Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

MUHIMMAN BAYANAI GAME DA SHIRIN LAXMMI BOMB


🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

Muhimman Bayanai Game Da Shirin Laxmmi Bomb (2020)

 


• Banner - Cape of Good Films, Tusshar Entertainment House, Shabinaa Entertainment, Fox Star Studios

• Status - Completed

• Release Date - 09 November, 2020

• Genre - Comedy, Drama, Horror

• Producer - Tusshar Kapoor, Shabina Khan

• Star Cast - Akshay Kumar, Kiara Advani, Tarun Arora, Rajesh Sharma, Ayesha Raza Mishra, Ashwini Kalsekar, Manu Rishi Chadha

• Writer - Raghava Lawrence

• Background Music - Amar Mohile

• Choreographers - Ganesh Acharya, Bosco Martis, Caesar Gonsalves

• Costume Designer - Tanya Ghavri, Navin Shetty, Devraj Das, Uma Biju, Jimmy’z Designer

• Publicity PRO - Hype

• Censor Details: - Censor Dates
Not Available.

• Censor Certificate No - Not Available.

• Runtime - Not Available.

• Certification - Not Available.

• Presenter - Fox Star Studios

• Music Director - Tanishk Bagchi, Shashi – Khushi, Anup Kumar

• Language - Hindi

• Director - Raghava Lawrence

• Lyricist - Vayu, Farhad Samji, Anup Kumar, Vaibhav Shrivastava, Gagan Ahuja

• Editor - Rajesh G. Pandey

• Cinematographer - Vetrivel Palanisamy, Khush Chhabria

• Screenplay - Raghava Lawrence, Farhad Samji, Tasha Bhambra, Sparsh Khetarpal

• Dialogue - Farhad Samji, Tasha Bhambra, Sparsh Khetarpal

• Publicity Design - Himanshu Nanda, Rahul Nanda

• Shooting Location(City & Country) - India

• Sound - Parikshit Lalwani, Kunal Mehta

• Music Company - Zee Music Company

• Production Designer - Wasiq Khan

• Casting Director - Parag Mehta

• Action Director - Sham Kaushal

• Executive Producer - Manan Sampat, Prafull Salunke


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

Share:

FASSARAR WAƘAR O BEKHABAR

Fassarar Waƙar O Bekhabar


• Waƙa - O Bekhabar

• Fim - Action Replayy

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2010

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Irshad Kamil

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Shreya Ghoshal
 
• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon ko na badha

Kada ka ƙara (min yawan) rashin sukuni na. 

• Dekh le hai pyaar ka kaisa nasha mujh pe chadha

Kalli yadda mayen so ya hau kaina. 

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon ko na badha

Kada ka ƙara (min yawan) rashin sukuni na. 

• Dekh le hai pyaar ka kaisa nasha mujh pe chadha

Kalli yadda mayen so ya hau kaina. 

• Kaisa nasha mujh pe chadha x3

Wane irin mayen so ne ya faɗa kaina?

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon bechainiyan hain jawaan

Rashin sukuni ya tsananta. 

• Meri nazar dhoonde tujhe tu kahan

Idanuwana suna nemanka. 

• Haan tujhko main aankhon ka kaajal bana loon

Ina so in maida kai kwallin idanuwana. 

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon bechainiyan hain jawaan

Rashin sukuni ya tsananta. 

• Chaahungi main yun hi tujhe bepanah

Zan ci gaba da sonka a haka ba tare da adadi ba. 

• Haan tujhko khushi sa labon pe saja loon

Zan ƙawataka kamar farinciki akan Laɓɓana. 

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon ko na badha

Kada ka ƙara (min yawan) rashin sukuni na. 

• Dekh le hai pyaar ka kaisa nasha mujh pe chadha

Kalli yadda mayen so ya hau kaina. 

• Kaisa nasha mujh pe chadha x3


Wane irin mayen so ne ya faɗa kaina?

• Roop hoon teri dhoop hoon

Ni ce ɓadda kamarka, ni ce hasken ranar ka.

• Tu suraj hai mann ka mere

Kai ne ranar zuciyata. 

• Ya ghani main hoon roshni

Ko kuma ni ce hasken? 

• Ab chalti hoon dhalti hoon tujhko hi

Ina tafiya ne ɓoye a inuwarka. 

• Haan mere ik pehar tu kahe thehar

Idan ka ce in dakata na ɗan wani lokaci. 

• Toh jaaon na dar se tere

Ba zan taɓa barin dokin ƙofarka ba. 

• Har ghadi mushkilon bhari

Kowane lokaci cike yake da wahala. 

• Kyun lagti hai jo bhi badalti hai bin tere

Me ya sa hakan ke afkuwa idan babu kai? 

• Tu mile toh silsile ho woh shuru

A sanda ka haɗu da ni sai waɗannan abubuwa suka fara afkuwa. 

• Jo hai khuda ki raza

Waɗanda Allah ya hukunta. 

• Tere bina hai zindagi bemaza

In babu kai rayuwar ba ta da daɗi. 

• Tu mil jaaye toh main jahan se chhupa loon

Idan na same ka, zan ɓoye ka daga wannan duniyar. 

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon ko na badha

Kada ka ƙara (min yawan) rashin sukuni na. 

• Meri nazar dhoonde tujhe tu kahan

Idanuwana nemanka suke yi. 

• Aa tujhko main aankhon ka kaajal bana loon

Taho, Ina so in maida kai kwallin idanuwana. 

• O bekhabar 

Ya kai mara sani. 

• O pyaar bhi yun kabhi kabhi

So shi ma wani lokacin. 

• Kar deta pareshaan yun

Kan sa abu ya wahalta haka. 

• Har jagah wohi woh lagey

Ganin mutuminnan nake yi a ko'ina. 

• Woh aashiq anari jo dil de ke leta

Wannan ɗan koyon da ya sace min zuciya. 

• Ya paas bhi ho woh door bhi

Gashi dai a kusa kuma yayi nisa. 

• Yeh kyun ho woh batlaaye na

Ta yaya (hakan) zai kasance, bai faɗa min ba. 

• Dil darre minnate kare

Zuciya a tsorace take tana mai addu'a. 

• Ab usko yeh bolo ke aaye toh jaaye na

Cewa kada ya tafi bayan ya zo. 

• De pata agar ho pata

Faɗa min in ka sani.

• Kya hai yahi dil ki khata ki saza

Shin wannan shi ne hukuncin kuskuren da zuciya ta aikata? 

• Khud mein hi main hoti hoon kyun laapata

Me yasa na ɓacewa kaina. 

• Main jaanu na iss dil ko kaise sambhalun

Na rasa yadda zan tafiyar da wannan zuciyar tawa. 

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon bechainiyan hain jawaan

Rashin sukuni ya tsananta. 

• Meri nazar dhoonde tujhe tu kahan

Idanuwana suna nemanka. 

• Haan tujhko main aankhon ka kaajal bana loon

Ina so in maida kai kwallin idanuwana. 

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon ko na badha

Kada ka ƙara (min yawan) rashin sukuni na. 

• Dekh le hai pyaar ka kaisa nasha mujh pe chadha

Kalli yadda mayen so ya hau kaina. 

• Kaisa nasha mujh pe chadha 

Wane irin mayen so ne ya faɗa kaina?

• O bekhabar o bekadar

Ya kai mara sani, ya kai halitta mara kula. 

• Betaabiyon ko na badha

Kada ka ƙara (min yawan) rashin sukuni na. 

• Dekh le hai pyaar ka kaisa nasha mujh pe chadha

Kalli yadda mayen so ya hau kaina. 

• Kaisa nasha mujh pe chadha 

Wane irin mayen so ne ya faɗa kaina?


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN DILWALE DULHANIA LE JAYENGE


Fassarar Kalaman Fim Ɗin Dilwale Dulhania Le Jayenge


Shekarar Fita - 1995

• Toh kya hua agar maine jhoot sirf tumhe paane ke liye kaha tha ... toh kya hua agar tumhare chehre ke sivah mujhe koi aur chehra dikhai nahi deta ... toh kya hua agar tumhare naam ke sivah mujhe koi aur naam yaad nahi rehta ... toh kya hua agar yeh awara tumhe deewano ki tarah pyar karta hai ... toh kya hua ... pyar sab kuch toh nahi hota na. 

Sai me don na yi ƙarya saboda in same ki... Sai me don bana iya ganin fuskar kowa face taki... Sai me don bana iya tuna kowane suna face naki naki... Sai me don wannan taƙadarin yana sonki kamar hauka... Sai me... Tun da dai so ba shi ne komai ba. 

