Barka da zuwa Bankin Bayanai

 • This is default featured slide 1 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 2 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 3 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 4 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

 • This is default featured slide 5 title

  Go to Blogger edit html and find these sentences.Now replace these sentences with your own descriptions.This theme is Bloggerized by NewBloggerThemes.com.

A INA YA KAMATA NA YI RIJISTAR JAMB? 10


SAHIHAN CIBIYOYIN RIJISTAR JAMB A JIHAR KATSINA✔️✔️


  A INA YA KAMATA NAYI RIJISTAR JAMB?

   
    Kashi Na Goma 


A fafutukar wannan Program na lalubowa Dalibai Amintattun Guraren da hukumar Jamb ta Yarje musu domin zuwa suyi rijista, wato Approved Cbt Centres, dasuke a fadin Jihohin Arewacin Najeriya guda Goma Sha Tara, Dakuma Babban Birnin Tarayya Abuja,

   A yau zamu Cigaba program dinne da Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu a Jihar Katsinan Dikko, tareda Adireshin kowacce Cbt Centre.


   Jihar Katsina dai tanada Cbt Cbt Centres guda Goma Sha Biyu,


   Gasu Kamar haka:


1• Al - Qalam University, MS - II ICT Centre, Tafawa Balewa Way, Along Dutsinma Road, Katsina State

2• Barda International School, Near GRA General Mosque, Katsina, Katsina State

3• CBT Centre Zonal Education Quality Assurance, Malumfashi, Katsina State

4• CBT Centre, Zonal Education Quality Assurance, Daura, Katsina State

5• CBT Centre, Zonal Education Quality Assurance, Dutsinma, Katsina State

6•Funtua Zonal Education Quality Assurance Office, CBT Centre, Funtua, Katsina State

7• Isah Kaita College Of Education, Dutsin - Ma, Katsina State

8• JAMB STATE OFFICE, KATSINA (REGISTRATION ONLY)

9• Kuramy Academy, Adjacent GSS, Bakori Katsina State

10• Umaru Musa Yaradua University, Computer Lab 1 Centre, Dutsinma Road, Katsina, Katsina State

11• Umaru Musa Yaradua University, Faculty Of Natural & Applied Sciences, Dutsinma Road, Katsina, Katsina State

12• Yusufu Bala Usman College Of Legal and General Studies, Daura.

 

  Wadancan 🖕 Cbt Centres din da muka lissafo a sama, Sune Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu a yanzu haka a Jihar Katsina.

   ∆ Yanada Kyau Dalibi yasani cewar yin rijista a wani gurin da ba Cbt Centre ba, Kan Iya haifar masa da Matsala a lokacin Jarrabawarsa, dan haka yanada kyau a kiyaye.


   A Kashi na Goma Sha Daya na wannan Program din, zamuzo muku dauke da Approved Cbt Centres, na Jiha ta Gaba, a cikin Jerin Jihohin da muke dasu a fadin Arewacin Najeriya.


  NB: Kusani Cewar wadannan CBT Centres ne da JAMB ta Tabbatar dasu a 2021, Adadin nasu zai Iya Raguwa ko Kuma Karuwa, anan gaba.


     MUNGODE


Daga Ofishin Secretary General


Marubuci: MIFTAHU AHMAD PANDA (PRO ASOF ONLINE JAMB ORIENTATION COMMITTEE).


@ ASOF 2021


(08039411956 /08088119753).
Share:

GOVERNMENT DARASI NA 59

ASOF - 2021

GOVERNMENT DARASI NA 59

Gabatarwar-Abdulrashid Abdullahi, Kano

Indirect Election
Kaikataccen zabe

Kaikataccen zabe zabe ne na ƙungiyar siyasa ce ta zaɓaɓɓen wakilai, ko ƙananan hukumomi, da aka sani da shugabanin zaɓe, waɗanda kuma daga baya su zaɓi mutane zuwa ofishin siyasa. Ana yin hakan a madadin mutane.

Amincewa da kaikataccen zabe
 1. Ana ganin ‘yan majalisar a matsayin wadanda suka fi cancanta su zabi shugabannin siyasa
 2. Tsarin ba shi da tashin hankali.
 3. An sanar da membobin kwalejin zabe game da dan takarar.
 4. Babu damar Magudin zabe 
 5. Tsarin bashi da tsada
 
Rashin cancantar kaikataccen Zabe

1- 'yancin yan kasa na zabar wakilinsu babu.
 2. Zai iya haifar da cin hanci da rashawa
 3. Tsarin bai dace da dimokiradiyya ba.
 4. Za'a iya zaban shugabanni marasa gaskiya
 5. Membobin hadakar zaɓe na iya cutar da juna.
 6. Wasu membobin na iya yin zabe saboda son kai
7- zababbun membobi an dora su akan mutane

Zaben cike gurbi

Zaben cike gurbi zabe ne da ake gudanar da shi domin cike gurbin mukamai sakamakon rashin cancanta, murabus ko kuma mutuwar wanda ke rike da wannan mukamin

Kashe zaben ko kuri’a ta biyu

Lokacin da babu ɗayan ɗan takarar da ya ci zaɓe da cikakken rinjaye a Babban zaɓen, za a sake gudanar da wani zaɓen

Zaben matakin farko

Zaben fidda gwani zabe ne da ake gudanarwa a tsakanin jam’iyyun siyasa don zaba ingantattun ‘yan takarar da za su iya isar da wakilcin muradin jam’iyya a kowane zabe.

Raba gardama

Kuri'ar raba gardama ita ce ko a'a kuri'ar mutane musamman a kan doka a cikin tsarin siyasa da aka bayar
Indirect Election is the body of elected representative ,or local government units, known as electoral college , who in turn elect people into political office . This is done on behalf of the people.

Merit of Indirect Election

 1. The legislators are seen as best qualified to vote for political leaders
 2. The system is less violent.
 3. Members of the electoral college are well informed about the candidate.
 4. Rigging is partially absent.
 5. The system is less costly
 
Demerits of indirect Election

1- the citizens right to elect their representative is absent.
 2. It can lead bribery and corruption
 3. The system is undemocratic.
 4. Dishonest leaders may get elected
 5. Members of electoral college may victimise one another.
 6. Some members may vote out of selfish desire
7- elected members are imposed on the people

By-election

By-election is an election that takes place to fill vacant elective post as a result of disqualification , resignation or death of the individual holding that office

Run off election or second ballot

When none of the candidate wins the election by absolute majority in General election , another election would be conducted

Primary election

Primary election is an election conducted within a political party to choose credible candidates that can adequately represent the interest of the party in any election

Referendum

Referendum is a yes or no vote of the people particularly on law in a given political system

Abdulrashid Abdullahi musa
6 april 2021 phone 09067298607

Share:

A INA YA KAMATA NA YI RIJISTAR JAMB? 09


✍️SAHIHAN CIBIYOYIN RIJISTAR JAMB A JIHAR KANO✍️


  A INA YA KAMATA NAYI RIJISTAR JAMB?

   
    Kashi Na Tara


     A Kokarin wannan Program na Bayyanawa Dalibai Amintattun Guraren da Hukumar Jamb ta Yarje musu domin zuwa suyi rijistar su ta Jarrabawar Jamb UTME da Direct Entry, wato Approved Cbt Centres, dasuke a fadin Jihohin Arewacin Najeriya guda Goma Sha Tara, Dakuma Babban Birnin Tarayya Abuja,


   A yau zamu dora program dinne da Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu a Jihar Kanon Dabo ko da me kazo Anfika, tareda Adireshin kowacce Cbt Centre.


   Jihar Kano dai tanada Cbt Cbt Centres guda Talatin Da Daya,


   Gasu Kamar haka:


1• Amnet Institute of Information Technology, No. 13C, Hauren Shanu, Near Zone 1 Police H/Q Before Kofar Gadon Kaya, Kano State

2• Audu Bako College of Agriculture, KM 56, Along Kano - Daura Road, Danbatta, Kano State

3• Bayero University, Kano, New Site, Berger Learning Centre, Gwarzo Road, Kano, Kano State (ASOF tayi hadin Gwuiwa da Wannan Cbt Centre, munayiwa Dalibanmu dasukaje can rijista, tare da tabbatar da cewa sun cike bayanansu dai-dai)

4• Bayero University, New Site, e- Learning Centre, Gwarzo Road, Kano, Kano State

5• Bayero University, Old Site, IGR Learning Centre, Kano State

6•Bayero University, Old Site, PTDF Block, Kabuga, Kano, Kano State

7• BMG Institute of Information Technology, No. 13 Bataiya House Gyadi - Gyadi Along Zaria Road

8• Digital Bridge institute (Former Nitel Training School,) No. 532 Katsina Road By Airport Round About, Kano, Kano State

9• Federal College Of Education (Technical), Bichi

10• Federal College of Education, Kabuga Kofar Famfo, Kano, Kano State

11• IITC CBT CENTRE, HADIZA SHARU HOUSE, LAILA BUHARI STREET, UDB ROAD, TARAUNI, KANO

12• JAMB CBT Centre, Beside National Centre For Mass Literacy, Adult and Non - Formal Education, Farawa, Kano State

13• JAMB STATE OFFICE, KANO (REGISTRATION ONLY)

14• Kano State Polytechnic, (School Of Technology), Computer Science Department, Matan - Fada Road, Kano

15• Kano University of Science and Technology, AEE Resource Centre, Gaya Road, Wudil, Kano State

16• Kano University of Science and Technology, Engineering Cbt Centre, Gaya Road, Wudil, Kano State

17• Kano University of Science and Technology, Main Library, Gaya Road, Wudil, Kano State

18• Makama School of Technology, Old Motor Part, Along FCE(T) Road, Bichi, Kano State

19• Moslima Institute of Information Technology, No. 1 Sarkin Yaki, Opposite A.A Rano Filling Station, Airport Road, Kano

20• MS World ICT Institute of Information Technology, No 84, Airport Road, Opposite Chediya Uku, Nomansland, Kano, Kano State

21• NCC CBT Centre, Kano University of Science and Technology, Wudil

22• Over - One Consult and Investment Limited CBT Centre, No 85 Gandu GRA, Atiku Abubakar Road, Kano

23• Pioneers ICT Nigeria Limited, Suite 3 - 4 Gidan Saude, Beside First Bank, Zoo Road, Kano, Kano State

24• Prestigious ICT Investment Ltd, Sani Kabara Street, Sheka, Off Zoo Road, Kano State

25• Rainbow Digital Technology, Rijiyar Zaki Opposite Dorawar Yan Kifi, Kano State

26• Saadatu Rimi College of Education, Zaria Road, Naibawa, Kano

27•Skyline University Nigeria, No 2, Zaria Road, Kano

28• SMS ICT Institute of Training LTD., No. 84 Nomansland by Airport Road, Opposite Shediya Uku, Kano, Kano State

29• The Light College, No. 2 Panshekara, Opp., Police College Panshekara, Kano State

30• Vitae Computer Institute Centre - 2, Kings Garden, By Airport Rd, Opposite Total Filling Station, Brigade, Kano

31• Vitae Computer Institute, Kings Garden by Airport Road, Opposite Total Filling Station, Brigade, Kano.


