Barka da warhaka

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

YADDA ZA KA CI GALABA AKAN SHAIƊAN


YADDA ZA KACI GALABA AKAN SHAIƊAN
-
GABATARWA:
Muhammad Umar Baballe 
-
"Shaiɗan la'ananne wata halitta ce da malamai ma kansu suka ƙarawa junansu ilmi wajen fayyace cewa shin shima acikin jinsin mala'iku yake, ko kuwa acikin jinsin aljanu yake, to wannan dai ba shine abinda dubawa ba, abinda dubawar anan shine sanin hanyar da za kabi domin ka kuɓuta daga kaidinsa ƙullalle"
-
"Shaiɗan ya sha alwashi a gaban Allah, a daidai lokacin da Allah maɗaukakin sarki ya fifita annabi Adam akansa, ya kuma umurce shi dayin sujjada ga annabi Adam alaihissalam, sai shaiɗan yaƙi yayi, sai Allah ya kore shi daga cikin rahamarsa"
-
"Daga nan ne sai shaiɗan ya ɗauki alwashin sai ya dilmiyar da dukkanin ilahirin zurri'ar annabi Adamu domin goge wancan takaici na nesanta shi daga rahamar Allah da akayi"
-
Dalilin haka sai ya zamto cewa kowa yana cikin hatsarin shaiɗan sai wanda Allah ya tseratar, to kaima domin neman tserata daga gareshi kanada aiyuka a gabanka, amma ga kaɗan daga cikinsu:
-
💦Yawan ambaton Allah.
💦Neman kariya daga shaiɗan.
💦Zikiran safiya da maraice.
💦Nisantar aiyukan shaiɗan.
💦Nisantar abinda Allah ya hana.
💦Zaƙewa aiyukan ɗa'a ga Allah.
-
"Waɗannan hanyoyi ne kaɗan daga cikin waɗanda za kayi ta'ammuli dasu wajen yin katanga a tsakanin ka da shaiɗan, musamman ma juriya wajen aikata kyawawan aiyukan da zasu daɗa kusantar dakai izuwa ga Allah"
-
"Wannan wani faɗa ne da yake a tsakãninka da shaiɗan, wanda kuma dole sai ɗaya yayi nasara akan ɗaya, kodai kayi nasara akansa, ko kuma shi yayi nasara akanka, amma idan ka nemi taimakon Allah sai kaga kaine kayi nasara akansa"
-
Ya Allah ka bamu ikon yin nasara akan shaiɗan la'ananne, Ameen.
-
✍🏿
Muhammad Umar Baballe
Share:

RUBUTACCIYAR WAƘAR TARNAƘIWAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA 

Tarnaki

Tarnaƙi hana miƙa 3x

Majaujawa sai cillawa
Sasari kuma ɗaurewa
Tarnaƙi mai zargewa
Takunkumi mai shaƙewa
Tarko mai kamawa
Turaku ko na ɗaurewa
Sarƙa rikicin gangan ƙasar uwa da uba nawa
Tarnaƙi hana miƙewa
Sasari hana rugawa
Garƙami wandon ƙarfe masaka ba ya zaunawa. 


Tarnaƙi hana miƙewa
Sasari hana rugawa
Garƙami wandon ƙarfe a saka ba a zauna ba.

Ubangiji masanin gaibu da baɗini da faken kowa 
Adalin sarki rabbu da yai hanin cutar kowa 
Mai huwacewar mulki daidai da halayyar kowa 
Na taho da buƙatata tsare ni kadda amin arwa, tsare ni kadda a min arwa. 

Ɗan Aminatu tsanina da so da koyin halaye
Mai gidan asahabati da ahal baiti da sufaye
Mai ɗabi'u kyawawa gami da tsarkin halaye 
Nai riƙo da abin ƙauna abin yabon sarari har ɓoye, sarari har ɓoye. 

Kama zuwa daga 'yancin kai zuwa a yau ban kore ba
Ina batun ilimi namu hallanzu dai ba mu ƙosa ba 
Da tattalin arzurƙanmu zuwa a yau ba mu kama ba 
Bare a kai ga ginin birane har yanzu ba mu wuce ƙauye ba 
A shekara hamsin baya magani ba mu samar ba 
A shekaru hamsin har yau ko Keke Napep ba mui ba 
Industry ba ta zauna ba 
Ruwa na sha ba mu samar ba 
Da laturun ba ta zauna ba 
Ga agric ba mu kama ba
Ga ilimi ba a samu ba
Rayuwa ta ƙabilanci, rikicin addinanci ba inda ba mu yi asasi ba. 

Ƙasar da ba ta da jirgin kanta ɗiyanta na zazzagawa
Ƙasar da ba ta asusun kanta ɗiyanta ke da kuɗin cashewa 
Ƙasar da babu zani a jikinta ɗiyanta ke da zanin ɗaurawa 
Mutum guda a cikin 'ya'yanta dubu ɗari da ta haifawa 
Ya tattare arzurƙanta yana rawa da bazar kowa 
Suna kiɗa da bazar kowa 
Wai ma'aikata aka samarwa ko 'yan yasa muka samarwa? 
Wai 'yan ceto muka zaɓowa ko cuta muka ɗaukowa? 
Wai ɗalibai muka yayewa ko ɓeraye muka yayewa? 
Ƙasar babata, ƙasar abbana, Nijeriya ta. 


Share:

SAMUN SOYAYYAR ALLAH DA MANZONSA


#SAMUN SOYAYYAR ALLAH DA MANZONSA ﷺ

#ABUBUWA GUDA UKU SUNA SANYAWA ALLAH DA MANZONSA SU SOKA

Dukkan wanda ya rike waɗan nan abubuwa guda uku, to zai sami SOYAYYAR ALLAH DA MANZONSA A gare shi, insha Allah. 
1-Ka zama mai gaskiya a cikin maganganunka
2-Kiyaye Amana da bayar da amana ga mai ita
3-Kyautatawa makwanci da abokin zama. 