Shah Rukh Khan 

• Mohabbat ka naam aaj bhi mohabbat hai ... yeh na kabhi badli hai aur na kabhi badlegi

Har zuwa yau dai shi so sunan shi so... Sunan bai canja ba kuma ba zai taɓa canjawa ba. 

Anupam Kher 

• Koi bhi ullu ka patha sirf ek angoothi pehanakar tumko mujhse nahi cheen sakta ... tum meri ho, sirf meri. 

Babu wani sokon da zai iya ƙwace min ke ta hanyar sa miki zobe a hannu... Ke tawa ce, tawa kawai. 

Shah Rukh Khan 

• Main ek Hindustani hoon ... aur main jaanta hoon ki ek Hindustani ladki ki izzat kya hoti hai. 

Ni ɗan Indiya ne... Kuma na san irin darajar da 'yar Indiya ke da shi. 

Shah Rukh Khan 


• Joh shaadi waale ghar mein seva karta hai ... usko bahut sundar dulhan milti hai

Masu taimako a gidan da ake ɗaurin aure... Sukan samu kyawawan mata. 

Shah Rukh Khan 

• Agar yeh tujhe pyar karti hai toh yeh palat ke dekhegi ... palat ... palat!

Idan har tana sonka to za ta juyo ta kalle ka... Juya... Juya... 

Shah Rukh Khan

• Jab ladki jawan ho jaati hai na ... toh maa uski maa nahi rehti ... sehali ban jaati hai

A yayin da budurwa ta tasa... To mahaifiyarta ta tashi daga matsayin mahaifiya kuma... Ta zama ƙawarta kenan. 

Farida Jalal

• Bade bade deshon mein aaisi choti choti baatein ... hoti rehti hai

A manya-manyan birane irin waɗannan ƙanana-ƙananan abubuwan... Na ci gaba da faruwa. 

Shah Rukh Khan

• Ja Simran ... ja jeele apni zindagi ... ja beta ja
Go Simran ... go live your life ... go my child go

Amrish Puri 

• Agar tum galat raaste par chaloge ... toh ho sakta hai shuruvat mein tumhe bahut kamyabi mile, bahut khushiya mile ... magar anth mein tumhari haar hogi ... aur agar sahi raaste par chaloge ... toh bhale hi shuruvat mein tumhe kadam kadam par thokarein mile, musibaton ka samna karna pade, pareshani ho ... magar anth mein hamesha jeet hogi

Idan ka hau kan mummunar hanya... Ta yiwu da fari za ka samu nasara sosai da farinciki.. 
Amma a ƙarshe ba za ka yi nasara ba... Idan kuwa ka hau hanyar daidai... Ta yiwu da fari za a ƙi yarda da kai a kowane taku, za ka fuskanci ƙalubale da matsaloli... Amma a ƙarshe kai me za ka yi nasara. 

Shah Rukh Khan 

• Dimaag mein kitaaben bharne se jeben thodhi bharti hai

Ba ka iya cika aljihunka (da kuɗi) ta hanyar cika ƙwaƙwalwarka da Littattafai.

Anupam kher

• Zarooraton ne par kaat diye hai ... roti paon ki zanjeer ban gayi hai

Buƙatu sun datse fuka-fukaina, biredi ya zama sasarin ƙafata.

Amrish Puri 

• Fail hona aur padhai na karna ... hamare khandaan ki parampara hai

Faɗuwa da rashin karatu... Al'adun ahalinmu ne. 

Anupam Kher 

• Tumhari jaisi ladki ke saath, mere jaise ladke ka hona ... bahut zaroori hai

Abu ne mai muhimmanci wa budurwa kamar ki ta samu gaye kamar ni. 

Shah Rukh Khan 

• Ek pal mein beta bana liya ... aur doosre hi pal mein paraya kar diya

Lokaci ɗaya kun maida ni ɗanku... A lokaci na gaba kuma sai kuka maida ni baƙo. 

Shah Rukh Khan 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR KABHI KABHI MERE DIL MEIN (DIALOGUE)

Fassarar Waƙar Kabhi Kabhie Mere Dil Mein Khayal Aata Hai (Dialogue) 


• Waƙa - Kabhi Kabhie Mere Dil Mein Khayal Aata Hai (Dialogue) 

• Fim - Kabhi Kabhie

• Shekarar Fita - 1976

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Rubutawa - Sahir Ludhianvi

• Kamfani - EMI 

• Rerawa - Amitabh Bachchan 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Kabhi Kabhie mere dil mein khayal aata hai

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.  

• ke zindagi teri zulfon ki naram chhaon mein guzarne pati

Tamkar rayuwata ta wuce ta tsakanin inuwar kashin kanki. 

• toh shadaab ho bhi sakti thi

Da kuwa abin ya yi armashi. 

• yeh ranj-o-gham ki shayahi joh dil pe chayi hai ...

Wannan tawadar damuwar da ta watsu akan zuciya. 

• teri nazar ki shuaon mein kho bhi sakti thi ... 

Da ta ɓace a ƙyallin idanuwanki. 

• magar yeh ho na saka 

Amma hakan bai faru ba. 

• magar yeh ho na saka aur ab yeh aalam hai ... 

Amma hakan bai faru ba kuma yanzu dai haka abin yake.

• ki tu nahi tera gham teri justaju bhi nahi ... 

Ba kya nan, haka ma damuwarki. 

• guzar rahi hai kuch is tarah zindagi jaise 

Rayuwa tana wucewa ta tamkar. 

• isse kisi ke sahare ki aarzu bhi nahi

Kai ka ce ba ta buƙatar taimakon kowa.

• na koi raah, na manzil, na roshni ka suraag ...

Babu hanya, babu wurin zuwa kuma babu alamar haske.

• bhatak rahi hai andhero mein zindag i meri ... Rayuwata na ta bulayi a cikin duhu. 

• inhi andhero mein reh jauga kabhi khokar ... 

Zan kasance ɓatacce a cikin wannan duhun. 

• main janta hoon meri humnafas ... 

Na san cewa ƙawata... 

• magar yoon hi kabhi kabhi mere dil mein khayal aata hai

Amma wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata. ©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR WAƘAR MON AMOUR

Fassarar Waƙar Mon Amour


• Waƙa - Mon Amour

• Fim - Kaabil

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2017

• Sauti - Rajesh Roshan

• Rubutawa - Manoj Muntashir

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Vishal Dadlani

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 

• Kadam Se Kadam Jo Mile, Toh Phir Saath Hum Tum Chale

A yayin da takunmu ya zamo ɗaya, sai muka fara tafiya tare. 

• Chale Saath Hum Tum Jahaan, Wahin Pe Bane Kaafile

Wurin duk da muka fara domin zuwa (gare shi) to a nan ne ayarin zai haɗu. 

• Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Chhod Do Khud Ko Aise Meri Baahon Mein

Ki saki jikinki a hannuwana. 

• Jaise Hawaaon Mein Baadal Koi

Kamar yadda girgije ke sakewa a cikin iska. 

• Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Chhod Do Khud Ko Aise Meri Baahon Mein

Ki saki jikinki a hannuwana. 

• Jaise Hawaaon Mein Baadal Koi

Kamar yadda girgije ke sakewa a cikin iska. 

• Kadam Se Kadam Jo Mile, Toh Phir Saath Hum Tum Chale

A yayin da takunmu ya zamo ɗaya, sai muka fara tafiya tare. 

• Chale Saath Hum Tum Jahaan, Wahin Pe Bane Kaafile

Wurin duk da muka fara domin zuwa (gare shi) to a nan ne ayarin zai haɗu. 

• Zameen Bole Saari Ra Ra Ri Ra Ri

Duniya gaba ɗaya girgiza ta ke yi. 

• Ye Deewangi Ka Hai Shor…

Wannan sautin ƙauna ne/hauka. 

• Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Aaj Saare Sapne Chal Palkon Mein Bhar Le

Bari mu cika idanuwanmu da mafarkai yau. 

• Aaj Saari Khushiyon Se Yaarana Kar Le

Bari mu aboci farinciki yau. 

• Aaj Saare Sapne Chal Palkon Mein Bhar Le

Bari mu cika idanuwanmu da mafarkai yau. 

• Aaj Saari Khushiyon Se Yaarana Kar Le

Bari mu aboci farinciki yau. 

• Da Ra Di Da Ra Suno Toh Yaara

Ki saurare ni, ya abokiyar tarayya ta. 

• Aaja Kar Le Manmaani Thhodi Aur

Bari mu ɗan yi fasadi kaɗan. 

• Mon Amour… Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Say Yeah!

Ki ce eh! 

• Roz Roz Aaye Kahaan Yeh Neeli Shaamein

Waɗannan shuɗayen yammacin ba kullum za su ke zuwa ba. 