  Wadancan 🖕 Cbt Centres din da muka lissafo a sama, Sune Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu a yanzu haka a Jihar Kano.


   ∆ Yanada Kyau Dalibi yasani cewar yin rijista a wani gurin da ba Cbt Centre ba, Kan Iya haifar Masa da Matsala a lokacin Jarrabawarsa, dan haka yanada Kyau a kiyaye.


   A Kashi na Goma na wannan Program din, zamuzo muku dauke da Approved Cbt Centres, na Jiha ta Gaba, a cikin Jerin Jihohin da muke dasu a fadin Arewacin Najeriya.


  NB: Kusani Cewar wadannan CBT Centres ne Wanda JAMB ta Tabbatar dasu a 2021, Adadin Nasu zai Iya Raguwa ko Kuma Karuwa, anan gaba


     MUNGODE


Daga Ofishin Secretary General


Marubuci: MIFTAHU AHMAD PANDA (PRO ASOF JAMB ONLINE ORIENTATION COMMITTEE).


@ ASOF 2021


(08039411956 / 08088119753).Share:

GOOGLE TRANSLATORASOF_2021 KANO CHAPTER 


KO KANA DA MASANIYA AKAN GOOGLE ONLINE TRANSLATOR ?


    Kai tsaye ba komai ake nufi da google online translator ba face kawai wata manhaja (Software) wacce zaka iya amfani da ita wajen neman ta fassara maka wani harafi, kalma, jimla cikakkyiya da dai sauran makamantansu, daga wani harshe zuwa wani harshe, sabanin Dictionary wanda shi ya ta'allaka ne wajen fayyace maka bayanin da ya shafi Kalmomi,

    Kamar yadda na fada cewa wannan manhaja tana fassara wani harshe zuwa wani harshe, to haka abun yake, 

   misali:- Daga yaren Turanci zuwa Hausa, Hausa zuwa Turanci, Larabci zuwa Turanci, Turanci zuwa Larabci, da dai sauran su, domin kuwa akwai harsuna da dama a cikin wannan manhaja.

    Kasan cewa ta Dan karami a cikin daliban Illimi yasanya naga dacewar na bada gudunmawa ta zuwa ga Yan uwa Dalibai iri na, wanda bamu iya magana da yaren turanci ko larabci ba, a wasu lokutan har yaren mu na Hausar, yakan Wahalar damu,

  <•> Kwarewar ka wajen iya turanci bashi yake nuna Cewar bazaka yi amfani da wannan software ba.


YADDA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN Manhaja (SOFTWARE)


   Da farko dai zaka ziyar ci rumbun Adana Manhajoji (Playstore), sai ka rubuta GOOGLE ONLINE TRANSLATOR, daganan zai nuna maka manhajar, sai ka sauke ta akan wayarka ta hannu (Installed), daga nan kuma sai ka fara amfani da manhajar ta hanyar rubuta mata abun da kake bukatar ta fassara maka, tareda baka ma'anar da ta dace da abun da ka rubuta Mata. 


Rubutawa🖊️ Khalil Shuaibu Garunbabba ASOF member. WhatsApp/Call 07048767377.
Share:

SABON TSARIN BUƊE PROFILE NA JAMB 2021✍️ JAMB 2021; SABON TSARIN BUDE PROFILE✍️


    •√Shin yaya tsarin bude Profile din Yakoma ?

  •√Menene matsayin lambar Katin Dan kasa da Akace za'ayi Amfani da ita a Bana ?
    •> Hukumar Shirya Jarrabawar Jamb ta sauya tsarin da ake bude Profile domin Samar da lambobin Profile Code, wadanda Ake amfani da su domin Sayen lambobin E-pin, hukumar ta sauya tsarin ne a bana, inda ta Wajabta yin Amfani da lambobin Katin Shaidar Zama Dan kasa domin bude Profile din,


    A yanzu dai dukkannin Dalibin da zai bude Profile wajibine yayi amfani da Lambobin Katinsa na Dan kasa domin Bude Profile din.


•>Tunda tsarin yacanja shin ta wacce hanya zan bude Jamb Profile a Bana ?

    Tsarin da hukumar ta fito dashi a Shekarar bana, domin bude Profile din, Shima ba tsarine mai wahala ba, saidai ya banbanta da na shekarun da suka gabata, a lokacin da ba'ayin amfani da lambobin Dan kasa,

   Idan kana Bukatar bude Jamb Profile a bana, abinda zakayi shine : Zaka shiga Gurin Rubuta Sako (Message) a wayarka, Sai ka Rubuta kalmar NIN sai kuma kasanya Lambobin Katin Dan Kasarka a Gaba, Misali "NIN 12345678910", daga nan kuma Sai katura Sakon zuwa ga lambar 55019 kamar yadda aka saba a shekarun baya, 

   Idan ka Aiwatar da hakan to Shikenan kabude Jamb Profile, sai kajira dan lokaci Kadan, inda hukumar zata Aike maka da Lambobin Profile Code a layinka, ta hanyar Sakon Message, Muddin da Akwai Kudin da basu Gaza Naira 50 ba a layin da ka Aike Sakon dashi.


 
     Daga Alkalamin : Miftahu Ahmad Panda (PRO ASOF ONLINE JAMB ORIENTATION COMMITTEE).


     @ASOF 2021


08039411956 / 08038485677.
Share:

ISLAMIC STUDIES DARASI NA 63


ASOF - 2021

ISLAMIC STUDIES DARASI NA 63

Gabatarwar-Abdulrashid Abdullahi, Kano

The meaning of doing justice between wives
Ma'anar yin adalci tsakanin mata

Kamar yadda yazo a hadisi mutumin da ya auri mace sama da daya kuma ya aikata rashin adalci a tsakanin su za'a tashe shi tare da sassan jikinsa suna fadowa (Abu dawud nisa'i da ibn majah)

Adalcin da ake buƙata na miji tsakanin mata shine dangane da kulawar su (ciyarwa, suttura, masauki) da kuma duk wata kyauta da zai bayar. Hakanan yana wajabta masa nutsar da lokacinsa daidai saboda kowane yana da rabon kamfaninsa.

Koyaya, yayin da zai yiwu ga maigida ya mallaki wannan bangare na samarwarsa da halayensa, ba zai yiwu ya hana kansa jin kaunar mace daya fiye da wata ba. An gane wannan a wata ayar qur'an

وَلَنْ تَسْتَطِيعُوا أَنْ تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّسَاءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ ۖ فَلَا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوهَا كَالْمُعَلَّقَةِ ۚ وَإِنْ تُصْلِحُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمًا
Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin(1) mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
                             (Alkurani 4: 129)

Don haka ko da a yankin da yake da matukar wahalar aunawa da sarrafa halayensa, miji ba zai bari soyayyar da yake wa wata matar ta haifar da sakaci da wata ba, don haka sai a bar ta cikin shakku, tana jin rashin tabbas kuma ba ta bukata.

Lallai sharadin yin adalci tsakanin mata yana da wuyar haduwa, kuma duk wani miji da ke tunanin shiga wani aure na biyu ko wanda zai biyo baya ya kamata ya yi la’akari sosai da irin nauyin da ke kansa da kuma matsalolin da zai iya fuskanta yayin yin adalci.

According to a hadith a man who marries more than one woman and who act unjustly between them will be resurrected with parts of his body falling off ( Abu dawud nisa'i and ibn majah)

The justice required of a husband between wives is in respect of their maintenance ( feeding , clothing, accomodation) and also of any presents that he may give . It also obliges him to divede up his time fairly so that each has a share of his company.

However, while it is possible for a husband to control these aspect of his provision and behavior , it is not possible to stop himself from feeling more love for one wife than another . This is recognized in another qur'anic verse                             (Quran 4:129)

Therefore even in the area where it is most difficult to measure and control his behavior, the husband is not to allow his love for one wife to lead to neglect of another , so that she is left to in suspense , feeling uncertain and unwanted.

