 

Amrish Puri

• Mere bete aayenge, mere Karan Arjun aayenge ... zameen ki chaati phad ke aayenge, aasman ka seena cheer ke aayenge

Yarana za su zo, Karan da Arjun ɗina za su zo... Za su keta ƙirjin ƙasa su zo, za su keta ƙirjin samaniya su zo. 

Rakhee Gulzar

• Hamare ghar ki bahu betiyan jab kabhi beizzati ke daldal mein kadam rakhti hai ... toh hum unhe haveli ki char deewari mein zinda chunwa dete hai

A duk lokacin da 'ya'ya mata ko surikai mata suka tafka abin kunya a ahalinmu... Binne su muke yi da ransu a ƙusurwoyi huɗun gidan. 

Amrish Puri 

• Waqt ka marham ... zindagi ke har zakhm ko bhar deta hai

Lokaci shi ne maganin da... Ke cike kowane gurbin ciwo. 

Rakhee Gulzar

• Mere dushmano ko sar chupane ke liye jagah dene waalon ... main tumhari chittaon ko jalne ke liye jagah nahi doonga

Ku da ke ba maƙiyana wurin zama... Ni ko ƙaburburanku ba zan ba wurin ƙonawa ba. 

Amrish Puri 

• Marte insaan ki antim ichcha poori karna ... is sansar ka sabse bada punya hove hai

Cika burin mamaci... Shi ne nagarta mafi girma a duniyar nan. 

Ashok Saraf

• Daulat se insaan keemti bistar khareed sakta hai, magar neend nahi khareed sakta ... daulat se insaan roti khareed sakta hai, magar bhook nahi ... daulat se insaan jism khareed sakta hai, magar sacha pyar nahi khareed sakta

Mutum na iya siyan gado mai tsada in yana da kuɗi, amma ba zai iya siyan bacci ba... Mutum na iya siyan biredi in yana da kuɗi, amma ba zai iya siyan yunwa ba... Mutum na iya siyan jiki idan yana da kuɗi, amma ba zai iya siyan soyayyar gaskiya ba. 

Kajol 

• Apne raaste se kaanto ko hata dena aur dushmano ko mita dena ... hamare khandan ki parampara hai

Kawar da ƙayoyin hanyar mu da kuma kau da maƙiyanmu... Waɗannan su ne al'adun gidanmu. 

Amrish Puri 

• Aaisi maut maroonga is kamine ko ... ki bhagwan yeh punar janam waala system hi khatam kar dega

Zan kashe wannan ɗan iskan ta yadda... Ubangiji ma da kansa zai daƙile wannan tsarin na sake haihuwar mutum. 

Amrish Puri 

• Pyar mein jab tak maut se na khelo ... milne waali zindagi ka mazaa nahi aata

Matuƙar ba ka yi wasa da mutuwa ba a soyayya... To babu wani jin daɗi a rayuwar da ka samu. 

Shah Rukh Khan 

• Daayan haath jeb mein rakh lo seth ... varna zindagi bhar aapko baayen haath se khana, khana padega

Bar hannunka a cikin aljihu... Ko kuma ka koma cin abinci da hagu har tsawon rayuwarka. 

Salman Khan 

• Khoon ki Holi khelne waale, aaj main dekhti hoon ... khoon kiska behta hai aur laashein kiski girti hai

Ka yi bikin Holi da jini, amma yau zan gani... Jinin waye zai zuba kuma gangar jikin waye za ta faɗi. 

Rakhee Gulzar

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FASSARAR WAƘAR TERA HUA

FASSARAR WAƘAR TERA HUA


• Waƙa - Tera Hua

• Shiri - Loveratri

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2018

• Sauti - Tanishk Bagchi

• Rubutawa - Manoj Muntashir

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Atif Aslam

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 

Mmm… Hmm… O…

• Tere Qareeb Aa Raha Hoon

Ina matsowa kusa da ke. 

• Khud Se Main Door Jaa Raha Hoon

Kuma ina matsawa nesa da kaina. 

• Yeh Bewajah Toh Nahi Hai

Hakan yana faru ne bisa dalilin... 

• Tu Jo Mila…

Haɗuwarki da ni. 

• Dheere Dheere Se Tera Hua

A hankali A hankali na zamo naki. 

• Haule Haule Se Tera Hua

Da sannu da sannu na zamo naki. 

• Rafta Rafta Tera Hua

Da kaɗan da kaɗan na zamo naki. 

• Tere Bin Main Hoon Be Nishaan…

Ni ba komai bane idan babu ke. 

• Dheere Dheere Se Tera Hua

A hankali A hankali na zamo naki. 

• Haule Haule Se Tera Hua

Da sannu da sannu na zamo naki. 

• Rafta Rafta Tera Hua

Da kaɗan da kaɗan na zamo naki. 

• Tere Bin Main Hoon Be Nishaan…

Ni ba komai bane idan babu ke. 

O O O O… O O O O…

• Samjho Zara Samjho Ishaara

Ki ƙoƙarta ki fahimci alamomin. 

• Tera Hoon Main Saara Ka Saara

Ni naki ne gaba ɗaya (na) 

• Jaise Mujhe Tumse Hua Hai

Irin son da nake yi miki. 

• Yeh Pyaar Na Hoga Dobara

Irin wannan son ba zai ƙara faruwa ba. 

• Dil Mein Teri Jo Jagah Hai

Irin wuri na musamman da kike da shi a zuciyata. 

• Uski Koi Toh Wajah Hai

Yana nan ne bisa wani dalili. 

• Yeh Bewajah Toh Nahi Hai

Hakan yana faru ne bisa dalilin... 

• Tu Jo Mila…

Haɗuwarki da ni. 

• Dheere Dheere Se Tera Hua

A hankali A hankali na zamo naki. 

• Haule Haule Se Tera Hua

Da sannu da sannu na zamo naki. 

• Rafta Rafta Tera Hua

Da kaɗan da kaɗan na zamo naki. 

• Tere Bin Main Hoon Be Nishaan…

Ni ba komai bane idan babu ke. 

• Dheere... Dheere... Dheere Dheere Se…

A hankali A hankali A hankali. 

• Dheere Dheere Se Tera Hua

A hankali A hankali na zamo naki. 

• Haule Haule Se Tera Hua

Da sannu da sannu na zamo naki. ©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

Fassarar Waƙar Tu Hi Toh Hai

FASSARAR WAƘAR TU HI TOH HAI 


🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

• Waƙa - Tu Hi Toh Hai

• Shiri - Holiday

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2014

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Irshad Kamil

• Kamfani Zee Music Company 

• Rerawa - Benny Dayal

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman


• Awaaragi, Karta Hoon, Par Main Aawara Nahi

Na kan yi hauka, amma ni ba mahaukaci bane. 

• Chhoda Khulla, Dil Ko Magar, Khudko Bigaada Nahi

Na bai wa zuciyata cikakken 'yanci, amma ban sangartata ba. 

• Aisa Lage, Tere Bina, Ab Toh Guzaara Nahi

Da alama abu ne mai wahala in tafiyar da wani lokaci ba tare da ke ba. 

• Kisika Bhi, Honga Na Main, Hua Jo Tumhara Nahi

Ba zan kasance tare da kowa ba in ba ke ba. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Zinda Hoon Tujhpe Marke

Ina raye ne saboda ina mutuwa akanki. 