• Roz Roz Honge Na Aise Hungamein

Waɗannan shagulgulan ba kullum za su ke zuwa ba. 

• Ay Benga, Baila, Baila, Baila

Taho mana, yi rawa, yi rawa, yi rawa. 

• Roz Roz Aaye Kahaan Yeh Neeli Shaamein

Waɗannan shuɗayen yammacin ba kullum za su ke zuwa ba. 

• Roz Roz Honge Na Aise Hungamein

Waɗannan shagulgulan ba kullum za su ke zuwa ba. 

• Da Ra Di Da Ra Suno Toh Yaara
Listen to me, my partner

• Da Ra Di Da Ra Suno Toh Yaara

Ki saurare ni, ya abokiyar tarayya ta. 

• Say One Two Three Four

Ce ɗaya, biyu, uku, huɗu 

• Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Chhod Do Khud Ko Aise Meri Baahon Mein

Ki saki jikinki a hannuwana. 

• Jaise Hawaaon Mein Baadal Koi

Kamar yadda girgije ke sakewa a cikin iska. 

• Kadam Se Kadam Jo Mile, Toh Phir Saath Hum Tum Chale

A yayin da takunmu ya zamo ɗaya, sai muka fara tafiya tare. 

• Chale Saath Hum Tum Jahaan, Wahin Pe Bane Kaafile

Wurin duk da muka fara domin zuwa (gare shi) to a nan ne ayarin zai haɗu. 

• Zameen Bole Saari Ra Ra Ri Ra Ri

Duniya gaba ɗaya girgiza ta ke yi. 

• Ye Deewangi Ka Hai Shor…

Wannan sautin ƙauna ne/hauka. 

• Mon Amour…

Masoyiyata. 

• Mueve Su Cuerpo Mi Angel

Malaika ta, juya jikinki mana.

• To Feel The Heat, Corazón

Ki ji sautin, zuciyata. 

• Mueve Su Cuerpo Mi Angel

Malaika ta, juya jikinki mana.

• To Feel The Heat, Corazón

Ki ji sautin, zuciyata. 

• Mon Amour... Mon Amour…

Masoyiyata. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

DARUSSAN TELUGU 13


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            13

141. Bhojanam aayindha? - Ka/kin ci abinci kuwa?
142. Adhi cheppakandi - Kada ka/ki ce haka.
143. Somavaaram - Litinin
144. Mangalavaaram - Talata
145. Budhavaram - Laraba
146. Guruvaaram - Alhamis
147. Shukravaram - Juma'a
148. Shanivaaram - Asabar
149. Aadhivaaram - Lahadi
150. Nenu na samanu kolpoyanu - Abu na fa ya ɓata
151. Nenu Meeku bodhisthanu - zan koya maka/miki wannan.
152. Nishabdhanga undandi - yi shiru
153. Nenu intiki velthunnanu - zan tafi gida
154. Ekkada noppi ga undhi? - Ina ne ke ciwo?
155. Ikkada noppi ga undhi - nan ne ke min ciwon
156. Naaku thalanoppi undhi - kaina na min ciwo
157. Naaku kadupunnoppi undhi - cikina na min ciwo
158. Chadhavadham na abhiruchi - karanta littafai shi na fi so/ƙwarewa
159. Meeru mee vidyani poorti chelsaara? - ka/kin kammala karatunka ne?
160. Aame ela undhi - ya take?

Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 12

✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            12

121. Ghoduma - ruwan ƙasa
122. Pasupupacha - ruwan ƙwai
123. Gulabi - pink
124. Paalu - madara
125. Perugu - soya
126. Beeyam - shinkafa
127. Naaku vennunoppi - Ina fama da ciwon baya
128. Naaku doctor avasaram undhi - Akwai buƙatar in je wurin likita
129. Naaku chaai kaavali - Ina buƙatar Shayi
130. Ee aushadham thisukondu - sha wannan maganin
131. Aame eela undhi - yaya take?
132. Baasha - harshe/yare
133. Ankelu - lamba
134. Malli cheppandu - sake maimaitawa
135. Iroju emi roju - yau wace rana ce?
136. Vellodhdhu - Kada ka/ki tafi don Allah
137. Naaku gondi noppi undhi - maƙogwarona na min ciwo/zafi
138. Naaku Vaanthi vachalega undhi - ji nake kamar zan yi amai
139. Athanu velthaadu - zai tafi
140. Nenu jabbupadi unnanu - bani da lafiya.

Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

DARUSSAN TELUGU 11

✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            11


201. Kaagitham - takarda
202. Pusthakamu - littafi
203. Samayam - lokaci
204. Ellappudu - abada
205. Chevi - kunne
206. Tala - kai
207. Mukhamu - fuska
208. Thinu - ci
209. Taagu - sha
210. Nadavadam - sha
211. Chaduvu - karatu
212. Enti Idi - menene wannan?
213. Athanu Ekkada - waye shi?
214. Kobbarikaya - kwakwa
215. Rangu - kala
216. Nalupu - baƙi
217. Telupu - fari
218. Neelam - shuɗi
219. Aakupacha - kore
220. Erupu - ja


Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR WAƘAR KABHI KABHIE MERE DIL MEIN PART I


Fassara Waƙar Kabhi kabhie Mere Dil Mein - Part I

• Waƙa - Kabhi kabhie Mere Dil Mein - Part I

• Fim - Kabhi Kabhie

• Shekarar Fita - 1976

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Sauti - Khayyam 

• Rubutawa - Sahir Ludhianvi

• Kamfani - EMI 

• Rerawa - Mukesh 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata. 

• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata. 

• Ke jaise tujhko banaya gaya hai mere liye 

Cewa lallai an halicce ki ne kawai saboda ni. 

• Ke jaise tujhko banaya gaya hai mere liye 

Cewa lallai an halicce ki ne kawai saboda ni. 

• Tu ab se pehle sitaron mein bas rahi thi kahin 

Kafin yanzu kina rayuwa ne a tsakanin taurari. 

• Tu ab se pehle sitaron mein bas rahi thi kahin 

Kafin yanzu kina rayuwa ne a tsakanin taurari. 

• Tujhe zameen pe bulaya gaya hai mere liye

An kira ki zuwa duniya ne kawai saboda ni. 

• Tujhe zameen pe bulaya gaya hai mere liye

An kira ki zuwa duniya ne kawai saboda ni.

• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata. 

• Ke yeh badan yeh nigahein meri amanat hai 

Cewa wannan jikin da waɗannan idanuwan duka nawa ne. 

• Ke yeh badan yeh nigahein meri amanat hai 

Cewa wannan jikin da waɗannan idanuwan duka nawa ne. 

• Yeh kesuon ki ghani chhaon hai meri khatir 

Inuwar goran kitsonnan duk nawa ne. 

• Yeh honth aur yeh baahein meri amanat hai 

Waɗannan laɓɓan da waɗannan hannayen nawa ne. 

• Yeh honth aur yeh baahein meri amanat hai 

Waɗannan laɓɓan da waɗannan hannayen nawa ne. 

• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata. 

• Ke jaise bajhti hai shehnaiyan si raahon mein 

Cewa bushe-bushen (shagullan) aure suna tashi akan hanya. 

• Ke jaise bajhti hai shehnaiyan si raahon mein 

Cewa bushe-bushen (shagullan) aure suna tashi akan hanya. 

• Suhaag raat hai ghoonghat utha raha hoon main 

Kamar daren tarewarmu kuma ina yaye miki mayafi. 

• Suhaag raat hai ghoonghat utha raha hoon main 

Kamar daren tarewarmu kuma ina yaye miki mayafi. 

• Simat rahi hai tu sharma ke apni baahon mein

Kuma kina tahowa ga hannuwana cike da kunya. 

• Simat rahi hai tu sharma ke apni baahon mein

Kuma kina tahowa ga hannuwana cike da kunya. 

• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata. 

• Ke jaise tu mujhe chahegi umar bhar yoon hi 

Cewa za ki so ni har abada kamar haka. 

• Uthegi meri taraf pyar ki nazar yoon hi

Cewa za ki kalle ni cike da so kamar haka. 

• Main jaanta hoon ke tu gair hai magar yoon hi

Na san cewa ke baƙuwa ce a wajena, amma duk da haka. 

• Main jaanta hoon ke tu gair hai magar yoon hi

Na san cewa ke baƙuwa ce a wajena, amma duk da haka. 

• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.

• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai 

Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR MAIN PAL DO PAL KA SHAYAR HOONFassarar Waƙar Main Pal Do Pal Ka Shayar Hoon


• Waƙa - Main Pal Do Pal Ka Shayar Hoon

• Fim - Kabhi Kabhie

• Shekarar Fita - 1976

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Sauti - Khayyam 

• Rubutawa - Sahir Ludhianvi

• Kamfani - EMI 

• Rerawa - Mukesh 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman • Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Mujhse pehle kitne shayar aaye 

Marubutan waƙa da dama sun zo kafin ni. 

• Aur aakar chale gaye

Sun zo kuma sun tafi. 

• Kuch aahein bharkar laut gaye 

Wasu kan yi kuka kuma su dawo. 

• Kuch nagme gaakar chale gaye 

Wasu kan yi waƙa su tafi. 

• Woh bhi ek pal ka kisa the 

Su ma wani ɓangare ne na wannan lokacin. 

• Main bhi ek pal ka kisa hoon 

Nima wani ɓangare ne na wannan lokacin. 

• Kal tumse juda ho jaunga 

Gobe zan yi nesa/rabu da ke. 

• Woh aaj tumhara hisa hoon 

Duk da cewa ina cikin yau ɗin ki. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Kal aur aayenge

Wasu kaɗan za su dawo gobe. 

• Nagmo ki khilti kaliyan chunne wale 

Waɗanda za su zaɓi waƙoƙi masu tashe. 

• Mujhse behtar kehne wale 

Za a samu waɗanda suka fi ni iya bada labari. 

• Tumse behtar sunne wale

Da kuma masu sauraro fiye da kai/ke 

• Kal koi mujhko yaad kare

Ina fata wani zai tuna da ni a gobe.
• Kyun koi mujhko yaad kare

Amma me yasa wani zai tuna da ni? 

• Mashroof zamana mere liye 

Me ya sa wannan duniyar mai cike da uzuri

• Kyun waqt apna barbad kare 

Za ta ɓata lokacinta a kaina?

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon I'm a poet only for a moment or two
  
©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR TUM SE HI


Fassarar Waƙar Tum Se Hi

• Waƙa - Tum Se Hi

• Fim - Sadak 2

• Harshe - Hindi - Hausa 

• Shekarar Fita - 2020

• Sauti - Ankit Tiwari

• Rubutawa - Shabbir Ahmed

• Kamfani - Sony Music

• Rerawa - Ankit Tiwari & Leena Bose

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 
 

• Do Dil Safar Mein Nikal Pade

Zukata biyu sun fara tafiya a tare. 

• Jaana Kahaan Kyun Fikar Karein

Ba tare da damuwa da bigiren (da za su) ba. 

• Kahaan Thikana Ho Raat Ka

A ina za mu kwanta in dare ya yi? 

• Subah Kahaan Pe Basar Kare

Ina za mu je yayin da gari ya waye? 

N• Khoya Khoya Dil Mera Kehta Hai

Ɓatacciyar zuciyata tana ta kai komo akan cewa. 

• Haan... Tum Se Hi, Bas Tum Se Hi

Saboda ke ne kawai, saboda ke ne kawai. 

• Meri Jaan Hai, Bas Tum Se Hi

Ina jina a raye ne, kawai saboda ke. 

• Dil Ko Mere Aaraam Hai

Zuciyata na cikin kwanciyar hankali. 

• Pareshaan Hai, Bas Tum Se Hi

Zuciyata kan damu ne, kawai saboda ke. 

• Jo Dard Ko, Sukoon De

Wacce ke gamsar da raɗaɗina. 

• Woh Dard Tum Se Milta Hai

Ke kaɗai ke bani irin wannan raɗaɗin. 

• Aye Dil Zara Itna Bata Kyun Ishq Unse Hota Hai

Ya ke zuciyata, ki faɗa min me ya sa nake sonta? 

• Saanson Ko Ab Jeene Ka Jaise Sahara Mile Gaya

Numfashina ya samu dalilin numfasuwa yanzu. 

• Khoya Khoya Dil Mera Kehta Hai

Ɓatacciyar zuciyata tana ta kai komo akan cewa. 

• Haan... Tum Se Hi, Bas Tum Se Hi

Saboda ke ne kawai, saboda ke ne kawai. 

• Meri Jaan Hai, Bas Tum Se Hi

Ina jina a raye ne, kawai saboda ke. 

• Dil Ko Mere Aaraam Hai

Zuciyata na cikin kwanciyar hankali. 

• Pareshaan Hai, Bas Tum Se Hi

Zuciyata kan damu ne, kawai saboda ke. 

• Aashiqui Hoti Hai Kya

Shin menene so?

• Dil Ko Mere Maloom Na Thha

Zuciyata ba ta san wannan ba. 

• Ek Bhi Teri Tarah Chehra Koi Masoom Na Thha

(saboda) bata taɓa ganin fuska irin taki ba sai yanzu. 

• Haan Yun Laga Iss Jaan Mein Ek Jaan Si Daakhil Hui

Ji na yi kamar wata rayuwa ce (ta daban) ta shiga jikina. 

• Ab Toh Har Lamha Mujhse Kehta Hai...

Matuƙar (zuciya) ta ci gabada faɗa min hakan bayan kowane minti. 

• Haan Haan... Tum Se Hi, Bas Tum Se Hi

Saboda kai ne kawai, saboda kai ne kawai. 

• Meri Jaan Hai, Bas Tum Se Hi

Ina jina a raye ne, kawai saboda kai. 

• Dil Ko Mere Aaraam Hai

Zuciyata na cikin kwanciyar hankali. 

• Pareshaan Hai, Bas Tum Se Hi

Zuciyata kan damu ne, kawai saboda ke. 

• Tum Se Hi... Woo....

Saboda ke ne kawai. ©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

BAN HAƘURI


BAN HAƘURI

Assalamu alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu. 'yan uwa da abokan arziƙi na nesa da na kusa ina muku Barka da warhaka tare da fatan kuna lafiya.

A watannin baya na sanar da cewa masu so in fassara musu waƙoƙi su turo da sunayen waƙoƙin domin in fassara musu in na samu hali. To mutane da dama sun turo nasu, sai dai an yi rashin sa'a na rasa list ɗin, hakan ya sa bani da sunayen a tare da ni. Da haka nake ba kowa haƙuri tare da fatan za a sake turo sunayen waƙoƙin domin na fara shirya sabon list. Amma a daure a rubuta cikakken sunan waƙa da kyau.

Nagode, Allah ya bar zumunci.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

FASSARAR WAƘAR BURJKHALIFA


🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

Fassarar Waƙar Burjkhalifa


• Waƙa - Burjkhalifa

• Fim - Laxmmi Bomb

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2020

• Sauti - Shashi - Dj Khushi

• Rubutawa - Gagan Ahuja

• Kamfani - Zee Music Company

• Rerawa - Shashi - Dj Khushi & Nikhita GandhiMATASHIYA: Burj Khalifa wani dogon gini ne da ke birnin Dubai a United Arab Emirates. Tsawon ginin ya kai mota 829.8 wanda hakan ya bashi damar zama gini mafi tsawo a duniya. Taj Mahal kuma wani gini ne mai farin fenti da ke kudancin kogin Yamuna na garin Agra. Mughal emperor Shah Jahan ne ya bada izinin gina shi a shekara ta 1632 domin ya rufe kabarin matarsa Mumtaz Mahal. Ginin yana ɗaya daga cikin gine-ginen da aka fi so a duniya, haka kuma yana daga cikin abubuwan ban mamaki bakwai na duniya da aka ayyana, kuma ana alaƙanta ginin da soyayya. Kylie Jenner kuma wata kyakkywar mace ce da ke harkar kayan kwalliya kuma ta shahara a duniya ta wannan fanni. Ita kuwa FIFA, ita ce babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya. 


• Hot Tere Manner Ni, Manner Ni...

Ɗabi'arki zazzafa ce. 

• Chhapte Tere Banner Ni, Banner Ni... Tere Banner Ni...

Har a jikin allunan talla ake manna ki. 

• Hot Tere Manner Ni, Chhapte Tere Banner Ni
Ɗabi'arki zazzafa ce, Har a jikin allunan talla ake manna ki. 

• Fashion Tu Kardi Jiven Kylie Jenner Ni

Salonki iri ɗaya da na Kylie Jenner

• Ho Munda Thakda Nahi Kar Kar Ke (x2)

Gayu ba sa gajiya. 

• Teriyaan Tareefan...

Da yabonki. 