Indeed the condition for doing justice between wives are hard to meet , and any husband thinking of embarking on a second or subsequent marriage should consider carefully the responsibilities that he is taking on and the difficulties he is likely to face in doing justice

Abdulrashid Abdullahi Musa
9/April/2021 phone 09067298607
Share:

FRIDAY MESSAGES 317


Assalaam, Yah-Gaffar, Your forgiveness leads to Your mercy, forgive our sins, Yah-Afuwwu. Your mercy creates a clean record and new beginnings for Your servant, have mercy on us. Yah-Zuljalali wal'ikhram, nothing is greater than Your mighty power, forgive our sins with Your power, make our records clean with Your forgiveness, save us from Your punishment in this life, in the grave and the day of judgment. Aameen. Jumma'at mubaarak. Ma'assalaam
Share:

FRIDAY MESSAGES 316


May Almighty Allah sustain our Honour, Uplift our dignity, Answer our prayers, Bless our home and families, 4gv our sins, purify our hearts & grant us unlimited Mercy & endless Favour Fid-duniya Wa Fil-Akhira. Ameen🤲
Juma’at mubarak
Share:

MATA TUBALIN AL'UMMA


Shrin: *MATA TUBALIN AL’UMMA*
Rubutawa: *ZAINUDDEEN ZAIN* _DR.ZAIN_
Maudu’i: _wa cece kishiya? Ya ya dace a zauna da kishiya?_
*KISHIYA* : kalma ce da ke nuna haduwar abubuwa guda biyu karkashin abu daya, ta inda ko wanne daga cikin nau’I na abu biyun, ke kokaarin zama gwani ko tozali a idanun abinda suke kishi a kai. A auratayya, kishiya wata halattaciyar mace ce da ubaangiji ya yi umarni da mazaje su mallaka, ma’ana su auri mace biyu har zuwa uku, matsawar suna da yakinin yin adalci a tsakanin matan.
Kishiya zamu iya kirantaa wata abokiyar zama da ake aurowa mace a gidan mijinta, wacce za ta zama abokiyar rayuwarta da shi mijin nasu har ya zuwa karshen rayukaansu.
Ubangiji shi ya yi umarni ga mazaje da su auri mace sama da daya *(Qur’ani Surah ta 4 aya ta 3).* Idan haka ne kuwa saninmu ne ubangiji da ya halicci dan”adam ya fi sonsa fiye da mahaifiyarsa, akwai hadisin manzo Allah SAW da yazo, bayan kammala yaki, sai suka ga wata mata tana tona gawarwakin mutane tana kuka, sai cen ta ga dan karamin danta, ta dauko shi ta rungume kamar ta hadiye shi, sai manzon Allah ya ce; “kuna ganin waccen matar za tai ya kada danta cikin wuta?” sahabbai suka amsa da “ko da alama ya manzon Allah” sai ya ce; “ubangiji da ya halicce ku, ya fi ku tausayin kawunanku, fiye da tausayin matarnan zuwa ga danta”. Na kawo wannan domin na nuna muna cewa, ubangiji ba ya umarni da abinda zai cutar da mu, da ace kishi mugun abu ne da ubangiji bai ba wa maza dmar karo aure ba.
Ga wata tambaya da members na *MATA TUBALIN AL’UMMA* suka min “_Dr. Zain; da ace matarka za ta karo aure, ko ka tabbatar budurwarka tana tare da wani ya za ka yi/ji?”_ sai a lokacin na kara fahimtar dalilai da ya sa ubangiji bai shari’anta maza su yi kishi ba ta hanyar auren maza sama da daya, domin shakka babu, za a yi kashe-kashe. Su kuwa mata ubangiji ya halicce su da sanyin zuciya da iya barin abu a rai komai zafinsa, da kuma rauni musamman na girman kwakwalwa (inji malaman kimiyya) kan wannan sai ya halatta su yi kishi, saboda za su iya dauka.
*YADDA YA KAMATA A ZAUNA DA KISHIYA*
Tunda addini bai haramta zama da kishiya ba, ba shakka dole addini ya shimfida yadda ya kamata zaman kishiyoyi ya kasance, a rubuce ko a tarihance. Bamuda babban misali na zaman kiyoshi fiye da zaman matan manzon Allah SAW ga wasu daga halayyar da ya dace kiyoshi su dinga kasancewa a kai:
*TAKARA WURIN FARANTAWA MIJI RAI*: maza da dama ana burge su ne idan ana faranta musu rayuwa, duk da sakin fuska da adalci irin na manzon Allah, idan ya shiga dakin Zainab yakan dade, har matansa suka fara tsarguwa a haka, sai daga baya suka fahimci ashe zuma take bashi, shi kuwa Allah ya halicce shi da son zuma, ‘yaruwa, me zai hana ki fahimci abinda mijinki ya fi so kema ki dinga birge shi da shi, domin ki sami kujerar zama a gidanki? Ki lura idan ya fi son kwalliya ta guntun skirt ko jeans da dai sauransu, sai ki dinga yi masa, ki gani yadda hankalinsa zai dawo kanki. Haka ake kishi, ba kullum saai makota sun shigo rabon fada ba.
*TAKARA WURIN TAIMAAKA MASA*: wasu mata, ko sunada abin hannunsu, sun fi so namiji ya ba da nashi a kashe, wannan halayyar ko ba kya da kishiya bai dace ba, amfi so ki dinga tausayawa mijinki kina taimaka masa musamman a cefane da sauransu, ba kullum bani-bani ba. A lokacin da kike yawan rokonsa, ita kuma kishiyarki tama tausaya masa kuma tana taimakonsa, sai kigaa ta kwace gida, ki dawo aza annu a ka kina fadin “ta sihirce shi” bayan laifinki ne. rayuwa fa tanason mai tausaya masa.
*TAKARA WURIN TSAFTA*: tsafta abar so ce kusan a kowacce al’ada haka a dabi’ar dan’adam, idan kishiyarki ta fi ki iya tsafta, gaskiya kina cikin damuwa.
Wadannan kadan kenan kan yadda ya kamata mata su yi kishi a gidajensu ba wai fadace-fadace ba.
Haka yanada kyau, abokan zama (kiyoshi) su hada kawunansu a gidajen mazajensu, susan cewa a gobe kiyama, za’a tambaye su kan irin zama da suka yi da junasu, kar ki kalli kishiya a matsayin makiyiya ko wata muguwa, ki mu’amalance ta a matsayin kanwa ko yaya, haka sai kiga shi karan kansa mijin naku sai ya rasa wace yafi so, kuma duk yadda yaso ya nuna bambanci idan kawunanku suna hade, ba yadda ya iya, dole ya kwatanta.
*KIRA GA MAZA*
Inaso nayi amfani da wannan gabar na kira hankulan maza musamman masu nuna bambanci tsakanin matansu a bayyane, ubangiji ya fada duk yadda muka so ba zamu iya yin adalci dari bisa dari ba, haka zancen yake, amma ko da a ranka ka fi son daya, sai ka bar wannan sirrin a zuciyarka, ka yi mu’amala da kowacce yadda addini ya umarce ka. Mu sani fa, duk wanda baiyi adalci ba a tsakanin matansa, ubangiji zai tada shi rabin jikinsa a shanye.
Wasu maza idan suka lura kawunan matansu na a hade, su kuma gasu da son tada fitini, sai su koma annamimai, su dinga shiga da fita ta yadda zasu raba kawunan matan ta hanyar guntayen maganganu, wannan ma babban laifi ne a wurin ubangiji.
Allah yaimunaa jagora.
*DR. ZAIN*
*MATA TUBALIN AL’UMMA*
Share:

BA YA HALASTA A YI RANTSUWA DA ANNABI ﷺ*BA YA HALATTA AYI RANTSUWA DA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)*

Tambaya

Assalamu Alaikum Dr.ya halatta na ce n arantse da Annabi muhammadu maimakon na rantse da ALLAH ?

Amsa
Wa alaikum assalam Bai halatta ba. 
Duk wanda zai yi rantsuwa, ya wajaba ya yi da Allah ko siffa daga cikin Siffofinsa kamar yadda hadisi ya tabbatar.

Allah ne mafi sani 

Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

21/07/2019

Zaku iya bibiyar mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Share:

HUKUNCIN TUSAR GABA*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*Daga zauren*_
_*📌 Albahral Ilmu 🌴*_
.
.
_*HUKUNCIN TUSAR GABA*_
.
.
_*TAMBAYA*_
:
_Mene ne hukuncin Iskar da ke fita ta Farjin Mace Shin tana karya alwala ko a'a??_
:
_*Amsa:*_
:
_Malamai Ma'abota Ilimi sunyi Saɓani Dangane da hukunci akan Iskar dake fita ta gaban Mace, Mazhabin Hanafiyya da Malikiyya Sun tafi ne a kan cewa dukkan wani abu da zai fita ta gaban Namiji ko kuma ta gaban Mace wanda kuma asali abisa al'ada ba tanan ba ne hanyar fitarsa, wato kamar irin iskar da take fita ta farjin Mata a waɗan su lokuta ko kuma tsakuwa ko tsutsa ta fita ta wajen Malamai sukace irin wannan ba ya warware alwala, domin wannan Iskar ba daidai take da Tusa ba, Sannan sukace ba a samu wani Nassi afili Ƙarara da yake nuna cewa wannan Iskar tana warware alwala, domin Mαnzon Allαh(ﷺ) cewa yayi:_
:
*"لا وضوء إلا من صوت أو ريح"*
*(رواه الترمذي)*
MA'ANA:
_Ba a sake alwala Sai dai idan anji Sautin (fitar tusa) ko kuma anji warin (tusar):_
:
_Amma Mazhabin Shafi'iyya da Hanabila Sukace dukkan wani abu da zai iya fita ta Farjin Mace ko Zakarin Namiji koda kuwa a bisa al'ada ba hanyar fitarsa bace kamar irin wannan Iskar ko wani abun da yake Nadiran (abinda ba a saba gani yana fita ta wajen ba) sukace dukkan waɗannan abubuwa suna warware alwala, Sannan ita kuma iskar dake fita ta Farjin Mace sunyi kiyasin ta ne da tusar dake fita ta dubura, sukace tunda dai tusa tana karya alwala to duk hukuncinsu yazama Ɗaya da na tusa kenan, danhaka dole a sake alwala._
:
_Amma zance mafi inganci shine dukkan wata iska da zata iya fitowa daga gaban Mace to bata warware alwala, amma inda ta fita ne daga duburarta to ko Shakka babu alwala ta warware domin dukkan Malamai Sunyi ijmā'i akan cewa tusar dake fita ta dubura tana karya alwala danhaka dole sai an sake wata kenan, Sai dai wasu daga cikin Malamai sukace idan Mace taji wannan iska ta fito daga Farjinta to abu mafikyau shine ta sake alwala don ta kubuta daga cikin Sabanin da Malamai sukayi_
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©​​✍🏽 ​​Abdulkadeer Umar Alshinkafawy*_
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*
*_​•Ga mai sha'awar shiga Zauren 📌Albahral -Ilmu _​*🌴
_*​ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_​​​​   
      _**_
 _*07064746551*_   
〰〰〰〰〰〰〰〰
Share:

