Rayuwa a Tertiary Institution (19/03/2021)
A Wannan Shirin Karo Na 5 ASOF. Ta Tattauna Da Matashin Dalibi Mai Fafutukar Kawo Sauyi a Rayuwar Matasa.
@ASOF: DAFARKO ZAMU SO KA GABATAR MANA DA KANKA A TAQAICE!
Mohiddeen: Sunana Muhammad Auwal Ahmad, Wanda akafi Sani Da Mohiddeen, haifaffen garin Bayamari da ke jihar Yoben Nigeria.
Ni ma'abocin Al’amuran na'ura ne da kimiyya da fasaha a takaice, sannan ina rubuce-rubuce kan wadannan bangarori har da kasuwanci, a wasu lokutan.
kasancewata matashi na kan bawa ’yan’uwana matasa shawarwari don mu gudu tare mu tsira tare!
Batun karatu ina aji uku a jami'a, ina karanta Computer Science (kimiyyar na’ura Mai kwakwalwa) Na gama sakandare ta a 2015.
@ASOF: SHIN MECECE MANUFA DA HANGEN NESAN KA, A FANNIN DA KAKE DA KWAREWA NA COMPUTER?
@Mohiddeen:
Babbar manufata itace don cigaban yankinmu na Arewa da Nigeria baki daya.
A hangena, Arewa da Nigeria za su ci gaba sosai matukar dai mun tashi tsaye, tsayin-daka don yin abun da gaske.
@ASOF: WADANNE KALUBALE NE ZAKACE KANA FUSKANTA, A WAJEN CIMMA WADANNAN MANUFOFIN?
@Mohiddeen: Na farko rashin madafa, ko da’ace matashi yana da wata dama ko kishin son gyara a zuciyarsa, to hakika wasu abubuwa su kan dakile hakan kamar rashin samun goyon bay, Mu kan taso haikan za mu yi abu, amma saboda rashin samun goyon baya sai mu watsar.
Hakika wannan babban kalubale ne a bangaren cigaba.
Na biyu rashin tallafi bayan samun goyon baya, dole akwai bukatar a tallafi bangaren da ya dace don ingiza wannan tafiyar da ta dage a kan cigaba, amma a Nigeria mun rasa wannan dama.
Tabbas matashi ba kowa ba ne kuma ba shi da komai, amma abu daya da yake da shi shi ne kishin cigaba.
Matukar jagorori ba su tallafa wa tafiyar matasa ta cigaba ba, to hakika ba ta jimiri kuma ta kan iya rushewa.
@ASOF: WACCE HANYAR CE KAKE DA TUNANIN KO KAKEBI A YANZU DAN SAMUN MAFITA A IRIN WADANNAN KALUBALEN DON SAMUN MAFITA?
@Mohiddeen: Babbar hanyar da na ga ta fi dacewa ita ce, yin aiki tukuru ba tare da tunanin cewa wani zai zo mu yi da shi tare ba.
Hakika ba kowa ba ne zai fahimci manufata da kuma yadda nake ganin za ta iya kawo canji a rayuwarmu ta yau, ni kadai na san yaya nake jinta a raina, Don haka abunda ya fi dacewa da ni shi ne na tashi tsaye na habbaka ta da kaina, watakila zuwa nan gaba idan mutane suka fahimce ta sai su shigo mu yi tafiyar da su tare.
@ASOF: BAYAN KAMMALA SIKANDIRE KACI KARO DA WANI KALUBALE KAFIN Zuwa JAMI'A?
@Mohiddeen:
Eh kwarai;
Na farko na fuskanci kalubale a jarrabawar JAMB wacce ta kasance dole sai da ita za a shiga jami'a.
Na biyu samun gurbin karatu a jami'a, Shi ma dai wannan kusan kowa yana fuskanta, abu ne wanda ya kasance ruwan dare.
@ASOF: KAFIN SHIGAR KA JAMI'A BAZA'A RASA WANI TUNANI BA A ZUCIYAR KA DANGANE JAMI'A BAYAN SHIGAR KA JAMI'A TUNANIN KA YA SAUYA KOKUMA YANA NAN DARAM?
@Mohiddeen: Kafin shiga ta jami'a na so karanta likitanci amma hakan bai yiwu ba.
Na yi tunanin shiga fannin na'ura don kawo canji a rayuwarmu ta yau, Bayan na shiga jami'a sai na ga har yanzu babu inda muka je a bangaren fasaha, na fahimci har yanzu muna baya a bangarorin kimiyya da fasaha, don haka sai na yi tunanin kara kaimi don tabbatar da cewa ba ni kadai ba ma, har ’yan’uwana sun fahimci tsarin karatun yanzu ya canja, don haka sai mu tashi tsaye mu dage.
Babbar manufata ita ce: dukkanmu mu fahimci wadannan bangarori da harshenmu don mu kawo cigaba maras iyaka a kasarmu
@ASOF: RAYUWAR JAMI'A RAYUWA CE TA HADA MUTANE DABAN-DABAN DAGA JIHOHI DABAN-DABAN SHIN WANNAN YAYI TASIRI A MU'AMALAR KA?
@Mohiddeen: Kwarai kuwa, Na hadu da mutane da dama daga wurare daban-daban a fadin Nigeria, kuma na koyi abubuwa dayawa a Rayuwa ta.