• Jee Karda Dila Doon, Tainu Burj Khalifa

Zuciyata na so ta siya miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa, Ho Tainu Burj Khalifa

(siya) miki Burj Khalifa, (siya) miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa 

(siya) miki Burj Khalifa,

• Ho Tainu Burj Khalifa, Tainu Burj Khalifa

(siya) miki Burj Khalifa,siya) miki Burj Khalifa 

• Ho Tainu Burj Khalifa, Tainu Burj Khalifa Ho

(siya) miki Burj Khalifa,siya) miki Burj Khalifa 

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

• Yeah!

• Ho Tainu Vekh Ke Chadh Gaye Ishqe

Da ganinki sai na kamu da sonki. 

• Tu Diamond Wangu Lishke

Sai ƙyalli kike yi kamar lu'ulu'u 

• Ho Tainu Vekh Ke Chadh Gaye Ishqe

Da ganinki sai na kamu da sonki. 

• Tu Diamond Wangu Lishke

Sai ƙyalli kike yi kamar lu'ulu'u

• Na Karni Siftaan Taj Mahal

Ba sa yabon Taj Mahal haka. 

• Jinni Tere Baare Likhde

Kamar yadda suke yabonki. 

• Oh Munde Tainu Follow Karde

Gayu sai binki suke yi. 

• Munde Tainu Follow Karde

Gayu sai binki suke yi. 

• Chhad Gaye Soccer Fifa

Suna barin ƙwallon ƙafa da FIFA ma gaba ɗaya. 

• Jee Karda Dila Doon, Tainu Burj Khalifa

Zuciyata na so ta siya miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa, Ho Tainu Burj Khalifa

(siya) miki Burj Khalifa, (siya) miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa 

(siya) miki Burj Khalifa

• Ho Tainu, 

(siya) miki 

• Tainu, Ho Tainu

(siya) miki 

• Tainu

(siya) miki 

Yeah Aye

• Hot Mere Manner Ni, Oh... O...

Ɗabi'ata zazzafa ce. 

• Chhapde Mere Banner Ni, Oh Yeah...

Har a jikin allunan talla ake manna ni. 

• Hot Mere Manner Ni

Ɗabi'ata zazzafa ce. 

• Chhapde Mere Banner Ni

Har a jikin allunan talla ake manna ni. 

• Look Ton Jealous Kardi Ae, Kylie Jenner Ni

Kyawuna har sa Kylie Jenner kishi yake yi. 

• Mere Husn De Charche Charche (x2)

Irin yabon da ake yi wa Kyawuna. 

• London To America

(ya watsu) daga Landan zuwa Amurka. 

• Mundeya Dilaade Mainu Burj Khalifa

Ɗan gaye! Ka siya mini Burj Khalifa. 

• Mainu Burj Khalifa, Ho Mainu Burj Khalifa

(siya) mini Burj Khalifa, (siya) mini Burj Khalifa. 

• Mainu Burj Khalifa

(siya) mini Burj Khalifa

• Ho Mainu Burj Khalifa, Mainu Burj Khalifa 

(siya) mini Burj Khalifa, (siya) mini Burj Khalifa. 

• Ho Mainu Burj Khalifa, Mainu

(siya) mini Burj Khalifa, (siya) mini Burj Khalifa

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

Share:

FASSARAR WAƘAR CHAL TERA SHUKRIYA


Fassarar Waƙar Chal Tera Shukriya


• Waƙa - Chal Tera Shukriya

• Fim - Sadak 2

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2020

• Sauti - Jeet Gannguli

• Rubutawa - Rashmi Virag

• Kamfani - Sony Music

• Rerawa - Shreya Ghoshal

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 
 

• Zindagi Chal Tera Shukriya

Ya ke rayuwata! Ina godiya a gareki. 

• Shayad Mile Na Tu Kal Ki Subah

Ta yiwu ba za mu haɗu a safiyar gobe ba. 

• Jo Diya Humne Hans Ke Liya

Duk abin da ka bani, na karɓe shi da murmushi. 

• Aye Zindagi Chal Tera Shukriya

Ya ke rayuwata! Ina godiya a gareki. 

• Har Saans Ka, Har Khwaab Ka

Wa dukkan numfashi, wa dukkan mafarki. 

• Ummeed Ke Sailaab Ka

Wa tekun burika/fata. 

• Tujhse Judi Har Baat Ka, Shukriya...

Godiya ga dukkan wani abu da ke da jiɓi da kai. 

• Teri Dhoop Ka, Barsaat Ka

Wa hasken rana, Wa ruwa. 

• Thaama Jise, Uss Haath Ka

Wa hannun da ke riƙe da nawa. 

• Acche Bure Haalat Ka, Shukriya...

Godiya ga dukkan wani yanayi mai kyau ko mara kyau. 

• Shukriya... (x4)

Nagode. 

• Milna Bichhadna, Aana Jaana

Haɗuwa da rabuwa, zuwa da tafiya. 

• Taiy Hai Sab Kuch Pehle Se

Komai a ƙaddare yake. 

• Pyaar Bhare Pal, Baandh Ke Rakhle

Ka ajiye kyakkyawan tunani (a ƙwaƙwalwarka) 

• Baaki Sab Kuch, Rehne De

Ka manta da komai. 

• Kuch Nahi, Haath Aayega Yahaan

Ba Za ka cimma komai ba anan. 

• Phir Bhi Aye Zindagi Tera Shukriya...

Amma wa dukkan abin da ka bani, nagode maka. 

• Kuch Nahi, Haath Aayega Yahaan

Ba Za ka cimma komai ba anan. 

• Phir Bhi Aye Zindagi Tera Shukriya...

Duk da haka wa komai, ya ke rayuwa, ina godiya a gare ki. 

• Alvida, Rehna Tu Khush Sada

Sai anjima kenan, fatan za ka kasance cikin farin ciki na har abada. 

• Shayad Mile Na Tu Kal Ki Subah

Ta yiwu ba za mu haɗu a safiyar gobe ba. 

• Alvida, Rehna Tu Khush Sada

Sai anjima kenan, fatan za ka kasance cikin farin ciki na har abada. 

• Shayad Mile Na Tu Kal Ki Subah

Ta yiwu ba za mu haɗu a safiyar gobe ba. 

• Om Namah Shivaay... (x4)

Sujjada da girmamawa ga ubangiji shiva. 

• Namah Shivaay

Sujjada da girmamawa ga ubangiji shiva. 

• Shukriya... (x2) 

Nagode.


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 10

✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            10


181. Kajjur - dabino
182. Paleelu - gyaɗa
183. Kooragaaya - kayan lambu
184. Mokkabutta - masara
185. Keera dhosakaaya - kwakwamba
186. Parugethu - gudu
187. Puttinaroju subhashankalu - Barka da murnar ƙara shekara
188. Konadam - siyayya
189. Sare - rijiya
190. Chedu - maras kyau
191. Paravaaledu - shikenan
192. Edhi? - wanne?
193. Emi? - mene?
194. Ekkada? - Ina?
195. Eppudu? - Yaushe?
196. Endhuku? - akan me?
197. Etlu? - ta yaya?
198. Yavaru? - waye?
199. Entha? - guda nawa?
200. Enni? - nawa?


Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

DARUSSAN TELUGU 09


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            09

161.i Vellaledhu - ban tafi ba
162. Mabbu -hazo
163. Manchu - danshi
164. Sambandham - alaƙa/dangantaka
165. Ivvagalara - za ka/ki iya bayarwa?
166. Premisthunnanu - na faɗa soyayya
167. Sabbu - Sabulu
168. Gurtu chestaara? - ka/kin tuna ni?
169. Durvaasana - wari
170. Nidhram - bacci
171. Navvu - murmushi
172. Bhojanam - abinci
173. Pandlu - 'ya'yan itatuwa
174. Draksha - inabi
175. Nimmakay - lemon tsami
176. Kamala pandu - lemo
177. Boppaya - gwanda
178. Danimma - ruman
179. Cheruku - rake
180. Jeedi Pappu - Yazawa


Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 08


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            08

141. Kathi - Wuƙa
142. Paatralu - tasa
143. Thaalchadam - shafa/shafawa
144. Pattinchikuno - rashin damuwa da
145. Dwaaramu - ƙofar gida
146. Nadikattu - ɗamara
147. Pilavagalaara? - za ka kira?
148. Phalahaarashaala - gidan cin abinci
149. Dheggarilo - kusa-kusa
150. Vididhi gruhum - loji
151. Cheyocha? - za mu iya?
152. Endhuku Vellatledu - me ya sa baka yi ba?
153. Kirana dhukanam - shagon siyar da sarƙoƙi
154. Chirunaama - adireshi
155. Chudavacha - zan iya ganin?
156. Maarchokovachu - ana iya canjawa
157. Istapaduthunnara - kana/kina ra'ayi?
158. Vellaru - ya tafi
159. Okasaari - sau ɗaya
160. Vellanu - na tafi

Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 07


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            07

121. Velthunnanu - tafiya zan yi
122. Mee vadha - wa kai/wa ke
123. Somaripothu - malalaci
124. Kastamunadhi - Abu mai wahala
125. Veldham - Mu tafi
126. Vasthunnara? - Yana zuwa?
127. Cheyyaku - Kada ka/ki aikata
128. Evarkosamyna? - da mutum?/Sai kuma wa?
129. Veldhama? - muna iya tafiya?
130. Bhavaalu - taɓi
131. Athanu - shi (ba mutuntawa)
132. Athaniki - shi (da mutuntawa)
133. Marchipondi - manta kawai
134. Chesaaru - ya aikata
135. Usnogratha - zazzaɓi
136. Saukaryanga
137. Kaavala? - kana/kina so?
138. Pattukuntaara - ka kama shi?
139. Jalleda - rariya 
140. Penamu - kwanan rufi

Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 06


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            06

101. Vulli kaada - Albasa mai lawashi
102. Moththam - Jimilla
103. Ichaara? - ka/kin samu kuwa?
104. Ichaaru - Na samu
105. Chinthinchakandhi - Kada ka/ki damu
106. Mirchi - Barkono
107. Kukka godugu - tauriƙiƙi
108. Pudeena - na'a na'a
109. Vaamu - basil
110. Mirapa - shambo
111. Bhataani - pea
112. Aava aakulu - mustar/mustard
113. Endu mirapakaaya
114. Dalchina chekka - kirfa
115. Sompu - Anisi
116. Pilavandi - kira
117. Vantariga - a kaɗaice
118. Undha? - akwai?
119. Jarigindhi - abin da ya faru
120. Thelusu - sani


Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 5


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            05


81. Panchadara - sukari
82. Agni - Wuta
83. Aapandi - tsaya
84. Donga - ɓarawo
85. Panchangam - kalanda
86. Thedi - kwanan wata
87. Iroju - yau
88. Ninna - jiya
89. Repu - Gobe
90. Prathiroju - kullum
91. Vaaram lo okasaari - sau ɗaya a sati
92. Roju - yini
93. Subhakanshalu - Taya murna
94. Prayanam - tafiya
95. Konni - wasu
96. Konchem - kaɗan
97. Manchi - Da kyau
98. Avunu - Eh
99. Kaadhu - a'a
100. Lekha - wasiƙa

Zan ci gaba in sha Allah
©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 4


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            04

61. Tholutheeyadam - ferewa
62. Veyinchadam - gasawa
63. Veginchadam - soyawa
64. Koyyadam - yankawa
65. Kalapadam - cakuɗawa
66. Uthakadam - Wankewa
67. Visaradamu - niƙawa
68. Vanta gadhi - ɗakin girki
69. Dhahamga - ƙishirwa
70. Kuchabacha? - zan iya zama?
71. Kurchondi - eh zauna
72. Velluli - tafarnuwa 
73. Allam - Citta
74. Lavangaalu - kanunfari
75. Nalla geelakarra - Masoro
76. Vellandi - tafi
77. Vadhalandhi - barshi
78. Paavu - ƙafa
79. Jam Pandu - gwaiba
80. Mamidi Pandu - mangwaro


Zan ci gaba in sha Allah 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

DARUSSAN TELUGU 03


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            03

41. Manam - Mu
42. Illu - gida
43. Amma - mama
44. Nanna - Baba
45. Annaya - babban yaya
46. Thammudu - ƙani
47. Akka - yaya mace
48. Chelli - ƙanwa
49. Thathaiya - kaka namiji
50. Ammama - kaka mace
51. Nuvvu - kai
52. Meeru - kai (mutuntawa)
53. Gamyasthaanamu - bigire
54. Thadupari - gaba/na gaba
55. Vellipovadam - fita/kofar fita
56. Ullipaaya - Albasa
57. Aalugadda - Dankali
58. Paalakoora - Alayyaho
59. Tamaata - tumatir
60. Chinta Pandu - tsamiya

Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            02

21. Guddu - Ƙwai
22. Idhi thiyaga undhi - Yana da zaƙi
23. Idhi uppuga undhi - yana da gishiri
24. Chaala Manchidhi - Yayi kyau/dakyau
25. Naaku thelusu - Na sani
26. Nijama? - Dagaske?
27. Nannu khsaminchandi - Ka/ki yafe min 
28. Veldham - Muje
29. Jiguru - Danƙo
30. Kaadhu - A'a
31. Sneham - Aboki/ƙawa
32. Aaharam - Abinci
33. Dhanyavaadalu - Nagode
34. Naaku Neeru avasaraam - Ina buƙatar ruwa
35. Paravaledu - Shikenan
36. Avunu - Eh
37. Subhodayam - Barka da safiya.
38. Madyanam - Barka Da Rana
39. Sayantram - Yamma/Barka da yamma
40. Nenu - Ni


Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

DARUSSAN TELUGU 01


✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            01

 1. Alphaahaaram - Karin Kumallo
 2. Kadukondi - Wanke shi
 3. Chudu - Gashi/kalle shi
 4. Pani - Aiki
 5. Kaaryaalayam - Ofishi
 6. Ippude - Yanzu
 7. Ethu - tsayi
 8. Chala - sosai
 9. Mukyamynadhi - Muhimmanci
10. Navvuthunaaru - Dariya
11. Manam - Mu
12. Chillika - Cokali Mai yatsu
13. Chemcha - Cokali
14. Vechi - Jira
15. Theliyadhu - Ban sani ba
16. Batta - Kayan sawa
17. Arati - Ayaba
18. Kobbari kaaya - Kwakwa
19. Puchakaaya - Kankana
20. Uppu - Gishiri

Zan ci gaba in sha Allah

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

SHARHIN FIM ƊIN THERI


SHARHIN FIM ƊIN THERI 

Theri (ma'ana tartsatsi) fim ɗin Indiya ne da aka shirya shi cikin harshen Tamil kuma ya fita ne a cikin shekara ta 2016. Wannan fim ya yi matuƙar kyau kuma ya samu karɓuwa a wajen 'yan kallo. 

• Bada Umurni - Atlee

• Ɗaukar Nauyi - Kalaipuli S. Thanu

• Labari/Rubutawa - Atlee & S. Ramana Girivasan
(Dialogue)

• Sauti/Take - 
G. V. Prakash Kumar

• Horas Da 'Yan Wasa - 
George C. Williams

• Tacewa - Ruben

• Kamfanin Da Ya Shirya - 
V. Creations

• Kamfanin Da Ya Yaɗa - 
SPI Cinemas (Chennai)
Friday Film House (Kerala) 
Carnival Motion Pictures (Kerala)

• Ranar Fita - 14 April 2016

• Tsayin Shirin - mintuna 158 

• Ƙaaa - India

• Harshen Shiri - Tamil

• Kasafi - est. ₹75 crore

• Kasuwancin Box office
est. ₹160 crore

An fara ɗaukar wannan shiri ne a farkon watan Yulin 2015 a garin Chennai. An ɗauki sashen faɗace-faɗacen shirin ne a cikin watan Nuwambar wannan shekara, sai dai kuma an samu matsala a yayin ɗaukar sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a garin na Chennai. Hallau dai, rashin yanayi mai kyau ya sa suka soke ɗaukar wani sashe na shirin a ƙasar sin su ka koma Bangkok. 

An saki wannan fim ne a ranar 14 ga watan Afrilun 2016. Haka kuma an fassara shirin zuwa harshen inda aka sa masa suna Policeodu. A ƙarshen kwanakinsa shida da fara haskawa a sinima, Theri ya kawo kuɗi kimanin ₹1 billion (US$14 million). A United Kingdom kuwa, ya karya tarihin da fim ɗin Enthiran (2010) ya kafa na box office collection for the first weekend. Vijay ya lashe gasar Entertainer of the Year da rawar da ya taka a shirin a bikin 6th South Indian International Movie Awards da aka yi a shekarar 2017

LABARIN SHIRIN 

Joseph Kuruvilla yana rayuwa ne cikin jin daɗi da nishaɗi a birnin Kerala tare da 'yarsa mai suna Niveditha wacce ake kira da Nivi. Yana kuma sana'a biredi tare da Rajendran. A haka dai har ƙaddarar rayuwa ta sa ya haɗu da Annie wacce ita kuma malama ce a makarantar su Nivi, har dai suka zama abokai. 
Bayan wasu faɗi tashi gami da tataburza tare da 'yan dabar yankin, Annie sai ta fahimci cewa Joseph ba kowa bane face marigayi Vijay Kumar. Joseph ya ba Annie labarinsa a matsayin Vijay, amma ya gargaɗeta da kada ta faɗa wa Nivvi. 