Daga Anas bn Malik رضيَ الله عنه, yac, Manzon Allah ﷺ yace:-
*(Idan kuna son Allah da MANZONSA su so ku, to ku kiyaye halaye guda uku* :-
①-Gaskiya a cikin magana
②-Kiyaye Amana da bayar da amana ga masu ita 
③-Kyautatawa makwanci da abokin zama 
@السلسلة الصحيحة (2998)*

          Allah ne mafi sani 

Allah Ya bamu ikon kiyayewa, ya Allah ka azurta mu da soyayyarka da ta Manzonka a gare mu har zuwa mutuwa.
Share:

RUBUTACCIYAR WAƘAR BURI UKU A DUNIYAWAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA TARE DA FATI NIJAR 
Buri Uku A Duniya

Sarƙaƙiya guda uku
Tai sansani a zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya. 

Sarƙaƙiya guda uku
Tai sansani a zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya. 

Daure masoyi daure daure
Ka san lago na zuciya
Ka san abin buƙatar ruhi
Sarƙa ta sarƙe zuciya
Ni na yi durƙuson
Gwiwoyi kuka ka bi idaniya
Tanyo nake buƙata gunka
Buri uku a duniya
Na zo da mazubin ƙoƙona
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya. 

Ma-dama rayuwa na nan
Ruhi fa za ya wazaya
Ma-dama zuciya na nan
Buri fa za ya antaya
Ga rai da lafiya na nan
Tilas jiki ya hau ƙaya
Tsumma maƙunshe cuta na nan 
Sarƙaƙiya ƙarangiya 
Buri fa yai wa ruhi zobe 
Sarƙa ta ɗaure zuciya 
Buri uku a duniya 
Buri uku a duniya. 

Buri uku a duniya
Sun zam mini ƙarangiya
Sautin bugu na zuciya
Ya sa jiki galauniya
Sarƙaƙiya ƙarangiya
Buri uku a duniya
Burin cikinta zuciya
Na kasa buɗe zuciya
Ɗa zai ɓace a ragaya
Ceto jiki da zuciya.

Ruhi duka da zuciya
Fansa gareki gimbiya
Na gamsu babu karaya
Zan baki duka zuciya
Komai da ke a duniya 
Nau'in dukkansu dukiya 
Tarin kuɗi da dukiya 
Garken awaki saniya
Fansa gareki gimbiya
Burinki dukka duniya 
Share:

ASARA GA WANDA BA YA SALLOLIN NAFILA


ASARA GA WANDA BAYA YIN SALLOLIN NAFILA

*1-YIN NAFILA RAKA'A 12 A KOWANE YINI*

Banbanci tsakanin wanda yake kiyaye Sallolin nafila na yini da dari guda 12,ashe shekara daya yana da;
*"Raka'a 4320 na nafila a shekara daya"*.

Ashekara goma yana da;
*Raka'a 43,200*

Ashe kara Talatin yana da;
*Raka'a 129,600*.

Wanda bayayin nafila yayi Asarar dukkan wadan nan baki daya.

*2-KIYAYE YIN WUTRI RAKA'A DAYA A KOWANE DARE*

Banbanci tsakanin wanda yake yin wutri aqalla sau daya akowane dare da wanda bayayi.

Wanda yakeyin wutri da raka'a daya a kowane dare,Shekara guda yana da;
*Raka'a 360*

Ashe kara goma yana da;
*Raka'a 3,600*

Ashe kara Talatin yana da;
*Raka'a 10,800*

Wanda babayi duk shekara yana yin asarar raka'a 360 duk shekara.

Ashekara goma asarar raka'a 3,600.

Ashekara Talatin asarar raka'a 10,800.

*3-KIYAYE RAKA'A BIYU NA WALLAHA KOWANE YINI*

Awanda yake kiyaye akalla raka'a biyu na sallar wallaha a kowane yini,yana samun;

Ashekara daya yana da;
*Raka'a 720*

Ashekara goma yana da;
*Raka'a 7,200*

Ashe kara Talatin yana da;
*Raka'a 21,600*

Wanda baya yin Sallar wallaha ashekara daya yana asarar:
*Raka'a 720*

Ashekara goma yana asarar:
*Raka'a 7,200*

Ashekara Talatin yana asarar;
*Raka'a 21,600*

Ka mu manta akowace raka'a akwai;
*Sujada guda biyu*
Wanda sujada itace mafi lokacin da bawa yake samun kusanci zuwa ga Allah.Kuma Allah yafi amsa adduar bawansa a wannan lokaci.

*Ruku'u daya*
Wanda itace mafi girma nuna kaskancin bawa zuwa ga Allah,kuma shine lokacin mafi girma na girmama Allah.

*Karatun Fatiha*
Wadda itace babban rukune daga cikin rukunnan sallah baki daya bayan Niyya,kuma itace sura mafi girma daga cikin surorin Alqurani baki daya.

Kuma kada mu manta da;
*Yin kowace sujada guda daya tana yiwa mutum sanadiyyar shiga aljanna,kuma babu wata sujada da zakayi face Allah ya daukaka matsayinka da darajarka.

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Ina yi maku Umarni da Wasiyya akan ku yawaita yin Sujada,domin kai bazaka taba yin Sujada ga Allah ba face sai Allah ya daukaka Darajarka kuma ya kankare maka zunubanka)*
@رواه مسلم.

Kuma kada mu manta Sahabin da Manzon Allah ﷺ yace dashi;
*(Roki??)*sai yace ina rokon na zama makwabcinka a aljanna,sai Manzon Allah ﷺ yace;
*(Ka taimakeni a kanka da yawaita yin Sujada)*
Ma'ana yawaita yin nafila.
@صحيح الجامع.