• Bhoola Sab Kuch Tujhko Padhke

Na manta komai tun daga lokacin da na karanta zuciyarki. 

• Kaise Hai Pyaar Tera Haan…

Kalli yadda na zama a soyayyarki... 

• Jo Meri Khwahishein Tujhi Se Hi Lipat Gayi

Muradaina sun amshe ki. 

• Kyun Meri Duniya Tujhi Mein Hai Simat Gayi

Yanzu duniyata a kulle take da ke. 

• Na Jaane Kaise Ghatnayein Hai Yeh Ghat Gayi

Bansan ta yaya waɗannan abubuwan suka faru ba. 

• Main Fida Hoon Tujh Par

Na yi hauka sosai a kanki. 

• Jo Saari Baaziyaan Khayalon Ki Ulat Gayi

Duk cacar da ke kaina sun juye. 

• Kyun Meri Chaahatein Tujhi Pe Mar Mit Gayi

Na sallamar da soyayyata kaf a kanki. 

• Na Jaane Kaise Ghatnayein Hai Yeh Ghat Gayi

Bansan ta yaya waɗannan abubuwan suka faru ba. 

• Main Fida Hoon Tujh Par

Na yi hauka sosai a kanki. 

• Naaraazgi, Teri Ada…

Yawan fushi shi ne salon ki... 

• Pyaari Lagi, Teri Ada…

Salon naki ma na ga abin so ne. 

• Hai Saadgi, Teri Ada…

Sauƙin kai shi ne salon ki... 

• Yeh Jaadu Hai Kaise Tera

Wane irin sihiri ne ke tattare da ke haka? 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Main Ana Tere Aage Dekho Dil Haara Hoon

Kalli, na rasa zuciyata a gabanki. 

• Main Ana Jaise Bhi Hoon Jo Bhi Hoon Tumhara Hoon

Koma menene ni, ni kawai naki ne. 

• Jo Teri Chaahatein Samete Woh Kinara Hoon

Ni be gaɓar nan da ke karɓar soyayyar ki. 

• Kaise Main Yeh Kahoon

Ta yaya zan iya bayyana miki hakan duka? 

• Main Ana Tere Liye Zameen Pe Utaara Hoon

Saboda ke ce kawai na faɗo duniya. 

• Main Teri Bholi Bhaali Aankhon Ka Ishaara Hoon

Ni ne alamar da idanuwanki ke bayarwa. 

• Jo Teri Chaahatein Samete Woh Kinara Hoon

Ni be gaɓar nan da ke karɓar soyayyar ki. 

• Kaise Main Yeh Kahoon

Ta yaya zan iya bayyana miki hakan duka? 

• Tu Paas Bhi, Zara Zara…

Kina kusa da ni, kaɗan. 

• Tu Pyaas Bhi, Zara Zara…

Ke ce ƙishirwata, kaɗan. 

• Tu Raaz Bhi, Zara Zara…

Ke ce sirrina, kaɗan. 

• Main Ho Gaya Hoon Tera

Na zamo naki. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Zinda Hoon Tujhpe Marke

Ina raye ne saboda ina mutuwa akanki. 

• Bhoola Sab Kuch Tujhko Padhke

Na manta komai tun daga lokacin da na karanta zuciyarki. 

• Kaise Hai Pyaar Tera Haan…

Kalli yadda na zama a soyayyarki... 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫


Share:

Fassarar Waƙar Hum Tum Se na kuchFassarar Waƙar Hum Tumse Na Kuchh


• Waƙa - Hum Tumse Na Kuchh

• Shiri - Ziddi

• Harshe - Hindi - Hausa 

• Shekarar Fita - 1997 

• Sauti - Dilip Sen, Sameer Sen

• Rubutawa - Sameer

• Kamfani - Saregama

• Rerawa - Hariharan, Krishnan Nair Shantakumari Chitra (K.S. Chitra)

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 

Aaa…. Aaa…

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kema kin kasa faɗa min komai. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kema kin kasa faɗa min komai. 

• Lagta Hai Darr Yeh, Baat Ye Dil Ki, Dil Mein Na Reh Jaaye…

Ina tsoron kada abin da ke zuciyata ya kasance a cikinta har abada. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa maka komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kai ma ka kasa faɗa min komai. 

• Lagta Hai Darr Yeh, Baat Ye Dil Ki, Dil Mein Na Reh Jaaye…

Ina tsoron kada abin da ke zuciyata ya kasance a cikinta har abada. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kai ma ka kasa faɗa min komai. 

• Tum Suno Gaur Se Kya Keh Raha Hai Samaa

Ki saurara da kyau ki ji abinda yanayi ke cewa. 

• Humnashi Chhed Do Chaahat Bhari Dastaan…

Ya kyakkywa, fara taɗin so. 

• Kitne Dinon Tak, Kuchh Na Bataaye, Tum Humko Tadpaaye

Tsawon kwanaki ba ka ce min komai ba kana azabtar da ni. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kai ma ka kasa faɗa min komai. 

• Pyaar Kya Hai Sanam Tum Humko Samjha Gaye

Masoyiyata, ke ce kika fahimtar da ni haƙiƙanin menene so. 

• Faasle Na Rahe Itne Kareeb Aa Gaye…

Ka kusanta da ni ta yadda babu sauran tazarar da ta rage. 

• Dekho Humari, Khushboo Tumhari, Saanson Ko Mehkaaye

Kalli, ƙamshi na yana ƙamsasa numfashinka. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kai ma ka kasa faɗa min komai. 
 
• Raat Bhar Jaagkar Karwat Badalte They Hum

A farke nake ina ta juye-juye na kasa bacci tsawon dare. 

• Kya Kahein Kis Tarah Dilbar Machalte They Hum…

Ta yaya zan iya bayyana maka irin azabtuwar da nake jurewa? 

• Kaise Batayein, Tanha Akele, Hum Kitna Ghabraaye

Ta yaya zan iya bayyana maka irin tsoron da nake ji idan na kaɗaice? 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kema kin kasa faɗa min komai. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa maka komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kai ma ka kasa faɗa min komai. 

• Lagta Hai Darr Yeh, Baat Ye Dil Ki, Dil Mein Na Reh Jaaye…

Ina tsoron kada abin da ke zuciyata ya kasance a cikinta har abada. 

• Hum Tumse Na Kuch Keh Paaye

Na kasa faɗa miki komai. 

• Tum Humse Na Kuch Keh Paaye

Kai ma ka kasa faɗa min komai. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

SHARHIN FIM ƊIN BHAIRAVA


SHARHIN FIM ƊIN BHAIRAVA 


Bairavaa fim ɗin Indiya ne da aka fitar a shekara ta 2017 cikin harshen Tamil. Bayan an fara ɗaukar shirin a farkon shekara ta 2016, an ci gaba da aikin shirin a ƙarƙashin suna Vijay 60, inda daga baya aka canza masa suna zuwa Bairavaa a cikin watan Satumbar 2016. An saki fim ɗin a duniya baki ɗaya a ranar 12 ga watan Yuli 2017. Sai da aka yi kwanaki 50 cif ana kallon shirin a gidajen kallo bayan fitarsa kuma ya taɓuka abin a zo a gani ma a harkar kasuwancinsa. 