Shekaru biyar da suka gabata, Vijay Kumar nagartaccen ɗan sanda ne mai gaskiya da ya kai matsayin DCP a Chennai. Watarana sai ya karɓi kundin wani laifi na fyaɗe da kuma kisa da aka yi wa wata ɗalibar na'ura mai suna Raji. Binciken da yayi sai ya gano cewa ba kowa bane ya aikata wannan laifi Ashwin, ɗan gidan Labor Minister Vanamaamalai. Vijay sai ya kashe Ashwin kuma ya bayyana kansa a matsayin makashin wa Vanamaamalai wanda shi kuma ya sha alwashin ɗaukar fansa a kansa. Ana cikin haka ne kuma, sai Vijay ya faɗa soyayyar wata ɗalibar likitanci mai suna Mithra inda ba a jima ba suka yi aure jikin jin daɗin rayuwa. 

Sai dai kash! Jin daɗin su bai ɗore ba, domin kuwa Vanamaamalai, da ɗan uwansa Ratnam tare da 'yan dabarsu sun faɗo musu gida inda suka kashe Mithra da mahaifiyar Vijay. Sannan kuma sun jigata shi kansa Vijay ɗin matuƙa. Da har sun yi niyyar halaka jaririyarsu Nivvi, amma sai Mithra ta samu damar cetonta yayin da take gab da mutuwa. Mithra ta roƙi Vijay da ya kula mata da 'yarta a bayan ranta tare da tirsasa shi ya yi mata alƙawarin zai bar aikin ɗan sanda gaba ɗaya. Vijay sai ya yi ƙaryar ya mutu, ya canja sunansa zuwa Joseph Kuruvilla ya kuma koma Kerala tare da Nivvi tare da abokinsa kwanstabul Rajendran domin ya kare Nivi daga Vanamaamalai da 'yan dabarsa. 

Watarana, yayin da Nivi ta hau wata motar bas tare da sauran ɗalibai da nufin da nufin zuwa yawon buɗe ido, sai birkin motar ya karye motar ta faɗa ruwa da ƙyar da siɗin goshi dai Vijay da Annie da Rajendran tare da mutanen wurin suka ceto Nivi da sauran yaran. Daga baya sai Vijay ya gano cewa Vanamaamalai ne ya yi sanadiyar faruwar wannan hatsari da nufin ya kashe Nivi bayan ya gano suna raye. Hakan yasa Vijay ya harzuƙa kuma ya sha alwashin ajiye alƙawarin da ya ɗauka ya kashe Vanamaamalai kawai kowa ya huta. 

Daga nan sai Vijay ya fara aiki a matsayin fatalwar kansa inda ya fara yi wa yaran Vanamaamalai ɗauki ɗai-ɗai. Da fari dai ya kashe SipetaKarikalan wanda yana daga cikin yaran Vanamaamalai da aka je gidansa da su aka kashe Mithra. 'yan sanda sai suka ruɗe, domin an yi kisan ne a cikin ofishin kuma su duk tsammaninsu shi ne Vijay ya mutu. 

Daga nan fa sai mace-mace ya fara ƙaruwa inda Vijay ya hankaɗo Ratnam daga saman ginin da yake yi ya mutu. Daga nan kuma sai aka fara zargi Vanamaamalai saboda sun samu saɓani, hakan ya sa dole shima ya ɓoye. Daga ƙarshe dai sai Vijay ya bari yaran Vanamaamalai suka kama shi saboda ya shiga mafakarsa. Bayan ya kashe shi tare da yaran nasa sai ya sagale shi a sama ya bar wajen. Da 'yan sanda suka zo suka ga ba kowa sai gawawaki, sai hankali fa ya ƙara tashi.


Ashe kwamishinan 'yan Sandan Chennai wato Sibi Chakravarthi ya san cewa Vijay yana raye, kuma shi ne ma ya ɗauke shi aiki a asirce domin ya yaƙi ta'addanci, amma kuma sai ya fito ya ke bayyanawa duniya cewa Vijay fa ya mutu. 

Bayan wasu shekaru, sai Vijay, Nivi, Annie da Rajendran suka koma Ladakh inda Vijay ya canja suna zuwa Dharmeshwar. Amma ya ci gaba da aikinsa na kawar da ta'addanci a asirce. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

TALLAR LAXMMI BOMB TA KAFA TARIHI


TALLAR LAXMMI BOMB TA KAFA TARIHI 

Izuwa yanzu dai duk inda ka duba a shafukan yanar gizo babu labarin da ya fi jan hankali a harkar fina-finan Indiya sama da sabuwar tallar shirin jarumi Akshay Kumar da ta fita a jiya juma'a mai suna Laxmmi Bomb. Tarihi ya kafu, kuma mutane sun sha mamaki cikin kofuna bayan tallar ta haɗa jimillar makallata miliyan saba'in (70 Million Views) a cikin awoyi ashirin da huɗu bayan fitar tallar. Hakan ya sa ta zama talla mafi kalluwa daga cikin tallolin fina-finan Indiya baki ɗaya. Sai dai abin tambayar shi ne? Wani saƙo wannan fim ke ɗauke da shi? Kuma menene 'yan kallo za su tsammata daga wannan fim? Ga wasu abubuwa da zan iya tsakurowa daga cikin tallar wannan shiri. 

 1. FIM ƊIN AKSHAY KUMAR NE: Wanda duk ya san wanene jarumi Akshay Kumar to baya buƙatar sai an yi masa dogon sharhi akan abinda jarumin zai iya yi a fim. Ko da yake wannan fim ya zo da wata sabuwar siga da ba a taɓa ganin jarumin a cikinta ba, babu shakka shirin na ɗauke da duk wani abu da masoyan jarumin ke so dangane da shi. 
 
 2. HAƊI NA MUSAMMAN: Wannan shiri shi ne fim na farko da jarumi Akshay Kumar zai fito tare da tsaleliyar kyakkywar jarumar nan mai tashe wato Kiara Advani. Hakan ya jawo hankalin mutane da dama duba da irin ganiyar nasara da kowannensu ke ciki a yanzu tare kuma da tunanin abin da zai ka iya fitowa daga gare su idan suka haɗu a fim tare. Kuma kamar yadda tallar ta nuna, haɗin zai bada citta har da masoro. 
 
3. FIRGICI DA BAN TSORO: Fim ɗin Laxmmi Bomb fim ne na ban tsoro, don haka 'yan kallo sai su shirya. Domin kuwa mun gano jarumi Akshay Kumar yayin da fatalwar wata mace ta shiga cikinsa inda kafin ka ce kwabo ya canja daga mai barkwanci zuwa masheƙi. 

 4. NISHAƊI: Bisa ga dukkan alamu wannan shiri na Laxmmi Bomb ya shirya tsaf domin tabbatar wa da duniya laƙabin nan da aka kiran jarumi Akshay Kumar da shi wato Mr. Khiladi. Domin kuwa tallar Laxmmi Bomb ta nuna mana irin nishaɗin da za a samu a cikin shirin musamman ta fuskar barkwanci. 

 5. TARIN KODUMO: Duba da irin yadda wannan talla ta samu karɓuwa, na san ko ba a faɗa ba za ku iya fahimtar gamsarwar da ke cikinta. Akwai Suburbuɗa, calikanci, soyayya, waƙa mai daɗi, ban tsoro, madarar kafce da kuma sunƙi-sunƙin buhunan kodumo! 

Tabbas alamu sun nuna za ta fashe sosai a bikin diwalin bana. Shin ko Akshay Kumar zai zama sabon sarkin Diwali da Laxmmi Bomb kamar yadda yanzu ya zama sabon sarkin Bollywood? Lokaci ne zai bamu wannan amsar. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

 
Share:

FASSARAR WAƘAR DIL HAARA REFassarar Waƙar Dil Haara Re 

• Waƙa - Dil Haara Re 

• Fim - Tashan

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2008

• Sauti - Vishal-Shekhar

• Rubutawa - Piyush Mishra

• Kamfani - YRF Music

• Rerawa - Sukhwinder Singh 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Pagal manwa, kaise bhage re

Mahaukaciyar zuciya tana tsere.

• Pagal manwa

Mahaukaciyar zuciya. 

• Tabadtod naach loon naach loon naach loon

Bari in yi ta tiƙar rawa babu tsayawa. 

• Naach loooon re

Bari in yi rawa. 

Ho oh

• Chappan taare thod naach loon

Zan kaɓo taurari 56 daga sama kuma in yi rawa. 