Kuma kada mu manta da cewa;
*Ana cire gurbin abinda ya baci ko ya kasa na sallar farillah ana cike sane da nafila*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Farkon abinda za'a fara yiwa bawa na aiyukansa hisabi a ranar alqiyama shine Sallah,idan taci kuma tayi kyau to ya rabauta kuma ya tsira,amma idan ta samu tawaya to ya tabe yayi Asara,sai Allah yace kuyi dubi acikin aiyukan bawana shin yana yin Sallar nafila sai ku cike gurbinsu........)*
@صححه الألباني في صحيح سنن الترمذي.

*Mafi alkhairin aiki awajan Allah shine wanda aka dauwama ana yinsa komai kankantarsa*

Allah ne mafi sani.

Allah ya bamu ikon kiyayewa ya bamu kiriya daga wannan asara.
Share:

WANI SHASHANCI


WANI SHASHANCI DA MUTANEN YANKIN IFRIKIYA SUKA MAIDA SHI BA KOMAI BA:

Idan ɗan ƙasar Faransa bai iya turanci ba, 'yan Afirka sai su girmama shi. 

Idan ɗan Sipaniya bai iya turanci ba, 'yan Afirka sai su girmama shi. 

Yayinda ɗan ƙasar Sin ya zamana bai iya turanci ba, shi ma sai 'yan Afirka su girmama shi. 

Idan ɗan ƙasar Rasha bai iya turanci ba, sai 'yan Afirka su girmama shi. 

Kai ɗan kowace ƙasa daga cikin ƙasashen turai in bai iya turanci ba 'yan Afirka girmama shi suke yi. 

Amma idan ɗan uwansu ɗan Afirka ya zama bai iya turanci ba, sai su maida shi sakarai, daƙiƙi, jahili, soko kuma wawa. 

Wannan shi ne matakin shashanci mafi girma da muke fama da shi a matsayinmu na mutane. Muna amfani da iya turanci wajen gwada baiwa da karamar mutanenmu, har ma da yara ƙanana. 

A makarantunmu, ana sa yara su ji cewa su banzaye ne kuma wawayen da basu da amfani kawai saboda ba su iya magana da harshen da ba su tashi da shi ba a yankunansu. 

Ya ku 'yan Afirka, mu daƙile wannan mummunar ɗabi'ar daga yaɗuwa a ƙwaƙwalenmu da kuma al'ummarmu. Mu koyar da yaranmu harshensu na gado kuma mu bar sauran jama'ar da ke zagaye damu su yi magana da harsunansu cikin 'yanci da aminci ba tare da tsangwama ba. 

Kada mu bawa azzalumai gudunmuwa wajen aikata zalunci akan 'yan uwanmu. 

Idan har ka amfana da wannan saƙo, kana iya turawa wasu domin su amfana, amma a tunanina kowa daga cikin jama'armu yana buƙatar ya ji wannan maganar. 

Na barku lafiya. 


Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

MANYAN FA'IDOJIN SADAKA GUDA 8


MANYAN FA'IDODIN SADAKA GUDA 8

*A-Na farko:*
Fa’idojin Sadakar Tadauwu’i Akan Mutum

*1-Tsarkake zuciya*
Allah Madaukakin Sarki ya ce,
*(Ka karbi sadaka daga dukiyoyinsu,ka tsarkake su ka gyara su da ita)*
@Attauba:103.

*2–Koyi ne da Shugabanmu Muhammad( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ )*

Saboda yana cikin halayensa kyauta da alheri,yana yin kyautar wanda ba ya tsoron talauci,yana cewa Bilal R.A:
*(Bilal ka ciyar,kada ka ji tsoron kadan daga wajen Ma’abocin Al’arshi (Allah) [Talauci])*
@Al-bazzar ne ya rawaito shi.

*3–Allah yana mayar da abin da aka ciyar, kuma wanda ya bayar ya qara samun Daukaka*

Allah yana cewa : *(Babu wani abin da zaku ciyar face sai Allah ya mayar da shi,shi ne mafi alherin masu azurtawa)* 
@Saba’i:39.

*4-Tsarkake dukiya ne daga haniyar ciniki*

An karbo daga Qais Dan Abi Garazata – Allah ya yarda da shi ya ce;“Mun kasance a zamanin Manzon Allah( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ana kiranmu dillalai, sai Manzon Allah ya wuce ta wurinmu,ya sanya mana sunan da ya fi kyau, ya ce mana:
*(Ya taron attajirai,a cikin kasuwanci akwai yasassun maganganun da rantse-rantse,to ku gauraya shi da yin sadaka)*
@Abu Dawud ne ya rawaito shi.

*5-Samun lada da kankarewar zunubai*

Saboda fadin Manzon Allah( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ)
*(Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabino na dukiyar halal – Allah ba ya karba abu sai mai tsarki – to Allah zai karbi wannan sadaka da hannun damansa, sannan ya rene ta ga mai ita,kamar yadda Dayanku yake renon dan dokinsa,har ta zama kamar dutse mai girma)*
@Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi.

*6-Ci gaba da amfanuwa da ladan sadaka mai gudana bayan mutuwa*

An kabo daga Abu Huraira–Allah ya yarda da shi – ya ce, *“Idan mutum ya mutu,ayyukansa sun yanke sai guda uku, sai sadaka mai gudana,ko ilimi da ake amfanuwa da shi,ko Da na gari da yake masa addu’a”* @Muslim ne ya rawaito shi.

*B-Na biyu:*
Fa’idodin Da Suka Shafi Al’umma Gabadaya
*7-Sadaka tana cika saqon da zakka take isarwa a cikin mutane.*

*8–Samar da hadin kai da taimakon juna da soyayyya a cikin al'ummar musulmi*

ALLAH NE MAFI SANI

*Allah ka bamu wadata da ikon yawaita Sadaka dan girman Hannayenka masu ciyarwa akowane lokaci.*
Share:

WAƘAR ZAIDU IBRAHIM BARMO

ZAIDU IBRAHIM BARMO

Da sunan Rabbana zan fara waƙar Zaidu
Kogin maliya babu mai ganin ƙarshenka. 

