Barka da zuwa Bankin Bayanai

YA YI ZINA DA MATAR AURE

*YAYI ZINA DA MATAR AURE* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Malam _Don Allah a sakaya sunana_ 
 _Malam don Allah ayi kokari duk abinda na fada a wallafa shi a wannan zauren mai albarka don ya zama darasi garemu baki daya._ 

 _Ni dai ma'aikacine kuma yanzu haka ina wata jiha don aiki kamar yadda daga lokaci zuwa lokaci aiki yakan kaini. Zuwata wannan jihar sai na hadu da wani abokina har ya zamanto banda wurin fira sai wurinshi._ 

 _A nan wata rana na hadu da wata yarinya inda daga karshe dai na karbi lambar wayarta. Hira tsakanina da yarinyar nan ya wuce na tsakani da Allah daga karshe har sai da muka yi zina (Astagrirullah wa atubu ilaihi)._ 

 _Kafin wannan mummunan abin ya faru, abinda na iya sani a game da yarinyar daga wurin abokina shine; ta taba aure amma mijin ya gudu ya barta ba a san inda yake ba, kusan shekara daya kenan amma yanzu kotu ta raba auren wand ita ko da wasa bata taba fada min hakan ba. Sai dai cewa tayi tana da saurayi amma ya yaudareta ya gudu ya barta._ 

 _Mun ci gaba da abinda dani da ita muka kira soyaiya duk da cewa wallahi har cikin zuciyata ni na san bana sonta sai dai ban san abinda ke cikin nata zuciyar ba._ 

 _Kada dai in tsawaita wannan labarin, daga karshe dai ranar wannan sallan babba sai ita da kawarta suka kawo mini abinci sai naji a zuciyata kuma yanzu babu wanda hankalina ya karkata wurinta sai kawar. A dai dai wannan lokacine ita yarinyar take cemin zata yi tafiya zuwa wani wuri amma ba zata dawo ba sai bayan wata daya._ 

 _Bayan ta tafi sai na koma kiran ita kawar a waya wanda daga baya na samu hadin kanta da sunan soyaiya. Cikin irin firar da mukeyi ne, ita kuma don ta samu gindin zama sosai a zuciyata ta fada min abinda shine dalilin tashin hankalin da bana taba shiga ba. Watau abinda ta fada min shine. Ko na san cewa wannan yarinyar tana da aure? Nace wallahi ban sani ba. Kuma hakane wallahi ban sani din ba. Abinda na sani shine an kashe aurenta da mijinta da ba a san inda yake ba._ 

 _Tafiyar nan da take cewa tayi zatayi wata daya a wurin ashe gidan mijinta ta koma. Kuma duk da cewa ta koma gidan mijin tana kirana kuma muna waya har da maganganu na batsa. Amma ban san cewa a gidan mijin take ba._ 

 _Allah ya gafarta malam. A daidai wannan lokacine nake baran addu'a a wurin yan uwa, ubangiji Allah ya yafemin wannan abinda na aikata. Lallai wannan ya zama dalilin tuba a gareni. Kuma ina mai tuba zuwa ga Allah. Ina son wannan abin ya zamo darasi ga kowa. Maza da mata, muji tsoron Allah._ 

 _Shin ko Allah zai karbi tubata? Sannan kuma malam wadanne irin addu'o'I ya kamata in rika karanta wa don tuba da neman yardar Allah. Ina cikin tashin hankali wanda ban taba shiga cikinsa ba a rayuwata._ 

 __Allah kadai yasan halin da nake ciki har a yanzu da nake wannan rubutun._ 

 *AMSA* 👇

 _Tabbas kayi katobara, ka zalunci kanka. Ka aiwatar da Babban Kaba'ira._ 

 _Amma babban abinda ya bani haushi kuma ya bani mamaki acikin wannan dogon labarin naka shine:_ 
 _Wato kai ba wai kana yin nadamar aikata Zina bane. A'A. Kai kana yin nadama ne kawai saboda ance maka matar aure ce!!!_ 

 _Agaskia dunia ta rudeka. Kuma shaitan ya riga ya rinjayeka. Ka zama nasa._ 

 _Kuma tabbas mazinata suna haduwa da Qaskanci da wulakanci da Qaskanci da talauci tun daga nan dunia kafin aje lahira._ 

 _Don haka ka tuba izuwa ga Allah. ka kaurace ma zinan da kakeyi. Kuma ka dena duk wata hulda tare da abokananka wadanda kuke yin zinar nan tare.._ 

 _Ka yawaita istighfari da aiyukan alkhairi wadanda Allah yake kankare Zunuban bayinsa dominsu. (Kamarsu azumin nafila, tasbihi da salatin Annabi saww.)_ 

 _Sannan kaje ka nemi gafarar mijinta domin shiga hakkinsa da kayi. Idan kuma neman yafewarsa zata janyo maka tozarta da kuma tashin hankali, to sai kaci gaba da yi masa addu'a. Kana nema masa gafara awajen Allah._ 

WALLAHU A'ALAM

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Share:

No comments:

Post a comment

Total Pageviews

Translate

Featured post

DARUSSAN RAYUWA EPISODE 08

Darussan Rayuwa Episode 08 kenan, ku buɗe ku sha kallo lafiya. Ku shiga wannan link domin samun sauran bidiyoyin mu  https://youtube.com/cha...

Contact form