Barka da warhaka

SHIN NAWA NE KOFIN ƘIYAYYA?

SHIN NAWA NE TSADAR KOFIN ƘIYAYYA? 

Ban taɓa sanin cewa haka yake da tsada ba. Ina so ne in san tsadar ƙiyayya, don haka sai na sauka a wani shagon da ake siyarwa. A matsayinsa na nagartaccen ɗan kasuwa wanda ke neman kwastoma, nan da nan sai mai shagon ya rugo wajena domin jin ko me nake so. Sai na ce masa kofi ɗaya kawai nake so na ƙiyayya, daga nan sai ya yi murmushi kuma ya tambaye ni ko zan iya siya?

 'Shin nawa ne tsadar kofin ƙiyayya? Na tambaye shi. Hmmmmm! Ya kawo wani gwauron numfashi ya sauke sannan ya fara: 

 👉🏼 Da farko dai za ta ɗauke maka duk wata nutsuwa da ke tare da kai. 

 👉🏼 Za ta haifar maka da damuwa iri-iri kuma marasa magani.

 👉🏼 Za ta cinye zuciyarka. 

 👉🏼 Za ka faɗa cikin ƙunci a duk lokacin da ka ga wanda kake ƙin. 

 👉🏼 A duk lokacin da mutane ke taya shi murnar wani abu, kai kuma za ka fara duban dalilan da suka sa kake ganin bai cancanci wannan abun ba. 

 👉🏼 Zai zamana ka suƙe kuma ka gaji da ganin wannan mutumin. 

 👉🏼 A duk lokacin da ya yi dariya kai kuma sai ka yi kuka. 

 👉🏼 A lokacin da mutane ke ƙoƙarin gina rayuwarsu, kai kuma za ka zama kana ta gina masa ramin mugunta ne domin ka kada shi. 

 👉🏼 Tsoron Allah da imani da shi za su fita daga zuciyarka sannan za ka zama dandamalin da shaiɗanu za su dinga taruwa. 

 👉🏼 Za ka fara fuskantar matsalolin lafiya irin su Hawan Jini, ciwon sikari, shanyewar ɓarin jiki, cutar daji, cutar hanta, cutar ƙoda da dai sauransu. Matuƙar dai ka sha daga kofin ƙiyayya to baƙin ciki, riƙo a zuci, rashin yafiya, gaba, fushi, kishi, ƙiyayya da makamantansu duk za su bika. Abu mafi hatsari shi ne babu wani magani da za ka siya ka sha da zai magance maka wannan cutar. 

 👉🏼 Za ka kashe kanka tun gabanin lokacinka ya yi. 

Mai shagon ya ci gaba da zayyano min irin abubuwan da kofi ɗaya na ƙiyayya zai iya ja min in rasa har dai na ce ya dakata haka nan, saboda na fahimci cewa kofin yana da matuƙar TSADA. Na ƙi yarda in biya wannan kofi da tsada haka alhalin ina iya nuna soyayya cikin sauƙi kuma da arha.

Ya ku 'yan uwa, kada ku yarda wani ya ƙwace muku farincikinku ta hanyar siyar ko baku ƙiyayya ku amsa. Ku ƙauracewa gulma, ƙiyayya, fushi da sauransu saboda a mafi yawancin lokuta, abin da ka ji dangane da wani ne ke haifar da ƙiyayya. Kada ka kashe kanka kafin lokacinka ya yi. 


Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form