Ɗa wurin Ibrahima na layin su Sa'idu
Gwarzonmu a yau muna maka sam-barka. 

Tsira gurin manzonmu wanda ya hana daudu
Kuma shi yazo da sallah yace kar mu yi shirka. 

Kun san mata su ke amfani da tandu
Shi ɗan jibiyawa ko sai dai waraƙa 

In ko rubutu kake so ka je gun Zaidu
Ko ma ba ka iya ba to za ya koya maka. 

Ƙimarsa ta zarce arewa har ta je ga kudu
Watarana duniya ƙwarai za ta yabe ka. 

Maƙiyanka da sun gane ka sai dai su gudu
Murhu da garwashi to wai wa zai taka? 

Masu yi maka hassada suna ruwa kai ko a tudu
Ka yi musu nisa babu mai iya kamo ka. 

Allah kare ka alfarmar Mahamudu 
Ya sa ka zamo a saman maƙiyanka. 

Ana maganar buhu wa ke zancen mudu? 
Kai me gayyar tsiya tafi abinka. 

Ka taka ka rausaya malam Zaidu
A MZM mun sani fa sam ba tamkarka

Allahu ya kiyasheka kamun gafiyar ɓaidu
Ya sa ka zamo cikin ni'ima a kabarinka.

Amin.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FALALAR ZIYARAR 'YAN UWA DA KUMA SON JUNA DOMIN ALLAH


FALALAR ZIYARAR YAN UWA DA KUMA SAN JUNA SABODA ALLAH.

Zayara da sadar da zuminci da yn soyayya dan Allah,yana cikin mafi girman aiyukan alkhairi da suke samu soyuwa da matsayi awajan Allah, shiyasa Annabi s.a.w ya kwadaitar damu yinsu agurare masu yawa kuma shima yayi hakan a aikace.

1-Manzon Allah s.a.w yace:
(Lallai Allah zai ce a ranar Alqiyama:Ina masu yin Soyayya dan girmana "ma'ana masu yin soyayya dan Allah dan girman Allah" a yau zan sanya su a inuwata ranar da babu wata Inuwa sai Inuwata).
@صحيح مسلم 

2-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Abubuwa guda ukku wanda ya samesu ya sami dandanon zakin Imani,
-Allah da Manzonsa su sukafi soyuwa agare shi fiye da dukkan komai.
-Kuma yana son bawane badan komai ba sai dan Allah.
-Kuma yana kyamata a koma cikin kafirci bayan Allah ya tsamoshi daga cikinsa kamar yadda yake kyamatar a sanya shi wuta).
@صحيح البخاري - رقم: (21)

3-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai wani mutum ya tafi ziyarar dan uwansa zuwa wani gari,sai Allah ya tura masa Mala'ika akan hanyarsa,sai Mala'inkan ya tambayesa ina zakaje?? Sai yace: zanje ziyarar dan uwana a wancan gari,sai Mala'ikan yace:Shin zakajene dan kwadayin wani abu da kakeso ya baka?sai yace: A'a babu abinda zai kaini zuwa wajan sai dan ina sonsa dan Allah kadai.sai Mala'ikan yace da shi: Ni dan Sakon Allah ne,hakika Allah yana sanka kamar yadda kake son dan uwanka dashi).
@صحيح مسلم - رقم: (2567)

4- 3-Annabi s.a.w yana cewa:
(Imanin dayanku baya cika har sai ya soma dan uwansa irin abinda yake soma kansa).
@صحيح البخاري - رقم: (13-45)

5-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Duk wanda yaje duba marar lafiya ko ya kaiwa dan uwansa ziyara dan Allah,sai wani mai kira yayi kira yace:
Ka dace ka rabauta kuma an tanada maka mazauni acikin aljanna) حسنه الألباني ف صحيح الترمذی @

6-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Mutumin da ya kai ziyara ga dan uwansa wani gari dan Allah,yana samun aljanna).
@حسنه الألباني في صحيح الجامع - رقم: (2604)

7-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Allah madaukakin sarki yana fada:
Soyayyata ta wajaba ga masoya guda biyu da sukeyin soyayya sabodani,da masu jama da junansu sabodani,...... da kuma masu ziyartar junansu sabodani).
@صححه الألباني في
📚 صحيح الجامع - رقم: (4331)

8-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai mafi cikar samun matsayi a musulinci shine mutum yayi soyayya dan Allah kuma yayi kiyayya saboda Allah).
@الألباني في صحيح الجامع - رقم: (2009)

Allah ka bamu ikon yi soyayya da kuma ziyarar yan uwanmu da abokin arziki da sauran musulmai dan Allah
Share:

RUBUTACCIYAR WAƘAR GUGAN ƘARFE


WAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA 


Gugan Ƙarfe

Masu fagabniya a gari
Jure kwaramniya bidiri
Balle ma ta taƙadari
Ɗanduƙusuru mai bidiri
Masu kamar yabo a gari
Ga su kamar suna zikiri
Baƙin halinsu ƙona gari
Ya sattaru Al-ƙadiri
Tsare mu baƙin shirin ja'iri
Kamar na ashana ƙona gari.

Jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari, Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari.

A yau ƙoƙon bara na taho gurin mai juya al'amari
Kashe mani gobarar kogi da ta fi ta zahiri bidiri
Wuta daga bahari kogi kasan da akwai shirin garari
Idan ka tsaya mani wuturi
To bani shirin ganin bidiri.

Muhammadu sahibul bushra da ke horo da ai haƙuri
Naziru na gargaɗin da kake da ribar masu yin haƙuri
Muna roƙon gwani wuturi
Ya ƙara dubu-dubun zikiri
Gurin Musbahu cinye-gari
Muhammadu sahibul bashari.