• Bada Umurni - Bharathan

• Ɗaukar Nauyi - B. Venkatarama Reddy

• Labari/Rubutawa - Bharathan

• Sauti - Santhosh Narayanan

• Horas Da 'Yan Wasa - M. Sukumar

• Tacewa - Praveen K. L.

• Kamfanin Da Ya Shirya - 
Vijaya Productions

• Kamfanin Da Ya yi Dillanci - 
Sri Green Productions

• Ranar Fita - 12 January 2017

• Tsayin Shirin - Mintuna 169

• Ƙasa - India

• Harshe - Tamil

• Kasuwancin Box office - ₹114 crore

Bairavaa wani jami'in karɓar haraji ne a bankin ICCI da ke garin Chennai. Mutum ne mai gaskiya wanda a shirye yake ya yi amfani da kowace hanya wajen amso kuɗaden da masu karɓar bashi suka amsa. 

Watarana ana bikin 'yar manajansa sai ya haɗu da Malarvizhi wacce ita kuma ɗalibar kiwon lafiya ce daga garin Kallidaikurichi da ke yankin Tirunelveli kuma nan take ya kamu da son ta. Yayin da ya je madakatar Koyambedu domin ya bayyana mata soyayyarsa kafin ta bar Chennai, sai ya ga wasu gungun 'yan daba sun kewaye ta da nufin za su kashe ta saboda suna zargin tana da sa hannu akan harin da aka kai wa ɗan gidan Minista Charan. Ana cikin haka, sai suka fasa kashe ta sakamakon kiran da suka samu daga PK cewa kada su taɓa ta. Hakan ya sa Bhairava ya tambayi Malar abin da ke faruwa in da ita kuma ta zayyane masa komai. 

Malar tana karatu ne a makarantar PK Medical College da ke Tirunelveli, to shugaban makarantar wato PK wani babban ɗan daba ne kuma ɗan siyasa a lokaci guda. Shi da na hannun damarsa Kottai Veeran suna aikin daba da siyasa tare. To ita wannan makaranta babu kayan aiki a cikinta, gininta ba mai nagarta bane kuma babu isassun ma'aikata da likitoci. Wannan ya sa Malar da ƙawarta Vaishali suka shigar da ƙorafi wa MCI, in da shi kuma ya sha alwashin saka makarantar a baƙin littafi bayan ya ga matsalar da idonsa. To amma PK saboda ya kare mutuncinsa sai ya haɗa baki da wasu jami'an MCI akan su soke takardar dakatarwa da aka zana, shi kuma zai basu damar yin lalata da ɗaya daga cikin 'yan matan makarantar. 

Bisa tsautsayi kuwa sai aka zaɓi Vaishali, in da washegari sai tsintar gawarta aka yi bayan an mata fyaɗe. Mahaifin Malar wani ɗan sanda ne mai gaskiya, hakan ya sa ya fara bincike akan alaƙar da ke tsakanin PK da mutuwar Vaishali, amma sai PK ya kashe shi shima. Bayan mutuwar mahaifinta sai Malar ta kai PK ƙara kotu in da alƙali ya yanke hukuncin cewa kada a kore ta daga makaranta kuma kada wani abu ya sameta har sai an kammala wannan shari'a. Ko da yake PK ya yarda da wannan hukuncin, sai ya dinga kai wa Malar farmaki ta hanyar malaman makarantar da kuma yanke lantarki da wutar da ke yankinta kuma ya sha alwashin da zarar an gama shari'ar ya samu nasara zai kashe ta. 

 To a wajen ɗaurin auren ne Malar ta miƙa bidiyon da ke ƙunshe da hujjojin mutuwar Vaishali ga Charan, akan cewa tun da shi ɗan gidan Minista ne zai iya taimakawa a binciki bidiyon. Amma sai PK ya aika yaransa suka ƙwace bidiyon kuma suka maƙala wa Malar laifin. Da Bairavaa ya ji wannan labari, sai ya yanke shawarar zai taimake ta don haka ya bi ta suka tafi Kallidaikurichi tare. 

Ta hanyar basaja a matsayin mai karɓar haraji Bairavaa ya shiga gidan PK ya yi bincike har ya samo hujjojin da yake buƙata. Ba a jima ba kuwa sai PK ya fahimci cewa Bairavaa fa so yake ya ga bayansa, hakan ya sa aka fara tata-burza a tsakaninsu in da daga ƙarshe dai PK ya samu nasarar karɓe hujjojin ya kuma lalata su. Ko da yake Bhairava ya rasa hujjojin, ya yi ƙoƙarin samun ƙarin kwanaki biyar kafin a kulle shari'ar 

To ana cikin haka ne kuma sai matar Kottai Veeran ta mutu, don haka sai Bairavaa ya yi amfani da son da Kottai Veeran ke yi wa matarsa domin gabatar da shi a matsayin shaida akan shari'ar da ake yi. Shi ne sai ya canja wa PK robar shaƙar iskarsa da sinadarin nitrous oxide. PK shi kuma ya shaƙa ba tare da ya sani ba kafin ya je bikin janazar matar Kottai Veeran. Hakan ya sa shi dariyar babu gaira babu dalili har aka gama janzar, hakan ta sa shi kuma Kottai ya fusata ya juya masa baya kuma ya karɓi yayin Bhairava na zan bada shaida a kotu. Saboda jin haushin abin da ya yi mai, sai PK ya tari Kottai Veeran inda suka gwabza har ya kashe shi. 

Daga nan sai Bairavaa ya yanke hukuncin kashe PK kawai kowa ya huta saboda ta haka ne kawai zai iya rama wa Malar da Vaishali abin da aka yi musu. Don haka sai ya ƙala wa PK sharrin cewa yana shirin kashe Firimiyan India yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kudankulam domin dasa aikin wani makami mai linzami. Ai kuwa nan take labari ya watsu a gari har ta kai an bada izinin da an ga PK kawai a harbe shi. Da dai PK ya ga an rutsa shi, sai ya yi nufin ya kashe Bhairava amma sai bai yi nasara ba. Daga nan kuma sai Bhairava ya yi shiga irin ta kwamandawan NSG ya sace da na gaskiyar waɗanda suka zo kashe PK. 

A ƙarshe dai an bayyana cewa Malar ce ke da gaskiya, an kama yaran PK an kulle sannan aka kwashe ɗaliban PK Medical College akai kai su wata kwalejin. 

Ko da yake Bairavaa yana goyon bayan gina makarantun kuɗi, ya ce abu ne mai muhimmanci a shugaban wannan wuri ya zama mai gaskiya kuma nagartacce domin ya tabbatar da tsaron lafiyar ɗalibai da kuma samun ingantaccen ilimi. 