CIWON MARA GA MAI CIKI
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*Daga zauren*_
_*📌Albahral Ilmu 🌴*_
*_CIWON MARA GA MAI CIKI_*
:
*_TAMBAYA_*
:
_Assalamu alaikum malan mace ne cikinta ya kusa wata tara amma mararta da cikinta suna yawan ciwo kome zatayi amfani dashi, Allah ya saka?_
:
*_AMSA_*
:
_TO Za'a iya samun ganyan naa naa sai arika tafasa wa ana yin Shayinsa tana sha da zuwa sau 2 arana._

_Bayan haka za'a iya hulba da kuma habbatusauda sai ahada waje ɗaya arika sanya zuma mara haɗi tarika shan cokali 2 sau uku arana._

_Ko asamo ɗuman rafi sai tarika dafawa kaɗan ta tace tasanya madara tasha._

_Ko kuma a busar dashi ayi garin sa sai tarika ɗiban karamin cokali tana sanyawa cikin madara tana sha Insha Allah za'a dace._
_Allah yasauketa lafiya ameen_
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©​​✍🏽 ​​Abdulkadeer Umar Alshinkafawy*_
.
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*
*_​•Ga mai sha'awar shiga Zauren📌 Albahral Ilmu _​*🌴
_*​ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_​​​​   
      _*07064746551*   
        ​
Share:

MENENE BANBANCI TSAKANIN SALLAR MACE DA NA NAMIJI?

*TAMBAYA TA 10810:*


Assalamu Alaikum
Shin menene banbancin tsakanin sallar mace da namiji inason aqaramin sani?
=
=
*AMSA:*
=
=
_Babu banbanci tsakanin sallan namiji da mace, mace da namiji duk suna daidaita a cikin sallah, saboda fadin manzon Allah (saw) *kuyi sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah* saboda haka wannan ya hada maza da mata. Wannan kuma shine ra'ayin Ibrahimun nakha'i a inda yace; a cikin sallah mace zata aikata ayyukan sallah kamar yadda namiji yake aikatawa. *A duba sifatu salatin nabiyyi can karshen littafin.* Saboda haka babu wani banbanci tsakanin sallan mace da namiji_
=
=
Allah Ta'ala Yasa Mudace.

Via~📚 MATA MUMINAI 📚

*+2348108407420*
*+2347033537189*
*+2348168315013*

Domin kasancewa damu ta shafinmu na facebook se abi ta wannan hanyar a shiga ayi like
https://www.facebook.com/MATA-muminai-1841397762846865/

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anla ilaha illa anta astagfiruka wa'atubu ilaika".
Share:

RAINI DA WULAƘANCI


*RAINI DA WULAKANCI*


Idan Allah Ya nufi bai wa mutum wani abu ba shawara yake da shi ba, 

Wannan abin kudi ne,ko mukami, ko ilmi, ko kyau ko wanin haka, 

Kamar haka idan ya so sai ya karbe abin sa ba tare da shawara ba, 

Hakan ne ya sa ya hana raina wani ko wulakanta shi, 

Allah Yana da kishi idan aka raina masa halitta sai ya dau fansa, 

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai mutum ya yi zurfi cikin sharri, idan ya raina dan uwansa Musulmi”. Muslim. 

Kwace daya daga cikin wadancan abubuwa a wajen Allah (SWT) bai kai zare gashi daga cikin ruwa wahala ba. 
 
Allah Ya kare mu daga wadannan munanan halaye.


Daga
*Miftahul ilmi*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
Share:

AN KUSA BIKINA, AMMA YANZU NA JI NA TSANI WANDA ZAN AURA


*AN KUSA BIKINA, AMMA YANZU NAJI NATSANI WANDA ZAN AURA..*
DAGA ZAUREN
📘 *HISNUL MUSLIM*📘
*TAMBAYA*
Assalamu alaikum mln Dan Allah inaneman shawara nibudurwace toh akwai wandamuke soyayya dashi da inasanshi amma yanxi da akakawo kudin gaisu yanxi sai yaxamana natsaneshi kwata kwata banasanshi banasan ganinshi gashi manya sunshiga narasa yaddaxanyi Dan Allah mln kabani shawara
*AMSA*
To gaskiya baki kyautaba domin baki kawo abinda yasa kika tsaneshiba kuma zamu dauki wannan amatsayin hange da buri ne suka cika miki zuciya kika canza tunani to amma irin wannan matsalar gaskiya mudai munsan galibi shedanun aljanu ne suke haifarwa da mace wannan matsalar zakaga mace tana soyayya da mutum lafiya lau amma daga anfara maganar aure saikuma kaga mace tatsani mutum wani lokacin kuma namijinne daga kinfaramar maganar aure zakiga yatsaneki kodai yatafi babu wani rigima yadaina zuwa amma idan mutum yazo kuna soyayya lafiya lafiya babu maganar aure saikiga bawata damuwa amma daga ankawo maganar aure ciki saikiga talalace to galibi wannan yana cikin abinda aljanu suke haifarwa ga mata awannan lokacin dayawa wannan yahana mata aure batarada sun fargaba Wani lokacin tun anahaka saikuma mace taga gaba daya mazan sundaina kulata andaina zuwa neman auranta kwata kwata 
Allah shine masani
➿➿➿➿➿➿➿
Masu buqatan kasancewa damu ta WhastApp
🔰🔰♻✳🔰🔰
+2348065523065
+2349039510396
〰〰〰〰〰〰〰
🆓facebook.com/hisnullmuslim

http://T.me/hisnulmuslim01

(( ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ))
____________________
Ga wanda yaga Gyara yanasanar damu ! "Wanda yayi nuni zuwaga alheri, yana da ladan wanda ya aikata alherin"...
Share:

MAGANIN YAWAN MANTUWAR KARATU

*MENENE MAGANIN YAWAN MANTUWAR KARATU..?*
DAGA ZAUREN
📘 *HISNUL MUSLIM*📘
*TAMBAYA*
Assslama alaikum mlm don Allah mainini maganin yawan mantuwar karatu
*AMSA*
Wa alaikumussalam warahmatullah wabarakatuhu 

Naci da mayar da hankali kan karatun shi karatu yana bukatar naci koda kahaddace kaita muraja'a kana maimaitawa lokaci bayan lokaci dasunnah zaizaun saikaga koda kadade bakaiba karatun yananan baizubeba sannan yazama hankalinka yanakan karatu bawai kaje kashagala da abubuwan duniyaba kuma sai anjima kace zakadawo kan haddar-a dakayi hakika zaka nema karasa sannan kowa da irin basirar da Allah yabashi wani zaimaimaita aya ko shafi sau 100 kafin yahaddace wani kuwa idan yamaimaita sau 20 anwuce wajan karatun zaizauna wannan kuwa daga Allah ne ni nasan wani dan uwa basaina kama sunansaba idan yarubuta shi yana rubutawa ne a allo tsarine na karatun allo idan yarubuta saiya rike carbi saiya karanta sau dubu koda kwana nawa zaiyi saiya karanta sau dubu saiyatafi wajan malam dan bayar da hadda amma wlh idan yaje gaban malam to farkon karatunma sai antunamar yakara komawa yakaranta sau dari 200 amma idan yazo karshe 3ana zuwa gaban malam ko farkon bazai iya fadiba to aikaga wannan yanada aiki to kowada basirar da Allah yayimar amma wannan abubuwan naci da mayarda hankali wannan shine maganin karatu Allah shine masani
➿➿➿➿➿➿➿
Masu buqatan kasancewa damu ta WhastApp
🔰🔰♻✳🔰🔰
+2348065523065
+2349039510396
〰〰〰〰〰〰〰
🆓facebook.com/hisnullmuslim

http://T.me/hisnulmuslim01

(( ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ))
____________________
Ga wanda yaga Gyara yanasanar damu ! "Wanda yayi nuni zuwaga alheri, yana da ladan wanda ya aikata alherin"...

Share:

ME YA SA RABON GADON MAZA YA FI NA MATA?


Tambaya
:
Malam Mecece hikimar da ta sa rabon gadon namiji yafi na mace yawa?
:
AMSA:
:
Da farko dai babban abin da ake buƙata a wajen musulmi Mumini shi ne yayi imani da dukkan wani hukunci da yazo daga wajen Allαн(ﷻ) ko Mαnzonsa(ﷺ), domin a matsayinsa na bawa anaso ne kaitsaye yaji zuciyarsa ta sallama da wannan hukunci, kuma yaji a ransa cewa hakan shi ne ƙarshen adalci da Allαн(ﷻ) yayi. Shin ya gano hikimar da tasa Allαн(ﷻ) yayi hakan ko kuma bai gano ba, domin Allαн(ﷻ) yana yin abin da yaga dama ne akan bayinsa kuma duk abin da yayi adalci ne babu zalunci aciki, domin Allαн(ﷻ) yana cewa:
:
"وما كان لمؤمن ولا مؤمنة إذا قضي الله ورسوله أمرا أن يكون لهم الخيرة من أمرهم"
(سورة الأحزاب/الآية36)

MA'ANA:
Bai kasance (bai kamataba) ga mumini (namiji) da kuma mumina (mace) idan Allαн(ﷻ) da Mαnzonsa(ﷺ) suka zartar da hukunci cikin wani al'amari ya kasance (muminai) suna da wani zaɓi a cikin al'amarinsu.
:
Danhaka sallamawa da miƙa wuya shi ake buƙata ga mumini.