Akwai su gwani akwai nagwanaye akwai agwanaye duk a gari
Akwai 'yan bani ni na iya akwai 'yan mu muke a gari
Akwai 'yan mu da mu aka fara sannan mu muke da gari
Akwai 'yan mu muke fa da gado ba mu bari a karɓi gari.

Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari, jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari.

Akwai 'yan ba mu sha kuma ba mu bari wasu ma su sha a gari
Su jaɓa da an sako baki a yau kwalara ta watsu gari
Da masu shirin gada ta zare suna tarko na mai haɗari
Da an kai walƙiya sun zam kamar sun sha ruwan tsari.

Suna da faran-faran a kama suna da wutsilniyar badari
Ga zulwajahaini guntsi-baza kullum aikinsa zaga gari
Yana hana mai zuma talla, yana tallar maɗi a gari
Gari ya watstsake kure yana kiwo tsaka ta gari.

Akwai su ƙuda mazan kwaɗayi halak da raham yana marari
Da yaki-halak da yaki-haram yake burga kamar mazari
Ina ranar sanin ilimi na hauni da dama ai nazari
Kamar jaki da littattafai cikin akumare ba nazari.

Akwai su biri uban ɓarna gata a birai fa taƙadari
Akwai su dila uban wayo da sari ka noƙe ba tare
Akwai kura da kan rago cikin babbansu al'amari
Umurun almushtabiha sai dai dafa'i na yin zikiri.

Akwai riga ta malanta da kan sawa a zare kwari
Da kambun baki al'ainu da yasan ƙage duk sihiri
Hawayena a kunduƙuƙi ina roƙonka Al-ƙadiri
Tsare mu balahirar maƙiya mayar masu dukkanin ƙuduri.

Waɗansu wutar ciki tamkar an bai maye riƙon jinjiri 
Waɗansu ko handama tamkar loma aka bai wa almajiri 
Suna hannu-baka-hannu-ƙwarya tamkar su cinye gari 
Idon su da kunnuwa a rufe summum-buƙumum cikin garari. 

Jure kwaramniya gugan ƙarfe kwana alif da ɗari, Allah in ya yarda da kai ba mai iya saka a garari.
Share:

HIKAYAR AUREN SUNIL DUTT DA NARGIS


HIKAYAR AUREN SUNIL DUTT DA NAGIS

Wato wannan jarumi Sunil Dutt yasha wahala kafun samun auren wannan jaruma. To mukoma baya. 
Jaruma Nagis ta kasance babbar jaruma a wancan lokacin kuma ta kasance budurwar jarumi Raj Kapoor wato baban Rishi Kapoor, Randhir Kapoor da sauransu haka kuma kakan su Ranbir Kapoor Kareena Kapoor Karishma Kapoor da sauransu to lokacin yana saurayinta kuma idan sukai film tare sai film din yayi nasara sosai. 
To jarumi Sunil Dutt yakamu da sonta kuma yana so ya aureta Amma kuma yana tsoran jarumi Raj Kapoor to kuma gashi sonta ya mamaye shi harma yana cewa in babu ita a rayuwarshi to fa sai ya rasa ranshi to lokacin da za a fara Aikin film din MOTHER INDIA ba ai niyar Sanya jarumi Sunil Dutt ba Amma kuma jarumin sai yane mi da Director na film din da yasanya shi a film din domin yasamu kusanci da ita sai kuwa akai sa a aka sashi a film din kuma bayan sun gama Aikin film din sai jarumin ya gayawa jaruma Nagis bukatar shi sai bata bashi amsa ba hakan ya tsorata shi gar yadinga tunanin kar ta gayawa Raj Kapoor am a kuma daga baya sai aka dinga jita jitar wai sunyi aure anan ma tsoran yakama shi domin kar zancen yaje kunnen babban kwaro Raj Kapoor Amma kuma sai daga baya ta amshi soyayyar shi kuma sukai aure a boye kuma ba a San sunyi aure ba har sai da ta haifi jarumi Sanjay Dutt sannan labari ya bazu cewa sunyi aure wato Sunil Dutt da Nagis. 

To jama'a anan zan dakata dafatan zaku Tara wani lokacin domin riskata da wani sabon shirin da haka nake cewa bissalam.
Share:

FASSARAR WAKAR YEH LADKA HAI ALLAH


Fassarar Waƙar Yeh Ladka Hai Allah


• Waƙa - Yeh Ladka Hai Allah

• Fim - Kabhi Khushi Kabhie Gham...

• Harshe - Hausa 

• Shekarar Fita - 2001

• Sauti - Jatin Lalit

• Rubutawa - Sameer 

• Kamfani - Sony Music

• Rerawa - Alka Yagnik & Udit Narayan 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 


• Banno ki mehndi kya kehna

Lallin amaryar ya haɗu kuwa. 

• Banno ka joda kya kehna

Kayan amaryar sun haɗu kuwa. 

• Banno lage hai phoolon ka gehna

Amaryar ta fito kamar adon fulawa. 

• Banno ki aankhen kajrari

Idanun amaryar sun sha kwalli. 

• Banno lage sabse pyaari

Amaryar ta fito gwanin ban sha'awa. 

• Banno pe jaaon main vaari vaari

Ina mamakin kyawun amaryar. 

• Banno ki saheli, resham ki dori

Ƙawayen amaryar sun sa kayan siliki. 

• Chhup chhup ke sharmaaye, dekhe chori chori

A sirrance kuma a nutse take jin kunya. 

• Yeh maane ya na maane main to ispe mar gaya

Ko da ta yarda ko ba ta yarda ba, ina mutuwa akanta. 

• Yeh ladki haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan yarinyar ko, wayyaho Allah. (wane irin kyau gareta haka?) 