Hakika rayuwa a jami'a rayuwa ce sabuwa, a kan hadu sabbin abubuwa.
A tsarin mu'amala, rayuwar jami'a ta yi tasiri kwarai da gaske wajen canja yanayin tunanina daga kallon da nake yi wa wasu.
@ASOF: ME ZAKACE DANGANE DA RAYUWAR JAMI'A DAKAYI KUSAN FIYE DA SHEKARU UKU KANAYI?
@Mohiddeen: Duk yadda ka dauki jami'a haka za ka ganta, Wato wasu kafin shigar su jami'a suna tunanin wuri ne kawai na holewa, don haka idan suka shiga ba wani abunda za su kula da shi face abunda suke tunani, Wasu kuma su kan dauka wuri ne na koyon komai kamar karatu, mu'amala har da tarbiya, to su ma haka su kan iya samun ta
@ASOF: SHIN KANADA ABOKAI WANDA KAKEJIN BAZAKA IYA MANCEWA DASU BA, A RAYUWAR KA WANDA KUKA HADU A JAMI'A?
@Mohiddeen: Kwarai akwai su, Na hadu da mutane da dama wadanda suka zama abokai kuma ’yan’uwa
@ASOF: MENENE ABUNDA YAKE BAKA HAUSHI A JAMI'A WANDA BAZAKA MANTA DASHI BA?
@Mohiddeen: Yadda Wasu malamai suke takura wa dalibai cewa sai sun haddace abunda suka koya musu, Hakika wannan abun yana min ciwo sosai, malami ba zai fayyace wa dalibi karatu har Dalibi ya fahimta ba sai dai ya haddace
@ASOF: MENENE ABUNDA IDAN KATUNA A JAMI'A Kullum Kake Yin Farin Ciki?
@Mohiddeen: Yadda rayuwar jami'a ta canja tunanina, yadda na hadu da abokan arziki da yadda na ga karamci
@ASOF: KAFITO DAGA JIHAR YOBE, JIHAR DA A KWANAKIN BAYA ANSAMU KAI HARE-HARE A WASU MAKARANTU KAMAR SIKANDIREN DAPCHI, DAKUMA WASU A GARURURUWAN GUJBA, DA POTISKUM SHIN HAKAN BAI KAWO MAKA CIKAS KO RAGE MAKA KARFIN GWIWA BA A NIYYAR TAYIN KARATU?
@Mohiddeen: Bai rage mn ba ko kadan, sai ma kara ingiza ni da ya yi, Hakika na fuskanci kalubake a rayuwar sakandare, don a shekara ukun da na yi, sai da na shafe zango uku ban rubuta jarrabawa ba sakamakon rufe makarantu da ake yi saboda kai hare-hare, Hakan ya taba zuciyata, Amma ba kai na nake tunani ba, ina tuna yadda wasu za su iya kai gwiwa kasa a harkar karatu don wannan dalilan
@ASOF: GIRKI KO SIYAN ABINCI A CAFETERIA WANNE KAFISO?
@Mohiddeen: Ya danganta, Idan ni kadai ne na fi son saya, idan kuma da abokaina ne na fi son girkawa
@ASOF: KARATU A LOKACIN EXAM; DARE KO DA RANA KO DUKA BIYU?
@Mohiddeen: Duka biyu, amma na fi son da dare saboda babu hayaniya kuma na fi samun sukuni
@ASOF:A KARSHE MENENE RA'AYINKA HADA KARATU DA SANA'A KO KARATU KADAI?
IDAN KANADA RA'AYIN HADA KARATU DA SANA'A WACCE SHAWARA ZAKA BAWA DALIBAI?
KAINE KA KAFA MAUDU’IN ZABURAR DA MATASA Na Zo Mu Gina KAMFANI MENENE KARIN BAYANIN KA AKAI?
Mohiddeen: Gaskiya akwai wahala hada karatu da sana’a, amma ba zan kore hakan kai-tsaye ba Nima ina dan taba sana'a ta lokaci zuwa lokaci kuma ina karatu, amma hakan bai janyo min tangarda a karatun ba
Matukar sana'a za ta janyo targarda a karatu, to barinta shi ya fi alheri, idan an gama karatun sai a ci gaba.
Na kirkiri maudu'in #ZoMuGinaKamfani ne don zaburar da matasa sanin muhimmancin gina kamfani da kuma yadda za su iya bunkasa kananan sana'o'insu zuwa babban kamfani
@ASOF: MENENE FATAN KA AKAI
SHIN KUMA ANFARA NASAR A?
Mohiddeen: Fatana shi ne ganin matasa sun tashi tsaye tsayin-daka a kan duk wata harka ta cigaba.
kwarai an fara samun Cigaba, matasa a shirye suke su tallafa wa kansu don tashi tsaye a bangaren kimiyya da fasaha dakuma kasuwanci
@ASOF: ASOF. TANA FATAN NAN GABA ZAKA DAUKI MEMBOBIN TA AIKI A KAMFANIN KA!
MUNGODE KWARAI DAGASKE ALLAH UBANGIJI YAQARAWA RAYUWA ALBARKA
Insha Allah. Amin na gode kwarai Malam Ismail Allah Ya yi jagora.
@ASOF-2021
WHATSAPP 08038484677
Zaku iya Tuntubar Mu Domin Shigowa Shirin a Mako Mai Zuwa.