Alalhaƙiƙa Malamai sun faɗi irin hikimar da tasa Allαн(ﷻ) ya fifita rabon gadon Ɗa namiji akan na Ƴa mace daga cikin waɗannan hikimomi sukace:
:
(1)-Shi dai Namiji dama Allαн(ﷻ) ya ɗora masa wani nauyi a kansa irin wanda ba a ɗorawa mace shi ba:
:
(2)-Namiji ne zai biya sadaƙi yaje ya auro mace:
:
(3)-Shi ne zai nema mata muhallin da zata zauna:
:
(4)-Shi ne zai ciyar da ita:
:
(5)-Shi ne zai ciyar da dukkan 'ya'yan da ta haifa masa:

(6)-Shi ne zai ɗauki dukkan wani nauyi da yake da alaƙa da su:
:
Amma fa ita mace babu wani nauyi da aka ɗora mata a cikin waɗancan abubuwan da a ka ambata, domin ita mace asali kafin ayi mata aure tana zaune ne a gidansu kuma iyayenta musamman uba shi ne yake ci da ita kuma yake ɗaukan dukkan ɗawainiyarta.

Ko kuma ya kasance ɗan'uwanta ne namiji (Brother) yake ɗaukan dukkan nauyinta.

Sannan kuma idan tayi aure to fa dukkan nauyinta ya koma kan mijinta ne:
:
Sannan kuma misali: sau da yawa idan a ka raba gado tsakanin mace da namiji sai aga rabon gadon shi namijin ya ƙare ya bar na macen, domin dama ita nata rabon ba taɓashi a ke ba, kuma wataƙilama ba ta da kowa sai wannan ɗan'uwan nata da aka raba musu gadon tare, gashi kuma yanzu nauyinta yana kansa kenan, kuma dole da dukiyarsa zai riƙa ɗaukan nauyinta har kafin tayi aure:
:
Sannan kuma abin lura anan shi ne, ba fa a kowanne irin hali na rabon gado ba ne namiji yake ɗaukan kaso biyun 'ya mace ba, a'a akwai gurare da yawa na rabon gado inda namiji da mace rabonsu yake zuwa daidai a tsakaninsu. Sannan kuma akwai yanayin da rabon gadon 'ya mace yake fin na namiji yawa, akwai kuma wajen da mace take iya cin gado amma shi kuma namiji bai ci ba. Misalin inda rabonsu yake zuwa daidai shi ne.
:
Mutum ne ya mutu yana da uwa da kuma uba sannan kuma yana da Ɗa, to anan rabon da za a bawa uwa da uba daidai suke ba fifiko, domin kowa a cikinsu za a bashi kaso ɗaya bisa shida (1/6)ne na dukiyar. Shi kuma ɗan sai ya kwashe sauran.
:
Misalin wajen da gadon mace yake fin na namiji shi ne, mace ta mutu tana da miji da kuma 'yarta guda ɗaya, to a nan za a bawa ita 'Yar rabin dukiya ne, yayinda shi kuma miji za a bashi kaso ɗaya bisa huɗu (1/4)ne, sannan kuma abinda ya rage na dukiyar za a bawa ita wannan 'yar ne duk ta haɗa ta riƙe.

※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Share:

HUKUNCIN WANDA BA YA GAMSAR DA IYALINSA SABODA AZUMIN NAFILA


*MENE NE HUKUNCIN WANDA BA YA GAMSAR DA IYALINSA SABODA AZUMIN NAFILA?*

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Malam barka da warhaka, wani bawan Allah ne yake azumin Litinin da Alhamis, ga shi yana shiga hakkin matarsa wani lokachin, tayimishi magana amma yace shi ba zai daina ba so yake ya saba da azumin, komai zaifaru sai dai ya faru, malam azumin ko sauke hakkin matarsa? Allah ya kara daukaka mlm na gode.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salamu, Tabbas yana daga cikin haqqoqi na wajibi na ma'aurata a kan junansu sauke wa juna haqqin aure ta ɓangaren saduwa, kuma rashin cika wannan haqqin na iya sa ɗaya daga cikin ma'aurata ya kusanci saɓon Allah ta hanyar zina musamman idan aka samu raunin imani, ko kuma hakan ya haifar da mutuwar aure ma baki ɗaya.
Shi kuma yin azumin Litinin da Alhamis sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah ﷺ , saboda haka ya sauke wajibin iyalinsa a kansa shi ne a gaba akan yin azumin nafila, saboda katange matarsa ga aikata abin da bai dace ba, kamar yadda yake faɗin komai zai faru ya faru, wannan magana tasa kuskure ne.
Saboda rashin gamsar da juna a tsakanin ma'aurata kaɗai na iya haifar da faruwar fitinar da ba za a iya shawo kanta a tsakaninsu ba in ba ta wannan hanyar gamsarwar ba. Saboda haka sai ya rage yin azumin a kai a kai ko da ba zai daina ba gaba ɗaya tun da yana son koyi da sunnah, kuma ita kanta gamsar da iyali akwai lada a cikinta, kamar yadda azumin taɗawwu'i yake da lada.
Idan kuma ya qi ji, to ta yi haquri da shi akan hakan, saboda kada matsawarta a gare shi ya haifar da wata fitina a tsakaninsu, matuqar dai ba kusantarta ne ba ya yi baki ɗaya ba.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Share:

HUKUNCIN MAFARKI

*HUKUNCI MAFARKI* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarkaatuh.

Shin meye Hukuncin Mafarki da mukeyi a bacci, wani kyakkyawa mai faranta rai wani kuma mummuna mai bakanta rai?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Wasu zaka samu insukayi mafarki mara kyau toh sai kaga sun sanya kansu cikin damuwa da tashin hankali su rinka ganin kaman abinda suka gani a bacci gaskiya ne kuma zai faru dasu, wasu hakan tana sa har zargi ta shiga tsakaninsu da iyalansu su rinka ganin kaman suna aikata alfasha sabida kawai abinda suka gani acikin bacci.

 *Toh meye Hukuncin Mafarki Mai Kyau?* 

Duk wanda yayi mafarki mai kyau Mai faranta rai toh ya godewa Allah, kuma yana da daman ya sanar da na kusa dashi, domin wannan mafarki daga Allah take

Abu Sa’eed(Radiyallahu anhu) Ya rawaito hadisi daga manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) Annabi yace: “idan dayanku yaga mafarki wanda yakeso, toh ya godewa Allah sannan ya bada labarin wannan mafarkin”
Bukhari Ya rawaito.

Haka nan a wata riwaya ta bukhari
Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yace: “kyakkyawan mafarki daga Allah ne”

Abinda ya dace mutum yayi in yaga mafarki mai kyau:
Idan mutum yaga mafarki mai kyau acikin baccinsa toh bayan ya tashi sai yayi wa Allah godiya akan wannan mafarki yana mai fatan Allah ya tabbatar da ita,
Sannan kuma sai ya sanar da nakusa dashi.

 *Hukuncin ganin mummunan mafarki* 

Wanda duk yayi Mafarki mummuna, toh Kada ya daukesa da wani mahimmanci ballanta har ya gina wani Hukunci akansa, domin wannan daga shaidan ne.

An rawaito daga manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) yace: “Mummunan mafarki daga shaidan ne,duk wanda yayi mafarkin abinda yake tsoro toh ya nemi tsari daga Allah sannan yayi tofi a gefen hagunsa,sharrin wannan mafarki bazata cutar dashi ba” Albukhari.

A wata riwaya kuma:
“Idan mutum yaga mummunnan mafarki wanda bayaso, toh ya nemi tsari daga Allah, sannan Kada ya sanar da kowa shi.”

Abinda mutum zaiyi idan yaga mummunan mafarki:
Ya nemi tsari daga Allah daga shaidan.
Yayi tofi a gefen hagunsa sannan ya canza gefen da yake kwance akai.
Sannan inso samu ne ya tashi yayi nafila raka’a biyu.
Sannan kada yabaiwa kowa labari kuma kada ya damu kansa ko kuma ya kullace wani a dalilin wannan mafarki.

Daga Karshe akwai wani Bangare mai kama da mafarki amma ba mafarki bane, shi ana kiransa zancen zuci. Shine mutum zai sanya wani abu a ransa kyakkyawa ko mummuna yayi ta tunaninsa toh inyazo acikin baccinsa ma sai wannan abu yayi ta zuwa masa, toh itama wannan ba’a daukan ta komai ba’a kuma yin la’akari da ita.
Allah ya sa mudace. 

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Share:

YA YI ZINA DA MATAR AURE

*YAYI ZINA DA MATAR AURE* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Malam _Don Allah a sakaya sunana_ 
 _Malam don Allah ayi kokari duk abinda na fada a wallafa shi a wannan zauren mai albarka don ya zama darasi garemu baki daya._ 

 _Ni dai ma'aikacine kuma yanzu haka ina wata jiha don aiki kamar yadda daga lokaci zuwa lokaci aiki yakan kaini. Zuwata wannan jihar sai na hadu da wani abokina har ya zamanto banda wurin fira sai wurinshi._ 

 _A nan wata rana na hadu da wata yarinya inda daga karshe dai na karbi lambar wayarta. Hira tsakanina da yarinyar nan ya wuce na tsakani da Allah daga karshe har sai da muka yi zina (Astagrirullah wa atubu ilaihi)._ 

 _Kafin wannan mummunan abin ya faru, abinda na iya sani a game da yarinyar daga wurin abokina shine; ta taba aure amma mijin ya gudu ya barta ba a san inda yake ba, kusan shekara daya kenan amma yanzu kotu ta raba auren wand ita ko da wasa bata taba fada min hakan ba. Sai dai cewa tayi tana da saurayi amma ya yaudareta ya gudu ya barta._ 

 _Mun ci gaba da abinda dani da ita muka kira soyaiya duk da cewa wallahi har cikin zuciyata ni na san bana sonta sai dai ban san abinda ke cikin nata zuciyar ba._ 

 _Kada dai in tsawaita wannan labarin, daga karshe dai ranar wannan sallan babba sai ita da kawarta suka kawo mini abinci sai naji a zuciyata kuma yanzu babu wanda hankalina ya karkata wurinta sai kawar. A dai dai wannan lokacine ita yarinyar take cemin zata yi tafiya zuwa wani wuri amma ba zata dawo ba sai bayan wata daya._ 