• Babul ki galiyaan na chad ke jaana

Ba zan taɓa barin gidan ubana ba. 

• Paagal deewana isko samjaana

Kai wawa mahaukaci, ka fahimci hakan. 

• Dekho ji dekho yeh to mere peeche pad gaya

Kalli, kalli wannan yadda yake ta bi na. 

• Yeh ladka haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan gayen ko, wayyaho Allah. (wane irin mutum ne shi kam?) 

• Lab kahe na kahe bolti hai nazar

Ko da laɓɓa sun yi magana ko ba su yi ba, kallonki ya bayyana komai. 

• Pyar nahi chupta pyar chhupane se

Shi so ba a iya ɓoye shi. 

• Roop ghoonghat mein ho to suhana lage

Idan aka ɓoye kyau a mayafi, sai ya ƙayatar. 

• Baat nahi banti yaar batane se

Bai kamata ba, bayyana sunan masoyi gatsau. 

• Yeh dil ki baatein dil hi jaane ya jaane khuda

Abinda zuciya za ta faɗa, Allah ne da zuciyar kawai suka sani. 

• Yeh ladki haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan yarinyar ko, wayyaho Allah. (wane irin kyau gareta haka?) 

• Yeh ladka haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan gayen ko, wayyaho Allah. (wane irin mutum ne shi kam?)

• Mangne se kabhi haath milta nahin

Wani lokacin buri bashi kai wa ga gaci. 

• Jodiyaan banti hai, pehle se sabki

Allah ya riga ya ƙaddara wa kowa abokin zamansa. 

• Oh leke baaraat ghar tere aaonga main

Yauwa, zan ɗauki ɗawainiyar bikin in taho gidanku. 

• Meri nahin yeh marzi hai rab ki

Wannan ba son raina bane, Allah ne ya so. (hakan ya faru)

• Are ja re ja yun jhooti muthi baatein na bana

Kai tafi can, ka daina wannan shashancin.

• Yeh ladka haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan gayen ko, wayyaho Allah. (wane irin mutum ne shi kam?)

• Banno ki saheli, resham ki dori

Ƙawayen amaryar sun sa kayan siliki. 

• Chhup chhup ke sharmaaye, dekhe chori chori

A sirrance kuma a nutse take jin kunya.  

• Babul ki galiyaan na chad ke jaana

Ba zan taɓa barin gidan ubana ba. 

• Paagal deewana isko samjaana

Kai wawa mahaukaci, ka fahimci hakan. 

• Yeh maane ya na maane main to ispe mar gaya

Ko da ta yarda ko ba ta yarda ba, ina mutuwa akanta. 

• Yeh ladki haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan yarinyar ko, wayyaho Allah. (wane irin kyau gareta haka?) 

• Yeh ladka haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan gayen ko, wayyaho Allah. (wane irin mutum ne shi kam?)

• Yeh ladki haay Allah haay haay re Allah

Wayyo Allah, wannan yarinyar ko, wayyaho Allah. (wane irin kyau gareta haka?) 
©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FASSARAR WAƘAR TU HI MERA

Fassarar Waƙar Tu Hi Mera

• Waƙa - Tu Hi Mera

• Fim - Jannat 2

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2012

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Sayeed Qadri

• Kamfani - Sony Music

• Singer: Shafqat Amanat Ali 

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman 

• Ho tere ishq mein dooba rahe din raat yunhi sada

Bari ranakuna da dararena su nutse a cikin soyayyarki har abada. 

• Mere khwaab se aankhein teri ik pal na hoye judaa

(Allah) Yasa kada idanuwanki su kauce daga kan mafarkaina ko da sau ɗaya. 

• Mera naam tu haathon pe apne likhe baar haan

(Allah) Yasa ki rubuta sunana a hannuwanki da yawa. 

• Aye kaash ke aisa bhi ik din laaye woh khuda

Allah ya kawo irin wannan rana. 

• Tu hi mera mera mera (x8)

Ke tawa ce kaɗai. 

• Tu hi mera... aaa (x2)

Ke tawa ce kaɗai. 

• Tu hi mera mera mera (x4)

Ke tawa ce kaɗai. 

• Hai teri chaahat teri zaroorat

Tabbas, soyayyarki dole ce. 

• Sooni hai tujh bin duniya meri

Idan babu ke zuciyata kaɗaici take yi. 

• Naa reh sakunga main door inn se

Ba zan iya ƙauracewa hakan ba. 

• Hai meri jannat galiyan teri

Aljannah ta tana hanyarki ne. 

• Hai teri chaahat teri zaroorat

Tabbas, soyayyarki dole ce. 

• Sooni hai tujh bin duniya meri

Idan babu ke zuciyata kaɗaici take yi. 

• Naa reh sakunga main door inn se

Ba zan iya ƙauracewa hakan ba. 

• Hai meri jannat galiyan teri

Aljannah ta tana hanyarki ne. 

• Ummeed yeh seene mein leke main hoon jee raha

Da wannan burin ne a zuciyata, nake ci gaba da rayuwa. 

• Kabhi tu mile mujhse kahe ke main hoon bas tera

Watarana za ki haɗu da ni kuma ki ce ni naki ne kaɗai. 

• Tu hi mera mera mera (x9)

Ke tawa ce kaɗai. 

• Tu hi hai kismat tu hi hai rehmat

Ke ce nasara ta kuma ke ce karamcina. 

• Tujhse judi hai meri har khushi

Da ke ne duk wani farinciki nawa ya ta'allaƙa. 

• Tu hi hai kismat tu hi hai rehmat

Ke ce nasara ta kuma ke ce karamcina. 

• Tujhse judi hai meri har khushi

Da ke ne duk wani farinciki nawa ya ta'allaƙa. 

• Paata hoon khud ko har ghadi tere bina tanha

Nakan samu kaina a cikin kaɗaici a duk sanda ba ki. 

