Barka da warhaka

IDAN KIN GYARU...


*🌴IDAN KIN GYÃRU🌴*
                *To dukkan al’umma*
                                 *🌴TÃ GYÃRU🌴*

*Laifi na sittin ɗaya (61): Karya murya da rangwaɗa ga maza waɗanda ba muharramai ba:*

👉🏼 Yin ƙasa-ƙasa da murya da rangwaɗa ga maza waɗanda suke ba muharramai ba hakan haramun ne, kuma ana yawan yin hakan musamman idan ana waya!

📚 Allah (SWT) yana faɗa game da mãtan babban gida iyãyen muminai cikin Suratul Ahzãb ãya ta(32) cewa: ((Yã mãtan Annabi! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kunyi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a cikin zuciyarsa ya yi tammani, kuma ku faɗi magana ta alheri)).

👉🏼 Wannan fa an faɗã ne ga mãtan Annabi (SAW)! To, ina kuma ga wasu mãtan da ba su kaisu a tsoron Allah ba!kuma ba su kaisu matsayi a duniya da lãhira ba!

✍🏼 Sannan kuma ki sani ya ke ‘yar uwa karya murya hanya ce da take kaiwa ga zina!

📚 Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratul Isrã’ ãya ta (32) cewa: ((Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã munãna ga zama hanya)).

📚 Kuma Allah (SWT) yana faɗa cikin Suratut Nur ãya ta (30-31) cewa: ((Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã’antãwa().

📚 Kuma ka ce wa muminai mãtã su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu…)).

Kasance da mu a Facebook 👇🏼
-https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp

Ko a Telegram 👇🏼
https://t.me/AbbaLHassan

*📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}.*
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form