Jaruman Shirin 

• Vijay - Bairavaa

• Keerthy Suresh - Malarvizhi

• Jagapathi Babu - Periyakannu/ PK

• Daniel Balaji - Kottai Veeran

• Sathish - Shanmugam

• Thambi Ramaiah - Narayanan

• Mime Gopi - Karuvadu Kumar

• Sija Rose - Poongodi

• Harish Uthaman - Prabha

• Aparna Vinod - Vaishali

• Papri Ghosh - Shailaja Venkatesan

• Sriman 

• Aadukalam Naren 

• Sharath Lohitashwa - Union Minister

• Roshan Basheer - Charan

• Rajendran - M. Rajendran

• Y. G. Mahendran - R. Venkatesan

• Vijayaraghavan 

• Seema G. Nair 

• G. Marimuthu - Pandurangan

• Malavika Avinash - Judge

• Charles Vinoth - MLA

• Shanmugarajan 

• Sugunthan 

• Vishalini 

• Vittal Rao 

• Subhashini 

• Baby Monika Siva 

• Thavasi Raj 

• Rajee Vijay Sarathy - Mrs. Venkatesh

• Abhirami 

• Ananya 

• Santhosh 

• Vaishali 

• Osthi Ramu 

• Besant Ravi - special appearance

• Dinesh special appearance 

• Thangamani Prabhu - Medical College Investigation Officer

Waƙoƙin Shirin 


1. "Pattaya Kelappu" 
2. "Nilaayo" Vairamuthu 
3. "Pa Pa" 
4. "Azhagiya Soodana Poovey" 
5. "Varlaam Vaarlam Vaa Bairavaa" 
 
©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR WAƘAR TUM HI AANA


Fassarar Waƙar Tum Hi Aana


• Waƙa - Tum Hi Aana

• Shiri - Marjaavaan

• Harshe - Hindi - Hausa 

• Shekarar Fita - 2019

• Sauti - Payal Dev

• Rubutawa - Kunaal Vermaa

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Jubin Nautiyal

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Tere Jaane Ka Gham, Aur Na Aane Ka Gham

Raɗaɗin tafiyarki, Raɗaɗin rashin dawowarki. 

• Phir Zamaane Ka Gham Kya Karein

Da kuma ƙarin raɗaɗin wannan duniyar, me ya zan yi? 

• Raah Dekhe Nazar, Raat Bhar Jaag Kar

Idanuwana sun kafe suna jiranki tsawon dare. 

• Par Teri Toh Khabar Na Mile

Amma duk da haka ban samu wani bayani akan ki ba. 

• Bahut Aayi Gayi Yaadein

Tunanuka da dama sun zo sun wuce. 

• Magar Iss Baar, Tum Hi Aana

Amma a wannan lokacin, ke kaɗai nake so ki dawo. 

• Irade Phir Se Jaane Ke Nahi Laana

Kada ki zo da niyyar da za ki tafi ki bari. 

• Tum Hi Aana

Ina so ki zo. 

• Meri Dehleez Se Hokar, Baharein Jab Guzarti Hai

Duk lokacin da bazara ta wuce ta ƙofa ta. 

• Yahaan Kya Dhoop Kya Saawan, Hawayein Bhi Barasti Hain

Babu iska, babu damina, iskokin ma kansu shawa suke komawa a nan. 

• Humein Poocho Kya Hota Hai

Tambaye ni yadda ake ji (idan) 

• Bina Dil Ke Jiye Jaana
(Aka) Rayu ba tare da zuciya ba.

• Bahut Aayi Gayi Yaadein

Tunanuka da dama sun zo sun wuce. 

• Magar Iss Baar, Tum Hi Aana

Amma a wannan lokacin, ke kaɗai nake so ki dawo. 

Ho... Ooo... Ooo...

• Koi Toh Raah Woh Hogi, Jo Mere Ghar Ko Aati Hai

Ba Za a rasa hanya ta zuwa gidana ba. 

• Karo Peecha Sadaaon Ka, Suno Kya Kehna Chaahti Hai

Ki saurari kiran zuciyata ki ji abin da take cewa. 

• Tum Aaoge Mujhe Milne
That You will come to meet me

• Khabar Yeh Bhi Tumhi Laana
I want You Yourself to bring me this news

• Bahut Aayi Gayi Yaadein
So many memories have come and gone

• Magar Iss Baar, Tum Hi Aana
But this time, I want You to come

• Marjaavaan, Marjaavaan
I am ready to die(for You/for Your love), I am ready to die

 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR TUJH MEIN RAB DIKHTA HAI FEMALE

FASSARAR WAƘAR TUJHE MEIN RABB DIKHTA HAI (FEMALE) 

• Waƙa - Tujh Mein Rab Dikhta Hai (Female)

• Rab Ne Bana Di Jodi

• Harshe - Hausa = Hindi 

• Shekarar Fita 2008

• Sauti - Salim-Sulaiman

• Rubutawa - Jaideep Sahni

• Kamfani - Yash Raj Music

• Rerawa - Shreya Ghoshal 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Na Kuch Poocha

Ba ka tambayi komai ba. 

• Na Kuch Maanga

Ba ka ce a yi /in yi maka komai ba. 

• Tune Dil Se Diya Jo Diya 

Duk abin da ka yi ka yi shi ne daga zuciyarka (da zuciya ɗaya) 

• Na Kuch Bola

Ba ka ce komai ba. 

• Na Kuch Tola

Ba ka duba komai da komai ba. 

• Muskuraake Diya Jo Diya

Duk abin da za ka bada kana ba da shi ne da murmushi. 

• Tu Hi Dhoop Tu Hi Chaaon

Kai ɗumi ne, kai Inuwa ce. 

• Tu Hi Apna Paraya

Kai nawa ne kuma kai baƙo na ne. 

• Aur Kuch Na Janoon Main, Bas Itna Hi Janoon

Ba lallai in san abubuwa sosai ba, amma na san cewa... 

• Tujh Mein Rab Dikhta Hai

Ina ganin ubangiji a tare da kai. 

• Yaara Main Kya Karoon

Masoyina, me ya kamata na yi?

• Sajde Sar Jhukta Hain

Na sunkuyar da kaina zuwa gareka. 

• Yaara Main Kya Karoon

Masoyina, me ya kamata na yi?

• Tujh Mein Rab Dikhta Hai

Ina ganin ubangiji a tare da kai. 

• Yaara Main Kya Karoon

Masoyina, me ya kamata na yi?


• Rab Ne Bana Di Jodi Haaye…

Ubangiji ne ya haɗa waɗannan ma'auratan. 

 ©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN SULTAN

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN SULTAN

• Shekarar Fita - 2016


• Asli wrestler woh nahi hota joh medal uthaye ... asli wrestler woh hota hai joh zindagi se lade aur usse haraye

Ɗan kokawa na asali ba shi ne wanda ya ɗaga lambar yabo ba... Ɗan kokawa na asali shi ne wanda yake faɗa da rayuwarsa kuma ya yi nasara a kanta. 

Salman Khan 

• Izzat aur guroor mein dhaage bhar ka pharak hove hai

Banbancin da ke tsakanin girmamawa da kuma girman kai ba shi da kauri kamar zare. 

Anushka Sharma

• Hindustan apno ka, rishton ka, mitti ki value ka desh hai

India ƙasa ce ta waɗanda kake so, waɗanda kake mu'amala da su kuma darajar ƙasarka ce. 

Parikshat Sahni

• Manne lage hai ki angrezi mein ladki jaldi pate hai ... I love you bolo aur uske baad seedha kiss hove hai

Ina jin cewa budurwa ta fi saurin faɗawa da wuri idan ka yi mata turanci... Kawai ka ce mata I love you nan take sai sumba ta biyo baya. 