• Mujhe thaam le mujhe rok le

Ki kama ni, ki tsai da ni. 

• Bhatka hoon main bhatka

Ina hanyar ɓata ne. 

• Tu hi mera mera mera (x9)

Ke tawa ce kaɗai. 

• Tu hi mera... aaa (x2)

Ke tawa ce kaɗai. 

• Tu hi mera mera mera (x8)

Ke tawa ce kaɗai. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com


Share:

SHIN NAWA NE KOFIN ƘIYAYYA?

SHIN NAWA NE TSADAR KOFIN ƘIYAYYA? 

Ban taɓa sanin cewa haka yake da tsada ba. Ina so ne in san tsadar ƙiyayya, don haka sai na sauka a wani shagon da ake siyarwa. A matsayinsa na nagartaccen ɗan kasuwa wanda ke neman kwastoma, nan da nan sai mai shagon ya rugo wajena domin jin ko me nake so. Sai na ce masa kofi ɗaya kawai nake so na ƙiyayya, daga nan sai ya yi murmushi kuma ya tambaye ni ko zan iya siya?

 'Shin nawa ne tsadar kofin ƙiyayya? Na tambaye shi. Hmmmmm! Ya kawo wani gwauron numfashi ya sauke sannan ya fara: 

 👉🏼 Da farko dai za ta ɗauke maka duk wata nutsuwa da ke tare da kai. 

 👉🏼 Za ta haifar maka da damuwa iri-iri kuma marasa magani.

 👉🏼 Za ta cinye zuciyarka. 

 👉🏼 Za ka faɗa cikin ƙunci a duk lokacin da ka ga wanda kake ƙin. 

 👉🏼 A duk lokacin da mutane ke taya shi murnar wani abu, kai kuma za ka fara duban dalilan da suka sa kake ganin bai cancanci wannan abun ba. 

 👉🏼 Zai zamana ka suƙe kuma ka gaji da ganin wannan mutumin. 

 👉🏼 A duk lokacin da ya yi dariya kai kuma sai ka yi kuka. 

 👉🏼 A lokacin da mutane ke ƙoƙarin gina rayuwarsu, kai kuma za ka zama kana ta gina masa ramin mugunta ne domin ka kada shi. 

 👉🏼 Tsoron Allah da imani da shi za su fita daga zuciyarka sannan za ka zama dandamalin da shaiɗanu za su dinga taruwa. 

 👉🏼 Za ka fara fuskantar matsalolin lafiya irin su Hawan Jini, ciwon sikari, shanyewar ɓarin jiki, cutar daji, cutar hanta, cutar ƙoda da dai sauransu. Matuƙar dai ka sha daga kofin ƙiyayya to baƙin ciki, riƙo a zuci, rashin yafiya, gaba, fushi, kishi, ƙiyayya da makamantansu duk za su bika. Abu mafi hatsari shi ne babu wani magani da za ka siya ka sha da zai magance maka wannan cutar. 

 👉🏼 Za ka kashe kanka tun gabanin lokacinka ya yi. 

Mai shagon ya ci gaba da zayyano min irin abubuwan da kofi ɗaya na ƙiyayya zai iya ja min in rasa har dai na ce ya dakata haka nan, saboda na fahimci cewa kofin yana da matuƙar TSADA. Na ƙi yarda in biya wannan kofi da tsada haka alhalin ina iya nuna soyayya cikin sauƙi kuma da arha.

Ya ku 'yan uwa, kada ku yarda wani ya ƙwace muku farincikinku ta hanyar siyar ko baku ƙiyayya ku amsa. Ku ƙauracewa gulma, ƙiyayya, fushi da sauransu saboda a mafi yawancin lokuta, abin da ka ji dangane da wani ne ke haifar da ƙiyayya. Kada ka kashe kanka kafin lokacinka ya yi. 


Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

KAICO!


Kaico!

Bissmillah da sunan ilahi
Wanda ya aiko ɗan Abdullahi
Zan yi batu da tambihi
Bani dama sarkina ilahi.

Mu yaran zamani yau
Ba mu magana ayau
Iyaye na ta fama
Mu kuma muna ta fankama.

Ba mu tsoron ɓaci na ransu
Ba mu yin ladabi garesu
Ba ma biyayya garesu
Amma in buƙata ta tashi mu je wurinsu.

Ra'ayinmu kawai muke bi
Ko mara kyau ne shi za mu bi
Ra'ayinsu ko ba mu bi
Ko da mai kyau ne ba mu bi.

A hakan muke so wai mu ci gaba 
Alhali da uwarmu muke gaba 
Mun ce mu ne za mu shige gaba 
Wai shugabancin ya fi ƙarfin uba. 

To ta yaya ma zamu haske? 
Bayan albarkar mun make? 
Mun aje uwarmu a gefe 
Mun ɓoye ubanmu a shinge. 

Kaico! Wannan lamari da gyara 
Shi ya sa ma har na ɓara 
Ku ka ji ni ina ta ƙara 
Sai ka ce wanda sago ya sara. 

To wallahi mu yi hankali
An ce duniya ɗamarar jangali
Dole sai an bi ta a hankali
Ko kuma mu faɗa baƙin hali.

Allah ka ƙara wa iyaye lafiya
Ka sa mu gama da su lafiya
Mu zamo masu ƙaunar tarbiya
Ga manyanmu mu zam masu biyayya.

Sarki ka shiryar da mu 
Da abokai da ahalinmu 
Da dukkan 'yan danginmu 
Ka sa shiriya a zukatanmu. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

WASU SHAWARWARI DA ZA A IYA BI WAJEN DASAWA YARA KYAWAWAN ƊABI'U


WASU SHAWARWARI DA ZA A IYA BI WAJEN DASAWA YARA KYAWAWAN ƊABI'U. 


