Barka da warhaka

MAFARKI MAI KYAU DAGA ALLAH NE, MUMMUNA DAGA SHAIƊAN


*Kyakkyawan Mafarki Daga Allah Ne, Mummuna Kuma Daga Shaidan Ne.*

Shin meye Hukuncin Mafarki da mukeyi a bacci, wani kyakkyawa mai faranta rai wani kuma mummuna mai bakanta rai?

Wasu zaka samu insukayi mafarki mara kyau toh sai kaga sun sanya kansu cikin damuwa da tashin hankali su rinka ganin kaman abinda suka gani a bacci gaskiya ne kuma zai faru dasu, wasu hakan tana sa har zargi ta shiga tsakaninsu da iyalansu su rinka ganin kaman suna aikata alfasha sabida kawai abinda suka gani acikin bacci.

Toh meye Hukuncin Mafarki Mai Kyau?
.
.
Duk wanda yayi mafarki mai kyau Mai faranta rai toh ya godewa Allah, kuma yana da daman ya sanar da na kusa dashi, domin wannan mafarki daga Allah take,
Abu Sa’eed(Radiyallahu anhu) Ya rawaito hadisi daga manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) Annabi yace: “idan dayanku yaga mafarki wanda yakeso, toh ya godewa Allah sannan ya bada labarin wannan mafarkin”
Bukhari Ya rawaito.
Haka nan a wata riwaya ta bukhari
Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yace: “kyakkyawan mafarki daga Allah ne”
Abinda ya dace mutum yayi in yaga mafarki mai kyau:
Idan mutum yaga mafarki mai kyau acikin baccinsa toh bayan ya tashi sai yayi wa Allah godiya akan wannan mafarki yana mai fatan Allah ya tabbatar da ita,
Sannan kuma sai ya sanar da nakusa dashi.
Hukuncin ganin mummunan mafarki
Wanda duk yayi Mafarki mummuna, toh Kada ya daukesa da wani mahimmanci ballanta har ya gina wani Hukunci akansa, domin wannan daga shaidan ne.
An rawaito daga manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) yace: “Mummunan mafarki daga shaidan ne,duk wanda yayi mafarkin abinda yake tsoro toh ya nemi tsari daga Allah sannan yayi tofi a gefen hagunsa,sharrin wannan mafarki bazata cutar dashi ba” Albukhari.
A wata riwaya kuma:
“Idan mutum yaga mummunnan mafarki wanda bayaso, toh ya nemi tsari daga Allah, sannan Kada ya sanar da kowa shi.”
Abinda mutum zaiyi idan yaga mummunan mafarki:
Ya nemi tsari daga Allah daga shaidan.
Yayi tofi a gefen hagunsa sannan ya canza gefen da yake kwance akai.
Sannan inso samu ne ya tashi yayi nafila raka’a biyu.
.
.
Sannan kada yabaiwa kowa labari kuma kada ya damu kansa ko kuma ya kullace wani a dalilin wannan mafarki.
Daga Karshe akwai wani Bangare mai kama da mafarki amma ba mafarki bane, shi ana kiransa zancen zuci. Shine mutum zai sanya wani abu a ransa kyakkyawa ko mummuna yayi ta tunaninsa toh inyazo acikin baccinsa ma sai wannan abu yayi ta zuwa masa, toh itama wannan ba’a daukan ta komai ba’a kuma yin la’akari da ita.
Allah ya sa mudace. Wassalamu Alaikum.

Daga 
Miftahul ilmi
ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Share:

No comments:

Post a comment

FITATTU GOMA

Total Pageviews

Translate

Featured post

WAƘAR CORONA 2

Waƙar Coronavirus 2 Bissmillahi Jallah sarki Rabbana Sarki gurina Za na fara da sunan ka Rabbana mahaliccina Za na yi waƙe ak...

Contact form