Salman Khan 

• Maine usse ladte huye dekha hai ... uske zor mein hosh hai aur hosh mein josh hai ... jeetna uska shauk nahi, uski aadat hai ... aur harana uski aadat nahi, uska hunar hai ... uski aankh mein bijli aur baazu mein dum hai ... uska ek daav, dus ke barabar hai

Na ganshi yayin da yake faɗa... A cikin faɗan nasa akwai wayar da kai, kuma a cikin wayar da kan akwai soyayya... Cin nasara ba wai aikinsa bane, halinsa ne... Yin nasara ba halinsa bane, basirarsa ce... Akwai walƙiya a idanuwansa da kuma ƙarfe a damatsansa... Naushinsa ɗaya shi ne goman na wasu. 

Parikshat Sahni

• Kahi baar dard ka ilaaj dard hi hove hai

Sau da dama maganin zafi shi ne zafin kansa. 

Anushka Sharma

• Wrestling koi khel nahi hai ... yeh woh dangal hai joh insaan apni zindagi mein apne aap se ladta hai

Kokawa ba wasa bane kawai... Yaƙi ne da mutum ke yi a rayuwarsa da kansa. 

Salman Khan 

• Agar tune aaj give up kiya ... toh shayad bahar se zinda reh jaye ... magar andar se mar jayega hamesha ke liye

Idan ka karaya yau... To wataƙila ka rayu... Amma ta ciki za ka zama matacce har abada. 

Anushka Sharma

• Kisaan aur pehalwan mein ek hi cheez ek jaise hove hai ... woh hai maati

Abu ɗaya ne ya kamanta manomi da ɗan kokawa... Shi ne ƙasar da aka haife su a ciki tare.

Salman Khan 

• Asli pehalwan ki pehchaan akhade mein nahi, zindagi mein hove hai ... taki jab zindagi tumhe patke toh tum phir khade ho ... aur aaisa daanv maro ki zindagi chitt ho jaye

Mafaɗacin gaske ana iya gane shi a rayuwa, ba wai a filin dambe ba... Saboda ka miƙe yayin da rayuwa ta kada kai... Sannan ka yi wasa irin yadda sai ka yi nasara akan rayuwa. 

Salman Khan 

• Woh dus maarenge aur tu ek maarega ... us ek mein dus ka vazan hoga

Zai doke ka sau goma, za ka dake shi sau ɗaya... Wannan ɗaya zai maye gurbin goman. 

Randeep Hooda

• Koi tumhe tab tak nahi hara sakta ... jab tak tum khud se na haar jao

Babu mai iya kada kai... Har sai ka rasa kanka. 

Salman Khan 

• Khud ko Shahrukh Khan samjhe hai ke? ... Shahrukh ka mazaak mat udhao ... manne bahut pasand hai ... jab woh ladki ke aankh mein aankh daalke dekhe hai na toh andhi ladki bhi patt jaave hai

A tunaninka kai Shah Rukh Khan ne?... Kada ka yi ba'a wa Shah Rukh... Ina son shi sosai... A duk sanda ya kalli idanun yarinya, to ko makauniya ce sai ta kware masa. 

Salman Khan 

• Sapne dekhna achchi baat hai ... par kahi baar unke peeche daudte daudte na apne peeche choot jaate hai

Abu ne mai kyau ka zama mai mafarkai... Amma a wasu lokutan idan ka biye musu sai ka rasa masoyanka. 

Anushka Sharma

• Yeh joh tumhari society hai na ... is mein aaj bhi ladkiyan ghunghat ke peeche janam leve hai aur wahin mar jaave hai

A cikin wannan al'ummar taku... Har yau mata ana haihuwarsu ne a bayan labule kuma a nan suke mutuwa. 

Anushka Sharma


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR WAƘAR SHAITAN KA SAALA


FASSARAR WAƘAR SHAITAN KA SAALA 

 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

• Waƙa - Shaitan Ka Saala 

• Fim - Housefull 4

Shekarar Fita - 2019

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Sauti - Sohail Sen 

• Kamfani - T-Series 

• Rubutawa - Farhad Samji 

• Rerawa - Vishal Dadlani & Sohail Sen 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Bala Bala Bala Bala Bala Bala Bala Bala

Bala Bala Bala Bala Bala Bala Bala Bala

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

• Sab kahe mujhe shaitan ka saala ... Bala Bala Bala Bala 

Kowa na kira na da abokin shaiɗan.

• Looto looto looto looto japta hoon mala ... Bala Bala Bala Bala 

Na kan zurfafa tunani kuma in yi wa mutane sata. 

• Sab kahe mujhe shaitan ka saala ... Bala Bala Bala Bala 

Kowa na kira na da abokin shaiɗan.

• Log bole Bala kya cheez hai saala ... Bala Bala Bala 

Mutane na cewa Bala haɗaɗɗe ne. 

• Log bole Bala kya cheez hai saala ... Bala Bala Bala 

Mutane na cewa Bala haɗaɗɗe ne. 

• Ravan ne hai paala bole beti, mausi, khala

Duk matan sun ce Ravana ne ya tayar da ni. 

• Gore se gore ka munh karta hoon kaala 

Ina iya sukar mafiya girma daga cikin su. 

• Khud ki Diwali aur auron ka diwala

Murna nake yi yayin da wasu ke kuka. 

• Bala Bala Bala Bala chichori pathshala 

Makarantar Bala cike take da fitina. 

• Bala Bala Bala Bala keeda of the naala 

Bala ƙwaron cikin kwata ne. 

• That's right! 

Haka yake. 

• Khata hoon main murga dalke masala 

Nakan ci kaji masu yaji sosai. 

• Gareebon ke munh se cheenu main niwala

Nakan sace abinci daga bakin talaka. 

• Bala Bala Bala Bala peg patiala 

Bala tamkar ƙaton tulun giya yake. 

• Bala Bala Bala Bala keeda of the naala 

Bala ƙwaron cikin kwata ne. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala Bala Bala chichori pathshala 

Makarantar Bala cike take da fitina. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

A SAN MUTUM A SAN CI IKONSA


A SAN MUTUM A SAN CINIKIN SA DAGA TASKAR 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

 JARUMI AKSHAY KUMAR 

--> Ya yi shura da matsayin Khiladi Kumar of Bollywood. Ya yi fice da fina fina-finan dambe da faɗa waɗanda ke sa a yi ta magana a kansu lokaci bayan lokaci. 

--> Bayan da ya samu Black belt a Taekwondo yayin da yakeIndia, he ya koyi wasan tsalle-tsalle da faɗa a Bangkok,
Thailand, inda ya koyi Muay Thai kuma ya yi aiki a matsayin mai dafa abinci. 

--> Yayin da ya dawo Mumbai sai ya fara koyar da martial arts.

--> Ɗaya daga cikin ɗalibansa sai ya ba shi bashi shawarar ya fara modeling, a awa biyu da yake yi a gaban kyamara sai ya zamana yana samun 5,000, maimakon albashinsa na da wato 4,000 a wata. 

--> A wata safiya, Kumar ya rasa jirginsa na zuwa Bangalore domin ɗaukar wata talla. Jikin rashin jin daɗi sai ya ɗauki kayansa ya shiga yawo studio studio domin neman aikin fim. Cikin sa'a kuwa sai Pramod Chakravarthy ya zaɓe shi a matsayin wanda zai jagoranci shirin Deedar.

--> fim ɗin Deedar, wanda suka fito tare da Karisma Kapoor shi ne fim ɗin da Akshay Kumar ya fara sa wa hannu, amma Saugandh aka fara fitarwa. 