1. A yayin da kuka shigo gida, ku gaishe da su ko ma ku rungume su. Hakan zai gina soyayya da darajawa a zukatansu.

2. Ku yi kyakkywar mu'amala da maƙwabtanku kuma kada ku yi munafunci. Kada ku dinga faɗan aibun wasu mutane da kuka haɗu da su kamar direbobi da ma'aikatan kan hanya a gaban su. Saboda yaran nan suna saurare, za su ɗauka kuma za su kwaikwaya. 

3. A duk lokacin da kuka kira mahaifanku, ku ƙarfafawa yaranku gwiwa su ma su yi magana da su. A duk lokacin da za ku kai ziyara gare su, ku tabbata kun je da yaran kuma ku mutunta su a gaban yaran. Saboda irin yadda suka ga kuna girmama iyayenku su ma haka za su girmama ku ko su kula da ku. 

4. Idan za ku kai su makaranta, kada ku kunna musu waƙoƙi ko kaɗe-kaɗe, a madadin hakan, ku basu gajerun labarai masu ƙarfafa gwiwa hakan yana da matuƙar muhimmanci a gare su- Ku yarda da ni! 

5. Ku dinga yi musu tatsuniyoyi, ƙissoshi da tarihin magabata ko kuma karanta musu ko da hadisi guda ɗaya ne a kowace rana. Ba wani lokaci mai tsawo hakan zai ɗauka ba, amma yana da muhimmanci wajen ƙara kusanci da kuma ƙirƙiran tarihin da za a dinga tunawa a tsakanin juna. 

6. Ku gyara gashi, ku wanke haƙora kuma ku sa kaya masu kyau ko da kuwa za ku zauna a gida ne. Saboda yara suna buƙatar su fahimci cewa yin tsafta da shiga ta kamala ba wai kawai sai za a je unguwa ake yi ba. 

7. Kada ku zama masu zagi ko duka ko kuma ƙorafi akan duk wani laifi da yaranku suka yi. Ku zamo masu haƙuri da kauda kai a wasu abubuwan. Yin hakan zai taimaka sosai wajen gina musu ƙarfin gwiwa da kuma sanin ya kamata. 

8. Ku nemi izini kafin ku shiga ɗakinsu. Ba wai kawai ƙwanƙwasawa za ku yi ba, a'a ku nemi izini baki da baki su baku izinin shiga. Suma za su koyi yin hakan yayin shiga ɗakinku ko na wasu. 
 
9. Ku nemi gafara idan ku ka yi wa yaranku laifi, ba su haƙuri da neman gafararsu hanya ce mafi sauƙi ta koya musu bada haƙuri da neman yafiya idan suka yi wa wani ba daidai ba. Sannan hakan zai dasa musu nagarta a zukatansu. 

10. Kada ku zamo masu yawan zolaya ko ci wa yaranku fuska ko da da wasa ne akan wasu zantuka ko ɗabi'u ko mu'amala. Hakan na da ƙona rai, in kuna yi musu hakan, to za su taso da tsana da kuma jin haushinku. 

11. Lallai ne iyaye su zama masu ba wa sirrin 'ya'yansu muhimmanci sosai.

12. Kada ku yi tunanin za su fahimci ko kuma su ɗauki duk abin da kuka faɗa musu nan take, ku zamo masu haƙuri da naci akan abin da kuke koya musu. 

13. Ku dinga yin sallah da addu'o'i tare, ku koya musu yadda ake yi da kanku. 

14. Bayan sallar Asubahi, ku zauna da su ku tambaye su irin abubuwan da suke sa ran yi a wannan yinin. Yaran da ba su da jadawalin abubuwan da za su aikata a kowane yini tabbas za su je su taimaka wa wasu wajen gudanar da nasu aikin ko ba mai kyau bane. Sannan hakan zai taimaka wajen koya musu tsara hanyar gudanar da rayuwarsu. 

15. Ku yawaita rungumar 'ya'yanku, ku yawaita yi musu addu'a da sa musu albarka a kowace safiya. Hakan na gadar da so da ƙauna tare da gadar da albarka a cikin wannan ahalin. 

Ku tuna, wasu iyayen na buƙatar jin irin waɗannan shawarwari, don haka babu laifi don kun tura musu. 

Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com
Share:

KUKAN KURCIYA

KUKAN KURCIYA

Da sunan sarkina zan fara
Wannan da shi ne ya yiwo fara
Ya yi kare kana ya yo kura
Ya yi ruwa kuma kana ya yo ƙura
Hikimar Allah sam ba ta da iyaka.

Tsira da aminci gun baban Zahra 
Wannan da cikin annabawa ya yo zarra
Wanda duk wata daraja tuni ya tara
Sahabbai da alaihi duka na tara
Salati gare sa na ke furtawa babu iyaka.

Wai mu yaushe ne za ko mu hankalta
Mu zam nutsuwa da neman mafita
A wayi gari junanmu za mu fifita
Ai ya fi ace kawunanmu muka fifita
Ko ba komai hakan ai zai fishe ka.

Mu kawunanmu kawai muke hange
Ba mu duban wanda yake a jikin shinge
Na ƙoluwa kawai muke hange
Taddo shi kawai muka daddage
Kai mai dogon buri kam kaiconka.

Ƙaddara dai kowa da akwai ta sa
Riga ce da babu mai cire ta sa
Da zamu gane mu daina sa-in-sa
Akan abin da zai zo ne komai nisa
In kuma munƙi za mu wahalta kamar wanda ya sha molanka.

Allah ka tsare mu da na shina
Ka sa mu zamo masu yin murna
Da Duk abin da ka tsara mana
Alfarmar annabinka mijin Nana
Ka sa kar mu zamu cikin masu yin shirka.

Jamilu ne ke waƙar daga nan gefen
Domin isar da saƙo ga 'yan can gefen
Fatana kowa ko ya amfana
Da ɗan abinda na samu a karatuna
Wannan ita ce riba da ba ta da iyaka.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Share:

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form