Barka da warhaka

HUKUNCIN IDDAR MACE MAI SHAYARWA


*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*Daga zauren*_
_*📌Albahral Ilmu🌴🌴*_
.
.
_*HUKUNCIN IDDAR MACE MAI SHAYARWA*_
:

_*Tambaya*_
:
Idan aka saki Mace tana Shayarwa yaya hukuncin Iddarta zai kasance idan Jinin-Al'ada yadena zuwa mata saboda Shayarwar da takeyi??
:
*_Amsa:_*
:
Wāto kamar yadda yake sanannen abu awajen Mutāne cewa akwai ​Nau'ikan-Mātā​ da yawa waɗanda ​Jinin-Al'āda​ yake tsayā musu alokacin da suke ​Shāyar​ da ​Jāriransu,​ wasu bazāsu sāke ganin ​Jiniba​ har sai sun yāye ​''Ɗan''​ da suke ​Shāyarwa,​ Saidai wasu ​Mātan​ jinin yakan dāwō musune bāyan Shekara ɗaya, wasu Mātan kuma bayan watanni Shidda(6) ko wani abu makamancin haka sai suga ​Jinin-Al'ādarsu​ yazo, yāyin da wasu Mātan kuma dāma kwata kwata su ​Jinin-Al'āda​ bāya tsaya musu sakamakon ​Shāyarwar​ da sukeyi, kawai da ​Jinin-Bīƙi​ yāɗauke musu sai kuma ​Jinin-Haila​ yabiyo bāyansa idan lokacin zuwansa yāyi,​
:
To idan ya kasance Mace batayin ​Jinin-Al'ada sakamakon ​Shāyar da Jariri​ da takeyi, ​Mālamai​ sukace irin wannan ​Mātar​ idan aka Saketa to zātayi ta jirane har sai randa tayi ​Jini-3​ koda kuwa hakan zai kaita zuwaga lokacin da zāta yaye ​Jaririn​ da take ​Shayarwar​ wato Shekaru biyu kenan, to dōlene har sai tagama waɗannan ​Jināne-Guda-3​ sannan ​iddarta zāta ƙāre,​ danhaka kenan idan ​Sakine​ irin na ​"Kōmē"​ to ​Mijin​ yana da dāmar yace yādāwō da ​Mātarsa​ koda kuwa bāyan Shekara biyune da yin ​Sakin​ matuƙar dai batayi ​Jini-3​ atsakāniba, wannan maganar kuma dukkan ​Mālamai-Fuƙahā'u​ sunyi ​Ijmā'i​ akan haka, ​Hujjarsu​ kuwa itace faɗin ​Aʟʟāн(ﷻ)​ dake cikin wannan ​āya​:​
:
​''والمطلقات يتربصن بأنفسهن ثلاثة قروء'' (البقرة/228)​
​​MA'ANA:​​
​​(Mātan da) aka Sakesu zāsu zaunane harsuyi Jini-3 (tsarki-3)​​
:
 ​Danhaka kenan idan Mace tanāso ​Jinin yazo mata​ da wuri to saita bāyar da ​Jārīrin​ nata wata ​Mātar​ ta ​Shāyar​ dashi, kokuma tayi amfani da wani magani wanda zai janyo mata al'adarta alokacin datake ​Shāyarwar​ amma da ​Sharaɗin​ ya kasance ba ​Saki​ bane irin na ​"Kōmē"​ domin idan ​Sakine​ irin na ​"Kōmē"​ to bai halatta tayi amfāni da māgani dan ta janyo al'ādarta ba, domin kuwa ​Mijinta​ yana da haƙƙi akanta na ya mayar da ita kokuma yarabu da'ita, amma idan ​Sakine​ irin wanda ba ​Sakin-Kōmēba​ to ya halatta tasha maganin da zai janyo mata jinin da wuri, amma shima da ​Sharaɗin​ ya kasance anāda tabbas kokuma zato mafi rinjane akan cewa maganin yadace da Jikinta bazai cūtar da'itaba,​
:
​To amma idan ya kasance ​Al'ādar-Mace​ tāɗaukene sakamakon wani ​Sababi​ kamar irin na ​Shāyarwa​ kokuma rashin lāfiya, daga baya kuma sai wannan ​Sababin​ yagushe, Misāli ace tawarke daga rashin lāfiyar, ko ta yāye ​''Ɗan''​ da take ​Shāyarwa,​ amma duk dahaka jinin bai zomata ba, to anan sai mafi yawa daga cikin ​Mālamai​ sukace Iddar irin wannan ​Mātar​ zata zaunane har tsawon ​Shekara guda cur,​ wāto ​watanni-9​ amatsayin mafi gālibin tsawon lokacin da mai ciki takeyi kafin ta haihu, Saikuma ​watanni-3​ amatsayin Idda, idan anhaɗa yāzama ​watanni-12​ kenan,​
:
​Danhaka idan yakasance ​Mace​ zatayi ​Iddāne​ na tsawon Shekara ɗaya, Misāli ace tayi ​watanni-11,​ kwatsam kawai sai taga ​Jinin-Al'āda​ yāzo mata, to yanzufa lissafincan da tayi na ​watanni-11​ yariga yārūshe, danhaka yanzu dolene sai tā sāke jiran zuwan ​Jini na-2 da na-3​ idan bai zoba har ta sākeyin wata Shekarar guda cur, to shikenan tāgama idda, amma idan taga ​Jini na-2​ yazo koda kuwa tasakeyin wasu ​watanni-11​ da zuwan na farko, to anan ma lissafinta yāsake rūshewa, danhaka dole sai tā sāke jiran wani ​Jini na-3​ yazo sannan tagama idda, idan kuma ​jini na-3n​ bai zoba har tasakeyin wata ​Shekarar​ shikenan tagama Iddarta,​
:
```(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)```
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*
*_​•Ga mai sha'awar 
* shiga Zauren 
*📌Albahral Ilmu 🌴🌴*

_*​ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_​​​​   
      _*07064746551*_
〰〰〰〰〰〰〰〰〰
        ​
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form