--> Akshay ya kasance kullum a shirye yake da samun aiki ta hanyar yin wasannin kickboxing, basketball, swimming, motsa jiki da sauransu a koda yaushe. 

--> Ya mallaki kamfanin kansa mai suna Hari Om Productions.

--> sun yi soyayya sosai da Shilpa Shetty kafin ya auri Twinkle Khanna.

--> ya fara iya martial arts Tun Yana ɗan shekara mataki na 8 kafin daga baya ya ƙara ƙwarewa a Bangkok.

--> A farkon farawarsa, ya sha samun dama a harkarsa saboda iya rawa da kuma tsabar kasadarsa. 

--> Akshay ya taɓa rera wata waƙa a cikin wani kundin Waƙoƙi na Punjabi, Sunan waƙar da ya rera 'Nirgun Raakh Liya'. Sai dai duk ribar da ya samu na kundin waƙoƙin ya sadaukar da su ne wa waɗanda harin bom ya rutsa da su a July 11.

--> Yana so a ke kiransa da Super Dad.

--> Shi ne ɗan baindiye na farko da kamfanin Adlabs suka fara ba kwantaragin aiyukan huɗu a lokaci guda. 

--> Yana son yin fina-finan faɗa waɗanda zai yi duk sina-sinan faɗan da kansa 

--> Akshay Kumar ya yarda da camfi sosai, ba ya fara rubuta komai a shafi face ya fara da Om a sama. 


--> Fina-Finansa da dama su kan zo da suna ko taken ‘Khiladi’.

--> Akshay mutum ne mai tashi da wuri, ya kan fara aikinsa tun ƙarfe shida na safe. 
 
--> In 2014, ya samar da wani shirin TV realty show Mai suna Dare 2 Dance.
 
--> shi ke da mallakin Khalsa Warriors a World Kabaddi League.


--> Akshay Kumar ba ya aiki a ranakun Lahadi. Kuma ya kan ɗauki hutu sau shida ko sau bakwai a kowace shekara, kuma kowane hutu kan ɗauki kwanaki shida ko bakwai domin kasancewa tare da iyalansa. 

--> Akshay yana son takalma sosai, domin bincike ya nuna ya ma fi matarsa Twinkle yawan takalma.

HAPPY BIRTHDAY SIR

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

Share:

HAPPY BIRTHDAY AKKI


🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻


HAPPY BIRTHDAY AKKI

Na gaida gwani na gwanaye wajen aiki ka wuce jaki, 
Namijin duniya kake sha-kundum kai ne tafki.

Majaujawar nasara kuke ji wannan shi ne Akki,
Balbela da farinta kun san ba ta biɗar wanki.

Gwarzon maza sannu da ƙara shekaru nawa,
Tabbas ka yi mun gani kuma dole mu yo tafawa.

Ka yi haƙuri ya zam nasara yau kai ke shanawa,
Zakaranka ya riƙa yau ga waƙa yana rerawa.

Happy birthday day muke ma domin yau ce ranar ka,
Kuma jajircewa har yau babu wanda ya kamo ka.

Mun yi murna muna ƙara domin muna ƙaunarka,
Aikinka ai na musamman ne shi yasa muke daɗa bibiyarka.

Maƙiya sun sha haushi kai kuma kullum sai tashi
Kai ne iska da ba ta biɗar fuffuke domin tashi.

Maƙiyinka fa kowaye sai mu ce a kamo shi,
Mu danne ɗan nema mu shafe mai ido da toshshi!

Happy birthday sir

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

Share:

MUHIMMAN BAYANAI DANGANE DA JARUMI AKSHAY KUMAR


MUHIMMAN BAYANAI DANGANE DA JARUMI AKSHAY KUMAR

DAGA TASKAR 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻


• Asalin Sunansa - Rajiv Hari Om Bhatia

• Ma'anar Sunan Akshay - Eternal, immortal, indestructable 

• Asalin Sunan - Indian

• Ranar Haihuwarsa - September 9, 1967

• Wurin da aka haife shi - Amritsar, Punjab, India

• Ƙasarsa - Indian

• Addininsa - Sikh

• Laƙubbansa - Akki, Mac, Khiladi, Raju, King Kumar

• Kirarin sa - Bruce Lee of India, Stunt Man of Bollywood, Super Khiladi, Machine Of Bollywood 

• Sana'arsa - Actor, producer, presenter

• Zodiac sign - Virgo

• Tsayinsa - 6' 1" (1.85 m)

• Ranar Aurensa - 14 January 2001

• Matarsa - Twinkle Khanna

• 'Ya'yansa - Araav An haife shi a ranar 15th September 2002 Sai kuma Nitara wacce aka haifa a ranar September 25, 2012 (in kuka lura shi da 'ya'yan nasa duk a watan Satumba aka haife su) 

• Mahaifinsa - Hari Om Bhatia 

• Mahaifiyarsa - Aruna Bhatia 

• 'Yar Uwarsa mace - Alka Bhatia

• Surukinsa - Rajesh Khanna 

• Surikarsa - Dimple Kapadia

• Ɗan Uwan matarsa - Surendra Hiranandani

• 'Yar uwar matarsa - Rinke Khanna

• Harshensa Na asali - Punjabi

• Harsunan Da Yake ji - English, Hindi, Punjabi

• Babban abokinsa a harkar fim - Saif Ali Khan

• Makarantun Da ya yi - Don Bosco School, Matunga, Mumbai Khalsa College, Mumbai

• Ayyukan da yake yawan yi - sauraron waƙoƙi, hawa dutse da kuma ninƙaya a ruwa
 
• Abin da ya fi son yi - Dabaru da siddabaru 

• Siyasa - Yana taimakon gajiyayyu da marasa ƙarfi sosai, amma bai faye sa kansa a harkar siyasa kai tsaye ba. 

• Wasannin da ya fi so - Kickbox, basketball, swimming, maditating, jogging, yoga, gymnastics. 

• Faɗin Ƙirjinsa inci 40 

• Faɗin ƙugunsa - inci 38 

• Lamabr Takalmansa - 12

• Lambar da ta fi ba shi sa'a - 9

• Taken sa - 'Kawai ka nishaɗantar da masu kallon ka' 

• His fit body and energy

• Wanda yake koyi da shi - Amitabh Bachchan

• Abin da ba ya so - A kira shi da jarumin barkwanci ko faɗa kaɗai.

• Lagonsa - Sweets 
 
• Abinda yafi tsoro - tsawo ko bisa 

•kayan da ya fi sawa - Laceless Tiger pumps, white t-shirts, blue denim jeans da baseball cap.

• Kaya mafi tsada da ya fara siya - Armani suit.

• Aiyukan da ya yi a baya - Modelling; chef Bangkok;instructor in Martial art; etc

• Fim ɗinsa na farko - Saugandh (1991)

• Lambar yabon da ya fara samu - Filmfare Award for Best Performance in a Negative Role 'Ajnabee' (2001)

• Wasu fitattun Fina-Finansa da suka yi kyau sosai sun haɗa da - Yeh Dillagi, Garam Masala, Namastey London,
Singh Is Kinng, Kambakkht Ishq, De Dana Dan, Housefull, Tees Maar Khan, Thank You, Desi Boyz,
Special 26, Holiday, Entertainment...