 _Bayan ta tafi sai na koma kiran ita kawar a waya wanda daga baya na samu hadin kanta da sunan soyaiya. Cikin irin firar da mukeyi ne, ita kuma don ta samu gindin zama sosai a zuciyata ta fada min abinda shine dalilin tashin hankalin da bana taba shiga ba. Watau abinda ta fada min shine. Ko na san cewa wannan yarinyar tana da aure? Nace wallahi ban sani ba. Kuma hakane wallahi ban sani din ba. Abinda na sani shine an kashe aurenta da mijinta da ba a san inda yake ba._ 

 _Tafiyar nan da take cewa tayi zatayi wata daya a wurin ashe gidan mijinta ta koma. Kuma duk da cewa ta koma gidan mijin tana kirana kuma muna waya har da maganganu na batsa. Amma ban san cewa a gidan mijin take ba._ 

 _Allah ya gafarta malam. A daidai wannan lokacine nake baran addu'a a wurin yan uwa, ubangiji Allah ya yafemin wannan abinda na aikata. Lallai wannan ya zama dalilin tuba a gareni. Kuma ina mai tuba zuwa ga Allah. Ina son wannan abin ya zamo darasi ga kowa. Maza da mata, muji tsoron Allah._ 

 _Shin ko Allah zai karbi tubata? Sannan kuma malam wadanne irin addu'o'I ya kamata in rika karanta wa don tuba da neman yardar Allah. Ina cikin tashin hankali wanda ban taba shiga cikinsa ba a rayuwata._ 

 __Allah kadai yasan halin da nake ciki har a yanzu da nake wannan rubutun._ 

 *AMSA* 👇

 _Tabbas kayi katobara, ka zalunci kanka. Ka aiwatar da Babban Kaba'ira._ 

 _Amma babban abinda ya bani haushi kuma ya bani mamaki acikin wannan dogon labarin naka shine:_ 
 _Wato kai ba wai kana yin nadamar aikata Zina bane. A'A. Kai kana yin nadama ne kawai saboda ance maka matar aure ce!!!_ 

 _Agaskia dunia ta rudeka. Kuma shaitan ya riga ya rinjayeka. Ka zama nasa._ 

 _Kuma tabbas mazinata suna haduwa da Qaskanci da wulakanci da Qaskanci da talauci tun daga nan dunia kafin aje lahira._ 

 _Don haka ka tuba izuwa ga Allah. ka kaurace ma zinan da kakeyi. Kuma ka dena duk wata hulda tare da abokananka wadanda kuke yin zinar nan tare.._ 

 _Ka yawaita istighfari da aiyukan alkhairi wadanda Allah yake kankare Zunuban bayinsa dominsu. (Kamarsu azumin nafila, tasbihi da salatin Annabi saww.)_ 

 _Sannan kaje ka nemi gafarar mijinta domin shiga hakkinsa da kayi. Idan kuma neman yafewarsa zata janyo maka tozarta da kuma tashin hankali, to sai kaci gaba da yi masa addu'a. Kana nema masa gafara awajen Allah._ 

WALLAHU A'ALAM

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Share:

HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI


*HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI* ! ! 

*Tambaya*

Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan ban yi ba za'a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai. 

*Amsa*
Wa'alaykumussalam, 

To dan'uwa Allah ya ba mu dacewa gaba daya, tabbas malamai sun tattauna akan hukuncin zaman makoki,
 saidai sun kasu kashi uku :

1. Akwai wadanda suka tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir RA wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Mun kasance muna kirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta" , Musnad : 6905, don haka suna cewa, saidai a hadu da wadanda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta'aziyya, wannan ita ce maganar Shafi'i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu'u 3\306 .

2. Akwai wadanda suka ta tafi akan cewa bidi'a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma'ad 1\527

3. Akwai malaman da suka tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A'isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid dan Haritha da Ja'afar dan Abu-dalib Annabi s.a.w. ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin cikin tare da shi, sai wani mutum ya zo ya ce masa : ga matan Ja'afar can suna ta kuka, sai Annabi s.a.w ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri" Bukhari hadisi mai lamba ta : 1299. Wadannan malaman suna cewa : Za'a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu :

A. Fadin nana A'isha cewa : ya zauna ana ganin alamun bakin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin, dalili ne da yake nuna cewa : yana zaune ne a wurin da mutane suka sani kuma suke zuwa su same shi.

B. Kasancewar bai hana matan Ja'afar taruwar da suka yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su.

Wannan maganar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya,, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi akan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303
Prof. Khalid Al-mushakih (daya daga cikin manyan daliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, saidai za'a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman :

1. Yawaita yin abinci, da masu karbar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa.

2. Nisantar yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi'o'in da ba su da hujja.

3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon bukata.
Duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na : 75

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

19/10/2014
Share:

TA YI AURE DA CIKIN SHEGE

*TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE??*

 *Tambaya:*

Assalamu alaikum. Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.
Yanzu sunyi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

*Amsa*

Wa'alaykum assalamu Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. 

Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa.

 Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra'i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. 

Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za'a raba wannan auren ko da sun haifi 'ya'ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. 

Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.

Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi'i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra'i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra'i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud: 1847.

Don neman karin bayani duba: AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, sai dai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

27/02/2016. 

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
*Gabatarwa:* Abu- Unaisa.

👉🏾 Darussunnah Foundation, 07035888158.

Share:

TA YI AURE DA CIKIN SHEGE

*TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE??*

 *Tambaya:*

Assalamu alaikum. Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.
Yanzu sunyi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

*Amsa*

Wa'alaykum assalamu Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. 

Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa.

 Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra'i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. 

Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za'a raba wannan auren ko da sun haifi 'ya'ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. 

Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.

Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi'i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra'i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra'i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud: 1847.

Don neman karin bayani duba: AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, sai dai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

27/02/2016. 

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
*Gabatarwa:* Abu- Unaisa.

👉🏾 Darussunnah Foundation, 07035888158.

Share:

ZINA💥 *PROHIBITED ACTIONS*
🎯 󠰠 *الأمور المنهى عنها* 

✍🏽 *بسم الله الرحمن الرحيم*
 In the name of Allaah, The Beneficent, The Merciful.
 
🗓 *DATE 19 RAJAB 1442AH*
        *WED: 3 - MARCH - 2021.*
        
📇 *TOPIC: ZINA*

🌴 *وعن أبي سعيد رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال‏:‏ ‏"‏لا ينظر الرجل إلى عورة الرجل، ولا المرأة إلى عورة المرأة، ولا يفضي الرجل إلى الرجل في ثوب واحد، ولا تفضي المرأة إلى المرأة في ثوب واحد‏"*
*(‏‏(‏رواه مسلم‏)‏‏)‏‏.‏*

🌴Abu Sa'id Al-Khudri ( _May Allah be pleased with him_) said: The Messenger of Allah (ﷺ) said, "A man must not look at a man's private parts nor must a woman look at a woman's private parts; neither should two men lie naked under one cover, nor should two women lie naked under the same cover."
[ _Muslim_].

❗ *الله تعالى أعلم*
Allaahu ta'aala a'alam.( _Only Allaah the most High Who really knows_)

🙏🏽 *رَبِّ زِدْنَا عِلْمًا*
*“My Lord! Increase us in knowledge!"*

🤲🏽 *اللَّهُمَّ اغْفِرْلنا، وَارْحَمْنا، وَاهْدِنا، وَاجْبُرْنا، وَعَافِنا، وَارْزُقْنا، وَارْفَعْنا.*
*_O Allah forgive us, have mercy on us, guide us, support us, protect us, provide for us and elevate us._*

*MUSA AHMAD WAZIRI* _IMAM KASU_.
Share:

NADAMAR BAYAN MUTUWA


*NADAMAR BAYAN MUTUWA*
-
GABATARWA:
Muhammad Umar Baballe.
-
"Haƙiƙa sau da yawa a wannan duniyar akanyi nadama bayan aikata kuskure sannan kuma nadamar tayi amfani, amma a ranar lahira nadama bata sanya mai yinta ya samu sauƙi daga cikin takaicin da yake addabarsa a gaban Allah"
-
"Anan duniya zaka iya aikata wani abu mara kyau, sannan daga baya kayi nadama ta zamto maka alkhairi kuma tasa ka sami yarda daga gurin mutane, amma a ranar lahira nadama abinda ke bin bayanta shine asara"
-
"Daga lokacin da aka binne ɗan adam, shikenan ya shiga cikin kogin yin nadamar me yasa bai aikata abu kaza da kaza ba, me yasa bai yiwa Allah biyayya a lokaci kaza ba, me yasa bai tsaya ya bautawa Allah yadda ya dace ba"
-
"Wannan nadama ce wacce bata da amfani, domin lallai amfaninta a duniya yake, to shi kuma ya riga ya bar duniyar, kaga kenan babu damar yin gyara balle nadamarsa tayi masa amfani"
-
"Wallahi bayan mutuwar mutum, zai so ace Allah ya ara masa koda second guda ne domin ya dawo wannan duniyar yayi wa Allah sallah koda raka'a ɗaya ce, to amma babu wannan damar, damar sa ɗaya ce, itace lokacin da yake a raye, to shi kuma yayi wasa da ita yau gashi har ya bar duniyar"
-
"Mutane sukan aikata zunubai masu tarin yawa, suna zullumin cewa ai nan gaba zasu tuba, sun manta da cewa ikon karɓar rayuwarsa ba a hannayen su yake ba, Allah ne kaɗai yake da sanin ranar mutuwar kowa"
-
"Sai bayan sun gama tafka kuskurensu, a ranar lahira kuma suzo da fuskar tausayi suna nuna nadama, alhalin kuwa wannan baza tayi musu aiki ba"
-
Ya Allah ka raba mu da yin nadama a ranar lahira, Ameen.
-
✍🏿Muhammad Umar Baballe
Share:

CHARITY IN ISLAM
➖➖➖
*CHARITY IN ISLAM*
➖➖➖
*The Hands That Gives Never Lack*
➖➖➖

Charity is a tenet among the pillars of Islam, everything a person has belongs to Allaah (ﷻ) and therefore a Muslim is obliged to share his wealth with the less privilege.

