Barka da zuwa Bankin Bayanai

AZUMIN WATAN RAMADAN 01*🌙AZUMIN WATAN RAMADAN 01🌙*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
*مجلس السنة*
📓📔
+2349032091131
+2348142100514
.
.
.
Yau 21/ 08/ 1439 wanda yayi dai-dai da 15/ 04/ 2018 muka fara wannan lekcar mai taken *AZUMIN WATAN RAMADAN*
=
=
*GABATARWA:*
=
*ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪَ ﻟِﻠَّﻪِ، ﻧَﺤْﻤَﺪُﻩُ ﻭَﻧَﺴْﺘَﻌِﻴﻨُﻪُ، ﻣَﻦْ ﻳَﻬْﺪِﻩِ ﺍﻟﻠﻪُ ﻓَﻠَﺎ ﻣُﻀِﻞَّ ﻟَﻪُ، ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﻀْﻠِﻞْ ﻓَﻠَﺎ ﻫَﺎﺩِﻱَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﺷْﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْﺪَﻩُ ﻟَﺎ ﺷَﺮِﻳﻚَ ﻟَﻪُ، ﻭَﺃَﻥَّ ﻣُﺤَﻤَّﺪًﺍ ﻋَﺒْﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟُﻪُ*
_Godiya ta tabbata ga Allah; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai 6atar da shi, wanda Ya 6atar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu wanda a ke bauta wa bisa cancanta sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa._
_Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa, akan haqqin binSa da taqawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa._
_Ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taqawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata. Kuma ku bi Allah da taqawa, Wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne._
_Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa, kuma ku fadi magana madaidaiciya. Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta zunubanku. Kuma wanda ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, tho, lalle, ya rabanta, babban rabo mai girma._
_Bayan haka: Yan uwana na wannan zauren mai albarka. Lallai mafi kyawun magana, (shi ne) littafin Allah, kuma mafi kyawun shiriya (ita ce) shiriyar Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Kuma mafi munin al'amura (su ne) abubuwan da aka qago (a cikin addini). Domin dukkan qagaggun abubuwa (wadanda ba su da asali a cikin Alqur'ani da Sunnah) bidi'a ce, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata (makomarta) cikin wuta._
_Bayan nan Kuma Jama'a. Azumin Ramadān na daya daga cikin rukunan Musulunci, kuma yana dauke da alhairai da martabobi da falala da darajoji masu yawan gaske. Wajibi ne a kan kowane Musulmi ya yi qoqarin sanin hukunce–hukuncensa, kasancewa jahiltar haka na iya haifar masa da matsala a cikin azuminsa. Da ya ke azumi ibada ce da Allah ya yi umurni da yi, Musulmi na buqatar sanin yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi azumi a lokacin da ya ke raye. Ta haka ne zai san abubuwan da ke gyara azumi ko su bata shi, ya san abubuwan da suka halasta ga mai azumi da wadanda ba su halasta ba, da dai sauransu._
_Tho Jama'a ganin yadda mutane ke nuna tsananin kwadayin sanin yadda za su yi azumi akan karantarwar Alqur’ani da ingantattun Hadisai bisa fahimtar magabata na qwarai, don su san falala da darajojin azumin, da abubuwan da ke bata shi da wadanda ba su bata shi, da nau’o’in ibada da ake son a yi a lokacin azumi, da hanyoyin da za a bi don ganin an dace da alhairan da ke cikinsa, naga ya dace inyi wannan dan takaitaccen lekca a matsayin tunatarwa gare ni da sauran yan’uwa Musulmi. Na taqaita bayanan da ke cikin lekcan nan ta yadda mai karatu zai yi amfani da su a matsayin jagora gare shi cikin azumi. Na sanya wa wannan lekcar sunar *AZUMIN WATAN RAMADAN*. Ina ba mai karatu shawarar bin hashiyar lekcar a lokacin da ya ke karantawa, kasancewar zata taimaka masa wajen kyautata fahimtar saqon da ke ciki._
_Ina roqon Allah Mai girma da daukaka ya karbi wannan dan aiki a matsayin ibada, Ya ba ni ladan da Ya tanadar wa wadanda ke qoqarin karatu da karantar da addininSa, kuma Ya yi sakamakon alhairi ga wadanda suka taimaka, ta kowace hanya a wajen tabbatar da lekcar ko Ina a social media. Ina roqon Allah Ya yafe mani kurakuran da ke ciki. Haka kuma, ina roqon wadanda suka ga kuskure acikin wannan lekcar, su fadakar da ni Domin a gyara._
=
=
Zamu dakata anan sai bayani na gaba Inshaa Allahu.
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
Mai yadawa
°
*_Bilyaminu Taheer Musa (Cameroon)_*
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Share:

No comments:

Post a comment

Total Pageviews

Translate

Featured post

DARUSSAN RAYUWA EPISODE 08

Darussan Rayuwa Episode 08 kenan, ku buɗe ku sha kallo lafiya. Ku shiga wannan link domin samun sauran bidiyoyin mu  https://youtube.com/cha...

Contact form