Barka da warhaka

MACE MAI MUMMUNAN HALI


🔥GOBARAR ZAMANI
05//

Wallafar:-- Mal. Aliyu Sa'id Gamawa

*Mace Mai Mummunan Hali*

Mace mai mummunan hali, ita ce mai waɗannan halaye: 

- Hauragiya, tsiwa (daga harshe ga mai gida) 

- Kwarmato, mita, gulma, qananan maganganu 

- Ɗora wa miji sai ya sayo abin da ya fi qarfin arzikinsa. 

- Rashin suturta jiki da ganin kai, da sha’awar munanan al’adu. 

- Qaryata mai gida, ko yi masa dariya yayin da ake hira. 

- Yawan yawo da qaurace wa mai gida a shimfiɗa

- Qin yin aikin ibada ko maganganun batsa. 

   Haka dai Malam Rumfa da uwar gidansa suka yi ta irin wannan tattaunawa har zuwa wani lokaci, daga qarshe dai Rahmatu ta ce, Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya, ya kuma ba ku sa’a. Malam Rumfa ya ce, amin. Don haka jibi da safe za mu tafi in Allah ya kai mu, tafiyar dai za ta ɗauke mu kwanaki goma (10), domin zuwa da dawowa kwana takwas ne (8). Sai dai an ce duk wanda ya yi tafiya ita take da shi, Ba shi ke da ita ba. Ma’ana sai an ga dawowarsa. Suna cikin hira sai Malam Rumfa ya hango wata takarda, ya tambayi Malama Ramatu, sai ta ce, “Jiya malamanmu suka raba mana a makaranta, wai tsaraba ce ta wani taro da suka halarta a can Duniyari a kan kula da lafiyar uwa da yara qanana, da halarcin yi musu rigakafi.” Malam rumfa ya ce, “ Ni a da ban yarda da duk surutun ’yan book da gwamnati a kan rigakafi ba, amma na saurari wani qwararre akan kiwon lafiya da sanin cututtuka, sai na gamsu cewa kusan ma wajibi ne mu kula da kanmu, iyalanmu da yaranmu wajen kiwon lafiya da yin rigakafi ga yara da manya. In muka ci gaba da kasancewa a cikin duhun kai da gujewa duk tsarin da ake kawo mana a kan kula da lafiyamu da ta iyalanmu, to haka za mu zauna har yaranmu su cutu.”

Zamu cigaba Insha Allah

✍️ Ibrahim Muhd Abu muhd

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form