• Shirye-shiryen Talabijin da yayi - Fear Factor: Khatron Ke Khiladi (season 1 and 2); MasterChef India (season 1);
Fear Factor: Khatron Ke Khiladi (season 4)

• fim ɗinsa na Ɗari - Waqt: The Race against Time (2005)
 
 • Abincin da yafi so - Thai, home made Punjabi khana. 

• Ɗan icen da ya fi so - Mangwaro

Wajen da ya fi so - Mauritius

• Yana son kayan - Tom Ford, Dolce & Gabbana 

• Jaruman da yafi so maza - Amitabh Bachchan, Salman Khan da Jackie Chan

• Jarumar da ya fi so - Sridevi, Kareena Kapoor da Katrina Kaif
• Fina-Finan da ya fi so - Life is Beautiful, Deewar, Rocky

• Waƙar Da ya fi so - 'Bheege Honth Tere'

• kalar da ya fi so - Baƙi

• Turaren da ya fi so - Cool Waters
 
• Adireshin gidansa - 203 A Wing, Benzer, Lokhandwala Complex, Andheri (W), Mumbai 400 053

• Akshay on Facebook: https://www.facebook.com/akshaykumarofficial

• Akshay on Twitter: https://twitter.com/akshaykumar

• Akshay on Instagram: http://instagram.com/akshaykumar

• Akshay on You Tube: http://www.youtube.com/akshaykumar

Happy birthday sir 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

Share:

FASSARAR WAƘAR KUCH DIN


FASSARAR WAƘAR KUCH DIN 

• Waƙa - Kuch Din

• Shiri - Kaabil

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar - 2017

• Sauti - Rajesh Roshan

• Rubutawa - Manoj Muntashir

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Jubin Nautiyal

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Kuch Din Se Mujhe Teri Aadat Ho Gayi Hai (x2)

Tsawon wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo hali na. 

• Kuch Din Se Meri Tu Zaroorat Ho Gayi Hai

Tun wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo lalurata. 

• Tere Labon Se Main Hasoon

Ina dariya ne da laɓɓanki. 

• Teri Lehron Mein Bahoon

Ina iyo a ruwan ki. 

• Mujhko Kasam Lage Agar

Gwamma in mace. 

• Tere Bina Main Jiyun

Da na rayu ba tare da ke ba. 

• Kuch Din Se Mujhe Teri Aadat Ho Gayi Hai 

Tsawon wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo hali na. 

• Kuch Din Se Meri Tu Zaroorat Ho Gayi Hai

Tun wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo lalurata. 

• Tere Labon Se Main Hasoon

Ina dariya ne da laɓɓanki. 

• Teri Lehron Mein Bahoon

Ina iyo a ruwan ki. 

• Mujhko Kasam Lage Agar

Gwamma in mace. 

• Tere Bina Main Jiyun

Da na rayu ba tare da ke ba.

• Teri Hawa Mein Hi Udoon

Tashi nake yi a cikin iskar ki. 

• Main Aaj Kal, Main Aaj Kal

(a) kwanakinnan, kwanakinnan. 

• Tere Kadam Se Hi Chaloon

Ina tafiya akan sawayenki. 

• Main Aaj Kal, Main Aaj Kal

(a) kwanakinnan, kwanakinnan. 

• Kuch Bhi Nahi Mujh Mein Mera

A wannan lokacin babu abin da ya yi saura a gare ni. 

• Jo Bhi Hai Woh Hai Tera

Komai ya zama naki. 

• Kuch Din Se Mujhe Teri Aadat Ho Gayi Hai (x2)

Tsawon wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo hali na. 

• Aksar Ata Pata Mera

A kwanakinnan, wa duniya. 

• Rehta Nahin, Rehta Nahin

Na ɓace gaba ɗaya, na ɓace gaba ɗaya. 

• Koi Nishaan Mera Kahin

Duk wata alama ta wanzuwa ta. 

• Milta Nahin, Milta Nahin

Ba a iya ganin ta, ba a iya ganin ta.

• Dhoondha Gaya Jab Bhi Mujhe

A duk lokacin da mutane ke nemana. 

• Teri Gali Mein Mila

Sai su ganni ina yawo akan layinku. 

• Kuch Din Se Mujhe Teri Aadat Ho Gayi Hai 

Tsawon wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo hali na. 

• Kuch Din Se Meri Tu Zaroorat Ho Gayi Hai

Tun wasu 'yan kwanaki, ki ka zamo lalurata. 

• Tere Labon Se Main Hasoon

Ina dariya ne da laɓɓanki. 

• Teri Lehron Mein Bahoon

Ina iyo a ruwan ki. 

• Mujhko Kasam Lage Agar

Gwamma in mace. 

• Tere Bina Main Jiyun

Da na rayu ba tare da ke ba.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
 
Share:

FASSARAR WAƘAR TOILET KA JUGAAD

FASSARAR WAƘAR TOILET KA JUGAAD 


• Waƙa - Toilet Ka Jugaad

• Shiri - Toilet - Ek Prem Katha

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2017

• Sauti - Vickey Prasad

• Rubutawa - Garima Wahal & Siddharth Singh

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Akshay Kumar & Vickey Prasad

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Duniya Chali Mars Pe

Duniya ta cimma bigiren Mars 

• Chaand Zameen Pe Dikh Rayo

Yanzu mutum na iya ganin wata daga wannan duniyar. 

• Arre Black And White Se Colour Hua

Daga (fina-finai) masu baƙi da fari zuwa masu kala. 

• Ab 3D Main Sab Dikh Raheyo

Ka na kuma iya ganin abubuwa a zubin 3D. 

• Duniya Chali Mars Pe

Duniya ta cimma bigiren Mars 

• Chaand Zameen Pe Dikh Rayo

Yanzu mutum na iya ganin wata daga wannan duniyar. 

• Arre Black And White Se Colour Hua

Daga (fina-finai) masu baƙi da fari zuwa masu kala. 

• Ab 3D Main Sab Dikh Raheyo

Ka na kuma iya ganin abubuwa a zubin 3D. 

• Hazaaron Chad Gaye Everest Ka Pahaad (x2)

Dubban mutane sun haura hau kan dutsen Everest

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Kab Tak Lega Tu Pedon Ki Aadh

Tsawon yaushe ne za ka ci gaba da tsuguno a gindin bishiyoyi? 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Public Mein Bhar Do Laaj Sharam, Sabhyata Yahi Sikhaaye

Ka sa kowa ya ji kunya, wannan shi ne abin da zama ɗan al'ada yake nufi. 

• Ghoonghat Khencho Pet Tak, Baitho Saari Uthaaye

Mata na zaune sun ja sarin su har ciki. 

• Bhabhi Nikli Tarke Tarke, Raste Khade Ladke Rehtey Taad

Suruka na tafe cikin jin kunya marasa kunyar unguwa/layi suna kallonta.

• Sun Le Kya Nature Ki Pukar

Kalli abin baƙin cikin da wannan al'amari ke kai. 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Kab Tak Lega Tu Pedon Ki Aadh

Tsawon yaushe ne za ka ci gaba da tsuguno a gindin bishiyoyi? 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Tourist Dekhe Kile Aur Mahal Jo Desh Ki Shaan Badhaye

masu yawon buɗe ido na zuwa fada da manyan wurare, hakan na ƙara daraja wa ƙasa. 