• Suraj chanda mod naach loon

Zan yi rawa in lauya rana da wata. 

• Ab toh tabadtod naach loon

Yanzu kam zan yi rawa babu tsayawa. 

• Main toh banjara re

N mai bulayi ne. 

Ho oh

• Chappan taare thod naach loon

Zan kaɓo taurari 56 daga sama kuma in yi rawa. 

• Suraj chanda mod naach loon

Zan yi rawa in lauya rana da wata. 

• Ab toh tabadtod naach loon

Yanzu kam zan yi rawa babu tsayawa. 

• Main toh banjara re

N mai bulayi ne. 

• Oh banke aawara main kis mele pe pahunch gaya hoon

Ina tafe sakaka da ni, me na cimma? 

• Koi toh roko, kho jaoon re

Don Allah wani ya dakatar da ni, zan iya ɓacewa fa. 

• Masti ka maara main kya bolun yeh kise kahun main

Cike nake da fasadi, me zan iya cewa? Wa zan faɗa wa? 

• Dil ka main haara ho jaoon re

Na zamo wanda ya rasa zuciyarsa. 

• Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Oh yaara re

Ya masoyiyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Aaj akele har ek haalat se aage

A yau kaɗai, na yo nesa da dukkan wani irin yanayi. 

• Zubani baat se aage chala aaya

Na yo nesa daga dukkan wata furtacciyar kalma. 

• Har taare ki aankh mein aankhe dale

Na tsayar da idanuwana akan idanun kowane tauraro. 

• Chandni raat se aage chala aaya

Na gabato zuwa gaba fiye da dare mai cike da hasken wata. 

• Kisko bolun main kaise bolun main

Wa yakamata in faɗa wa hakan, ta yaya zan faɗi hakan. 

• Koi mujh ko bata ke ja

Don Allah wani ya taimake ni ya tafi. 

• Koi toh bata ja re

Don Allah wani ya faɗa min. 

• Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Oh yaara re

Ya masoyiyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

Oh ho

• Rasta bola arre ki thak jayega

Hanyar na faɗa min cewa "za ka gaji". 

• Beech mein ruk jayega, abhi ruk ja

Za ka tsaya a hanya yayin da ka kai rabi, gara ka tsaya yanzu. 

• Arre aage jaake garaj ke aandhi hogi

(Idan ka) Ci gaba, akwai iskoki masu kaɗawa da ƙarfi. 

• Garaj ke toofan hoga abhi ruk ja

Akwai hadari mai rugugi, gara ka tsaya yanzu. 

• Main toh deewana, bola aa jana

Bani da hankali, sai nace duk su zo. 

• Donon sang mein chalenge haan

Dukkanmu za mu tafi tare. 

• Aa bhi ja, tu aaja re

Taho mana yanzu, muje mana. 

• Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 
• Oh yaara re

Ya masoyiyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina. 

• Tabad tod naach loon… hoiiii

Bari in yi rawa babu tsayawa. 

• Dil haara, Dil haara, Dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata. 

• Dil haara re, Dil haara re, dil haara re

Na rasa zuciyata. 

• Main haara re

Na rasa. 

• Dil haara haara dil haara haara main haara

Na rasa zuciyata, kuma na rasa kaina.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.comShare:

FASSARAR WAƘAR KALANK

🎷🇮🇳🎸🇳🇬🎸🇮🇳🎸🇳🇬🎸🎷

👨🏻‍🎤ARIJIT SINGH FANS NIGERIA👨🏻‍🎤

🎷🇮🇳🎸🇳🇬🎸🇮🇳🎸🇳🇬🎸🎷

KE GABATAR MUKU DA SHIRIN 

🎡🎤🎧🎡FASSARAR WAƘOƘIN ARIJIT SINGH🎡🎤🎧🎡

Tare da

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

Fassarar Waƙar Kalank (Title Track)


• Waƙa - Kalank (Title Track)

• Fim - Kalank

• Harshe - Hindi - Hausa 

• Shekarar Fita - 2019

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Amitabh Bhattacharya

• Kamfani - Zee Music Company

• Rerawa - Arijit Singh

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman • Hawaaon Mein Bahenge

Za mu tafi a tafiyar waɗannan Iskokin. 

• Ghataon Mein Rahenge

Za mu rayu a sararin samaniya. 

• Tu Barkha Meri

Ke ce ruwan sama na. 

• Main Tera Baadal Piya

Ni kuma ni nine girgijenki, abar sona. 

• Jo Tere Na Huve Toh

Idan har nan zamo naki ba. 

• Kisi Ke Na Rahenge

Ba kuwa zan zamo na kowa ba. 

• Deewani Tu Meri

Ke ce mahaukaciyar masoyiyata. 

• Main Tera Paagal Piya

Kuma nima mahaukacin masoyinki ne masoyiya. 

• Hazaaron Mein Kisi Ko Taqdeer Aisi

Irin wannan sa'ar ɗaya cikin miliyan ne kaɗai ke samu. 

• Mili Hai Ik Ranjha Aur Heer Jaisi

Ɗaya Kamar Ranjha ɗayan kuma kamar Heer

• Na Jaane Ye Zamaana Kyun Chaahe Re Mitaana

Ban san dalilin da ya sa duniya ke so ta goge wannan ba. 

• Kalank Nahi Ishq Hai Kaajal Piya… (x2)

So ba kamar tabo yake ba, kamar kwalli yake. 

• Piya, Piya, Piya Re... Piya Re… Piya Re...

Ya Masoyiyata! Ya Masoyiyata. 

• Piya, Piya, Piya Re... Piya Re… Piya Re...

Ya Masoyiyata! Ya Masoyiyata. 

• Duniya Ki Nazron Mein Yeh Rog Hai

A idon duniya kamar cuta yake. 

• Ho Jinko Woh Jaane Ye Jog Hai

Waɗanda suka faɗa cikinsa kuma sun fahimce shi ne kamar tunani. 

• Ik Tarfa Shayad Ho Dil Ka Bharam

Idan har na ɓangare ɗaya ne, to wannan gizo ne zuciya ke yi wa mutum. 

• Do Tarfa Hai Toh Yeh Sanjog Hai

Amma idan na ɓangare biyu ne, to ƙaddara kenan. 

• Layi Re Humein Zindgani Ki Kahaani Kaise Mod Pe

A wane irin juyi kuma labarin rayuwa ya jawo mu? 

• Huve Re Khud Se Paraaye

Mun zama baƙi wa kawunanmu. 

• Hum Kisi Se Naina Jod Ke

Bayan mun kalli wasu. 

• Hazaaron Mein Kisi Ko Taqdeer Aisi

Irin wannan sa'ar ɗaya cikin miliyan ne kaɗai ke samu. 

• Mili Hai Ik Ranjha Aur Heer Jaisi

Ɗaya Kamar Ranjha ɗayan kuma kamar Heer

• Na Jaane Ye Zamaana Kyun Chaahe Re Mitaana

Ban san dalilin da ya sa duniya ke so ta goge wannan ba. 

• Kalank Nahi Ishq Hai Kaajal Piya… (x2)

So ba kamar tabo yake ba, kamar kwalli yake. 

• Main Tera, Main Tera, Main Tera, Main Tera…

Ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

• Main Gehra Tamas Tu Sunhera Savera

Ni baƙar jiƙaƙƙiyar wuriya ce, ke kuma safiya mai haskawa. 

• Main Tera, Main Tera, Main Tera, Main Tera…

Ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

• Musaafir Main Bhatka Tu Mera Basera

Ni ɓataccen matafiyi ne, ke ce mafaka ta. 

• Main Tera, Main Tera, Main Tera, Main Tera…

Ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

• Tu Jugnu Chamakta, Main Jungle Ghanera

Ke ƙwaro ce mai haske, ni kuma daji ne mai duhu. 

• Main Tera Aa...

Ni naki ne. 

• O Piya Main Tera, Main Tera, Main Tera

Masoyiyata ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

• Main Tera, Main Tera, Main Tera, Main Tera…

Ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

• Ho... Main Tera, Main Tera, Main Tera, Main Tera…

Ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

• O... • Main Tera, Main Tera, Main Tera, Main Tera…

Ni naki ne, ni naki ne, ni naki ne. 

Ooo… O… Oo…


ƘARIN HASKE: (This is a reference to 

• Heer-Raanjha/Raanjhanaa wasu shahararrun masoya ne da aka taɓa yi a ƙasar Indiya waɗanda shahararsu ta kai shahara irin ta Romeo da Juliet. Amma a cikin wannan waƙar Heer na magana akan macen ne yayin da Raanjha kuma ke magana akan namjin tare da alaƙanta girman soyayyarsu da na waɗancan.


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form