Charity is an act of giving out to the people in need and society at large. Charity can be in the form of money, goods, food or even a simple act of spending time with those who need your assistance in any form. 

Life doesn’t offer equal opportunities for everyone; through charity we can share our blessings with those less privileged and thus try to bring balance to the society.

__
Different categories of charity are defined in Islam, the two most important are *Zakat (obligatory charity) and Sadaqat (voluntary charity).*

Allaah (ﷻ) says in the Glorious Qur'an: 

*يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنفِقُوا۟ مِمَّا رَزَقْنَٰكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِىَ يَوْمٌۭ لَّا بَيْعٌۭ فِيهِ وَلَا خُلَّةٌۭ وَلَا شَفَٰعَةٌۭ ۗ وَٱلْكَٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ*  


_“O you who have believed, spend from that which We have provided for you before there comes a Day in which there is no exchange and no friendship and no intercession.”_

(Al-Baqarah 2:254)

_
Allaah (ﷻ) also says:

*ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَٰلَهُم بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ سِرًّۭا وَعَلَانِيَةًۭ فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ*

_“Those who spend their wealth [in Allaah's way] by night and by day, secretly and publicly - they will have their reward with their Lord. And no fear will there be concerning them, nor will they grieve.”_

(Al-Baqarah 2:274)

_
He (ﷻ) says:

*لَن تَنَالُوا۟ ٱلْبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُوا۟ مِمَّا تُحِبُّونَ ۚ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِن شَىْءٍۢ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌۭ*

_“Never will you attain the good (reward) until you spend (in the way of Allaah) from that which you love. And whatever you spend - indeed, Allaah is Knowing of it.”_

(Aal-e-Imran 3:92)

The Prophet (ﷺ) said: *_“Your smile for your brother is a charity. Your removal of stones, thorns or bones from the paths of people is a charity. Your guidance of a person who is lost is a charity.”_*

(40 Hadith Nawawi 26)
  
*سبحان الله*

This means someone doesn't have to be a millionaire to give out charity.

Allaah's Messenger (ﷺ) also said: *_“Protect yourself from hell-fire even by giving a piece of date as charity.”_* 

(Ṣaḥīḥ al-Bukhārī 6195, and Ṣaḥīḥ Muslim 1016)

Shaykh ‘Abdul-‘Azeez bin ‘Abd-Allāh bin Bāz (رحمه الله) said: _“[Optional] Charity wards off an evil death, [wards off] calamities and extinguishes sins [the way water extinguishes fire].”_

[Majmū al-Fatāwa 4/183 | Shaykh ‘Abdul-‘Azeez bin ‘Abd-Allāh bin Bāz.] 

__
And Allaah (ﷻ) says:

*إِنَّ ٱللَّهَ يَجْزِى ٱلْمُتَصَدِّقِينَ*

_“Indeed, Allaah rewards the charitable.”_

(Yusuf 12:88)

Charity is our deen, not only does it act as a protection and witness to our deeds it helps to contribute to the society positively.

Charity is seen as multiplication of wealth in contrast to giving out money which keeps reminding Muslims about Akhirah and their accountability before Allaah (ﷻ). Thus, Islam heavily promotes charity and every Muslim is rewarded with something which is way better than what he gives up in the way of Allaah.

May Allaah (ﷻ) accept our offerings and protect us from becoming miserly.

*آمِيْن يَارَبَّ الْعَالَمِينْ*
 ==============================
🕋
Share:

RESPONDING TO HER HUSBAND


🌹Responding To Her Husband 

Shaykh Sālih Ibn Fawzān Al-Fawzān حفظه الله said:

“Rather, it is more befitting that she approaches him without him requesting; and that she prepare herself for that and beautify herself. For from that which is unfortunate is that some women beautify themselves when going out - while they have been prohibited from that - more so than they beautify themselves for their husbands while they have been commanded with this. All of that indicates ignorance of the responsibility or not following the legislation of Allāh. Indeed the woman establishing this matter and excellence in taking to it has a great effect upon the stability of the home; for the chastity of the husband and his pleasure with that which he has, and not feeling a sense of frustration and deprivation, results in the stability of the soul. How numerous are the men who live a life which is unstable due to their feeling deprivation because the woman has not given this matter importance or she does not know how to establish it correctly. Let the woman know her role in this regard; then let her think and research how to perform it.”

[A Woman’s Guide To Raising A Family, pg.33. Translated By Raha Ibn Donald Batts
Share:

AZUMIN WATAN RAMADAN 01*🌙AZUMIN WATAN RAMADAN 01🌙*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
*مجلس السنة*
📓📔
+2349032091131
+2348142100514
.
.
.
Yau 21/ 08/ 1439 wanda yayi dai-dai da 15/ 04/ 2018 muka fara wannan lekcar mai taken *AZUMIN WATAN RAMADAN*
=
=
*GABATARWA:*
=
*ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻟِﻠَّﻪِ، ﻧَﺤْﻤَﺪُﻩُ ﻭَﻧَﺴْﺘَﻌِﻴﻨُﻪُ، ﻣَﻦْ ﻳَﻬْﺪِﻩِ ﺍﻟﻠﻪُ ﻓَﻠَﺎ ﻣُﻀِﻞَّ ﻟَﻪُ، ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﻀْﻠِﻞْ ﻓَﻠَﺎ ﻫَﺎﺩِﻱَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻟَﺎ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ*
_Godiya ta tabbata ga Allah; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai 6atar da shi, wanda Ya 6atar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu wanda a ke bauta wa bisa cancanta sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa._
_Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa, akan haqqin binSa da taqawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa._
_Ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taqawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata. Kuma ku bi Allah da taqawa, Wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne._
_Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa, kuma ku fadi magana madaidaiciya. Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta zunubanku. Kuma wanda ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, tho, lalle, ya rabanta, babban rabo mai girma._
_Bayan haka: Yan uwana na wannan zauren mai albarka. Lallai mafi kyawun magana, (shi ne) littafin Allah, kuma mafi kyawun shiriya (ita ce) shiriyar Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Kuma mafi munin al'amura (su ne) abubuwan da aka qago (a cikin addini). Domin dukkan qagaggun abubuwa (wadanda ba su da asali a cikin Alqur'ani da Sunnah) bidi'a ce, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata (makomarta) cikin wuta._
_Bayan nan Kuma Jama'a. Azumin Ramadān na daya daga cikin rukunan Musulunci, kuma yana dauke da alhairai da martabobi da falala da darajoji masu yawan gaske. Wajibi ne a kan kowane Musulmi ya yi qoqarin sanin hukunce–hukuncensa, kasancewa jahiltar haka na iya haifar masa da matsala a cikin azuminsa. Da ya ke azumi ibada ce da Allah ya yi umurni da yi, Musulmi na buqatar sanin yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi azumi a lokacin da ya ke raye. Ta haka ne zai san abubuwan da ke gyara azumi ko su bata shi, ya san abubuwan da suka halasta ga mai azumi da wadanda ba su halasta ba, da dai sauransu._
_Tho Jama'a ganin yadda mutane ke nuna tsananin kwadayin sanin yadda za su yi azumi akan karantarwar Alqur’ani da ingantattun Hadisai bisa fahimtar magabata na qwarai, don su san falala da darajojin azumin, da abubuwan da ke bata shi da wadanda ba su bata shi, da nau’o’in ibada da ake son a yi a lokacin azumi, da hanyoyin da za a bi don ganin an dace da alhairan da ke cikinsa, naga ya dace inyi wannan dan takaitaccen lekca a matsayin tunatarwa gare ni da sauran yan’uwa Musulmi. Na taqaita bayanan da ke cikin lekcan nan ta yadda mai karatu zai yi amfani da su a matsayin jagora gare shi cikin azumi. Na sanya wa wannan lekcar sunar *AZUMIN WATAN RAMADAN*. Ina ba mai karatu shawarar bin hashiyar lekcar a lokacin da ya ke karantawa, kasancewar zata taimaka masa wajen kyautata fahimtar saqon da ke ciki._
_Ina roqon Allah Mai girma da daukaka ya karbi wannan dan aiki a matsayin ibada, Ya ba ni ladan da Ya tanadar wa wadanda ke qoqarin karatu da karantar da addininSa, kuma Ya yi sakamakon alhairi ga wadanda suka taimaka, ta kowace hanya a wajen tabbatar da lekcar ko Ina a social media. Ina roqon Allah Ya yafe mani kurakuran da ke ciki. Haka kuma, ina roqon wadanda suka ga kuskure acikin wannan lekcar, su fadakar da ni Domin a gyara._
=
=
Zamu dakata anan sai bayani na gaba Inshaa Allahu.
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
Mai yadawa
°
*_Bilyaminu Taheer Musa (Cameroon)_*
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Share:

A INA YA KAMATA NA YI RIJISTAR JAMB? 08

💯 AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM 💯


  A INA YA KAMATA NAYI RIJISTAR JAMB ?


   
    Kashi Na Takwas


  A Koƙarin wannan Program na bayyanawa Dalibai Amintattun Guraren da Hukumar Jamb ta Yarje musu domin zuwa su gudanar da rijistar Jarrabawarsu ta Jamb, wato Approved Cbt Centres, dasuke a Fadin Jihohin Arewacin Najeriya guda Goma Sha Tara, Dakuma Babban Birnin Tarayya Abuja,


   Bisa Alfarmar Faisal Jibril, Insha'Allahu a yau zamu Dora program dinne da Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu a Jihar Niger, tareda Adireshin kowacce Cbt Centre.