• Hum Toh Samajh Ke Baap Ka Maal Kone Bhigo Ke Aaye

Mu kuma da muke tunanin namu ne sai mu je mu jiƙe wurin (da fitsari) 

• Baas Maare Ab Apni Virasat, Naash Hua Achaar Vichar

Abubuwan da muka gada duk ɗoyi suke yi yanzu, duk al'adar da falsafar ta watse. 

• Tel Dekh Tu Tel Ki Dhaar

Dubi yadda datti ke malala. 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• Mehak Rahi Hai Desh Ki Galiyaan, Saans Lena Ho Gayo Muhaal

Duk hanyoyin gari sai wari suke, numfashi ma wahalar fita yake. 

• Swachh Banega Bharat Khud Hi, Dekh Le Apne Ghar Ka Haal

Shin sai yaushe ne Indiya za ta yi fes, dubi yadda lamarin ya ɓaci. 

• Nadi Kinare Baithega Tu, Sab Paani Mein Mil Jayego

Idan mutum ya tsuguna ya yi fitsari a gefen rafi, duk sai ya haɗe da ruwan kogin. 

• Wahi Bahega Nalkon Se, Phir Usko Hi Tu Pee Jayego

To kuma wannan ruwan ne dai yake dawo muku a famfo, maza ai sai a sha. 

• Haath Mein Leke Izzat Apni, Khada Hai Tu Kyun Maidaano 
Mein

ME yasa kuke tsaye a filin Allah da taƙamar ku a hannu? 

• Dikhe Koi Jo Dhar Maarta, Rapat Likha Do Tum Thaano Mein

Idan kuka ga wani na fitsari a fili, ku shigar da ƙorafi wa 'yan sanda. 

• Khule Mein Hai Jo Shaan Agar Toh, Dhoti Pehan Na Chhod De

In kuma kuna ganin akwai wata fa'ida ce da ke tattare da fitsari a fili sai ku daina saka kaya ma. 

• Har Cheez Parampara Nahi Re Pyaare

Ba komai ne yake al'ada ba masoyi/masoyiya. 

• Aad Tu Lena Chhod De (x3)

Ku daina tsaya a bayan irin waɗannan al'adun. 

• Mil Kar Mauka Na Sabhayta Pe Phaad

Kada ku lalata mana al'ada da miyagun aiyukan ku. 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Kab Tak Lega Tu Pedon Ki Aadh

Tsawon yaushe ne za ka ci gaba da tsuguno a gindin bishiyoyi? 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

HARUFFAN HAUSA

HARUFFAN HAUSA

Haruffan Hausa sune ƙwayoyin da Hausawa ke amfani da su a yayin ginin kalma ko gaɓa ko jimla, da sauransu. 

Haruffan sun rabu gida biyu kamar haka:

BAƘAƘE

Su ma baƙaƙen sun kasu gida uku, ga su kamar haka: 

Na Asali ko sanannu

B, C, D, F, G, H, J, K, L, M, N, R, S, T, W, Y, Z 

Ƙirƙirarru/gwagware/gajeru/ɗaiɗaiku 

Ɓ, Ɗ, Ƙ, 'Y


Masu goyo 

FY, GY, GW, KY, KW, ƘY, ƘW, SH, TS


WASULLA 

su ma wasullan sun rabu gida biyu kamar haka:

Sanannu/Na asali 

A, E, O, U, I

Aure/gwamammu/masu goyo/tagwaye 

Ai, Au, Oi, Ui 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR WAƘAR THE PADMAN SONG

🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

FASSARAR WAƘAR THE PAD MAN SONG 


• Waƙa - The Pad Man Song

• Shiri: Padman

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2018

• Sauti - Amit Trivedi

• Rubutawa - Kausar Munir

• Kamfani - Zee Music Company

• Rerawa - Mika Singh

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman


• Superhero, Superhero, Superhero, Haaye, Haaye, Haaye, Haaye…

Jarumi, Jarumi, Jarumi, Ayye, Ayye, Ayye, Ayye... 

• Ho… Thaanye Thaanye Na Goli Maare

Shi ba harba harsasai yake ba. 

• Dhaanye Dhaanye Na Entry Maare

Shi ba shigowar bajinta yake ba. 

• Slow Motion Mein Haddi Tode Na

Shi ba karya ƙasusuwa yake yi a hankali ba. 

• Arre Building Se High Jump Na Maare

Ba tsalle yake yi daga dogayen gine-gine ba. 

• Neeche Se Dialogue Na Maare

Ba ya ambato zantuka daga ƙasa 

• High Speed Mein Naache Gaaye Na

Shi ba rawa da waƙa yake yi da sauri ba. 

• Ho… Na Koi Multi-Storey Bangla

Shi bashi da ginin bungalo mai hawa biyu. 

• Na Hai Koi Udan Khatola

Shi bashi da abin hawa mai tashi sama. 

• Par Superhero Hai Yeh Pagla

Amma wannan zararren mutumin duk da haka jarumi ne. 

• O Waah Re Waah Re Waah Re Waah Re…

Ah Dakyau! Dakyau! Dakyau! O 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man…

Mai ƙunzugu 

Hey Hey Hey Hey….

• O Kaali Kalkatte Waali

Jinjina ga abar bauta Kali na Kolkata!

• Bhabhi Didi Biwi Saali

Ko surika ce ko mata 

• Poori Ya Aadhi Ghar Waali

Abokiyar zama ce ko budurwa. 

• Ya Ho Maiyya…

Ko ma Mahaifiya ce. 

• Item Ho Ya Laaj Ki Moorat

Ko 'yar batsula ce ko mai kamun kai ce. 

• Har Naari Ko Iski Zaroorat

Kowace mace tana buƙatar wannan. 

• Dhanno Ho Ya Munni Ho Ya Sheila, Laila…

Ko da Dhanno ce , Munni, Sheila ko kuma Laila

Hey Hey Hey Hey….

• Ho… Harkatein Risky, Risky

Aikinsa akwai kasada a ciki. 

• Fikar Isse Kiski, Kiski

Yana damuwa matuƙa akan kowa. 

• Hai Yeh Namuna Number One Ziddi…

Shi na musamman ne kuma ga taurin kai. 

• Kahe Jo Koi Kuch Bhi, Kuch Bhi

(Bai damu ba) da abinda kowa zai ce (game da shi)

• Raah Chale Sach Ki, Sach Ki

Shi kullum hanyar gaskiya yake bi. 

• Lagta Hai Yeh Kudrat Ki Galti…

Da alama dai shi kuskure ne a ƙaddara. 

• Haan Bhaad Mein Jaaye Re Angreji

Turanci ya ci ƙaniyarsa. 

• Nahi Chaahiye Imported Degree

Shi bai damu da baƙon digiri ba. 

• Made In India Hai Yeh Jigri

Mutum ne shi mai nagarta ɗan Indiya. 

• O Waah Re Waah Re Waah Re Waah Re…

Ah Dakyau! Dakyau! Dakyau! O 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man…

Mai ƙunzugu 

• Superhero, Superhero, Superhero, Haaye, Haaye, Haaye, Haaye…

Jarumi, Jarumi, Jarumi, Ayye, Ayye, Ayye, Ayye... (x2)

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Happy Birthday Akshay Kumar 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form