   Jihar Niger dai tanada Cbt Cbt Centres guda Goma Sha Bakwai,


   Gasu Kamar haka:


1• Air-Max Computer Institute, Beside St. Theresa Catholic Church, Madalla, Niger State

2• Bishop James Yisa Memorial School CBT Centre, Kwamba, Suleja, Niger State

3• Brilliant Impact International Academy CBT Centre, Plot 1, 2 &3 Brilliant Impact Street, Angwan-Boro Gauraka, Tafa L.G.A. Niger State

4• FH Investment Limited CBT Centre, Uphill rest house estate, kobwa,Kuta, Niger State

5• Federal Polytechnic, ICT Hall, Doko Road, Bida, Niger State

6•Federal Univeristy of Tech, E -exam Centre 3, Main Campus, Gidan Kwano, Minna, Niger State

7• Federal University Of Tech, Electronic Test Centre, Gidan Kwano Campus, Minna, Niger State

8• Federal University of Technology, E-Exam Centre 2, Main Campus, Gidan Kwano, Minna,Niger State

9• IBRAHIM BABANGIDA UNIV. LAPAI, E-LIBRARY CBT CENTRE, NIGER STATE

10• JAMB Zonal Office, CBT Centre, 3 Arms Zone, Maitumbi, JAMB Office, Minna, Niger State

11• JAMB/NCC CBT Centre, 3 Arms Zone, Maitumbi, Beside JAMB Office, Minna, Niger State

12• NIGER STATE POLYTECHNIC, BIDA CAMPUS (CABS), DOKO ROAD, NEAR FEDERAL POLYTECHNIC, BIDA, NIGER STATE.

13• Niger State College of Agriculture CBT Centre, Beside Railway Station, Mokwa, Niger State

14• Niger State Polytechnic, Zungeru-Bida Road, Zungeru, Niger State

15• Niger state College of Education, CBT Centre, Minna, Niger State

16• Sani Bello College ICT Centre

17• Spectrum Computer Centre, Beside Pinnacle Petrol Station, Opposite Polosa Junction, RafinSanyi, Suleja.


  Wadancan 🖕 Cbt Centres din da muka lissafo a sama, Sune Cbt Centres din da hukumar Jamb ta Amince dasu yanzu haka, a Jihar Niger.

   ∆ Yanada Kyau Dalibi yasani cewar yin rijista a wani gurin da ba Cbt Centre ba, Kan Iya haifar Masa da Matsala a lokacin Jarrabawarsa, dan haka yanada Kyau a kiyaye.


   A Kashi na Tara na wannan Program din, zamuzo muku dauke da Approved Cbt Centres, na Jiha ta Gaba, a cikin Jerin Jihohin da muke dasu a Fadin Arewacin Najeriya.


  NB: Kusani Cewar wannan CBT Centres ne da JAMB ta Tabbatar dasu a 2021, Adadin nasu zai Iya Raguwa ko Kuma Karuwa, anan gaba.


     MUNGODE


Daga Ofishin Secretary General


Marubuci: MIFTAHU AHMAD PANDA (PRO ASOF ONLINE JAMB ORIENTATION COMMITTEE).


    Tare da Taimakon:

FAISAL JIBRIL.


@ ASOF 2021


(08039411956 / 08088119753).

Share:

KU NISANCI ABUBUWAN BAKWAI MASU HALAKARWA

_*KU NISANCI ABUBUWA BAKWAI MASU HALAKARWA*_
        
_Hadisi Ya Tabbata Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yana Cewa *Manzon Allah (ﷺ)* Yace:_

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : *”ﺍﺟﺘﻨﺒﻮﺍ ﺍﻟﺴﺒﻊ ﺍﻟﻤﻮﺑﻘﺎﺕ“*، ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﺎ ﻫﻦ؟ ﻗﺎﻝ : *”ﺍﻟﺸﺮﻙ ﺑﺎﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﺴﺤﺮ، ﻭﻗﺘﻞ ﺍﻟﻨﻔﺲ ﺍﻟﺘﻲ ﺣﺮَّﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﺤﻖ، ﻭﺃﻛﻞ ﺍﻟﺮﺑﺎ، ﻭﺃﻛﻞ ﻣﺎﻝ ﺍﻟﻴﺘﻴﻢ، ﻭﺍﻟﺘﻮﻟﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺰﺣﻒ، ﻭﻗﺬﻑ ﺍﻟﻤﺤﺼﻨﺎﺕ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﺎﺕ ﺍﻟﻐﺎﻓﻼﺕ“* 
```{ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ٢٦١٥}```

_An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)*, Daga *Annabi (ﷺ)* Yace: *“Ku Nisanci Abubuwa Guda Bakwai Masu Halakarwa”.* Sai (Sahabbai) Sukace Wadanne Abubuwa ne? Sai Yace: 
1-“Hada Allah da Wani a Cikin Bauta,
2-da Yin Sihiri, 
3-da Kashe Ran da Allah ya Haramta (Sai da Dalili Na Shari'a),
4- Da Cin Riba, 
5- da Cin Dukiyar Maraya,
6_Da Guduwa a Fagen Dãgã, 
7_da Yiwa Mata Muminai Katangaggu Kazafi”.

```{Bukhari Ya Ruwaitoshi: 2615}```

Share:

ƊAGA HANNU A MAƘABARTA YAYIN ADDU'A GA MATATTU*DAGA HANNU A MAKABARTA YAYIN ADDU'A GA MATATTU ! ! !*

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Tanbaya malam.Malam meye hukuncin mutun in yamutu in an kaishi makabarta wasu suke daga hannu suna addua sai su shafa su tafi, nama wani malami tambaya ya ce ba daidai ba ne, ni kuma tunanina daga hunnun ayi addua shine mafi rinjaye, malam menene gaskiya ? 

*AMSA*👇

Wa alaikum assalam To dan'uwa ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta : 974 cewa : Annabi s.a.w. ya ziyarci makabartar Baki'a ya kuma daga hannu har sau uku yayin addu'a ga mamatanta" 
Hadisin da ya gabata yana nuna mustabbancin daga hannu yayin addu'a ga mamaci a makabarta.
Nawawy yana cewa Akwai hadisai da yawa wadanda suka zo akan daga hannu yayin addu'a, don haka duk wanda ya iyakance wuraren da Annabi s.a.w. ya daga hannaye, ya yi mummunan kuskure" Almajmu'u 3\489.
Saidai malamai suna cewa : yin addu'ar jama'a da murya daya a makabarta na daga cikin bidi'o'in da ba su da asali.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Share:

ZAKKAR MAI BASHI*ZAKKAR MAI BASHI:* 

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

 _As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah_ .

Manomin da 2/3 na kuɗin nomansa bashi ne ya ciwo, wai yaushe zai cire zakkah: Kafin ko bayan ya biya bashin ne?

 *AMSA*👇

 _Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .

(1) Al-Imaam Al-Baihaqiy ya ruwaito (7857) da irin isnadin Al-Bukhaariy (#7337) daga Sahabi As-Saa’ib Bn Yazeed _(Radiyal Laahu Anhu)_ cewa: Shi ya ji Uthmaan Bn Affaan _(Radiyal Laahu Anhu)_ yana huɗuba a kan mimbarin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ yana cewa: Wannan watan fitar da zakkarku ne. Sannan kuma ya ce:

فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ عَلَيْهِ دَيْنٌ فَلْيَقْضِ دِينَهُ ، حَتَّى تَخْلُصَ أَمْوَالَكُمْ ، فَتَؤَدُّوا مِنْهَا الزَّكَاةَ
Don haka, duk wanda akwai bashi a kansa to ya biya bashinsa, har sai dukiyoyinku su kuɓuta, to sai ku cire zakkar daga cikinsu.

Wannan ya nuna: A wurin Khalifah Uthmaan Bn Affaan da waɗanda suke tare da shi daga cikin Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ da Tabi’ai _(Rahimahumul Laah):_ Sai a bayan an cire bashi ne sannan ake cire zakkah.

(2) Sannan kuma Al-Imaam Al-Baihaqiy ya sake riwaitowa (7858) da ingantaccen isnadi daga Jaabir Bn Zaidin, daga Ibn Abbaas da Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhum)_ game da mutumin da ya ciwo bashi kuma ya kashe shi duk a kan gyara ’ya’yan itacen gonarsa da kuma iyalin gidansa. Shi ne Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya ce:

يَبْدَأُ بِمَا اسْتَقْرَضَ فَيَقْضِيهِ وَيُزَكِّى مَا بَقِىَ 
Sai ya fara da bashin da ya ciwo ya biya shi, sannan ya fitar da zakkar abin da ya rage.

Watau dukkan bashin da ya kashe a kan gonar da iyalinsa.

Shi kuma Ibn Abbaas _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ cewa ya yi:

يَقْضِى مَا أَنْفَقَ عَلَى الثَّمَرَةِ ، ثُمَّ يُزَكِّى مَا بَقِىَ
Sai ya biya bashin da ya kashe a kan gonar, sannan ya fitar da zakkar sauran da ya ragu.

Watau ban da ɓangaren bashin da ya kashe a kan iyalinsa.

Amma idan ya kashe dukkan bashin a kan gonar ce har ma ya ƙaro kamar sulusi (1/3) daga aljihunsa, kamar yadda ya zo a cikin wannan tambayar, sai amsar ta zama:

Daga buhuna ɗari biyar (500) ko ɗari bakwai (700) da ya samu a gonar sai ya fara da ware adadin buhunan da farashinsu ya yi daidai da yawan bashin da ke kansa, sauran buhunan kuma sai ya raba su gida goma ya bayar da kashi ɗaya (1/10), idan da ruwan damina ne aka shayar masa da gonar. Ko kuma kashi ɗaya cikin ashirin (1/20), idan da ban-ruwa ne ya shayar da ita.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

 _Wal Laahu A’lam._ 

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Share:

Total Pageviews

Translate

Featured post

DARUSSAN RAYUWA EPISODE 08

Darussan Rayuwa Episode 08 kenan, ku buɗe ku sha kallo lafiya. Ku shiga wannan link domin samun sauran bidiyoyin mu  https://youtube.com/cha...

Contact form